Yadda Ake Faten Shinkafa

0
570
 • Kaza ko Nama
 • Shinkafa
 • Kayan ƙamshi
 • Mai ɗanɗano
 • Tafarnuwa
 • Citta
 • Albasa
 • Cinammon
 • Persley
 • kayan miya
 • Koren tattasai

Yadda ake haɗawa

 1. Za a sami nama ko kifi, idan nama ne yana buƙatar a dafa shi kamar awa ɗaya, yadda zai yi laushi sosai
 2. Idan kifi ne za a wanke a sa masa sinadarai da kayan ɗanɗano, sai a saka shi  a tukunya, a ba shi wuta kaɗan, don su shiga jikinsa, amman kar a sa ruwa.
 3. Sai a zuba markaɗaɗɗen kayan miya, amma ba da yawa ba
 4. A kawo ɗan mai kaɗan, shi ma a zuba, a soya sama-sama, kar ya soyu sosai
 5. Sannan a kawo ruwa da ɗan dama a zuba da sinadaran ƙamshi, amma ba masu yawa ba.
 6. A wanke shinkafa a zuba, idan ya tafasa a zuba nama da ruwan naman, ana son akalla shinkafar ta yi awa ɗaya, dalon ta samu ta farfashe tunda romonta ake so. idan an ga ta yi kauri, sai a kawo kayan ɗanɗano da cinnamon a zuba a rage wuta, idan kuma da kifi ake yi to sai a zuba.
 7. Sannan a yanka koren tattasai da parsley da albasa a zuba a bar shi yayi  kamar minti 2 sai ki sauke.

Domin sanin yadda ake pancake  danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Pancake
Labarin na GabaYadda Ake Faten Shinkafa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.