Tir Da Ɓarin Imani da Sunan Kishi! 

0
23

A ƙoƙarin wasu daga cikin mata na su raba mijinsu da kishiyarsu, suna yin fatali da imaninsu ta hanyar zuwa wajen boka ko ɗan duba don a sihirce kishiyarsu, alhali tsafi a Musulunce kafirci ne, kuma yarda da shi ridda ce, kamar yadda ayoyin Alƙur’ani da ingatattatun Hadisai suka tabbatar. 

A wani ɓangaren kuma, wasu matan duk jarrabar da ta same su ta cuta ko asarar dukiyar da ta makamantansu; ba su raba ɗaya biyu sai su ce, “Kishiyarsu ce ta ɗora musu”. saboda ƙungurmin jahilci da tsananin raunin imani da suke da shi. 

A Musulunci, idan ma wasu ƙwararan alomomi da gamsassun hujjoji ake da su game da mugun nufin kishiya a kan kishiyarta, to ga Allah ake komawa a yi riƙo da ayoyin tsari da addu’o’in Manzo da ingantattun zikiri don murƙushe duk wani makaru da ƙulunboto, ko

kuma a bi hanyoyi na shari’a don murƙushe duk wani makaru da ƙuluboto, ko kuma a bi hanyoyi na shari’a don ɗaukar matakin da ya dace. 

A wasu lokutan kuma, wasu matan cutar da kishiyoyinsu suke yi ta salon yin biris da su da ƙin kula su, idan sun gaishe su, ko kuma su haɗe musu rai su turɓune fuska a duk inda suka gansu, ga shi kuma yin hakan laifi ne a Musulunce bayan zubar da ƙimarsu da yake yi. 

Domin Karanta Bayani akan Haramun Ne Aibata Halittarkishiya Ko Cin Mutuncin Ta Ko Gulmar Ta Ko Kuma Yi Da Ita Ko Kuwa Isgili Da Ita Danna nan

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Waɗanda suke cutar da muminai maza da muminai mata, ba tare da sun yi laifi ba, to haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayyanan ne”. (Surtul Ahzab,58). 

Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Kar ka raina abin kirki komai ƙanƙantarsa, ko da kuwa ka haɗu da ɗan’uwanka musulmi ne kana mai sakakkiyar fuska”. (Muslim ne ya ruwaito). 

Kuma an karɓo hadisi daga Amru ɗan Asi, Allah ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “ Wanda yake son a nesanta shi daga wuta, kuma a shigar da shi aljanna, kuma mutuwarsa ta zo masa yana mai imani da Allah da ranar lahira, to ya yi wa mutane abin da yake so su yi masa”. (Muslim ne ya ruwaito shi). 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Kuma an karɓo hadisi daga Anas ɗan Malik, Allah ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ɗayanku ba zai zama mai cikakken imani ba har sai ya so wa ɗan’uwansa (Muslimi) irin abin da yake so wa kansa (na alheri)”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi). 

Adalci Ne Ke Sanya Kishiya Faɗar Kirkin Kishiya 

An karɓo hadisi daga Muhammad ɗan Abdurrahman, Allah ya yarda da shi, cewa: “Haƙiƙa A”isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: “(Kishiyarta).. Zainab ‘yar Jahshi ta kasance tana gasa da ita wajen matsayi a gurin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (A’isha ta ce): “Tun da nake ban taɓa ganin mace da ta fi Zainab ba wajen addini da tsoron Allah da gaskiya a magana da sadar da zumunta da yawan sadaka…”. (Muslim ne ya ruwaito shi). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHaramun Ne Aibata Halittarkishiya Ko Cin Mutuncin Ta Ko Gulmar Ta Ko Kuma Yi Da Ita Ko Kuwa Isgili Da Ita
Labarin na GabaMatsayin Mai gida, Uwar gida da Amarya