KAYAN HAƊI
- Karfatar rago
- Ruwan Kal (vineger)
- Habbatus sauda
- Kayan ƙamshi
- Tafarnuwa
- Sinadarin ɗanɗano
- Albasa
- Tumatir
Yadda Za A Haɗa
A sami karfatar rago da ƙashinta a jikinta, a riƙa tsattsaga ta, sai a shasshafa mata vineger ko lemon tsami a daka habbatus sauda kaɗan da masoro da garlic da maggi da mai a cakuɗa, a shafe naman dashi.
Sai a ɗora a kan a farantin gashi da ruwa kaɗan, idan ya fara dahuwa sai a yanka albasa amma slicing ɗinta za a yi, sai a ɗora a kan naman, sai a yanka tumatir shima irin yadda kika yi ma albasar, sai a mayar cikin oven ya ɗan ƙara gasuwa. Idan ya dahu a kashe a fito da shi.