Waɗanne Abubuwa Ne Na Fili Dake Karya Azumi?

0
526

Amsa: Abubuwan fili da suke karya azumi su ne:

Cin abinci ta hanyar tauna ko haɗiya.

Shan ruwa ko wani abin sha mai kama da ruwa.

Kwanciyar aure ga masu aure.

Fitar da maniyi ga wanda bashi da aure ta hanyar kallace-kallace a fili ko mujalla ko wayoyin hannu ko talabijin.

Sauraran labaran batsa, ko na motsa sha’awa kai tsaye daga wani ko ta hanyoyin sadarwa da gangan.

Hujja: “Wanda yaci, ko ya sha, ko ya kusanci iyalinsa, ya karya azuminsa”.

Marawaici: Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim, Sunan Abu Dawud, Sunan Turmuzi, Sunan Nassa’i Sunan Ibn Maajah.

Domin karanta cikakken bayani akan Waɗanne Abubuwa Ne Ke Lalata Azumi A Ɓoye? danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Watan Ramadana 2 danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Azumin Watan Ramadana 2
Labarin na GabaWaɗanne Abubuwa Ne Ke Lalata Azumi A Ɓoye?
Lawan Bello
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.