A yau za mu koyi yadda ake fondant.
Abubuwan Da Ake Buƙata:
- Icing sugar
- 1 tbsp Corn syrup
- 1 tbsp Glucose
- 2 tbsp Gelatine
- 1 tbsp Glycerine
- ruwa 4 zuwa 5 tbsp
- 1 tbsp Cmc
- Corn flour
- 1 tbsp Flavour
- gishiri
- 1 tbsp Butter
Yadda Ake Haɗawa
- A sami kwano ɗan ƙarami, sai a zuba gelatine kamar cokali biyu, a sa ruwa kamar cokali 4 haka a juya.
- Sai a juya shi, amma zai iya ɗan burtsatsai bai yi smooth ba.
- A zuba ruwa a tukunya, a ɗora a kan wuta, amma ruwan ba mai yawa ba, yadda idan an sa kwanon da aka zuba gelatine ɗin ba zai sha kansa ba.
- Sai a sa glucose a juya sosai, sanna sai a sauke, sai a zuba flavour, corn syrup, glycerine a juya sanna a ɗan sa gishiri da butter.
- Sai a ringa juyawa ana ƙarawa, ana juyawa kamar ana kwaɓin dough, a haka za a ga yana ƙwari har sai an ga ya daina kama hannu.
- Sanna idan ana yi a tabbatar ana yin shi a kan leda ko irin waje me kyau da tsafta kuma idan ana murzawa kada a yi da yatsu, tafin hannu za a yi amfani da leda mai yatsu.
- Idan yana kamawa za a iya barbaɗa corn flour a ƙasan wajen ko icing sugar.
- Za a ga idan ya yi sosai, zai daina kama hannu, zai zama dough sosai, sai a sami Leda a sa a ciki, yadda iska ba za ta shiga ba, ya daskare.
- Sai a yi kwalliyar da ake so idan wani kala ake so, za a iya sawa a murza shi.
Domin sanin Yadda Ake Pizza danna koren ruutun nan.