Tag: yadda ake

  • Saƙo Maƙoƙo

    Saƙo Maƙoƙo

    Sallama farko na miƙo
    Ɗan ƙasa ne ko kwa baƙo
    Wanda ke sama to ya sauƙo
    Ya ji saƙon umma kuma ya karɓa.

    Magana zan yo a kanta
    Tsohuwar nan ta wahalta
    Ni fa tinda na zo cikinta
    Na fahimci akwai abin da bai ba.

    Nai mafarki ne da umma
    Ta faɗan magana da dama
    Dan akwai maganar da ai ma
    Ba buƙatar bayyana ta nan ba.

    Wata ƙila wanin ku zai ce
    Wacce umma hala mutum ce
    Ko kwa aljan to wace ce
    Ɗan uwa ƙasarmu nai nufi ba.

    Ƙorafinta da tai na farko
    Kan ɗiyanta na farko-farko
    Sai ta yo ƙasa can ta sakko
    Sai ta yo maganar da zan faɗi ba.

    Tunda nai aure na farko
    Ga sadaki har da baiko
    Har na haifi wasunku aiko
    Aka auran wanda ban nufi ba.

    Ku kuke nemo mazajen
    Da kuke so sai ku auren
    Sai su zo ƙarshe su cucen
    Su sakeni su bar ni da ciki ba.

    Kansu sau ni su illata ni
    Kalli duk sun raunata ni
    Ga jikina ya yi rauni
    Ni fa ko, ba zan ƙi in mace ba.

    Da abin a iya garen ne
    Kan tsaya to da sumul ne
    To fa kuma duk a jone
    Kuke kan wahalar da ke zuwa ba.

    Sai nace mata ya uwarmu
    Yanzu menene kalamu
    Wa kike so ne ki samu
    Ki yi wuff da abinki ne nufi ba.

    A a na ga kuna ta naci
    Za ku je tonan muruci
    So kuke ku daɗe ni ƙunci
    Ni da ku ai duk muna ta karɓa.

    Nifa dimukradiyar ce
    Bam biɗa in dai wannan ce
    Tinda an yi gwaji shiru ce
    Babu canji ko da na sile ba.

    Abba Marke ka cewa sauran
    Su ji tsoran rabbu sarkin
    Da ya yi ni ya yi ku haƙƙun
    Su fitar ni hannun birirrika ba.

    Don karanta Duka A Murɗe danna nan

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

     

  • Yin Amfani Da Maganin Sauro Na Ƙonawa

    Yin Amfani Da Maganin Sauro Na Ƙonawa

    Ana yin amfani da coil na sauro a sassa daban-daban na duniya, musamman a yankunan da suke fama da yawan cututtukan da sauro yake yaɗawa kamar zazzaɓin cizon sauro da ciwon Dengue. A Najeriya, inda ake fama da tsananin zafi da kuma yawan sauro, musamman tare da tsadar kayan masarufi, coil na sauro yana daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da shi wajen kare kai daga cizon sauro.

    Sai dai, akwai abin damuwa game da illolin lafiya da ke tattare da hayaƙin da coil na sauro yake fitarwa. Hakan yasa mutane suke yin tambayoyi a kan ingancin coil ɗin gaba ɗaya. Wannan maƙalar za ta yi bayani ne a kan dalilan da suka sa coil ɗin sauro ya zama sananne, illolin lafiyarsa, ƙalubalen amfani da shi, da kuma hanyoyin magance matsalar a cikin yanayin ƙasashe irin Najeriya.

    DALILIN SHAHARAR COIL NA SAURO 

    Babban dalilin da yasa coil na sauro ke ci gaba da shahara a Najeriya, kamar yadda yake a wasu ƙasashe masu tasowa, shi ne farashin sa da kuma yadda ake samun shi cikin sauƙi. Yawancin iyalai suna fama da ƙalubalen tattalin arziki kuma ba za su iya biyan ƙarin kudi don sayen wasu ingantattun kayan kare kansu daga sauro masu tsada ba, kamar yadda ake samu a wasu ƙasashe.

    Haka kuma, yawan dauke wutar lantarki yana sanya yin amfani da kayan lantarki masu korar sauro ya zamo bazai yiwu ba, wanda hakan ke sanya iyalai da yawa su koma yin amfani da coil na sauro. Coil ɗin sauro yana da amfani saboda ba ya buƙatar wuta ko wata na’ura ta musamman kuma yana iya ƙonewa har tsawon sa’o’i, yana samar da kariya daga cizon sauro cikin ƙananan kuɗi.

    Amma, ingancinsa yana da alaƙa da yadda ake barin shi yana ƙonewa da kuma yawan hayaƙin da yake fitarwa. A mafi yawan lokuta, dole ne a bar coil ɗin yana ƙonewa duka tsawon daren don tabbatar da kariya mai kyau daga sauro, saboda yawanci sauro sukan dawo da zaran hayaƙin ya gushe. Wannan yana haifar da matsala, kasancewar yana da alaƙa da illolin lafiyar da na ambata.

    ILLOLIN LAFIYA DA KE TATTARE DA COIL NA SAURO 

    Kodayake coil na sauro yana da tasiri wajen korar sauro, hayaƙin da yake fitarwa yana ɗauke da wasu sinadarai waɗanda suke iya yin illa idan aka shaƙe su na tsawon lokaci. Yawanci coil ɗin na fitar da sinadarai irin su “pyrethroids”, wanda shi ne sinadarin kashe ƙwari, da wasu ɓurɓushi masu illa.

    Bincike ya nuna cewa daɗewa ana yin amfani da hayaƙin coil na sauro yana iya haifar da matsalolin numfashi, musamman idan an yi amfani da shi a ɗaki maras isasshiyar iska. Wasu binciken kuma sun danganta hayaƙin coil ɗaya da na fiye da sigari 100, wanda ke nuna damuwa game da yiwuwar kamuwa da cututtukan huhu da sauran matsalolin numfashi.

    Duk da waɗannan illolin, hukumomin da ke kula da lafiya da na kare haƙƙin masu amfani da kayan masarufi ba su hana yin amfani da coil ɗin sauro gaba ɗaya ba. Wannan yana da alaƙa da cewa, idan an yi amfani da coil ɗin cikin taka-tsan-tsan a wuraren da ake samun iska, to, fa’idarsa ta rage yaɗuwar cututtukan sauro ta fi haɗarin lafiyar da ake ganin zai iya haifarwa.

    A yawancin gidaje, kaucewa kamuwa da zazzaɓin cizon sauro ko ciwon Dengue ya fi zama babban abin la’akari fiye da kamuwa da matsalolin numfashi a nan gaba sakamakon yin amfani da coil ɗin.

    BUƘATAR SAMAR DA ISKA A CIKIN ƊAKI DA TASIRIN INGANCIN COIL ƊIN 

    Don rage haɗarin lafiyar da ke tattare da hayaƙin coil na sauro, ana bayar da shawarar a yi amfani da shi a wuraren da ke samun iska mai kyau tana kewayawa. Amma, wannan shawarar tana da ƙalubale, kamar haka: a wurin da iska take kewayawa, yawan hayaƙin coil ɗin zai zamo babu yawa sosai, wanda hakan zai sanya coil ɗin ya kasa korar sauro yadda ya kamata. Don haka iyali suka gwammace su bar hayaƙin coil ɗin ya taru sosai, saboda ya iya korar sauro sosai.

    Wannan yana nufin cewa, domin coil ɗin sauro ya yi aiki yadda ya kamata, dole ne a bar shi ya ƙone gaba ɗaya a duk tsawon dare. Idan ba haka ba, to, sauro sukan dawo da zarar hayaƙin ya gushe. Amma kuma hakan zai iya sanya su shaƙi hayakin fiye da yadda ya kamata.

    MATSALOLIN TATTALIN ARZIKI DA RASHIN WADATATTUN ZAƁIN HANYOYIN KARE KAI DAGA CIZON SAURO

    A Najeriya, tsadar kayan masarufi, yawan ɗauke wutar lantarki, da kuma matsalolin tsadar rayuwa a yawancin gidaje suna haifar da wahalar iya sayen wasu wasu abubuwan korar sauro, waɗanda ba coil ba. Na’urorin lantarki masu korar sauro suna da tsada kuma suna buƙatar wutar lantarki, wanda ba a samu koyaushe. Haka kuma, ragar kwanciya da aka shafawa maganin kashe ƙwari (treated mosquito net) tana da tsada ga yawancin iyalai ko kuma ba a samunta a cikin sauƙi.

    A ƙauyuka, wannan matsala ta fi tsanani, inda coil ɗin sauro yake zamowa kawai shi ne mafita mai sauƙi. Amma daɗewa ana yin amfani da coil ɗin a cikin gidaje marasa isasshiyar iska yana ƙara haɗarin samun matsalolin numfashi, musamman ga yara da tsofaffi. Wannan ya sanya ƙwararrun ma’aikatan lafiyar suke nuna damuwa kan illolin daɗewa ana yin amfani da hayaƙin coil ga lafiyar jama’a.

    DAIDAITA YIN AMFANI DA COIL NA SAURO DA KUMA KIYAYE LAFIYA

    La’akari da matsalolin tattalin arziki da ƙarancin hanyoyin magance matsalar sauro, coil ɗin sauro yana cigaba da zamowa mafi sauƙin mafita ga yawancin iyali a Najeriya. Amma, akwai hanyoyin da za  a iya haɗa amfani dashi tare da kiyaye illolinsa. Misali, sanya coil ɗin sauro kusa da tagogi ko wuraren da sauro ke shiga zai iya sanya taruwar hayaƙin a wuraren sauron yake biyowa ya shigo ɗaki, yayin da kuma zai tabbatar da samun iska domin rage shaƙar ɓurɓushin da ke cutarwa.

    Bugu da ƙari, iyalai suna iya haɗa yin amfani da coil ɗin tare da wasu hanyoyi masu arha. Misali, amfani da fanka wacce za ta bayar da iska a cikin ɗakin zai ƙara ingancinsa yayin da kuma zai rage yawan hayaƙin da ake shaƙa. Sa’annan sanya ragar sauro a rufe tagogi da ƙofofi zai iya taimakawa wajen rage dogaro akan yin amfani da coil ɗin.

    Danna nan don karanta Ko Ka San Idanun Sauro Sun Fi 100?

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Tarihin Malam Muhammadu Na Ta’ala

    Tarihin Malam Muhammadu Na Ta’ala

    Malam Muhammadu Na Ta’ala ɗaya ne daga zuriyar Sheikh Abdullahi Alkanawi, almajirin Shehu Usman kuma jakadansa. Asalinsa mutumin Kano ne daga jinsin Gyanawa. Ya koma Sakkwato a lokacin da ya samu labarin bayyanar Shehu.

    Daga nan kuma ya cigaba da taimaka masa a Sifawa. Bayan an dawo Sakkwato, Shehu ya ba shi fili inda ya gina gidansa da makarantarsa; wadda aka fi sani da Gidan Kanawa. Bayan rasuwarsa sai ɗansa Halliru ya zama halifansa. Daga nan kuma sai ɗansa Umar, shi ma kuma ɗansa Ibrahim Dasuki ya gaje shi.

    Bayansa ne sai ɗan’uwansa Muhammad Na Ta’ala ya zama halifa. Wannan makaranta ba ta gushe ba ƙarƙashin ‘ya’yansa su Alhaji Bashir Muhammad Na Ta’ala da ɗan’uwansa Malam Ahmad Zaruƙu; inda suke cigaba da ilmantarwa da wa’azi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Malaman Mabera A Sakkwato Waɗanda Ke Tara Almajirai A Tsarin Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Kano Kashi Na Ɗaya(1) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ingantattun Hadisai Kan Falalar Ranar Ashura Da Azumin Ranar

    Ingantattun Hadisai Kan Falalar Ranar Ashura Da Azumin Ranar

    1- An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zo Madina; sai ya ga Yahudawa na azumi ranar Ashura. Sannan ya ce: mene ne wannan?

    Sai suka ce: wannan rana ce mai daraja, a wannan yini Allah ya kuɓutar da Banu Isra’ ila daga maliyansu; shi ne ya sa Annabi Musa yake yin azumin ranar. Sai ya Ce: “Ni na fi ku kusanci da Musa Sai ya yi azumin ranar; ya yi umarni da azumtar ranar (Bukhari Hadisi na 2004, azumtar ranar (Bukhari Hadisi na 2004, Muslim Hadisi na 1130).

    2- An karɓo daga Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Babu wata rana da Manzon Allah (Salallahu Alaihi Wasallam) yake kardadan azumi a cikinta; yake fifita ta a kan sauran ranaku, sai ranar Ashura. Sai kuma ranakun watan Ramadan. (Bukhari Hadisi mai lamba (2006) Muslim Hadisi mai lamba 1132).

    3- An karɓo daga A’isha (Radiyallahu Anha) ta ce: “Ƙuraishawa sun kasance suna yin azumin ranar Ashura a zamanin jahiliyya, sai Manzon Allah (Salallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni a rinƙa yin azumin ranar har zuwa umarni a rinƙa yin azumin zuwa lokacin da aka wajabta azumin Ramadan. Daga nan sai ya ce: “Wanda ya ga dama ya yi, wanda ya ga dama sai ya bari (Bukhari hadisi na 2001, Muslim hadisi na 1125).

    4- An karɓo daga Abu Ƙatada (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Haƙiƙa an tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) game da azumin Ashura, sai ya ce: “yana kankare zunuban shekarar da ta wuce”. (Muslim hadisi na 1162). Shi kansa watan Muharram ana son yawaita azumi a cikinsa saboda:

    5. An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wa Sallam) ya ce; “Mafificin azumi bayan azimin Ramadan, shi ne azumi a watan bayan azimin Ramadan; shi ne azumi a watan Allah Al-Muharram, mafificiyar salla bayan sallar farilla, ita ce sallar dare”. (Muslim hadisi na (1163). Shi azumin Ashura saboda muhimmancinsa ana iya ɗaukar niyyarsa bayan fitowar alfijir; ko da kuwa mutum ya ci wani abu, saboda:

    6- An karɓo daga Rubayyi’i Bint Mu’awwiz (Radiyallahu Anha) ta ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya aika unguwannin mutanen Madina a yi shela; “Wanda ya wayi gari ba ya ażumi ya kame bakinsa a ragowar yinin; wanda kuwa ya tashi da azumi, to ya cigaba da azuminsa. ” (Bukhari hadisi 1960, Muslim hadisi na 1137).

    Wannan hukunci har a yanzu mazhabar Malikiyya haka yake; kamar yadda Asshaikh Muhammad Ibn Ahmad Maiyara a cikin littafinsa Addurrus Samin Shafi na 454 yake cewa:

    “An keɓanci azumin ashura da cewa wanda ya wayi gari bai kwana da niyyar azumin ba; zai iya cigaba da niyyar azumin ko da kuwa ya ci abinci ana so a yi azumin ranar tara ga Muharram. Sannan kuma a yi na ranar goman wato Tasu’a da Ashura saboda:

    7- An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce; “A lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi azumin ashura kuma ya yi umarni a yi sai aka ce da shi, wannan fa rana ce da yahudu da nasara suke gimamawa”. Sai ya ce; “In Allah ya yarda shekara mai zuwa sai mun fara azumtar ranar tara (tasu’a) kafin shekarar Allah ya karɓi “ransa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

    (Muslim hadisi na 1134).

    Ƙarin Bayani

    Idan muka yi la’akari da hadisan da suka gabata za mu ga cewa; azumin ashura ya ƙetare matakai huɗu a sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) waɗànnan matakai su ne:

    Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya kasance yana yin azumin ashura; tun yana Makka kafin Hijira, amma bai umarci mutane da su yi ba.

    Lokacin da ya yi hijra zuwa Madina, ya ga yahudawa suna azumin ashura, kuma suna yahudawa suna azumin ashura. Kuma suna girmama ranar, shi kuma dama yana son ya dace da su akan abubuwan da ba a yi masa wani umarni a kai ba; sai ya ci gaba da azumtar ranar, ya kuma umarci mutane da yi, ya ƙarfafa umarnin, ya kwaɗaitar har ta kai Sahabbai suna sa ‘ya’yansu ƙanana su yi azumin.

    Lokacin da aka wajabta azumin watan Ramadan, sai ya daina yin umani da azumin ashura; wato sai ya tashi daga wajibi ya koma na sa kai (Mustahabbi).

    A ƙarshen rayuwarsa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi niyyar yin azumin Tasu’a tare da Ashura; sai ya koma ga Allah kafin lokacin, domin ya saɓawa yahudawa da Nasara.

    Domin karanta cikakken bayani akan Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlil Baiti (Radiyallahu Anhuma) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Suratul Baƙara

    Falalar Suratul Baƙara

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “kada ku mayar da gidajenku kamar maƙabarta; Haƙiƙa Shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara a cikinsa”. (Muslim 708).

    An karɓo daga Abu Umamah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa ya ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yana cewa; “ku riƙa karanta suratul Baƙara saboda riƙo da ita albarka ne, barinta nadama ne; kuma matsafa ba sa iyawa da ita”. (Muslim 804).

    Wato karanta suratul baraƙa yana maganin sihiri da tsafi da kuma sharrin shaiɗanu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Wajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Suratul Fatiha

    Falalar Suratul Fatiha

    An karɓo daga Abu Sa’id Ibnul Mu’alla (Radiyallahu anhu) yace; Na kasance ina salla a masallaci sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kira ni.

    Sai ban amsa ba, sannan sai ne je wajensa na ce salla neke yi. Sai ya ce; “Shin Allah bai ce: ” Ku amsawa Allah da Manzonsa ba idan suka kira ku? Sai ya ce; zan sanar da kai surar da ta fi kowace sura girma a cikin Alƙur’ani kafin ka fita daga masallaci”.

    “Sai ya riƙe hannuna, da muka kusa fita sai na ce; “Ka ce za ka sanar da ni surar da tafi kowace sura girma a cikin Alƙur’ani, sai ya ce; “Ita ce Alhamdu lillahhi rabbil alamin; Ita ce (Mai ayoyin) bakwai da maimaitawa kuma ita ce Alƙur’ani, mai girma da aka ba ni” (Bukahri: 4202).

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Suratul Baƙara danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Ziyarar Mara Lafiya danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Nasiha A Kan Rayuwa

    Nasiha A Kan Rayuwa

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi Yana cewa, “Ku yi ƙoƙarin danne abubuwa guda uku a cikin ranku, da rayuwarku.”

    1. Fushi
    2. Sha’awa
    3. Maganganunku.

    Ku himmatu wajen aikata abubuwa biyu:

    1. Ayyukan alhairi.
    2. Abokai na gari.

    Ku ci moriyar abubuwa uku:

    1. Ƙarfi
    2. Lokaci
    3. Lafiya.

    Ku nemi abubuwa uku:

    1. Gafarar Allah
    2. Ilimi
    3. Hikima.

    Allah ya ba mu ikon kiyayewa.

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

    Domin karanta Nasiha danna nan

  • Yadda Ake Lefe A Auren Hausawa

    Yadda Ake Lefe A Auren Hausawa

    Lefe wani kaya ne da ango yake ba wa amaryarsa a lokacin aure. Kyauta ce ta alfarma da soyayya wadda ta haɗa da sutura, takalma, kayan ƙarau, kayan bacci, kayan kwalliya, turaruka da sauransu.

    A shekarun baya sutura ce kala ɗaya ko biyu da takalmi da ‘ƴan ragowar kayan amfani na mata ake zubawa a cikin mazubi; wanda shi mazubin ake kira lefe. Sai mata dattijai a dangin ango su ɗauka a haɗa da kayan amfani kamar su lalle, hatsi da sauransu; su kai gidansu amarya. Daga can gidan su amaryar ma iyayenta mata ne za su karɓi kayan.

    Amma a yanzu abun ya canza; wataƙila saboda cakuɗuwar al’adu da kuma shigowar baƙi ƙasar Hausa. A yanzu saitin akwatuna ake cikawa da kaya. Saitin akwati yana iya kamawa daga mai biyu har zuwa mai guda shida. Iya yalwar arziƙin ango da danginsa da kuma gatan amarya iya yawan akwatunan da ake mata.

    Kama daga saitin akwati ɗaya har zuwa sama da goma ana yi. Kowanne nau’i na sutura ana ware musu akwatunansu; turamen zani, mayafai, kayan bacci, takalma da jakunkuna, kayan ƙarau, kayan kwalliya wasu lokutan ma harda abaya da kuma kayan turawa waɗanda ake kira ƙananan kaya; kowanne da akwatin su.

    Bayan akwatunan kuma sai a haɗa da goro da alawa, lalle, gero, shinkafa da kuma sukari; wasu a buhunhuna suke sakawa wasu kuma a ƙananun mazubi.

    Ranar da aka saka za a kai lefe sai dattijai mata daga dangin ango su ɗauka su kai. A nan za a yi musu tarba ta girma, idan suka tashi tafiya kuma sai a ba su tukwici wanda ya haɗa da kuɗi da kuma kayan ciye-ciye da lemuka wasu har da ruwan roba.

    A shekarun baya mata ne suke kai lefen kuma mata ne a dangin amarya suke karɓa, sai dai a yanzu maza ma suna kai wa kuma maza su karɓa. Malamai da shuwagabanni suna ta kiraye-kiraye a kan a daina yin wannan al’adar ta lefe, amma har yanzu ba su yi nasara ba.

    Wataƙila saboda yanda Hausawa suke alfahari da wannan al’adar ko kuma saboda yanda wasu matan bayan aure mazansu ba sa sake saya musu wata sutura bayan ta lefen.

    Danna nan don karanta Rabe-raben Auren Hausawa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

     

     

     

  • Falalar Shan Ruwan ZamZam

    Falalar Shan Ruwan ZamZam

    An karɓo daga jabir (Radiyallahu anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: A”Duk buƙatar da aka sha ruwan zamzam saboda ita, Allah zai biya wannan buƙatar”. (Sahihin hadisi ne duba sahihul jami’i 5502).

    Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu anhu) ya kasance idan zai sha ruwan zamzam yana karanta wannan addu’ar; Allahum inni as’aluka ilman nafi’an wa riziƙan wasi’an, wa shifa’an min kulli da’in”. Hakim ne ya ruwaito.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Salla A Masallacin Haramin Makka Da Madina danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita; RMK

  • Waƙar Neman Zaman Lafiya

    Waƙar Neman Zaman Lafiya

    Mawaƙi: Jamilu Alhassan
    Amshi: Zaman lafiya muke so,
    Allah daɗo ƙasata Rabba.

    Bisimilla Sarkin baiwa, Baiwarka ta ishe kowa,

    Bara nake kai nawa, Baiwar Ka yo ƙarawa,

    Bari nai nasiha babba.

    Ƙaro salati Jallah, Gare sa Manzon Allah,
    Ƙaunarsa ɗan Abdullah, Silar barin yin kwalla,
    Faɗar Ma’aikin Rabba.

    Waƙa nake ƙullawa, Zaman salam roƙowa,
    Allah Ka zam ƙarowa, Ƙasarmu Naija tawa,
    Mu daina yin tababa.

    Ku tabbata dangina, Kwai batu ruhina,
    Ku zo ku ji ikhwana, Ku daina yaƙar juna,
    Kuu san hakan ba riba ba.

    Zaman lumana duba, Yana da rana babba,
    Rashin sa ba riba ba, Mu daina yin wata gaba,
    In ji Shi Sarki Rabba.

    Ku tsaya ku ji wani zance, Mu riƙe shi sai mu yi dace,
    Fitina tana nan kwance, La’ana ta gun Mahalicce,
    Ga masu ta da ta duba.

    Aya cikin Anfali, Ashirin biyar ɗan kalli,
    Halin masifa kalli, Ba ta barin mai hali,
    Yaro fa har ma babba.

    Zama idan ai ba fis, Da ka ji an ce zan ƙis!
    Tamkar baru an ce is! Kowa yana yin tinƙis,
    Ba mu so ganin wannan ba.

    Wa’atasimu faɗar Mahalicci, Bihablillahi har da maƙoci,
    Jami’an, babu mai yin ƙunci, Idan mun farraƙe zai ɗaci,
    Rayunmu ban ƙarya ba.

    Idan ka ɗauki Afirka, Akwai ƙasashe leƙa,
    Waɗanda akke yaƙa, Wasunsu na yin kuka,
    Ba su samu zaman aunu ba.

    Burundi in ka dubi, Ruwanda har ma Libi,
    Ka tabbata sun ƙi bi, Kundi na mulki kitabi,
    Ba su daina yin yaƙi ba.

    Laberiya Somali, A nayinti-wan ɗan kalli,
    Sun ƙaurace nasu mahalli, Waɗansu an bar kwalli,
    Domin ba su ma zauna ba.

    Itofiya ita wannan, Iritiriya shi ke nan,
    Nayinti-et su biyun nan, Sun yaƙi juna rannan,
    Ba suy yi adalci ba.

    Sierra Leone har Sudan, Mutum fa wane metan,
    Gidansu sun bar wannan, Zaman rashin fis ke nan,
    Ya sa ba sa zauna ba.

    Idan ka zo nan Naija, Farin ido sai yai ja,
    Kano fa babbar haja, Na Marwa ne kuma yaj ja,
    Amman fa bai kyauta ba.

    Muhammadu na Marwa, Gyauronsa na can Yarwa,
    Ƙala-ƙato ban mantawa, Fitinar da sun shukawa,
    Da yawa akai binnewa, Ka ji halin ‘yan zamba.

    Zangon katab, wayyo ni! Hausa Birom kaico ni!
    Tivi-Jukun can ƙarni, Da yawansu ai sun rauni,
    Wasu ma ba su ko shura ba.

    Idan ka zo nan Yarwa, Boko haram kwai tsiwa,
    A Bama ban mantawa, Wasunmu na a kushewa,
    Abin fa bai kyawu ba.

    A Mubi har ma Gombe, Ba yau ba har ma gobe,
    Addu’arsu hannu tuɓe, Tamkar kwari ba kube,
    Salam salam, ya Rabba.

    Zaman salam kwai auki, Ya zarce ma ɗan sarki,
    Kowa yana nasa aiki, Ticas muna yin maki,
    Ba mu zam muna ganda ba.

    A Yobe nan ce jahata, Abin fa ya so ƙazanta,
    Gwamnanmu ai ya kyauta, Ya ce a bar yin wauta,
    Bai bar mu muna ihu ba.

    A 1st Disemba fotin, A YSU can hostel ɗin,
    Aka zo da kutse domin, A kashe ake yin yaƙin,
    A Monde ba zan manta ba.

    Salmanu sannan Sulfa, Sun zo suna sassarfa,
    Sawunsu sam ba safa, Sauran suna shan suffer,
    Subhana Sarki Rabba.

    Ciza nake tun ɗazu, A Yobe ai dai yanzu,
    Zama na lau ya wanzu, Mun roƙi Sarki Azizu,
    Bai ƙi ya yo amsa ba.

    A yanzu zan yo busa, Na ba ku labarinsa,
    Zaman lumana kansa, Ya zarce daɗin masa,
    Ta Bauchi ban ƙarya ba.

    Ga shawara zan bai wa, Gwamnanmu har ma kowa,
    Ga wanda ke son yalwa, Gun zaman lumana aiwa
    Mu kama Allah Rabba.

    Ina ƙiranmu jumulla, Mai ɗan kwali ko mai hula,
    Rawani da mai jan akala, mu kama Allah walla,
    Mafuta ba za mu rasa ba.

    Shi dai fa rai kwai tsada, Sojojinmu har ‘yan sanda,
    Sun ce sun ji sun kuma yarda, Su nasu ran sun sai da,
    Don kare ƙasata babba.

    A bar batun ɓangaranci, A bai wa kowa ‘yanci,
    Musulum, Kirista maƙoci, Mu mutunta juna.

    Domin karanta cikakken Yabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti danna nan.

    Domin karanta cikakken Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Don karanta cikakken Dangantakar Harshe da Waƙa danna nan.