Yadda Ɗabi’un Maza Suke

0
1188

Maza sun kasu kashi-kashi. Ya zama abu mai muhimmanci mu yi nazarin yadda ɗabi’unsu yake. Saboda haka zai ba mu fahimtar juna da zama lafiya.

Misali akwai:

Mai haƙuri
Mai tsabta/ƙazami
Mai kyauta/rowa.
Mai yawan surutu/zurfin ciki.
Mai saurin fushi amma yai afuwa.
Mai banbami da mita .

Mata sai mun fahimci cewa: Akwai wasu halaye da ɗabi’un miji halittace da Allah ba zai canja shi ba. Ya zama jarrabawa a gare ki. Sai ki dinga duba yardar Allah kike nema da kuma  dacewa, sai ki yi hakuri domin kuwa kowa da ƙaddararsa.

Domin ƙoƙarin canja wanda ba zai taba canjawa ba, ya zama kusan kamar taɓin hankali.

Sai dai ki guji yawan mita da ƙorafi a kan waɗannan halaye. Da nisantar duk abin da zai ɓata masa rai, da aikata abin da ya fi so, a mafi yawan lokuta. Sai hakan yasa ya tausaya ya rage wani halin, ya ringa ƙoƙarin kyautata miki.

Wani kuma a hankali cikin hikima da juriya na tsawon lokaci sai ki ga ya canja.

NAMIJI NA DA BUƘATAR WAƊANNAN ABUBUWA

YARDA: Duk sanda miji ke ƙoƙarin wani aiki, to fa yana buƙatar goya masa baya.

GODIYA: Shi miji yana da buƙatar godiya a dukkan ɗawainiyar da ya yi. Ko da ruwa ya shigo da shi. Hakan yana saka shi himma da ci gaba da hidima.

YABO: Duk Lokacin da ya girmama ki. Ko ya girmama miki iyayenki, da ‘yan uwa. To fa lallai yana bukatar yabo.

BURGEWA: Miji zai so ya ga yana burge matarsa. Sai ki koyi zuga shi da koɗa shi.

BA YA KARƁAR CANJI: Idan abu kore ne sai mijinki ya ce fari ne. To fa ba zai yarda ya ce farin ba ne. Shi Miji ya fi son mace ta karɓi abu a yadda shi ya ce kawai.

Idan ya buƙaci saduwa, kika ce tsaya in yi wanka ko wanke baki. Sai ya ji kawai ta fita a ransa. A sanda ya buƙata, a wannan lokacin kawai a biya masa bukatarsa.

Sai dai ki dinga zama da wanka, da wanke baki a kodayaushe.

Domin karanta yadda ake maraba da maigida ko yadda ake da maigida lokacin al’ada

A karshe Wadannan kadan da ga abubuwa da yakamata ki fahimta a irin bukatar Namiji .
Allah ne mafi Sani.

labarin da ya wuceYadda Ake Yogurt
Labarin na GabaAmfanin Zaitun A Jikin Ɗan Adam.
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.