Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani attajiri a wani gari ana kiran sa Albagadadi. Ba abin da yake so kamar ya ji wani yana neman taimako, domin ya taimaka masa. Duk ranar Jumma’a mutane kan taru maƙil a ƙofar gidansa, suna karɓar sadaka.

Ana nan, ana nan, wata rana sai wani saurayi ya je wajensa ya ce masa yana son masauki, ko ya sami aikin yi a garin. Sai Albagadadi ya sauke shi a gidansa. Sannu a hankali, sai yaron nan ya zama hadiminsa, watau ya riƙa yi masa aikace-aikacensa na gida. Yaron kuma makarancin Alkur’ani ne sosai.

Kullum idan Albagadadi zai je unguwa, ko dai wani wuri, to tare za su. Sai mutane suka sa wa yaron suna Sheikh Ali Albagadadi. Tun da yaron nan ya shiga gidan Albagadadi, sai komai nasa ya sauya; arziƙin uban gidansa ya yi ta bunƙasa. Duk abin da ya saya, ko gonar da ya noma, sai riba ta riɓanya ta da.

Wata rana Albagadadi ya zauna tare da abokansa, sai ya kira Sheikh Ali ya ce yana son duk wanda yake wurin ya ba shi wani labari da zai faranta masa rai, zuciyarsa ta kwanta. Sai Sheikh Ali ya ce: “Wanda duk ya yalwata wa wanda ke cikin matsi, to shi ma Allah zai yalwata masa duniya da lahira.

Wanda ya rufa asirin wani a yayin da yake buƙatar rufin asiri, to shi ma Allah zai rufa masa asiri duniya da lahira. Kuma duk wanda ya ba da sadaka tamkar wanda ya yi shuka ne, domin idan aka shuka masara kwaya uku, za katarar ta tsiro fiye da dubu uku. Kamar haka ne Allah yake saka wa masukyauta.”

Duk wurin aka yi tsit ana jin bayaninsa. Sai ya ci gaba da cewa: “Ita sadaka takan gusar da bala’i da masifa, ta karya maƙiyi da Shaiɗan, kamar yadda ruwa yake kashe wuta, kuma ta goge zunubin mutum.” Kafin Sheikh Ali ya gama zancensa mai amfani, sai ya ga hawaye na kwarara daga idanun Albagadadi.

Ganin haka sai ya dakatar da maganarsa. Rannan suna gida da daddare, sai suka ji muryar mutane a cikin gida. Ashe ɓarayi ne riƙe da makamai suka dira gidan da nufin yin sata, to amma ba sa iya ganin komai a cikin gidan. Can dai Ali Albagadadi ya yi tari, kuma tarinsa sai ya fasa ɓarayin, suka runtuma da gudu.

A garin gudu, ɗaya ɓarawon ya faɗa rijiya, wuyansa ya karye. Na biyun kuma ya faɗa wani gida a kan wani dutse mai kaifi, shi ma ya mutu. Na ukunsu da ya samu ya fita bayan gari yana gudun ’yan bin sawu, sai ya yi ƙundunbala ya faɗa a kan wani kwazazzabo da yake zato tafki ne.

A nan take shi ma ya sheƙa lahira. Da gari ya ƙarasa wayewa, jama’a suka daɗa taruwa, sai aka ɗebi ɓarayin nan aka binne su a rami. Mutanen garin suka yi ta mamakin yadda ɓarayin nan ba su saci komai a gidan Albagadadi ba, kuma sai suka riƙa cewa Allah ne ya kare shi saboda taimakon da yake yi wa mutane.

Wannan kariya da Allah ya ba Albagadadi daga muguwar aniyar ɓarayi ce sanadiyyar da mutanen garin idan za su nemi tsari daga maƙiyansu sukan ce: “Kamar mutuwar ɓarayin Albagadadi.” Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Ladabi da biyayya kan jawo arziƙi.
  • Mai arziƙin da ke tallafa wa mabuƙata Allah ne zai kare shi ya daɗa bunƙasa arziƙinsa.
  • Kyauta sadaka ba sa tauye arziƙin kowa.
  • Aikata alheri ga kowa, sakayya na wurin Allah.
  • Sadaka maganin asara.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi
Labarin na GabaTatsuniyar Ɗantsintuwa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.