Wasu Daga Fitattun Malamai A Ƙasar Sakkwato Da Kewayen Ta

0
40

Karatun Alƙur’ani a Sakkwato da kewayenta wanda ya haɗa da Gwandu da Gobir da Zamfara da Kebbi, ya sha bam-ban da karatun Alƙur’ani a masarautun Kanem-Barno.

Haka kuma ya sha bam-ban da karatu a masarautun Kano da kewayenta wanda ya ƙunshi Haɗeja da Zazzau da sauransu don haka, magana a kan yanayin malaman Alƙur’ani a waɗannan larduna sun sha bam-ban.

Makarantun Alƙur’ani a Barno da Kano da kewayen su sun fi ƙwarewa wajen haddace Alƙur’ani da naƙaltar logoginsa da shahara wajen rubuta shi da ka. Wannan ya sa ba sa kutsawa sauran fannonin ilmin Furu’a. A lardin Sakkwato da kewayen ta kuwa, koyo da koyar da Alƙur’ani ya fi ɗaukar salon ƙasashen Sudan da Mali da Mauritaniya, a inda ake haɗa Alƙur’ani da ilmi a cikin tsangaya.

Kodayake yanayin karatun iri ɗaya ne da sauran sassan Arewacin Najeriya ta fuskar karatu da alluna da darasu, amma fa da almajiri ya yi saukar fari, to sai ya fara sauran fannonin Fiƙhu da Lugga da Hadisi da sauransu. Wannan yakan jawo taƙaituwar shagaltuwar makarantu wajen haddace Alƙur’ani. Don haka ma abu ne mai wuya zaƙulo tsantsar mahaddacin Alƙur’ani, ballantana wanda ke rubuta shi da ka a Sakkwato.

A taƙaice dai kusan kowace makaranta Alƙur’ani a Sakkwato da kewaye za ka samu makaranta ce ko zaure ne na ilmi. Haka kuma duk wata cibiya ta ilmi, to akwai karatun Alƙur’ani a cikinta. Bugu da ƙari, babu cunkoson makaranta a wannan lardin kamar yadda abin ya ke a gabas kamar Maiduguri da Gaidam da Konduga da Potiskum da Paki da Haɗeja da makamantansu a yankin Kano da kewaye.

Masarautar Sakkwato ta kafu daga baya-bayan nan in an danganta ta da Gobir da Zamfara da Kebbi.

Shi kuwa rubutaccen tarihin yaɗuwar Addinin Musulunci a wannan yanki ya fi dangantuwa da ayyukan Shehu Usman da almajiransa. Tare da haka, tarihi ba zai manta da gudunmawar waɗanda suka fara kawo Musulunci wannan yanki ba, musamman ma ‘yan kasuwa Larabawa da gun-gun masanan nan da aka fi sani da “Malaman ‘Yan Doto”.

Domin kuwa a wannan lokaci Gobir na daga cikin ƙasashen Hausa da suka fara karɓar baƙuncin malamai masana daga yammacin Sudan. Irin waɗannan malamai sun bar Malle tun cikin shekara ta 835AH (1431CE) a inda suka sauka a Gobir da Katsina; kafin ma su isa Kano.

An ce Muhammad Korau (1445-1494), wan da ya kifar da sarautar Sarkin Katsina Kumayau; ne ya zama Sarkin Musulmi na farko a Katsina. Yana ɗaya daga irin wancan gungu na “Malaman ‘Yan Doto”; waɗanda suka yaɗa koyar da ilmin Alƙur’ani a lardin Sakkwato tun kafin bayyanar Shehu Usmanu.

Karatun aIƙur’ani da ilmi ya samu wata irin bunƙasa da yaɗuwa a wannan lardi a lokacin da Shehu Usmanu ya bayyana. Almajirai da masana kowa na baje kolinsa don cin kasuwar ilimin gwarazan masana irin su; shi kansa Mujaddadi da ɗan uwansa Abdullahi da ‘ya’yansa irin su Muhammadu Bello da Nana Asma’u da almajiransu irin su; Abdullahi Alkanawi da wasu malamai irin su Wazirin Sakkwato Junaidu da Yahaya Alnawawi (alƙalin lardi) da Alƙali Abubakar Ladan Rame da sauran su. Don haka za mu nazarci rayuwar wasu daga irin malaman Alƙur’ani da na ilmi a wannan lardin; musamman ma daga ƙarni na ashirin.

Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu)

An haifi Malam Attahiru a farko-farkon sarautar Sarkin Musulmi Abubakar na Uku. Malam Attahiru ya taso cikin tarbiyyar addini wurin mahaifinsa. Kasancewar gidansu gida ne na ilmi da yaɗa shi; ya sa shi gadar wannan sana’a ta koyar da Alƙur’ani da ilmi.

Duk da cewa a halin yanzu Malam Attahiru shi ne Limamin Masallacin Shehu da ke Sakkwato; duk da haka makarantarsa ba ta gushe ba ta na yaɗa addini a cikin garin Sakkwato tare da taimakon ‘yan’uwansa; musamman ma Malam Abubukar da Malam Ibrahim da Malam AbdurRahman da Malam Ahmad Zaruƙu.

Malam Attahiru Na Liman tsatson AIƙali Abubakar Ladan Rame ne, wanda ɗan Gwaggon Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ne. Wannan zuriya mai albarka ta cigaba da jiɓintar koyar da addini da alƙalanci har zuwa kan Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu da ke Sakkwato na yanzu).

Malam Buhari Siriddawa (Sarkin Malaman Sakkwato)

An haifi Malam Buhari, Sarkin Malaman Sakkwato a Unguwar Siriddawa da ke Sakkwato a shekara ta 1934. Ya yi karatu wurin mahaifinsa Malam lbrahim da Malam Na Ta’ala Gidan Kanawa Sakkwato; da Malam Mujeli Garge da Malam Shehu NaLiman (Limamin Masallacin Shehu).

A halin yanzu tsangayarsa cike ta ke da almajirai da makaranta sama da ɗari biyar; baya ga ɗumbin masu karatun littatafai kowace rana a wurinsa. Babbar baiwar Malam Buhari ita ce ƙwarewar da Ubangiji Maɗaukaki Ya ba shi a fagen ilmin Fiƙhu. A yanzu shi ne yake riƙe da ragamar jagorancin malaman Sakkwato a fadar Sarkin Musulmi. Makarantarsa na gudana ne tare da taimakon ɗansa Malam Sambo da wasu daga almajiransa.

Malam Muhammadu Na Ta ‘ala

Malam Muhammadu Na Ta’ala ɗaya ne daga zuriyar Sheikh Abdullahi Alkanawi, almajirin Shehu Usman kuma jakadansa. Asalinsa mutumin Kano ne daga jinsin Gyanawa. Ya koma Sakkwato a lokacin da ya samu labarin bayyanar Shehu. Daga nan kuma ya cigaba da taimaka masa a Sifawa. Bayan an dawo Sakkwato, Shehu ya ba shi fili inda ya gina gidansa da makarantarsa; wadda aka fi sani da Gidan Kanawa.

Bayan rasuwarsa sai ɗansa Halliru ya zama halifansa Daga nan kuma sai ɗansa Umar; shi ma kuma ɗansa Ibrahim Dasuki ya gaje shi. Bayansa ne sai ɗan’uwansa Muhammad Na Ta’ala ya zama halifa.

Wannan makaranta ba ta gushe ba ƙarƙashin ‘ya’yansa su Alhaji Bashir Muhammad Na Ta’ala; da ɗan’uwansa Malam Ahmad Zaruƙu, inda suke cigaba da ilmantarwa da wa’azi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Za Ki Yi Funkaso
Labarin na GabaZubar Da Miyau Ga Mai Juna Biyu