Akwai hanyoyi da yawa da shugabanni da ma’aikata suke bi wajen ɓarnatar da dukiyoyin al’umma kuma sai Allah ya hukunta su akansu domin nau’i ne na cin amana da rusa tattalin arziƙin ƙasa.
Kaɗan daga cikin waɗannan hanyoyi su ne;
1) Fantamawa da wadaƙar da shugabanni da manyan ma’aikata suke yi da su da iyalansu da abokansu da surukansu da barorinsu da dukiyar al’umma musamman a lokacin bukukuwansu.
2) Antaya dukiya ga wanda aka ga dama haka kawai saboda anga dama ya zama miloniya ya yi nashe-nashe yana muwalat ya zama kamar wani sabon mutum.
A can gefe kuma ga talakawa suna ta kuka wasu ma suna mutuwa an hana su ɗan abinda za su sayi abinci da magani.
Domin karanta bayani akan Mutuwa Da Rabon Gadon Bahaushe Danna nan
3) Tara dukiyar ƙasa da taskance ta da hana talakawa da sauran mabuƙata sai dai a yi ta cewa tattalin arziƙin ƙasa ya haɓaka, asusun gwamnati ya cika maƙil da kuɗi, amma babu wani talaka da zai gani a ƙwaryar tuwonsa sai dai a yi ta surutu maras kan gado. Wanda in ba su masu faɗar ba, babu mai fahimtar abinda suke faɗa.
4) Yin amfani da dukiyar al’umma akan buƙatun ƙashin kai, kamar motoci, injina, kayan aiki da kuɗin al’umma a gonakinsu, ko ma’aikatunsu ko gidajensu da sauransu.
5) Fifita manya da masu hannu da shuni akan waɗanda ba su da komai ko ba su san kowa ba, ta hanyar rage, ko yafe musu haraji ko kuɗin fito ko ɗaukar su ko ‘ya’yansu ko matansu aiki, ko ba su bashi don su juya wataƙila ma a ce an yafe musu.
6) Kashewa mawaƙa da makaɗa kuɗaɗe masu yawa don kawai neman suna, alhali ga malaman makaranta da likitoci da sauran talakawa suna fama da ƙarancin albashi wanda ya jawo taɓarɓarewar aikin gwamnati da rashin zaman lafiya a ƙasa, sai ka ga a lokaci guda wani mawaƙi ko ɗan bal ko wata ‘yar fim suna zama miloniyoyi a sama.
7) Kashe kuɗaɗe masu nauyin gaske akan harkokin zaɓe waɗanda da za a tsakuro ɗaya bisa ukunsu a sa a ɓangaren ilimi ko noma ko lafiya ko tsaro da anga canji a rayuwar al’umma. Amma ina sai ayi watsi-watsi da waɗannan kuɗaɗe masu ciwon gaske a yi abinda aka ga dama a ce an zaɓe wane ya ci wane ya faɗi.
8) Kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tarbar shugabanni na gida da na wajen domin ƙawata tituna, tara musu talakawa, shirya abinci da sauran abubuwa na ganin ido sai ka ga a yini ɗaya an kashe miliyoyin nairori na fitar hankali saboda wai shugaba wane zai kawo ziyara ƙasa ko jiha.
9) Ware wa harkokin wasannin kuɗaɗe masu ɗimbin yawa fiye da kuɗin da aka warewa ma’aikatar lafiya, tsaro, ilimi da sauransu waɗanda suka fi wasanni muhimmanci, amma dai haka suke rufe idanunsu su toshe kunnuwansu su narka kuɗi a can ba ruwan su.
10) Caɓawa masallatai ado wani lakacin da gwalagwalai amma a yi burus da limamai da ladanai da ma su kansu masallatan masu sallah a wasu masallatan sai ka ga adon yana shagalar da masu sallah maimakon su tara hankalinsu ga sallarsu, sai su yi ta kallon ƙyale-ƙyalen da aka yi.
Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan
A wasu ƙasashen kuma sai a gina masallaci gari guda amma kuma babu masu sallar, sai dai ‘yan yawon buɗe idanu ne za su rinƙa zuwa suna ɗaukar hotuna a cikinsa.
Kamar yadda a waɗansu ƙasashen ake ƙawata ƙaburburan shaihunai a kashe miliyoyin daloli domin kawai a samu goyon bayan mabiyan wannan mamacin (shehin).
11) Rashin kula da aiki ta hanyar zuwa a makare da tashi kafin lokacin ya yi, da ma ƙin yin aikin ai an je wurin aikin sai a ɓuge da hira ko karance-karancen jaridu ko matse-matsen waya da kallon talabijin, ka ga kuɗin da ake kashewa kan waɗannan ayyukan da ma’aikatan kusan duk asarar su ake yi.
12) Kashe dukiyar al’umma kan bukukuwa na ƙasa ko na siyasa ko bukukuwan da ake danganta su ga addini kamar bikin ranar samun ‘yancin kai, Bikin ranar demokuraɗiyya, bukukuwan mauludin Annabi da na shaihunai, sai ka ga an fitar da miliyoyin kuɗi an yi watandar su, alhali ga lalurorin rayuwa babu cikakkiyar kulawa.
13) Biyawa ‘yan siyasa da ‘yan jagaliya aikin hajji ba don komai ba sai don kawai sun yi wa shugaba yaƙin neman zaɓe sai ya saka musu da kujerun hajji, waɗansu ma in sun je hajijiya kawai za su yi su dawo.
Amma malamai masu koyar da alhazai aikin hajji da likitoci da sauran maa’aikatan da za su taimakawa alhazai su yi ibada cikin nutsuwa da inganci waɗannan babu wani laifi don gwamnati ta biya musu aikin hajji amma a ji tsoron Allah a yi gaskiya da adalci a dubi cancanta wajen zaɓar waɗanda za a biyawa.
14) Ha’inci wajen ba da kwangila ta hanyar kashe-mu-raba tsakanin ‘yan kwangila da jami’an gwamnati, sai a zaftare kuɗin ko dai a ƙi yin aikin sam ko kuma a yi shi mara inganci ta yadda da an kwana biyu zai tashi daga aiki, in titi ne sai ya ɓaɓɓagure in gini ne ya rushe in wasu injina ne su lalace. Subhanallah.
15) Wawashe kuɗaɗen al’umma a je a damfare su a bankunan ƙasashen turai, su yi ta gina kansu da su, ‘yan ƙasa kuma suna ta mutuwa. Waɗansu ma sai su je can su kafa masana’antu alhali ga miliyoyin ‘yan ƙasa ba su da aikin yi.
Domin karanta bayani akan Jinya Da Likitancin Bahaushe Danna nan
16) Tarukan siyasa musamman na neman zaɓe da karɓar waɗanda suka baro jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar gwamnati, in ka ji yawan kuɗin da ake kashewa a irin wannan harkar abin akwai matuƙar takaici da ɗaure kai.
17) Ware kuɗi mai yawan gaske da sunan wai za a yi addu’ar neman zaman lafiya ga ƙasa, ko kuma samun nasara a zaɓe. Sai dai abin takaicin shi ne mafi yawancin wannan kuɗi masu addu’ar ta gaske saboda Allah ko labarinsu ba su ji ballantana su gan su. Sai a yi ta dumbuza ana baiwa bokaye da miyagun malamai da matsafa da waɗanda ma ba musulmi ba.
In ya zama dole sai an fitar da wannan kuɗi kamata ya yi a bi talakawa da gajiyayyu da malaman zaure da na tsangayu da ɗalibansu a ba su abinda zai faranta musu rayuka su ma su sami sa’ida da walwala to ko ba su yi addu’a ba, Allah zai biya buƙata sakamakon faranta musu da aka yi.
A gaskiya hanyoyi da waɗansu shuwagabanni suke bi wajen tarwatsa da ɓarna da dukiyar al’umma suna da yawan gaske, abin fa ya zama sai dai a ce innalillahi wa inna ilaihirraji’un.
Ya Allah ka ba mu ikon gyaran halayen mu, ka yi mana afuwa da gafara ka azurta mu da shugabanni managarta masu ƙarfi da amana amin.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
HADISAI GOMA KAN HATSARIN SHUGABANCI
Shugabanci komai ƙanƙantarsa wani nauyi ne babba akan wanda ya hau kansa wanda in ba a ɗauke shi an sauke shi daidai ba, in ba a yi gaskiya da adalci ba, in ba a riƙe amana ba, tabbas zai zama nadama da takaici ga wanda ya yi wannan shugabanci.
Da mun san hatsarin da yake cikin shugabanci ko da an yi shi bisa gaskiya da riƙon amana, da babu wanda zai nemi a ba shi shugabanci. Da sai an zo ana bin mutum ana haɗa shi da Allah don ya karɓi muƙami yana gudu yana a kai kasuwa.
To amma rashin sanin hatsari da yake ciki da kuma kallon da kwaɗayin ɗan romon da yake cikinsa shi ne yasa ake ta yin kokawa har ma ana kashe kuɗaɗe masu ciwo da ma roƙon Allah duk don a ɗare kan karagar mulki.
Ga wasu daga hadisan da shugaban halitta ya faɗa akan hatsarin shugabanci:
HADISI NA ƊAYA
An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Kowane ɗaya daga cikinku makiyayi ne (shugaba ne) kuma za a tambaye shi a kan waɗanda aka ba shi kiwo, shugaba makiyayi ne kuma za a tambaye shi akan waɗanda aka ba shi kiwo (mabiyansa), magidanci makiyayi ne akan iyalansa kuma za a tambaye shi a kansu. Matar aure mai kiwo ce a gidan mijinta kuma za a tambaye ta akan waɗanda aka ba ta kiwo. Yaron gida/kanti makiyayi ne a cikin dukiyar uban gidansa, kuma kowa za a tambaye shi akan abinda aka ba shi kiwo. Dukkanninku makiyaya ne kuma za a yi masa tambaya akan abin da aka ba shi kiwo.
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
KARIN BAYANI
Wannan hadisi ne mai girma da muhimmanci wanda ya ƙunshi abubuwa da dama kaɗan daga cikinsu su ne:
- Shugabanci kalma ce mai faɗi bai taƙaita akan masu riƙe da madafan mulki ba, a a duk wani wanda waɗansu suke ƙarƙashinsa komai rashin yawansu to shi ma shugaba ne, kamar yadda hadisin ya faɗa:
Mai mulki shugaba ne, mai gida shugaba ne a gidansa, matar aure shugaba ce a gidan mijinta, bara ko yaron gida ko angulun kanti, shugaba ne akan dukiyar uban gidansa. Haka dai har shugaban aji da ɗalibai da na ƙungiyoyi da kwamitoci da sauransu.
- Kowa za a yi masa hisabi ranar lahira za a bincike shi kan yadda ya gudanar da shugabanci da aka ba shi.
- Duk azabar da za a yi wa azzalumin shugaba, da kuma falala da rahamar da Allah yake yi wa adalin shugaba zai samu mai gida da uwargida, da yaron gida da sarki har zuwa shugaban ƙasa, babu bambanci, sai dai kuma kayan wani sun fi na wani yawa da nauyi.
- A duk lokacin da ake maganar shugabanci yabo ko zargi alhairi ko sharri kafin ka yi tunanin shugaban ƙasa ko gwamna ko sarki ko wani na can sama, ka fara duba kanka ka yi wa kanka hisabi. Shi shugabancin da aka ba ka kana kula da shi yadda ya kamata? Shin kana ba da haƙƙoƙin da suke kanka?
HADISI NA BIYU
An karɓo daga Anas ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah zai tambayi kowane makiyayi akan abinda aka ba shi kiwo, shin ya kiyaye shi ko ya tozarta shi har ma za a tambayi mutum akan iyalansa”.
Ibn Hibban ne ya rawaito shi a cikin sahihinsa.
KARIN BAYANI
Lallai ne magidanta masu tozarta haƙƙoƙin iyalansu su bar ‘ya’yansu kamar marayu, matansu kamar kuyangi ba tarbiyya ba cikakkiyar lafiya har dabbobin da suke kiwatawa ma sai su fi iyalansu jin daɗinsu, su ji tsoron Allah su riƙe iyalansu da gaskiya su sani cewa amana ce Allah ya damƙa musu kuma za su yi bayani ranar ƙiyama kan wannan amanar.
HADISI NA UKU
An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda ya zama alƙali haƙiƙa an yanka shi ba da wuƙa ba”.
Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.
KARIN BAYANI
Duk alƙalin da ya yi rashin gaskiya akan aikinsa haƙiƙa ya yi babbar asara ya halaka, ba wai rayuwarsa kawai ya rasa ba, har ma da addininsa wato wanda aka yanka da wuƙa zai fi shi samun sauƙin mutuwa da halaka.
Wannan hadisi yana bayanin hatsarin da yake cikin alƙalanci, saboda haka ya zama wajibi ga alƙalai su yi taka-tsan-tsan su rinƙa kwatanta gaskiya da adalci su guji zalunci, da cin hanci da murɗe gaskiya.
HADISI NA HUƊU
An karɓo daga Auf ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “In kuna so zan ba ku bayani a kan shugabanci ko yaya yake? Sai na ɗaga muryata na ce yaya yake ya Ma’aikin Allah? Sai ya ce: Farkonsa zargi ne, na biyunsa nadama ce, na ukunsa azaba a ranar ƙiyama sai dai wanda ya yi adalci”.
Bazzar da Ɗabarani ne suka rawaito shi.
ƘARIN BAYANI
Wannan hadisi ne mai ɗimbin fa’ida da bayanin ɗabi’ar mulki duk daga taƙaitattun kalmominsa
– Mai mulki ba ya kuɓuta daga zargi da tuhuma da munana masa zato daga waɗanda yake mulka da abokan hamayyarsa komai ƙoƙarinsa na kwatanta gaskiya. Haka zai ta shan suka da ƙalubale ta kowanne ɓangare, dukkanin idanu da kunnuwa suna kansa komai ya faru shi ne ko bai sani ba, kuma ya fi ƙarfinsa.
– Yayin da abubuwa suka dagule,matsaloli suka kunno kai ta ko’ina , magoya baya suka fara juya baya ga shugaba, barazana da fargaba ta yawaita a gida da waje, shugaba yakan tsinci kansa a halin da-na-sani, da nadamar karɓar wannan shugabanci.
– Haka kuma bayan shugaba ya bar mulki musamman in an bi shi da jafa’i da bincike-binciken neman laifi da gazawa, wannan ma yana jefa masu mulki cikin kogin nadamar karɓar mulki.
– Mafi munin yanayi kuma shi ne matsananciyar azaba da take jiran azzaluman shugabanni a lahira da tozarta da wulaƙanta tun daga duniya.
A taƙaice wannan hadisi yana ɗauke da tsoratarwa akan shugabanci na zalunci da kwaɗaitarwa kan adalci saboda shi adalin shugaba babu ruwansa da wannan azabar.
HADISI NA BIYAR
An karɓo daga Abu Zarr (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Na ce ya Ma’aikin Allah shin ba ka ba ni wani muƙami ba? Sai ya ɗora hannunsa akan kafaɗata sannan ya ce: “Ya kai Abu Zarrin haƙiƙa kai mutum ne mai rauni, shi kuma shugabanci amana ne, kuma yana jawo kunyata da nadama ranar ƙiyama, sai dai wanda ya kula da haƙƙoƙin shugabanci ya sauke nauyin da yake cikin shugabanci.
HADISI NA SHIDA
An karɓo daga gare shi (Abu Zarr) Radiyallahu Anhu, haƙiƙa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da shi: “Ya kai Abu Zarr haƙiƙa na ga kai mutum ne mai rauni, kuma ina so gare ka abinda nake so ga kaina.
Saboda haka, kada ka shugabanci ko da mutum biyu, kuma kada ka karɓi riƙon dukiyar maraya.
Muslim da Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi.
ƘARIN BAYANI
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) shugaba ne da yake lura da halin kowa kuma yake ba shi aikin da ya dace da shi. Duk tsoron Allah na mutum da yawan ibadarsa bai kamata a ba shi shugabanci ba in dai ba shi da ƙarfi da gogewa kan al’amuran mulki. Wannan ne ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ƙi ya bawa Abu Zarr wani muƙami saboda ya san rauninsa da matsanancin sauƙin kansa da gudun duniya, har ma ya ba shi shawarar cewa ko da shugabancin mutum biyu aka ba shi kada ya karɓa, haka kuma kada ya karɓi ajiyar dukiyar marayu ba don yanatsoron zai cinye ba, a a sai don gudun kada tausayi ya sa ya yi sadaka da wannan dukiyar.
Ɗan’uwa idan an faɗawa Abu Zarr (Radiyallahu Anhu) duk da falalarsa, ina ga mutanen yanzu da za ka ga har kuɗi ake kashewa ko a yi ta yin rigima akan neman shugabanci ba kuma tare da wata cikakkiyar cancanta ko manufa ko tsari ba.
HADISI NA BAKWAI
An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzo Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa za ku rinƙa kwaɗayin shugabanci, kuma haƙiƙa zai zama sanadin nadama ranar alƙiyama. Madalla da mai shayarwa tir da mai yayewa”.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
Bukhari da Nasa’i ne suka rawaito shi.
ƘARIN BAYANI
Wannan abu da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa na tsananin kwaɗayin shugabanci kamar a yanzu yake maganar. Sai ka ga ɗaruruwan mutane suna takarar kujera ɗaya, kuma a yanzu kowa so yake ya zama shugaba sai ka ga komai da shugabansa kuma har ana rigima akan wannan shugabanci. Amma duka a ƙarshe nadama ce take biyo baya.
Mai shayarwa da mai yayewa shugabancin ake nufi, wato kamar yadda yaro yake jin daɗi lokacin da ake shayar da shi, kuma yake shan wahala da fama da laulayi iri-iri lokacin yaye shi to haka daɗin shugabanci yake a farkon da kuma wahala da damuwa da ake shiga in an sauka.
HADISI NA TAKWAS
An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Kaicon sarakuna, kaicon wakilai, kaicon amintattu. Wallahi waɗansu mutane (waɗanda suka karɓi shugabanci) a ranar ƙiyama za su yi burin ina ma da a ce a ɗaure gashinsu a jikin tauraron surayya, su yi ta reto tsakanin sama da ƙasa a maimaikon shugabancin da suka riƙe.
Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
HADISI NA TARA
An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Zamani ya kusa zuwa da mutum zai yi burin gara a ce ina ma ya faɗo daga tauraron Surayya (zai fi masa sauƙi) akan mulkin da ya yi komai ƙanƙantarsa”.
Hakim ne ya rawaito shi.
ƘARIN BAYANI
Waɗannan hadisai guda biyu suna bayanin hatsarin shugabanci ta yadda mutum zai ji a ransa cewa gara a rataye shi da gashinsa a jikin tauraro ya yi ta reto ko kuma a jefa shi daga can sama ya yi ƙasa ya ratattake a maimakon azabar da za a yi masa saboda rashin adalci da gaskiya da ya gudanar a shugabancin.
HADISI NA GOMA
An karɓo daga Abdurrahman bin Samura (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da shi: “Ya kai Abdurrahman ɗan Samura kada ka nemi shugabanci, saboda in ya zo maka ba tare da ka nema ba Allah zai taimake ka a kansa, in kuwa aka ba ka shugabanci saboda nema da ka yi sai Allah ya bar ka da dabararka”.
Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
ƘARIN BAYANI
Duk wanda ya san hatsarin shugabanci da makomarsa ba zai iya nacewa ya yi ta kokawar sai ya sami muƙami ba. To irin wannan idan aka ga cancantar su aka tilasta musu lallai sai sun karɓi muƙamin za su sami tallafi da agaji daga Allah.
Wanda kuwa ya nace sai an ba shi muƙami musamman in bai cancanta ba ko kuma yana da wata muguwar manufa a ransa to ba zai yi wani abin kirki ba sai hauma-hauma da zalunci.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan