Yadda Ake Chips Da Sauce Na Ƙundun kaza

0
2203
Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, A yau za mu koyi yadda ake chips da sauce na ƙundun kaza. Tare da ni Hafsat Shettimah.

chips na ƙundun kaza na mutune 2-3

Abubuwan haɗawa:
 • Dankalin Turawa (peeled and sliced)
 • Black pepper (masoro) pinch -optional
 • Gizzard (kundun kaza) ½ kg
 • Karas manya 2 (sliced)
 • Yankakken Koran Tattasai babba 1
 • Man gyaɗa
 • Albasa jajjagaggiya babba 1
 • Attaruhu 5 medium (to taste)
 • Maggi (3)
 • Garlic tafarnuwa medium Bari 1
 • Curry ½ chokali (teaspoon)
 • Thyme ½ (teaspoon)

Yadda ake haɗawa

 1. Ki ɗora kaskonki a wuta, ki sa manki ya yi zafi, sai ki ɗauko dankali kisa ɗan gishiri da black pepper ki juya ki sa a man. Kar ki yawaita juya shi zai fashe.

Idan ya yi, sai ki tsame a matsami. Yayin da man jikin dankalin ya ɗige, sai ki sa a kwano mai kyau, ki ajiye a gefe.

 1. A tabbatar ƙundun kazar ya wanku da kyau, sai a saka cikin tukunya a zuba maggi guda biyu, curry, thyme, tafarnuwa da rabin albasa a bar ruwan jikin ƙundun ya dafa shi.
 2. A cikin tukunya mai zurfi za a zuba mai chokali 3-4 a saka tafarnuwa da albasa idan ya soyu, sai a zuba ƙundun kaza shi ma, a soya shi, sai ya yi golden brown, sannan sai a ɗauko attaruhu da maggi 1 da karas, da romon ƙundu (in ƙwai) in kuma babu sai a zuba ruwa ¾ kofi a bar shi na minti 2, sai a zuba Koran Tattasai a sauke.
Domin koyan Yadda ake onion sauce dannan koren rubutun nan
labarin da ya wuceMene Ne Hawan Jini (HYPER TENSION)
Labarin na GabaYadda Ake Chocolate Cake Na Musamman