Tag: yadda ake

  • Matsayin Malamai Kan Kashe Husaini (Radiyallahu Anhu)

    Matsayin Malamai Kan Kashe Husaini (Radiyallahu Anhu)

    Malamai sun kasu gida uku dangane da kashe Husaini (Radiyallahu Anhu); biyu a gefe ɗaya a tsakiya:

    1. Ɗayan na gefe: suka ce an yi dai-dai da aka kashe shi, saboda ya fito ne dan ya raba kan musulmai, Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Duk wanda ya zo yana son ya raba kawunanku, alhali kuna bin wani shugaba guda ɗaya, ku kashe shi”. Suka ce Hussaini ya zo ne ya raba kan mutane, alhali suna ƙarƙashin shugaba ɗaya.

    2.Ɗaya gefen kuma suka ce shi Husaini shi ne shugaban Musulmai a lokaci wanda ya wajaba a yi wa biyayya, kuma imani ba ya cika sai da yarda shi ba za a yi sallar jam’i ko jama’a ba sai a bayan wanda ya naɗa, kuma ba za a yi jihadi ba sai da izininsa.

    3. Su kuwa waɗanda suke a tsaka-tsaki su ne Ahlussuna, ba su goyi bayan waɗannan ɓangarori biyu ba, abinda suke cewa Husaini an kashe shi ne bisa zalunci, kuma ya yi shahada, amma a lokacin ba shi ne shugaba ba, shi kuma wannan hadisi (Na ‘yan tawaye) bai shafi Husaini ba. Saboda lokacin da ya sami labarin kashe ɗan baffansa Muslim bin Akil, sai ya bar maganar halifanci ya nemi a ba shi dama ya tafi wurin Yazidu, ko ya tafi jihadi ko ya koma gida, amma suka ƙi, suka ce sai dai ya yarda a kama shi, yin hakan kuwa bai zama wajibi ba a kansa.

    Ya ɗan uwa musulmi mai neman gaskiya ka ga dai matsayin Ibn Taimiyya a kan wannan mas’ala shin ina alamun ƙin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma) ko goyon bayan abinda aka yi wa Husaini da iyalansa a cikin waɗannan bayanai?

    Ya kamata duk wanda ya ce maka Ibn Taimiyya ya ce kaza, to ya kawo maka littafin kuma a karanto maganar tun daga farkonta har ƙarshenta, ba wai a ciccizgo maganganun nan da can ba. Yaa Allah ka fahimtar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta. Ka ba mu ikon yin adalci ga wanda muke so da wanda ma ba ma so, ka fitar da gaba da riƙo daga zukatan mu. Amin.

    Yanzu kuma ga maganganun wasu fitattun ɗaliban Ibn Taimiyya:

    Shamsuddin Bn Kayyimul Jauziyya Rahimahullah (A.H.S 691 Y.M.S 751)

    Shi kuwa kuwa shaihin malami Ibnul Ƙayyim Muhammad Ibn Abubakar, babban almajirin lbnu Taimiyya (Rahimahullah) ga abinda yake cewa:

    Yana daga cikin hadisan ƙarya, hadisan falalar sa kwalli da yin ado, da yalwatawa iyali da yin wasu salloli ranar ashura da wasu falaloli da ake faɗa, waɗanda ko hadisi ɗaya bai inganta ba a kansu.

    Abinda kawai ya inganta shi ne yin azumi a ranar banda shi sauran duka ƙarya ne. Hadisi mai ɗan dama-dama a kan wannan shi ne hadisin yalwatawa iyali a ranar ashura (cika-ciki) shi kuma Imam Ahmad Rahimahullahu ya ce bai ingata ba”.

    Amma hadisin falalar sa kwalli da shafa mai da sa turare ranar ashura, haƙiƙa maƙaryata ne suka ƙirƙire su, sai kuma wasu (‘yan bidi’ar) suka ƙirƙiri nuna alhini da ɓacin rai domin su ƙalubalance su, duka su biyun ‘yan bidi’a ne, sun saɓawa sunna.

    Su kuwa ahlussunna, suna aikata abinda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi umarni da a aikata a ranar, suna nisantar bidi’o’in da shaiɗan ya yi umarni da su’.

    Ibn Rajab Al-Hambali (Rahimahullah) A.H.S 735 Y.M.S 795

    Babban malami Zainuddin Abul Faraj Abdurrahman Ibnu Rajab Al-Hambali ya Ce:

    “Dukkanin hadisan da aka rawaito a kan falalar sa kwalli da yin ƙunshi da wanka ranar ashura, ƙarya ne ba su inganta ba” amma an rawaito daga Abdullah ɗan Amr Ibnul As ya ce: “Wanda ya yi azumi ranar ashura za a ba shi ladan azumin shekara guda, wanda ya yi sadaka a ranar za a ba shi ladan sadakar shekara guda” Abu Usa Al-Madini ne ya fitar da shi.

    Maganar cika-ciki kuwa an tambayi Imam a kan wannan hadisin ‘sai ya nuna cewa bai inganta ba. Sai da Ibnu Uyaina yace shekararsu hamsin suna jarraba yalwatawa iyali ranar ashura, kuma suna ganin buɗi. Amma dai hadisin bai inganta ba.

    Amma ɗaukar ranar a matsayin ranar baƙin ciki da zaman makoki kamar yadda Rafilawa (‘yan shi’a) suke yi saboda a ranar ce aka kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) wannan aiki ne na ɓatattu amma suna ganin dai-dai suke yi; saboda Allah da Manzonsa ba su yi umarni a mayar da ranar da musibu suka afkawa annabawa ko ranar mutuwarsu ranar makoki ba, ballantana, waɗanda suke ƙasa da su”.

    Al-Hafiz Abul Fida Ibn Kasir (AH.S 701 Y.M.S 774)

    Babban malamin hadisi, malamin tafsiri kuma malamin tarihi; Al-allama lbn Kasir (Rahimahullah) shi kuma ga abinda yake cewa:

    “Ya kamata dukkanın musulmai su yi baƙin ciki da kashe Husaini (Radiyallahu Anhu). Saboda shi yana daga cikin shugabannin musulmai, kuma yana cikin sahabbai malamai, ga shi jikan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) na wurin ‘yarsa mafi daraja, kuma shi mai yawan ibada ne jarumi karimi.

    Amma duk da haka, abubuwan da ‘yan shi’a suke yi suke yi a ranar ashura na nuna raki da baƙin ciki wanda wani abin ma feleƙe ne kawai da riya, ba shi da kyau, a shari’ance. Saboda babansa (Sayyidina Ali Radiyallahu Anhu) shi ma kashe shi aka yi a ranar Juma’a 17 ga watan Ramadan a shekara ta 40 daga hijra ya fito zai tafi sallar Asuba, amma ba su mayar da ranar, ranar makoki ba.

    Haka kuma Sayyidina Usman (Radiyallahu Anhu) wanda a wajen ahlussunna ya fi shi. Tsare shi aka yi aka hana shi fita daga gidansa tsawon kwanaki, a cikin kwanakin aikin hajji a shekara ta 36 daga hijra, amma ba a mayar da ranar juyayi ba.

    Ga kuma Sayyidina Umar (Radiyallahu Anhu) wanda ya fi Usman da Ali (Radiyallahu Anhuma) daraja, yana sallar asuba yana tsaye yana karatun Al-ƙur’ani a masallacin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) aka kashe shi, amma ba a yin komai idan ranar takewayo. Su kuma dukkan su Sayyidina Abubakar (Radiyallahu Anhu) ya fi su falala, amma ranar mutuwarsa ba a mayar da ita ranar makoki ba.

    To kuma ɗungurungum shugaban taliƙai (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya koma ga Allah kamar yadda annabawan da suka gaba ce shi suka koma ga Allah, amma ba a aikata bidi’o’in’ da ‘yan shi’a suke aikatawa idan ranar kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) ta kewayo. Kuma babu wani wanda ya ce a ranar rasuwarsu waɗansu abubuwan mamaki na keta al’ada sun faru kamar yadda rafilawa suke cewa wai sun faru ranar mutuwar Husaini (Radiyallahu Anhu).

    Abu dai mafi kyau shi ne duk lokacin da aka tuna waɗannan musibu da makamantansu sai a ce; “lnna lillallahi wa Inna ilaihi raji’un” kamar yadda shi Husaini ya rawaito daga kakansa (Salallahu Alaihi Wa Sallam) cewa: “Duk wanda ya tuna wata masifa, komai tsawon lokacin faruwarta, ya ce: “Inna lillallahi wa inna ilaihir raji’un.” Za a ba shi ladan kamar a ranar masifar ta faru. Imam Ahmad da lbn Majah ne suka rawaito wannan hadisin. Kuma Ibn Kasir (Rahimahullah) ya ce:

    “Kuma a zamanin daular banu Buwaihe (daular ‘yan shi’a, a tsakankanin shekaru na ɗari huɗu daga hijra, Rafilawa sun kasance a ranar ashura a Bagdad suna fitowa tituna suna ta kaɗe-kaɗe, suna watsa toka da ɓuntu a kan hanyoyi da kasuwanni, suna maƙala ƙyallaye a jikin rumfuna, Suna koke-koke, wasu ma a daren ba sa shan ruwa, wai suna kwaikwayon ƙishirwar da Husaini ya sha ranar da aka kashe shi.

    Haka matansu ma suke fitowa, fuskokinsu a bayyane, ƙafafuwansu ba takalma, suna kururuwa suna marin fuskokinsu, suna dukan ƙirajensu, da dai bidi’o’i munana, wai kawai don su baƙantawa banu Umayya saboda a zamanin mulkinsu ne aka kashe Husaini (Radiyallahu Anhu).

    A gefe guda kuma waɗansu masu adawa da Ahlul Baiti (Nawasib) a Sham su kuma a ƙoƙarinsu na su ƙalubalanci ‘yan shi’a. sai su yi girke-girke a ranar, su yi wanka, su sanya sababbin kaya, su sa turare, su yi ta nuna farin cikin kamar ranar salla, wai don su ɓatawa ‘yan shi’a rai.

    Waɗansu sun yi tawili dangane da kashe Husaini da aka yi suka ce ai yana ƙoƙarin rarraba kan mutane ne, da yi wa shugaban da mutane suka zaɓa tawaye, wannan kuwa abu ne da manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya hana ya faɗi irin azabar da za a yi wa mai aikata hakan kamar yadda ya tabbata a Sahihu Muslim, to wannan tawili ne na jahilci, kuma bai kamata a y kisa a kansa ba. Da tun farko sun yarda da ɗayan abu uku da ya nuna a yi da shikenan, amma suka ƙi suka kashe shi.

    To kuma wannan ba zai zama hujjar da za ta sa a yi ta la’antar gaba ɗayan al’umma ba; saboda laifin wasu ‘yan tsiraru marasa kirki. Saboda mafi yawancin shugabanni sun yi tur da abinda ya faru tun wancan lokaci har ya zuwa yau. Babu wanda ya goyi bayan kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) sai wasu ‘yan tsiraru daga mutanen Kufa; waɗanda su ne suka gayyato shi amma da suka ga abin duniya suka yi watsi suka rabu da shi; wasu ma daga cikinsu suka koma bayan masu yaƙarsa.

    Kuma koda a cikin wannan runduna ba dukkansu ne suka goyi bayan kashe shi ba. Kai koda shi Yazid ɗan Mu’awiyya (Radiyallahu Anhu) bai goyi bayan kashe Husaini (Radiyallahu Anhu); a bisa kyakkyawan zato da shi ne ya kama shi, da ya masa afuwa, kamar yadda shi da kansa ya faɗa. Sannan kuma har tsinewa Ibn Ziyad ya yi, amma kuma duk da haka bai tsige shi daga kan muƙaminsa ba bai kumayi masa komai ba Allah shi ne masani.

    Har ila yau shaihin malami Ibn Kasir (Rahimahullahu) ya yi bayanin matsayi da darajar Husaini (Radiyallahu Anhu); da kuma kyakkyawar alaƙar da take tsakaninsa da Abubakar da Umar da Usman da kuma Mu’awiyya (Radiyallahu Anhuma); inda yake cewa:

    “A taƙaice dai Husaini ya yi rayuwa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma sun rabu lafiya; sai dai yana ƙarami lokacin wafatin Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wa Sallam).”

    Bayan nan Sayyidina Abubakar da Umar da Usman (Radiyallahu Anhuma) suna mutuƙar girmama shi. Ya rayu tare da mahaifinsa (Sayyadina Ali Radiyallahu Anhu) kuma ya yi riwaya a gurinsa; ya kasance tare da shi a dukkanin yaƙe-yaƙen da ya yi na Jamal da Saf’in. Sannan ya masa biyayya har zuwa lokacin da aka kashe shi.

    Lokacin da ɗan uwansa Hasan (Radiyallahu Anhu) ya zama halifa ya yi nufin yin sulhu da Mu’awiyya; ya nuna rashin amincewarsa, shi yana ganin gara a yi ta yin yaƙi. Shi kuwa Hasan (Radiyallahu Anhu); ya nuna ɓacin ransa ga wannan matsayi na ƙaninsa har ya yi barazanar ɗaure shi a kurkuku.

    A lokacin halifancin Mu’awiya (Radiyallahu Anhu) Hassan Da Husaini (Radiyallahu Anhu) suna yawan zuwa wurinsa; yana kuma matuƙar girmama su, yana yi musu kyauta ta girma; akwai ma ranar da a lokaci guda ya ba su dinarai dubu biyu har yace; “ku karɓa daga ɗan Hindu kyautar da ba ku taɓa samun irinta ba, haka kuma ba za ku sake samun irinta ba”, shi kuma Husaini sai ya ce; “kai ma ba za ka sake yin kyauta ga waɗanda suka fi mu daraja ba, kuma ba za ka taɓa yin irinta ba’.

    Bayan rasuwar Hasan (Radiyallahu Anhu) Husaini (Radiyallahu Anhu) ya ci gaba da zuwa wurin Mu’awiya; kuma Mu’ awiya ya cigaba da girmama shi da yi masa kyauta ta karamci. Yana ma daga cikin mujahidan da suka yi yaƙin Kustantiniyya a shekara ta hamsin da ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Yazidu’.

    To ɗan uwa ka ga fa yadda ‘ya ‘yan asali tsarkaka suka yi mu’amala ta mutunci da girmamawa da Mu’awiyya da sauran sahabbai; amma a yau masu cewa tafarkinsu suke bi ba su da aiki sai ƙin jini da La’antar waɗannan sahabbai waɗanda su ne abokai; aminai, surukai, mataimaka na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da ‘ya ‘yansu da jikokinsa (Ahlul Baiti Radiyallahu Anhuma).

    ‘Yan uwa a sake tunani a yi biyayya ta gaskiya da koyi na gaskiya ga Ahlul Baiti da sahabbai. Raditallahu Anhum Ajma’in) Allah ka ganar da mu.

    Imamuzzahbi Abu Abdullahi (A.H.S Y.M.S 748)

    Imamuz Zahabi MashahurIn masanin ilimin hadisi ne da tarihi da sauran fannoni; ga irin yabo da kirari da ya yi ga Imamu Husaini (Radiyallahu Anhuma) inda yake cewa; “Shi ne shugaba, sharifi kamili, Jikan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma abin ƙamshinsa; abin ƙaunarsa a duniya, baban Abdullahi ɗan sarkin Muminai baban Hasan Aliyu ɗan Abu Talib; ɗan Abdulmuttalib. ɗan Hashim, ɗan Abdul Munaf, ɗan Kusayyu, Bakuraishe, Bahashime”.

    Kuma yana cewa: Shugabanmu Aliyu yana cikin halifofi shiryayyu; waɗanda aka yi wa albishir da aljanna, muna matuƙar ƙaunarsa; amma ba za mu ce shi ko Abubakar Siddik ma’asumai ne ba. ‘Ya’yansa Hasan da Husaini jikokin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne; kuma su ne shugabannin samarin aljanna, sun can-canci halifanci.

    Bayan haka, ga kuma Imamus Suyuti wanda kowa ya yarda da shi, saboda ɗimbin iliminsa da tsoron Allah.

    Imam Jalaluddin Assuyuɗi (A.H.S 849 Y.M.S. 911)

    Imamus Suyuti Rahimahullahu ya ce; yana daga munanan bidi’o’i abinda wasu yan bidi’a suke aikatawa ranar ashura na ƙin shan ruwa; da nuna ɓacin rai da nuna alhini, abubuwan da Allah bai shari’anta su ba. Haka ma Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), ko wani daga magabata ko a cikin Ahlul Baiti, ko a waninsu; saboda kisan Husaini (Radiyallahu Anhu) wata musiba ta faru tuntuni kuma ta wuce.

    Kuma abinda ya wajaba shi ne a karɓeta da faɗin; “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” da kyakkyawan haƙuri kamar sauran musibu; amma ba a nuna raki da azabtar da kai ba, da yaɗa labaran ƙarya; da cin mutuncin sahabbai waɗanda ba su ji ba ba su gani ha, kamar dai yadda ‘yan bidi’a suke yi.

    Ibn Majah ya rawaito daga shi kansa Husaini ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma) ya ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce; “duk wanda ya tuna wata musiba da ta same shi, (sai ya sake mai-maita) “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’ un”; Allah zai ba shi lada kamar a lokacin musibar ta faru komai daɗewa kuwa da ta yi da faruwa”.

    Amma ɗaukar ranar ashura a matsayin ranar makoki da ɓacin rai; wannan sam ba musulunci ba ne ya mafi kusa da maguzanci. Kuma su masu yin wannan bidi’ar suna yi wa kansu asarar lada da falalar da ke cikin yin azumin wannan ranar.

    Waɗansu kuma sai suka ƙirƙiri bidi’o’i saɓanin na waɗancan su ne na yin wanka, da ƙunshi; da sanya kwalli da gaggaisawa da juna, wannan munanan bidi’o’i da aka gina su kan wani hadisi na ƙarya. Abinda kawai ya tabbata a sunna shi ne a yi azumi a ranar. Hadisin da aka rawaito wanda yake bayanin falalar yalwatawa iyali ranar ashura rarraunan hadisi ne.

    Tana yiwuwa masu wuce iyaka wurin girmama ranar ashura; suna yin haka ne domin ƙalubalantar ‘yan shi’a to yin hakan dai ba dai-dai ba ne; saboda shi shaiɗan burinsa dai ya ga ya ɓatar da mutum ta kowane hali. Ya kamata dai ‘yan bidi’a su guji bidi’a kawai ba wata Magana”.

    Ya ɗan uwana mai neman gaskiya; ka dubi wannan hadisi mai girma wanda shi da kansa Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu) ya rawaito shi daga kakansa. Ka ga duk masoyinsa mai goyon bayansa ya wajaba ya yi aiki da shi ta hanyar faɗin; “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” a duk lokacin da ya tuna da shahadarsa a Karbala illa iyaka; ba wai ya yi ihu da zage-zage ba. Allah ka ganar da mu.

    Shin mai imamai suka ce?

    A wannan gaɓa ina so mu yi nazarin maganganun da suka fito kai tsaye daga bakin shugabannin Ahul Baiti; waɗanda ake cewa saboda su ne ake yin ibadu da bukukuwan ashura domin mu tantance tsakuwa da tsaba; mu san gaskiyar addinin da suka koyar da kuma saɓaninsa.

    Da farko bari mu fara da shi kansa Imamu Husainni (Radiyallahu Anhu); mu ji wasiyyar da ya yi wa ‘yar uwarsa Zainab (Radiyallahu Anha) dab da zai yi shahada:

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasiyyar Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    • Dankali
    • Nama
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Maggi
    • Gishiri
    • Man gyaɗa
    • Fulawa ko garin busashen buredi

    *YADDA AKE HAƊAWA*

    Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan ya yi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba. Sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa ya yi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga, sai ki ɗauko ƙwai ɗanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busasshen buredi a ciki, ki sa gishiri da maggi ki juya sosai. ki ɗauki farantin suya ki zuba man gyaɗa ki ɗora a kan wuta ki dinga ɗiba kina zuba wa a cikin man gyaɗa mai zafi idan ya soyu za ki ga ya yi brown sai ki kwashe. Ki yi wa Oga ya yi breakfast da shi.

    ƘOSAN DANKALI 

    *KAYAN BUKATA*

    • Dankalin turawa
    • Nama
    • Fulawa
    • Kwai
    • Albasa
    • Attarugu
    • Gishiri
    • Maggi
    • Man gyada

    *YADDA AKE YI*

    Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ɗauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki haɗa da sauran kayan haɗin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan ƙwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyaɗa mai zafi ki soya, akwai daɗi matuƙa…

    Don karanta Yadda Ake Plantain Pie danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi

    Abubuwan da ake bukata

    • Fulawa   2cups
    • Bota  1/2cup
    • Baking powder 1tspn
    • Icing sugar 1,1/2
    • Gishiri 1tspn
    • Milk 1tspn

    Yadda ake haɗawa

    A tankaɗe fulawa a kwano daban.

    Sai a zuba mata icing sugar a ciki.

    Sannan a zuba gishiri da baking powder a ciki.

    Sai  a zuba bota a ciki a juya su har sai sun haɗe jikin su.

    Sai a zuba madara a kai a cigaba da cakuɗa su har sai sun haɗe jikin su.

    Sai a sa a kan faranti a bubbuɗa shi.

    Sannan a kawo abu mai faɗi amman rawun dai-dai girman da ake so.

    Domin karanta yadda ake yogurt ko ice cream custard danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hucewar Zazzaɓi (HERPES SIMPLEX)

    Hucewar Zazzaɓi (HERPES SIMPLEX)

    Hucewar zazzaɓi ko kuma wucewar zazzɓi ana kiranta “fever blisters” ko “cold sore” a likitance. Fever blisters wasu ‘yan ƙananan ƙuraje ne a cure a wuri ɗaya kuma suna gundar ruwa. Suna fitowa a gefen baki ne. Wasu ƙwayoyin cuta da ake kira herpes simplex virus (HSV) ne suke haddasa shi. Virus ɗin sun rabu gida biyu:

    1. Herpes simplex virus type 1 shi ne wanda yake haddasa fitowar hucewar zazzaɓi a baki, kuma ana iya ɗaukarsa ta hanyar sumba (kiss).

    2. Herpes simplex virus type 2 shi ne wanda yake haddasa fitowar hucewar zazzaɓi a al’aura, kuma yana ɗaya daga cikin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i (sexually transmitted diseases).

    Herpes simplex virus type 1 da type 2 sukan warkar da kansu ba sai an yi amfani da magani ba. Amma idan abin ya ta’azzara, to, sai a tuntuɓi likita domin ɗaukar matakin da ya dace.

    Bincike ya nuna cewa akwai ƙwayoyin herpes simplex virus type 1 a cikin bakin mutum, sai dai ba su da wani tasiri (inactive). Amma a lokacin da mutum ya yi fama da wata jinya kamar zazzaɓi ko mura, to, garkuwar jikinsa za ta yi rauni. Daga nan fever blisters za su iya fito masa.

    Amma ya kamata mu fahimci cewa abubuwan da suke sanya fever blisters sun bambanta daga mutum zuwa mutum, kamar haka:

    1. Raunin garkuwar jiki (weak body immune system) ko da kuwa a zahiri mutum bai ji alamar wata rashin lafiya ba. A lokacin da garkuwar jikinsa take da ƙarfi, takan yaƙi dukkan wasu ƙwayoyin cuta. Amma idan ta yi rauni saboda kamuwa da wata rashin lafiya, kamar mura ko zazzaɓi, to, herpes simplex zai iya tasowa. Shi yasa ma ake kiransa hucewar zazzaɓi.

    2. Sauye-sauyen zubar sinadarai (hormonal changes). Mace, takan fuskanci sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a lokacin al’ada, ko saka ƙwan haihuwa, juna biyu, ko shayarwa. Sa’annan idan mace tana fama da matsalar kumburin jakar ƙwan haihuwa (polycystic ovarian syndrome – PCOS) za ta fuskanci sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai a cikin jikinta. A waɗannan lokutan, za ta iya fuskantar herpes simplex. Shi kuwa namiji, zai iya samun herpes simplex ne idan ya sami sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran testosterone, ko cortisol, ko thyroid.

    3. Yanayin muhalli (environmental factors), yana iya tayar da herpes simplex, kamar tsananin zafin bazara, ko tsananin sanyin hunturu. Sa’annan gurɓacewar yanayin muhalli da ƙwayoyin cuta, ko ƙura duk suna iya tayar da shi.

    4. Gajiya (fatigue), sakamakon yin ayyukan wahala, ko rashin barci zai iya rage ƙarfin garkuwar jiki, kuma ya bayar da damar tasowar herpes simplex.

    5. Damuwa (stress), sakamakon matsalolin tattalin arziƙi, ko rashin zaman lafiya da iyali, ko rashin wani muhimmin abu a rayuwa duk za su iya haddasa raunin garkuwar jiki da kuma tasowar herpes simplex.

    6. Laulayin magunguna (side effect of drugs), domin wasu magungunan suna iya jirkita daidaiton zubar ruwan sinadaran jiki kuma su raunana ƙarfin garkuwar jiki. Daga nan sai herpes simplex ya taso. Misalinsu shi ne magungunan hana kumburi (corticosteroids) kamar prednisone da methotrexate, ko magungunan cutar cancer (chemotherapy drugs) kamar cyclophosphamide da doxorubicin da methotrexate, ko magungunan kashe cututtuka (antibiotics) kamar tetracyclines, ko magungunan dashen sassan jiki (antirejection drugs for transplant) kamar cyclosporine da tacrolimus.

    Babban maganin fever blisters shi ne mutum ya yi ƙoƙarin lura da abubuwan da idan suka same shi suke haifar masa da su, domin kauce musu.
    Danna nan don karanta Fitowar Haƙora Ga Yara, Faɗuwarsu Da Sake Fitowarsu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Tasbihi

    Falalar Tasbihi

    Hadisai da yawa sun bayyana ɗimbin falala da darajar tasbihi kamar haka:

    Ladan tasbihi da Alhamdulillahi yana cika tsakanin sama da ƙasa, Tasbihi yana kankare zunubai; tasbihi yana daidai da yin kalmomi, ladan tasbihi ya fi duniya da abinda yake cikinta; tasbihi kalmomi ne da Allah yake matuƙar ƙaunarsu, da sauran darajoji masu tarin yawa.

    An karɓo daga juwairiyya Haris (Radiyallahu Anha) ta ce; “Wata rana Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fita daga wurinta bayan sallar asuba; ya bar ta a zaune a wurin da ta yi salla, da ya dawo da hantsi ya tarar da ita tana nan dai a zaune; sai ya ce har yanzu kina nan a yadda na barki, ta ce na’am. Sai ya ce bayanki na faɗi waɗansu kalmomi huɗu da za a auna su da gaba ɗayan abinda kika faɗa yau sai su rinjaye su, su ne:

    “Subhanallahi wa bi hamdihi, adada khalƙihi wa rida a nafsihi wa zinata arshihi wa midada kalimatihi” (Muslim 2726).

    An karɓo daga Samarata Ibn Jundab (Radiyallahu Anhu) yace: “Abubuwa haɗu su ne zancen da Allah ya fi so, za ka iya farawa da kowanne daga cikinsu:

    “Subhanallah, Walhamdu Lillah, Wa La Ilahaillallah, Allahu Akbar” (Ibn Majah 3811)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Istigfari Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sujjadar Godiya Ga Allah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar La Ilaha Illallahu

    Falalar La Ilaha Illallahu

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Wanda zai fi kowa azurta da samun ceto na ranar ƙiyama, shi ne wanda ya faɗi “La ilaha illallahu” dan Allah (Bukhari: 99).

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “wanda ya ce:

    “La’ilaha illalahu wahdahu laa sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’ in ƙadirun” sau ɗari (100) a yini guda.

    Za a ba shi ladan ‘yanta bayi goma, za a rubuta masa lada ɗari, za a shafe masa zunubai ɗari, zai sami kariya daga shaiɗan a wannan yini har yamma, kuma babu wanda zai zo da wani abu da ya fi abinda ya zo da shi sai dai wanda ya aikata fiye da wannann. Kuma wanda ya ce:

    “Subhanallahi wa bi hamidihi” sau ɗari a yini guda.

    Za a zubar da zunubansa ko da yawansu ya kai kumfar teku. (Bukhari 3293, Muslim 2691)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Tasbihi Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Sallatut Tasbihi danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Istigfari

    Falalar Istigfari

    Istigfari shi ne neman gafarar Allah Ta’ala da yafiya bisa zunuban da mutum yake aikatawa.

    Istigfari ko tuba ba ya zama karɓaɓɓe sai ya cika sharaɗai huɗu:

    1- Yin nadama da baƙin ciki a kan zunubin da mutum ya aikata ko yake aikatawa.

    2- Niyyar barin zunubin.

    3- Barin zunubin nan take.

    4- Mayarwa da mai haƙƙi haƙƙinsa, ko neman yafewarsa, in zunubin ya shafi haƙƙin wani a dukiyarsa, ko mutuncinsa, ko jikinsa.

    Kaɗan Daga Cikin Amfanin Yawaita Istigfari:

    1- Istigfari hanya ce shahararriya zuwa aljanna.

    2- Istigfari yana shafe zunubai.

    3- Istigfari yana sa Allah ya saukar da albarka ruwa da abinci da ‘ya’ ya da daukiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Shugaban Istigfari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Haƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Falalar Zikiri Ya Ke

    Yadda Falalar Zikiri Ya Ke

    Zikiri shi ne ambaton Allah Ta’ala da kalmomin yabo da kirari da girmamawa da godiya; bisa ni’imominsa tare da nutsuwa da ƙasƙantar da kai da nuna gajiyawa; da ƙwadayin rahamarsa da neman tsari daga azabarsa.

    Zikiri kalma ce mai faɗi wacce ta ƙunshi ambaton Allah da harshe da biyayya a gare shi da gaɓoɓi; da kuma sanya Allah Ta’ala a cikin zuciya ta hanyar tunani kan ni’imominsa da falalarsa ga bayinsa da ƙoƙararin fahimtar hukunce- hukuncen addininsa da ma’anonin littafinsa.

    A kan haka za mu fahimci zikiri yana da nau’o’i daban-daban wanda ya ƙunshi karatun alƙur’ani, ibadu; zikiran safe da yamma, zikiran lokuta da halaye daban-daban, karatun ilimin addinin musulunci; da kuma dukkanin wani nau’i na zikiran harshe kamar hailala, salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) Istigfari, Tasbihi, lahaula wala kuwwata illa billahi da sauransu.

    Zikiri yana da falala mai ɗimbin yawa, ga kaɗan daga cikin irin waɗannan falala da darajoji:

    1- Allah Ta’ala yana yabon masu zikiri a cikn mala’iku.

    2- Allah Ta’ala Mala’ikunsa suna yin salati ga masu yin zikiri.

    3- Allah yana gafarta zunuban masu zikiri

    4- Mai yawan zikiri yana samun taimakon Allah.

    5- Zikiri yana sanya nutsuwa da sanyin rai ga mai yinsa.

    6- Zikiri yana raya zukata.

    7- zikiri yana sanya mutum ya samu kariya da ga wasiwasin shaiɗanu.

    8- Zikiri yana sanya a samu alkhairin duniya da lahira.

    9- A cikin kowacce ibada akwai zikiri.

    10- Allah yana sanya kwarjini da farin jini ga mai zikiri.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikirin Tashi Daga Majalisa Yake danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; Wanda Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Suratul Tabarakallazi Biyadihil Mulku

    Falalar Suratul Tabarakallazi Biyadihil Mulku

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: haƙiƙa wata sura a cikin Alƙur’ani mai ayoyin talatatin ta ceci wani mutum har sai da aka gafarta masa, ita ce:-

    “Tabarakallazi biyadihi mulku” (Abu Dawud, Tirmizi, Nisa’I Ibn Majah, Sahihul Jami’i 2091).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Sallar Tuba Da Falalarta danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Ayoyi Goma Na Farko Ko Ƙarshen Suratul Kahfi

    Falalar Ayoyi Goma Na Farko Ko Ƙarshen Suratul Kahfi

    An karɓo daga Abu Darda’i (Radiyallahu Anhu)

    Haƙiƙa Annabin Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: “Wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahafi, Za a kare shi daga Dujal” (Muslim 809) A wata ruwayar ayoyin goma na Ƙarshen suratul kahfi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Suratul Tabarakallazi Biyadihil Mulku Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’o’in Ɗawafi danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu