Tag: yadda ake

  • Mutuwar Mata Masu Jego

    Mutuwar Mata Masu Jego

    Duk mai jegon da bayan haihuwa ko da da kwana 1 ne ballantana a ce an kwana uku da haihuwa ta ji alamun zazzaɓi, ko ciwon kai, ko ciwon ƙirji da sauransu. Toh lallai ta sanar a hanzarta kai ta asibiti kar a kuskura! ina maimaitawa kar a kuskura! a ce ai ba komi ta sha paracetamol ko a ce za a nemo Maganin ulcer kurum a ba ta babu komi. Hakan tamkar tallafawa me ƙoƙarin kashe kai ne.

    Sau tari a yanzu akan zo taron suna me jego ba lafiya sosai, amma tai ta juriyar banza saboda cutar da kai, alhalin ƙwayoyin cuta sun sami hanya ta dalilin jinin nifasi da ke fita sun shiga cikin jijiyoyin jininta suna haifar matan da puerperal fever da zai kai ta ga “Puerperal sepsis” yai ta cinta a jika tana zaton abu ne da zai zo ya shige ƙarshe sai gawa.

    Galibi wannan shi ke kashe masu jego in kika cire batun zubar jini bayan haihuwa, musamman bayan kwana 3 da haihuwa zazzaɓin ya fi somawa domin incubation period ɗin kenan na ƙwayoyin cutar, shi yasa wata sai bayan an yi taron suna ana murna kurum a ji an wayi gari wance ta mutu, mutuwa me duka.

    Kada a taɓa ɗaukar hakan da wasa, ko baka da kuɗi ranto ka kai ta asibiti, matuƙar me jego tace ba ta lafiya ƙasa da kwana 40 da haihuwa kar ai wasa.

    Ku kuma ƙananun jami’an lafiya da ke bibiyar rubutuna kodayaushe ku sa wannan cikin kanku, kar me jego tace:-

    – Tanajin kasala,
    – Kanta na ciwo
    – Zazzaɓi
    – Fitar farin ruwa ko jini me ɗoyi
    – Ciwon Mara
    – Zafin fitsari
    – Ko har yau girman cikinta yana nan da sauransa kamar ba ta haihu ba ko kamar da sauran jariri a ciki

    Ku ce za ku ba ta maganin rage zugi kurum ku sallame ta, ko kuwa ku ce za ku yi gwajin Malaria don haka in ya nuna Negative sai dai ku ba ta pain reliever, ko kuma in aka yi kiciɓis ga Malaria positive ku ce iya Malaria ke damunta.

    Kuke buɗe tunaninku sosai for differentials diagnosis, kada a ce komai in ya haɗu da ciwon kai kurum Malaria ko Bp, ko Typhoid ne, duk macen da kuka ji ta yi muku ƙorafin ɗaya ko biyu daga waɗancan alamun na sama kai tsaye ku yi treating ɗinta for puerperal infection muddin me jego ce, domin hakan na da alaƙa da haihuwarta. Mai jego ita ce wadda ba ta wuce kwana 42 da haihuwa ba. Don haka ko da ta yi wata da haihuwa duk da haka tana cikin hatsari har na zubar jini.

    Ya rage naku ku je ku yi biyayya ga manyanku da kuke aiki ƙarƙashinsu, su ilmantar da ku magungunan da alluran da ake amfani da su wajen addressing din matsalar, don ba kowanne antibiotics ake ba su ba, in su ma ba su sani ba toh ku je sahihan journals na obstetrics and gynecology ku yi binkice ku ilmantar da kanku ba wai google ba. Wannan lamari ne da kan zamo Medical Emergency.

    Wannan tasa ko ɓari mace ta yi sai an ba ta magungunan antibiotics, haka ma bayan haihuwa domin riga-kafi koda ƙwayoyin cutar sun maƙale to zai magance su kafin su yi ƙarfin da za su shiga jini tunda ido bai iya ganinsu. AMMA wasu marasa tunanin cikin mata ba sa sha, ko in sun fara sai su bar sha tun kafin ya ƙare, toh masu irin wannan ku kuka da kanku, Domin ba zubar jini ne kurum abin tsoro ba bayan haihuwa.

    In muka kiyaye wannan za mu taimaka wajen rage wasu mace-macen na masu haihuwa.

    Allah yasa mu dace.

    Danna nan don karanta Rashin Kogon Al’aura Ga Mata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Sumbatar Mace Ga Me Azumi

    Sumbatar Mace Ga Me Azumi

    Babu laifi ga me azumi ya sumbaci matarsa matuƙar ya tabbatar zai iya kuɓuta daga faɗa mata, amma nisantar sumbatar mace ga me azumi shi ne ya fi alheri, amma annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla) ya kasance yana sumbatar iyalansa kamar yadda waɗannan Hadisai suka nuna haka:

    حدثنى مالك عن هشام بن عروة عن أبيه عن عا ئشة أم المومنين رضي الله عنها قالت ” أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يصب بعض أزواجه وهوصائم ثم  ضحهكت “

    An ruwaito daga Malik daga Hashim bin Urwata (shima) daga mahaifinsa daga Nana Aisha Uwar Muminai (R.A) itace tace “Tabbas Manzan Allah (S.A.W ya kasance yana sumbatar sashin matayansa sai ya yi murmushi”

    Saboda haka idan annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla) yana ɗakin ɗaya daga cikin matayensa guda tara ko goma sha ɗaya ko kuma goma uku ko goma sha biyar, yana sumbatar matarsa kuma a cikin watan Ramadan.

    Haka ma a cikin wani Hadisin ko a cikin littafan Risala na sheikh Muhammad Al-akhdhari wani yace  “Annabi yana sumbatar matarsa, sannan sai ya tafi masallaci, To a nan ka ga babu laifi ga wanda ya yi alwala ya sumbaci matarsa, sai dai nisantar aikata hakan shi ne ya fi alheri a gare shi, saboda komai zai iya faruwa.

    Akwai dalilai masu tarin yawa, wanda yasa addinin musuluncin ya nuna mana mahimmacin sumbatar mace, haka kuma hadisai da yawa haɗi da litittafai masu yawa sun kawo annabi ya kasance yana sumbatar matayensa, ita sumbatar mace, tana ƙara so da shaƙuwa a tsakanin ma’aurata ta yadda ba ka tunani haɗi da samun nutsuwa mai ɗorewa a cikin  zukatansu.

    حدثنى مالك عن يحي بن سعيد: أن عاتكة إبنة زيد بن عمر بن نفيل إمرأة عمر بن الخطاب,كانت تقبل رأس عمر بن الخطاب وهو صائم, فلاينهاها.

    An ruwaito daga Malik daga Yahaya bin Sa’idu (yace), haƙiƙa Atika ‘yar Zaidu bin Umar bin khaɗɗab ta kasance tana sumbatar kan (Sayyadina) Umar bin Khaɗɗab shi kuma (a lokacin) yana azumi bai hana ta ba.

    حدثنى مالك عن أبى نضر مولى عمر بن عبيد الله, أن عائشة بنت طلهة أخبرته : أنها كانت عند عائشة زوج النبي صلى الله عليه وسلم فدخل عليها زوجهاهنالك وهو عبدالله بن عبدالرحمن بن أبى بكر الصديق وهوصائم,قالت له عائشة :ما يمنعك أن تدنوا من أهلك فتقبلها وتلاعبها:أقبلها وأنا صائم قالت :نعم.

    An ruwaito daga Malik daga Abi-Nahir  ya yi wa Umar bin Ubaidullah hidima (yace), haƙiƙa Aisha yar Ɗalhatu ta ba shi labarin ita ta kasance a gurin Nana Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasallam) sai mijnta ya shiga gurinta (Nana Aisha) shi ne Abdullah bin Abudulrahman bin Abubakar Sadik a lokacin yana azumi, sai Aisha tace da shi, mai ya hana ku kusantar iyalanku, sannan ku sumbace su da wasa da  su? (sai mijin na ta) yace, na sumbace ta kuma ina azumi? (sai Nana Aisha) tace eh.

    Ka ga a nan ma babu wani laifi ga me azumi ya sumbaci matarsa ,kamar yadda sayyada Aisha ta yi wa wannan bawan Allah bayani, shi kuma sai maganar ta ba shi mamaki, saboda ya ga yana azumi daga ƙarshe tace ba komai , zai iya sumbatar matarsa haɗi da wasa da ita, amma idan ya san zai kubuta daga afka mata, Saboda kaffara azumi haɗi da ramuwa za su iya shiga ciki, matuƙar ya sadu da ita kamar yadda mu ka yi bayani a baya.

    حدثنى مالك عن زيد بن أسلم: أن أبا هريرة و سعد بن أبى وقاص كانا يرخصان فى القبلة للصائم.

    An ruwaito daga Malik daga Zaidu bin Assalama (yace), Lalle Abu-huraira da Sa’adu bin Abu-waƙas, sun kasance suna sauƙaƙawa game da sumbatar mai azumi.

    Saboda haka suna sauƙaƙawa ga mai azumi zai iya sumbatar matarsa, idan zai iya kuɓuta daga ganawa da ita, amma nisantar daga hakan shi ne yafi alheri kamar yadda wannan hadisin na annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ya nuna mana hakan.

    حدثنى يحي عن مالك أنه بلغ عليه, أن عائشة زوج النبي صلى الله عليه وسلم كانت إذا ذكرت أن رسول لله صلى الله عليه وسلم  يقبل وهو صائم نقول:أيكم أملك لنفسه من رسول لله صلى الله عليه وسلم.

    An ruwaito daga Yahaya daga Malik, haƙiƙa labari ya same shi, tabbas Nana Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ta kasance tana ambata mana haka, haƙiƙa manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana  sumbatar iyalansa, idan yana azumi, sannan kuma tana cewa; Na hane ku (da aikata haka, saboda shi annabi) ya mallaki zuciyar sa (Sallallahu alaihi wasalla), daga afkawa matayensa a wannan lokaci.

    Amma Urwata bin Zubair yana cewa shi bai ga komai ba a kan yin sumbatar mace,  sai alheri.

    حدثنى مالك عن زيد بن أسلم عن ألطاء بن ياسرأن عبدالله بن عباس سئل عن القبلة للصائم,فارخص للشيخ وكرها للشاب.

    An ruwaito daga Malik daga Zaidu bin Asalama daga Aɗɗa’u bin Yasir: Tabbas Abdullah bin Abbas an tambaye shi game da sumbata game azumi (sai yace) an sauƙaƙa a cikin sa ga tsoho, sannan kuma an hana aikata haka ga saurayi.

    Saboda a tunanin shi tsoho, zai iya kame sha’awarsa a wannan lokaci , sannan kuma sha’awarsa ta fara ƙasa, amma shi saurayi, yanzu ne sha’awarsa (take hau hawa da wuya ya iya kubuta da ka aikatawa haka, saboda haka ne ma za ka ga samari ba sa yin aure a cikin watan Ramadan).

    حدثنى مالك عن نافع أن عبيدالله بن عمر كان ينهى عن القبلة والمبا شرة للصائم

    An ruwaito daga Malik daga Nafi’u haƙiƙa Ubaidullah bin Umar ya kasance yana hana yin sumbata da runguma ga me azumi.

    Saboda yin sumbata (Kiss) haɗi da runguma, yana iya kawo fitar maniyyi, sannan kuma komai zai iya faruwa a tsakanin su, musamman ga saurayi da sauransu.

    Don karanta Sallar Idi danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Sallar Idi

    Sallar Idi

    Idin musulmi guda biyu ne, idin buɗa baki (karamar sallah), bayan watan Ramadan, da idin layya (Babbar sallah) bayan ranar Arfah. Allah Maɗaukakin Sarki ya canza mana da su daga idikan jahiliyya da ma duk wani idi ƙirƙirarre.

    An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya yarda da shi)ya ce, Mutanen jahiliyya suna da kwana biyu a shekara da suke wasa a cikinsu, yayin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya zo Madinah, sai ya ce, “Kuna da kwana biyu da kuke wasa a cikinsu, kuma haƙiƙa Allah ya sauya musu da waɗanda suka fi su alheri, idin buɗa baki, da idin layya” (Nisa’i ne ya rawaito shi).

    Ba ya halatta a yi tarayya da kafirai a cikin idinsu, saboda idi shi ne babbar alamar kowane addini ta fili, da tsarinsa. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, “Kada ka bi son zuciyarsu wajen barin abin da ya zo maka na gaskiya, kowanne daga cikinku mun sanya masa shari’arsa da tsarinsa” (Suratul Ma’ida aya ta 48).

    Idi a musulunci ya haɗa wasu ibadu da bayyana farin ciki da cin abubuwa daɗaɗa na halal, saboda haka waɗannan kwanaki suka zama kwanakin farin ciki da na jin daɗi, da ci da sha. Ba ya halatta a haɗa idi da abin da ya saɓawa koyarwar musulunci. Misali kamar cakuɗuwar maza da mata, ko tozarta lokutan salloli, ko shan abin da aka haramta, ko wasa da abin da Allah ya haramta, ko jin abin da Allah ya haramta, ko wanin haka daga cikin abubuwan haramun.

    Hukuncin Sallar Idi Biyu

    Sallar idi nafila ce, kuma abar kwaɗayi ne a kan kowane musulmi ya himmatu wajen zuwa idi, saboda ana samun lada mai tarin yawa sosai gami da gafarar Allah (S.W.A). Sannan kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi umarni da maza da mata su fita zuwa sallar idi, sannan kuma a sadar da zumunta gami da rarraba abinci da abin sha ga mabuƙata.

    Yadda Ake Sallar Idi Biyu

    Sallar idi raka’a biyu ce, ba a kiran sallah, ba a yin iƙama, ana bayyana karatu a cikinsu, ga yadda ake yin su :

    1. Raka’ar farko zai yi kabbara bakwai, bayan ya yi kabbarar harama, sai ya yi addu’ar buɗe sallah, kafin ya fara karatu. Amma a mazahabar Imamu Malik bin Anas, an ware wasu surori, wanda ake buƙata ya karanta a raka’a ta farko kamar Suratul A’ala, ko Suratul Ƙamar.

    2. Idan ya kammala raka’a ta farko, to a raka’a ta biyu, da zarar ya miƙe tsaye, zai yi kabbarta sau biyar ne, sai ya karanta Fatiha da wata surar. Ita ma a raka’a ta biyu a mazahabar Imamu Malik bin Anas an ware wasu surori da ake buƙatar a karanta su; Suratul Ghashiyati ko Suratul Kahfi, ko Suratul Shamsi da sauransu.

    Saboda haka, idan mutum ya duba da kyau, zai ga an yi kabbarori guda goma sha uku, duk da kabbarar harama. Sannan ita sallar idi, ba a yi mata nafila, saboda ita ma nafila ce. Haka kuma sallar idi sai an gama ta tsaf, sannan liman zai ta shi ya yi huɗuba, wanda sauraron huɗuban liman, Allah yana cewa da Mala’iku “Ku shaida dukkanin wanda ya tsaye a wannan wajen, na gafarta masa dukkanin zunubansa”.

    Wurin Da Ake Sallar Idi Biyu

    A sunna dai, shi ne a yi sallar idi a filin sallah, ba a cikin  masallaci ba, wato ita sallar idi ba a so a yi ta a inda yake da rufi, a fili fayau ake buƙatar a yi ta, amma idan  akwai buƙatar haka, wato ruwan sama ya cike inda za a yi sallar, ko kuma ruwan sama ya hana a yi sallar, ko sanyi ya tsananta, ko dai wani abu wanda shari’a ta amince da shi, sai ayi ta kawai a cikin masallacin Juma’a.

    Abubuwan Da Ake So A Idi

    1. Maza su yi ado da kyawawan kayansu, mata kuwa su fita sallah ba tare da ado da turare ba.

    2. Mutane su fito masallaci da wuri.

    3. Canza hanyar tafiya, wato idan mutum ya bi ta wata hanya a lokacin da zai tafi masallaci, to idan zai dawo sai ya canza wata hanyar.

    4. Yawaita kabbara tun daga gida har zuwa masallacin.

    5. Cin dabino kafin a yi sallar idi ƙarama, da kuma cin dabino bayan an yi sallar idi babba (dabino guda uku ko biyar ko bakwai).

    6. An so a jinkirta sallar idi ƙarama, don musulmi ya samu damar bayar da zakkar fidda kai, ga waɗanda ba su gama bayarwa ba.

    Hukunce-hukuncen Idi

    1. An karhanta sallar nafila kafin sallar idi da bayanta, sai dai in a masallaci za a yi ta, to sai a yi gaisuwar masallaci idan an shiga.

    2. Sunna ne idan sallar idi ta wuce, ko wani ɓangarenta ya kubce wa mutum, ya rama ta kamar yadda take, ya sallace ta raka’a biyu da kabbarorinta, haka ma abin da ya rasa daga cikinta ya rama shi kamar yadda take.

    3. Allah Maɗaukakin Sarki ya shara’antawa bayinSa, a ƙarshen Ramadan su yi masa kabbara, Allah ya ce, “Don ku cika adadin kwanakin (azumi), kuma don ku yi wa Allah kabbara a kan abin da ya shiryar da ku”. (Suratul Baƙara yaya 185). Ma’anar ku yi wa Allah kabbara shi ne, ku girmama shi a cikin zukatanku da harsunanku.

    Lafazin kabbarar shi ne : “Allahu Akbarul Lahu Akbar, La’ilaha Illal Lahu, Wal Lahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamdu”.

    4. Sunna ne maza su ɗaga muryarsu da mata kuwa za su ɓoye ta (ƙasa-ƙasa), a lokacin da suke yi waɗancan kabbarorin.

    5. Za a dinga yin waɗancan kabbarorin ne tun daga lokacin da aka ce an ga watan Shauwal (gama azumi) har zuwa lokacin da liman zai shigo masallaci, don yin sallar idi ƙarama, amma kuma idan a sallar idi babba ne, to mutum zai wuce da yin waɗancan kabbarorin ne har zuwa rana ta ukun bayan sallar idi, saboda ana so mutum ya yi waɗancan kabbarorin a gurbin kowace sallah ta ranar idi babba, wanda zai fara tun daga sallar azahar ɗin ranar har zuwa asubahin rana ta uku ga sallah, wanda idan mutum ya lissafa da kyau, zai ga an samu salloli goma sha biyar ke nan.

    Abin Da Ya Kamata Musulmi Ya Yi Ranar Idi

    1. Samun sallar asubar ranar Idi.

    2. Wankan zuwa Idi.

    3. Ba da zakkar fidda-kai ga mabuƙata.

    4. Cin abinci kafin tafiya masallaci (ga ƙaramar sallah, babba kuma sai an dawo).

    5. Sanya tufafi masu kyau.

    6. Takawa zuwa masallaci.

    7. Zikiri yayin tafiya.

    8. Ba a sallar nafila a filin idi.

    9. Sauraron huɗuba bayan sallar idi.

    10. Gaisawa da juna bayan sallah.

    11. Sauya hanyar tafiya wajen dawowa.

    12. Yara da mata da tsoffi duka na zuwa idi.

    13. Mata masu haila za su iya zuwa sallah, amma za su tsaya a gefen guda na masallaci.

    14. Ana son musulmi su yi wa junansu murnar idi.

    15. Ana son bayyana farin ciki da idi, da yi wa`yan uwa da masoya da makusanta murna.

    16. Idi wata dama ce da ya wajaba a ribace ta, don sada zumuncin da aka yanke, da sulhuntawa a tsakanin masu husuma.

    17. Ba shara’anta ziyarar maƙabarta ba a ranar idi, don hakan ya saɓawa farin cikin da annushuwa cikin idi.

    18. An shara’anta yalwatawa iyali da tufafi da abinci da kayan cin daɗi, waɗanda Allah ya halatta, a ranar idi, saboda idi kwanaki ne na farin ciki da annushuwa.

    Domin karanta Addu’ar Daren Lailatul Ƙadri danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Buɗe Sallah 2

    Addu’ar Buɗe Sallah 2

    Addu’ar buɗe salla (watau bayan anyi kabbarar harama) 2

    سُبحانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ وَتَبارَكَ اسْمُكَ وَتَعَالَى جَدُّكَ وَلا إِلهَ غَيْرُكَ.

    Subhanakal-lahumma wabihamdika watabarakas-muka wata’ala jadduka wala ilaha ghayruk.

    Tsarki ya tabbata gareKa, Ya Allah, tare da yabo gareka; Albarkatun sunanka sun yawaita; mulkinka da girmanka sun ɗaukaka; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.

    Danna nan don karanta Addu’ar Buɗe Sallah

    Edita@rumasau-kallamu

  • Rubutacciyar Fassarar Huɗubar Idin Ƙaramar Sallah (Eid Kabir) Daga Masallaci mai Alfarma

    Rubutacciyar Fassarar Huɗubar Idin Ƙaramar Sallah (Eid Kabir) Daga Masallaci mai Alfarma

    Mai Huɗuba: Sheikh Dr Abdurrahman bn Abdur’aziz Sudais

    Mai Fassara: Dr Abdulkareem Tahir Abdullahi

    Transcribe: Aminu Bashir

    Shugaban Shashi: Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Huɗuba ta farko:

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Maka – ya Ubangijina – kuma muna neman taimakonKa da gafararKa, muna tuba gare Ka, kuma muna yaba Maka da dukkan alheri.

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar Kabiran, walhamdu lillahi kasiran, wa subhanallahi bukratan wa asilan.

    Allah Shi ne Mafi girma, kuma dukkan yabo mai daɗin furtawa da kyawu naSa ne, Allah Shi ne Mafi girmam muddin zukatan masu kaɗaitawa za su ambace Shi kuma su Masa tasbihi mai tsawo.

    Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ya shar’anta mana lokuta masu daraja da bukukuwan idi, don tabbatar da amfani ga bayi a duniya da lahira, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma ManzonSa, mafi alherin bayi kuma mafi darajan masu bauta, Allah Ya masa salati, shi da Alayensa, da Sahabbansa, da Tabi’ai, da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa, kuma Ya masa sallama mai yawa har zuwa ranar sakamako.

    Bayan haka:

    Ku kiyaye dokokin Allah – ya ku bayin Allah – in kun kasance masu biɗan maƙurar ɗaukaka, da ƙololuwar rahamar shiriya, ((Kuma duk wanda ya bi Allah da ManzonSa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinSa, to, waɗannan su ne masu rabauta)).

    Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, to, zai sanya tsananinsa ya koma sauƙi, kuma Allah Zai girmama ladansa saboda taƙawa.

    Ya ku taron Musulmi na gabashin duniya da yammacinta: Shin kun san wane yini ne wannan? Shin kun san wane lokaci ne wannan? Lallai wannan lokaci ne na bikin idin ƙaramar Salla mai albarka, ina taya ku murnar idi mai albarka, kuma ina roƙon Allah Ya karɓa mana kyawawan ayyukan mu tare da ku, Ya kuma maimaita mana da shugabanninmu da ƙasashenmu da al’ummar Musulunci da alheri da yalwa da albarka.

    Ga shi Allah Ya muku ni’ima da riskar wannan yini mai daɗi, don haka ku yi farin ciki da idinku kuma ku yi murna, domin farin ciki da idi sunnar Musulmi ne, kuma alama ne daga cikin alamomin Addini, an shar’anta bayyana farin ciki da murna a bikin idi, ba bayyana baƙin ciki da damuwa ba, don haka ku yaɗa farin ciki, kuma ku bayyana murmushi, ku yaɗa jindaɗi da murna, ku kwantar da hankali, kuma ku kiyaye ƙaunar juna, don tutocin farin ciki su kaɗa a gidaje da unguwanni, da kasuwanni da hanyoyi, kuma ku kawar da dundumin baƙin ciki, ku hutar da jikkuna.

    Kuma duk wanda ya hango jindaɗi na haƙiƙa da fata da albishir da farin ciki na har abada a furuci da magana da kyakkyawar hangensa, to, wani mashaya da ya fi ruwan girgije garɗi kuma haskenshi ya fi tataccen zuma ƙyalli zai bayyana gare shi, kuma wannan mashaya ba komai ba ne face wasu gwalagwalai masu ƙyalli, daga tarihin mai kyakkyawar ɗabi’u da siffofi, mai tarin albarka, mafi alherin halittu, Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi darajan salati da mafi tsarkakar jinjina su tabbata a gare shi, wanda ya zo mana da shiriya mai haske da ƙyalli.

    Ya zo a Bukhari da Muslim, daga Uwar Muminai A’isha Allah Ya ƙara mata yarda cewa, lallai Abubakar ya shiga wajenta, alhali a tare da ita akwai kuyangu guda biyu suna rera waƙa kuma suna buga ganga, a wannan lokacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana lulluɓe cikin tufafinsa, sai Abubakar ya musu tsawa, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yaye fuskarsa, sai ya ce: (Ka ƙyale su ya Abubakar, saboda waɗannan kwanakin idi ne).

    Kuma an rawaito daga Uwar Muminai A’isha Allah Ya ƙara mata yarda ta ce: (Wallahi haƙiƙa na ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsayuwa a kan ƙofar ɗakina, alhali Habashawa suna wasa da masunsu a Masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana suturce ni da tufafinsa don na kalli wasansu, sannan sai ya tsaya don ni har sai na kai lokacin da ni da kaina zan tafi).

    Ya ku Muminai!

    A wannan yini na farinciki mai albarka, ku yalwata wa kawunanku da ‘ya’yanku, kuma ku shigar da farin ciki ga iyalanku da maƙoftanku da makusantanku, haƙiƙa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Yana daga mafi falalar aiki, shigar da farin ciki ga Mumini). Baihaƙi ne ya rawaito shi.

    Ku tsarkake zukatanku daga ƙeta da ƙullata da hassada da ƙiyayya da tsana da gaba, kuma ku karɓi uzuri, ku gyara kuskure, kuma kada ku juya wa juna baya, kada ku yi gaba, kada ku yi hassada, ku zama bayin Allah ‘yan’uwan juna.

    Idinmu mu Musulmi, idin murna da farin ciki da sada zumunci ne, ba idin yanke zumunci da ƙullata ba, ku sada zumuntanku, ku ziyarci juna, kuma ku kira wanda yake nesa da ku ta hanyar kafafen sada zumunta na zamani, wannan rana ce ta zumunci da ziyara da tausayi da sasanta juna da kau da kai, ku yafe wa wanda ya yi tuntuɓe ko kuskure, ku yi afuwa ga wanda ya yi zalunci kuma ya munana muku.

    Wannan rana ce ta ‘yan’uwantaka da haɗin kai, da curewa da dunƙulewa da tausayi, kuma waɗannan su ne alamomi da Musulunci ya ba wa muhimmanci matuƙar gaske sai ya ƙarfafa su, ya tabbatar da su kuma ya kafa su, ashe ba su ne ginshiƙan ƙarfi da tabbatawu ba bayan tauhidi da saboda shi ne aka aiko Manzanni kuma aka saukar da littaffafai, Allah Maɗaukaki ya ce: ((Ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini)).

    Kuma Maɗaukakin Sarki ya ce: ((Ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya, kada kuma ku rarrab. Kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya haɗa tsakanin zukatanku, sai kuka zamo ‘yan’uwan juna a sakamakon ni’imarsa)). Haka kuma ya kasance ne saboda abin da yake samuwa ta dalilin haɗin kai na so da ƙauna, da tunɓuke ƙeta da ƙullata.

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’laha illallah, wallahu akbar, Allahu Akbar, wa lillahilhamd.

    Ya ku Musulmi! Wannan idin Allah Ya shar’anta mana shi ne bayan ibadar azumi don mu yi farin ciki da shi bayan cikar azumi da doguwar tsayuwar dare, kuma haƙiƙa kun ba da zakkar fidda kai kuna masu son haka a zukatanku, ita kuma tsarkaka ce ga mai azumi daga maganar wargi da batsa, kuma abinci ne ga miskinai, Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Don ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da Ya yi, don ku yi godiya)).

    Kuma daga cikin shiriyarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai cewa lallai yana sanya mafi kyawun tufafi da yake da shi ranar idi, kuma ya kasance tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana fita a idin ƙaramar Salla da na layya yana mai ɗaga sautinsa da hailala da kabbara, kuma Ibnu Umar Allah Ya ƙara masa yarda ya kasance idan ya wayi gari ranar idi yana bayyana kabbara har sai ya iso filin Salla kuma liman ya zo.

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’laha illallah, Allahu akbar, Allahu Akbar, wa lillahilhamd.

    Kuma an rawaito daga Ummu Aɗɗiya Allah Ya ƙara mata yarda ta ce: (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umurce mu da mu fitar da zawarawa da ‘yan mata, da masu haila ranar idin ƙaramar Salla da ranar Sallar layya, su halarci alheri da addu’ar Musulmi). Ahmad ne ya rawaito shi a Musnadinsa.

    Allahu Akbar Kabiran!

    Wannan shi ne Addininmu tsarkakakke, kuma wannan ita ce shari’armu mai haske, shari’ar sauƙi da rahama da tsakatsakiya da daidaito Allah Ya ce: ((Kuma kamar haka ne Muka sanya ku al’umma tsakatsaki)), lallai ita ce haske mai ƙyalli da haskakawa, Ubangijin talikai Ya yi gaskiya da ya ce: ((Ba mu aiko ka ba face don ka zama rahama ga talikai)).

    Ya ku ‘yan’uwa Musulmi!

    Taya juna murnar idi yana ƙara ƙauna, da ƙarfafa soyayya, kuma an shar’anta a riƙa cewa a lokacin taya murna na idi: (Taƙabbalallahu minna wa minkum). An rawaito daga Wasilatu ɗan Asƙa’ ya ce: Na haɗu da Manzon Allah tsirda da amincin Allah su tabbata a gare shi a wata rana ta idi, sai na ce: (Taƙabbalallahu minna wa minka), sai ya ce: (Na’am, Taƙabbalallahu minni wa minka). Baihaƙi ne ya rawaito shi.

    Ya ku al’umma masu imani!

    Musulunci Addini ne na yalwa da yafiya da sassauci da sauƙi, da fahimtar juna da rayuwa tare da tattaunawa da ɗan’adamtaka, saboda haka ne hujjarsa ta bayyana, matsayinsa ya haskaka a cikin talikai, saboda ya ƙunshi maƙuran sassauci da sauƙi, da nisantar wahalarwa da tsanantawa, don haka, ku bayyana hakan ta hanyar furuci da aiki- Allah Ya kiyaye ku -, ku zama masu kira na gaskiya ta hanyar kyakkyawan furuci ((Kuma ku faɗa wa mutane magana mai kyau)), da aiki nagari, ku yaɗa fata nagari da daddaɗar kalma don koyi da Manzonku mai girma.

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana son kyakkyawan fata da daddaɗan zance, an rawaito daga Anas Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Alfa’alu yana birge ni), suka ce: Mene ne Fa’alu ya Manzon Allah? Ya ce: (Daddaɗar kalma). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

    Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan zai aiki wani sashe daga cikin Sahabbansa tare wani al’amari yana musu wasici da faɗinsa: (Ku yi albishir kada ku kori mutane, kuma yi sassauci kada ku tsananta). Muslim ne ya rawaito.

    Kuma an rawaito daga Ubayyu ɗan Ka’ab Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ka yi albishir ga wannan al’umma da ɗaukaka da matsayi da nasara da tabbatuwa a bayan ƙasa). Imamu Ahmad ne ya rawaito shi a Musnadinsa da isnadi ingantacce.

    Ya ku al’ummar Musulmi!

    Kada ku guji ayyukan ɗa’a bayan watan Ramadana, ku riƙe karsashinku na Ramadana har zuwa bayansa, kuma ku raba kawunanku da kasala da rauni da nawa, ku yi riƙo da sabuban rabauta da tsira, na tawakkali da himma da ƙoƙari, saboda manyan burace-burace ba a samun su da nawa, to dama ta ya ya mai nauyin jiki ƙasƙantacce zai samu maɗaukakan darajoji!

    Kuma lallai tabbatuwa a kan ayyukan ɗa’a da taƙawa yana daga alamomin karɓar aiki, Imamu Aliyu ɗan Abu Ɗalib Allah Ya ƙara masa yarda yana cewa: “Ku zama masu ba da muhimmanci ga karɓar aiki sama da ba da muhimmanci ga yin aiki”.

    Kuma haƙiƙa Imamu Muslim ya rawaito a Sahihinsa cewa lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Duk wanda ya azumci watan Ramadana, sannan ya bi bayanshi da azumin kwanaki shida na watan Shawwal, to, zai samu lada kamar wanda ya azumci shekara).

    Domin karanta Yadda Ake Yin Umara Dalla-dalla danna nan

    Don haka, ku kwaɗaitu wurin azumtarsu, kuma ku yi wasici wa juna da hakan, ku sadar da aikin ɗa’a da aikin ɗa’a, za ku kasance daga cikin karɓaɓɓu da izinin Allah.

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’ilaha illahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, wa lillahil hamd.

    Ya ku ‘yan’uwa mata masu daraja! Matsayinku a cikin addinin Musulunci kamar lu’ulu’u ne killatacce, ko kayan alatu mai daraja, kuma kun fi ma lu’ulu’u tsada, ku ɗabi’antu da kunya gwargwadon iyawarku, kuma ku yi riƙo da ɗabi’ar kamun kai da saka hijabi da rufe jiki, kuma ku kame ganinku, ku riƙa sadaka, ku yawaita istighfari, ku dena butulce wa ni’ima, ku kasance mafiya alherin mataimaka ga mazajenku a kan ayyukan ɗa’a, ku ƙara ƙaimi wurin tarbiyyantar da ‘ya’yanku ababen ƙaunarku, ku kange su daga fitintinu, domin su fuskanci kalubale da sauye-sauyen rayuwa da imani mai ƙarfi da azama tabbatatta.

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lillahil’hamd, Allahu Akbar kabira, Wa-lhamdulillahi kathira, Wa subhanallahi bukratan wa asila.

    Allah Ya albarkace mu da Alkur’ani da Sunna, Ya amfanar da mu da abin da ke cikinsu na ayoyi da hikima, ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da dukkan Musulmi daga dukkan kuskure da saɓo, saboda haka, ku nemi gafararSa kuma ku tuba zuwa gare Shi, lallai Shi Mai yawan karɓar tuba ne.

    Huɗuba ta biyu:

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illallah, wallahu Akbar, wa lillahil’hamd.

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ya kwararo mana ni’imomi masu yawa kuma masu girma, ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ya tsarkaka da daraja da ɗaukaka, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu Bawan Allah ne kuma ManzonSa, wanda aka zaɓe shi a cikin talikai da manzanci da matsayi.

    Ya Allah Ka yi daɗin tsira ga Annabinmu kuma masoyinmu abin koyinmu Muhammadu ɗan Abdullahi, da Alayensa wanda suka kai maƙura wurin ƙaunarsa, da Sahabbansa masu bin sunnarsa suna masu lizimtar ta da riƙo da ita, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa matuƙar rana da wata na bibiyar juna kuma suna nan.

    Bayan haka:

    Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku yi riƙo gaba ɗayanku da Littafin Ubangijinku, da Sunnar Annabinku Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, domin mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi sharrin al’amura su ne ƙirƙirarrunsu.

    Ya ku al’ummar Musulmi! Lallai daga cikin alamomin shiriya, akwai lazimtar tabbatattun abubuwa na shari’a, da kyawawan ɗabi’u, da riƙo da haɗinkai da kasancewa tare da jama’ar Musulmi, da abin da hakan ke lizimtawa na ji da biyayya ga shuwagabanni, an karɓo daga Ibnu Umar Allah Ya ƙara musu yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Al’ummata ba za ta taɓa haɗuwa a kan ɓata ba, saboda haka, ku lizimci jama’a, domin taimakon Allah yana tare ne da jama’a). Tirmizi da Ɗabarani ne suka rawaito shi da isnadi mai kyau.

    Lallai jama’a igiyar Allah ne ga mai addini saboda haka, ku yi riƙo da igiyar mai ƙarfi.

    Sau Nawa ne Allah Yake tunkuɗe bala’i ta dalilin shugaba.

    A cikin lamuran addini da na duniya don rahama daga gare shi.

    Ba don shugabanci ba da ba a amintar mana da hanyoyi ba.

    Kuma da masu ƙarfinmu sun danne masu rauni daga cikinmu.

    Da kasancewa tare da jama’a da biyayya ga shugaba ne aminci da zaman lafiya ke tabbata, kuma ababen guda biyu, ni’imomi ne da babu ni’imar da ta kai su girma, kuma kyauta ne da falala da babu abu mai daraja kamar su.

    Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukakin Sarki Ya fifita ƙasa mai tsarki da ni’imar aminci da zaman lafiya, sai Ya ce tsarki ya tabbata a gare shi: (Ashe ba su ga cewa lallai Mu mun sanya garin Makka mai alfarma ya zamto mai aminci ba, alhali ana fauce mutane a garuruwan da ke kewayensu).

    Saboda haka, wanzuwar zaman lafiya a ƙasa mai tsarki aƙida ce tabbatatta, tushenta na kafe cikin ƙasa, rassanta kuma su na sama, kuma hakan ya tabbata kuma ya ƙarfafu tun lokacin kafuwar wannan ƙasa har zuwa zamanin shugaban da ya haɗa sassan ƙasar, nagartaccen Sarki – Allah Ya kyautata makomarsa – cikin inuwa mai faɗi na tutar haɗinkai da ɗinkewa, da nesantar sharrin rarrabuwa da saɓani.

    Kuma a wannan zamani na bunƙasawa da hangen nesa da kyakkyawan tsari na shugabanci da cigaba da ginawa da rayawa da haɓɓakawa da daɗin rayuwa da kyawunta, da cin ma manufofinta ta hannun matasanta maza da mata, da tabbatar da kishin ƙasrsu da jinginuwarsu gare ta, wannan ƙasa tamu maɗaukakiya tana da daraja ta ɓangaren abin da ya shafi haɗinkan mutanen cikinta, da sauƙin rayuwa da riƙo da al’adu da tafiya kafaɗa da kafaɗa da zamani da cigaba da bunƙasa, kuma dama – da falalar Allah – ita ce ƙasar da take da girman tasiri ga Musulmi da Larabawa da duniya, da mahimmancin wurin da take da girman tarihinsa, da matsayinta mai girma a idon duniya, ga Allah kaɗai godiya da falala suka tabbata, Allah Ya ƙara mata haɗinkai da dunƙulewa da wadata, kuma Ya ƙare mata aƙidarta da shugabancinta da amincinta lumanarta, lallai Shi Mai yawan kyauta ne Mai karamci.

    Kuma bayan haka: Albishirinku ya ku waɗanda kuka yi azumi da tsayuwar dare, albishirinku ya ku waɗanda kuka yi Tahajjudi kuma kuka yi sadaka, haƙiƙa gajiya da wahala sun gushe, lada kuma ya tabbata in Allah Ya yarda, domin wannan rana ce ta kyaututtuka.

    Kuma daga cikin falalar Allah ga ƙasarmu, akwai abin da Allah Ya ɗaukaka ta da shi na hidimar Masallatai biyu masu alfarma, da abin da Ya ni’imta wa masu Umra da maniyyata na samar musu da wani yanayi na imani mai girma, da manyan hidindimu masu ban-ƙaye, saboda haka, ga Allah kaɗai yabo da godiya suka tabbata, kuma Allah Ya saka wa Hadimin Masallatai biyu masu alfarma da magajinsa amintacce da mafi alherin sakamako kuma mafi cikarsa a kan ƙoƙari da suke yi na gabatar da ayyuka masu girma na hidima ga Masallatai biyu masu alfarma da maziyartarsu, da taimako cikin lamuran da suka shafi Musulunci da Musulmi, na gaba daga ciki, shi ne lamarin da ya shafi Falsɗinu da Masallacin ƙudus, da ƙoƙarin wajen samar da aminci da zaman lafiya a duniya.

    Allah Ya karɓa mana kyawawan ayyuka, kuma Ya sa a kowace shekara ku cigaba da ni’imtuwa da alkhairai da jin daɗi, cikin aminci da lumana da natsuwa da kwanciyar hankali.

    Wannan kena! Allah Ya muku rahama, Ku yi aiki da umarnin Ubangijinku da Yake sakanta muku da lada mai girma a kansa, da matsayi maɗaukaki, sai Allah Madaukaki Ya faɗi magana mai daraja: ((Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).

    Ya Allah Ka yi daɗin tsira ga Annabi Muhammadu, da Alayensa nagartattu tsarkaka, da Sahabbansa masu hasken fuska masu albarka, da Halifofinsa shirayayyu, Abubakar da Umar da Usman da Ali, da sauran Sahabbai baki ɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako.

    Ya Allah ya ma’abocin girma da ɗaukaka, Ka daidaiata tsakanin Musulmi, Ka azurta su da shiriya da tsoron Allah da kamewa da wadatar zuci, ya Allah Ka datar da su ga haɗin kai da ƙaunar juna, Ka nesanta su daga sharrori da laifuka don falalarKa, Ka shiryar da su hanyoyin tsira.

    Ya Allah Ka datar da shugabanmu Hadimin Masallatai biyu masu alfarma ga ayyuka na ƙwarai da tsoron Allah, da aikin da Ka yarda da shi, kuma Ka yalwata masa tufafin waraka da lafiya, Ka datar da shi da magajinsa ga abin da yake ɗaukaka ne ga Musulunci da Musulmi, Ka azurta su da mashawarta nagari, waɗanda za su riƙa nuna musu alheri su riƙa kwaɗaitar da su a kan shi, ya Allah Ka game su da baiwarwaki masu kyawu, Ka ƙawata su da siffofin karamci, Ka kasance Mai taimako da agazawa da ƙarfafawa da ba da nasara a gare su cikin ayyukan alheri, Ka sanya su su zamto masu taimako ga Musulunci da Musulmi.

    Ya Allah Ka wanzar da aminci da zaman lafiya a garuruwanmu, Ka sanya su su rabuta da alheri da albarkoki, su kuɓuta daga sharrori da masifu.

    Ya Allah Ka datar da shugabannin Musulmi ga hukunci da shari’arKa, da bin Sunnar AnnabinKa Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Ka shiryar da su bisa tafarkin kyawawan ayyuka da tsira.

    Ya Allah Ka taimaki ‘yan’uwanmu masu rauni a kowane wuri.

    Ya Allah Ka ceto Masallacin ƙudus daga ta’addancin ‘yan ta’adda, da yahudawa ‘yan share wuri zauna, ya Allah Ka sanya shi ya zamto mai ɗaukaka da buwaya har zuwa Ranar sakamako.

    Ya Allah Ka taimaki ‘yan’uwanmu a ƙasar Falasɗinu, ya Allah Ka darkake maƙiyansu, Ka tarwatsa taronsu, Ka sanya su su zamto abin lura ga masu lura.

    Ya Allah Ka zartar wa wannan ƙasa wani al’amari na shiriya da za a ɗaukaka masu yi maka ɗa’a da shi, a shiyar da masu saɓa maka da shi, a yi umurni da kyakkyawan aiki da shi, a yi hani daga mummunan aiki da shi, ya Ma ji roƙo.

    Ya Allah Ka datar da jami’an tsaronmu, da masu dako a fagage da iyakokinmu.

    ((Ya Ubangijinmu Ka ba mu kyakkyawa a duniya, Ka ba mu kyakkyawa a lahira, kuma tsare mu daga azabar wuta)).

    Ya Allah Ka sanya Idinmu ya zamto mai daɗi, rayuwarmu ta zamto mai yalwa, aikinmu ya zamto daidaitacce, kuma Ka maimaita mana shi cikin shekaru masu yawa, da zamuna masu tsawo, muna cikin alheri da lafiya da rayuwa mai daɗi, ya Allah Ka maimaita mana shi tare da shugabanninmu da ƙasarmu da Musulmi cikin alheri da jin daɗi da albarka, ya Mafi alherin Wanda ake roƙo, kuma Mafi ɗaukakar Wanda ake fata.

    Ya Ubangijinmu Ka karɓa mana lallai Kai Mai ji ne kuma Masani.

    Ka karɓi tubarmu, lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne kuma Mai jinƙai.

    Ka gafarta mana da iyayenmu da dukkan Musulmi, rayayyu daga cikinsu da matattu, don tausayinKa ya Mafi tausayin masu tausayi.

    Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lillahil’hamd.

    Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa).

    Aminci ya tabbata ga Manzanni. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Danna nan don karanta Addu’ar Fita Daga Masallaci

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

     

     

  • Lailatul Ƙadri

    Lailatul Ƙadri

    Wasu kwanaki ne masu ɗimbin falala, waɗanda suka fi watanni dubu, sannan kuma ba a samunsu, sai a cikin watan Ramadan, a kwanakin goma ƙarshensa.

    حدثنى زياد عن مالك عن يزيد بن عبدالله بن الهاد عن محمد بن إبراهيم إبن الحارث التيمى عن أبى سلمة  بن عبدالرحمن عن أبى سعيد الخدرى أنه قال :كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعتكف العشرالوسط من رمضان فاعتكف عاما , حتى إذا كان ليلة إحدى وعشرين وهى اليلة التى يخرج فيها من صبحها من اعتكافه قال : من اعتكف معي فليعتكف العشر الأوخر, وقد رأيت هذه اليلة أنسيتها , وقد رأيتنى أسجد من صبحها فى ماء وطين فالتمسوهافى العشر الأخر والتمسوهافى كل وتر ,قال أبو سعيد فأمطرت السماء تلك اليلة وكان المسجدعلى عريش فوكف المسجد قال أبو سعيد :فأبصرت عيناي رسول الله صلى الله عليه وسلم إنصرف و على جبهته وأنفه أثر الماء والطين , من صبح ليلة إحدى وعشرين .

    An ruwaito daga Ziyadi daga Malik daga Yazidu bin Abdulllah bin Hadi daga Muhammad bin Ibrahim bin Haris Al-tamimi daga Abu-Salma bin Abdullahman daga Abu-Sa’idul Kudri, haƙiƙa shi ne yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana Ittakafi a goman tsakiyar watan Ramadan, sai ya yi Ittikafi a wannan shekarar, har sai da ya kasance daren ashirin da ɗaya (ta same shi a cikin masallaci) ita ce da ya fita safiyarta, wanda zai yi Ittikafi a cikinta yace “Duk wanda zai yi Ittikafi tare da ni, to a daren goma ƙarshen (Ramadan), haƙiƙa ya ga a cikin wannan daran, sannan sai ya manta da ita, haƙiƙa na ganni ina sujjada a cikin safiyarta, akwai ruwa da taɓo, sannan (sai annabi yace) ku neme ta a cikin kwanaki goman ƙarshen (Ramadan ), sannan (ya ƙara cewa) ku neme ta a cikin kowacce rana (na ranar).

    Saboda haka wannan hadisin ya yi magana a kan abubuwa guda biyu Ittikafi da lailatul ƙadri, Ibin Abdulbari yace wannan hadisi shi ne ya inaganta a wannan babi, saboda annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana Ittakafi a kwanakin goman tsakiyar watan Ramadan.

    Haka kuma  imamu Hafiz Ibin Hajar yace, shi ne da yi wa wawin damma da kuma sin sakina (ɗauri ko mara wasali), sannan kuma Ibin Abdulbarri yace wannan ruwarta (ta Manzon Allah) yana Ittikafi  har sai da ya kasance a daren ashirin da ɗaya, ita ce daren da ya fice a cikin ta da safiyarta, domin yin Ittikafi’’.

    Wannan ruwayar tana ɗaya daga cikin ruwayar Yahaya da Abubakar da shafi`i, amma a cikin ruwayar kala biyu ce da ta Ibin wahabi da Ibin Ƙasim, waɗanda suka fitar da ita (annabi yana Ittikafi), amma kuma ba su ambaci safiyar ba.

    Amma kuma shi Ibin Hazim ya faɗa misalin wannan ruwayar, inda yake cewa a cikin huɗubar  daren ashirin da ɗaya,  annabi ya shiga Ittikafi, ita ce daren ashirin da biyu, saboda abin da aka faɗa a ƙarshen wannan hadisi.

    Sai ya buɗe idonsa, sai ga  annabi (Sallallahu alaihi wasalla) a gefensa a ranar, sannan kuma sai ga alamar ruwa da taɓo a cikin safiyar daren ashirin da ɗaya.

    Abin nufi a nan shi ne, mutum ya shiga Ittikafi kafin daren ashirin da ɗaya (lailatul ƙadri), sannan sai ya manta da ita, sai yace “annabi ya ga mala’ika da haske da idonsa”, sannan kuma ya gani  a farkon wannan daren ya ga kaza da kaza a cikin daren, ya ga masallaci, mai girma kuma ga haske, sannan kuma a saman masallaci, ruwa yana zuba, saboda haka alamomin da ake iya gane daren lailati ƙadri ne.

    Misali kamar su gushewar rana, zubar ruwan sama, washewar sararin samaniya, gari ya yi tsit, rashin jin sautin karnuka ko dabbobi, da sauransu. Sannan kuma ana iya samu daren lailatul ƙadri a ranar daren ashirin da ɗaya ko da uku ko da biyar ko da bakwai, ko da tara waɗannan su ne ranakun da ake iya samun lailatul ƙadri.

    Amma Abi-Sa’id yace, sama ta kece da ruwa a wannan daren, sannan masallacin ya kasance tamkar ginshiƙi, sai masallacin ya tsaya, sannan kuma  Abi-Sa’id yace sai annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ya buɗe idanunsa, sai ya juya sai ga goshinsa da hancinsa akwai alamar ruwa da taɓo a daren Asubahin da ya shiga na watan Ramadan.

    An ruwato daga Ziyadu daga Malik daga Abudullah bin Dinari daga Abdullah bin Umar (yace) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) yace’’ ku binciki (ku kirdado) daren lailatul ƙadri a cikin bakwai ɗin ƙarshe.

    Abin nufi a nan shi ne a kwanaki ashirin da bakwai ɗin ƙarshen.

    حدثنى زياد عن مالك عن هشام بن عروة عن أبيه : أن   رسول الله صلى الله وسلم قال “تحروا ليلة القدر فى العشر الأخرين من رمضان .

    An ruwaito daga Ziyaddu daga Malik daga Hishamu “ku binciki daren Lailatul ƙadri a cikin (kwanaki) ashirin ɗin ƙarshen watan Ramadan.

    حدثنى زياد عن مالك عن أبى النضر مولى عمر بن عبيدالله : أن عدالله إبن أنيس الجهني قال لرسول الله صلى الله عليه وسلم : يا رسول الله , إنى رجل شاسع الدارفمرنى ليلة أنزل لها , فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم ” أنزل ليلة ثلاث وعشرين من رمضان ”

    An ruwaito daga Ziyadu daga Malik daga Abi-nadhir mai yi wa Umar bin Ubaidullah hidima (yace), haƙiƙa Abdullah bin Unaisu Aljuhaniyyu yace da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), ya manzon Allah ni mutum ne mai rusasshen gida, ka umarce ni da daren da aka saukar da ita (Lailatul ƙadri), sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) yace da shi “An saukar da daren (Lailatul ƙadri), ashirin da uku a cikin watan Ramadan”.

    Amma Ibin Abdulbarri yace wannan ruwayar yankakkiya ce, saboda Abi-nadhir bai riski Abdullah bin Unaisu ba, sannan kuma bai gan shi ba, amma haƙiƙa Imam Muslim ya sadar da wannan hadisin ta hanyar Dhahaku bin Usman daga Abidi daga Busra bin Sa’id daga Abdullah bin Unaisu da lafazin Hadisin Abi-Sa’id daga Daud ya sadar da shi ta hanyar Ibin Ishak daga Muhammad bin Ibrahim Attamimu daga Umrata bin Abdullah bin Unaisu daga mahaifansa kamar yadda wannan hadisin na Muwaɗɗa Malik ya nuna haka.

    An ruwaito daga Ziyadu daga Malik daga Humidu Aɗɗawilu daga Anas bin Malik, tabbas ne yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) ya fita tare da mu a cikin watan Ramadan, sai yace “ni na ga mutane biyu suna jayayya, sai suka dakata, (sai yace da su) ku neme ta a cikin (ashirin da) tara ko bakwai ko biyar’’.

    حدثنى زياد عن مالك أنه بلغه : أن سعيد بن المسيب كان يقول : من شهد العشاء من ليلة القدر , فقد أخذ بحظه منها.

    An ruwaito daga Ziyadu daga Malik (yace) haƙiƙa shin labari ya same shi lalle Sa’id bin Musayyibin ya kasance yana cewa, duk wanda ya shaida (ya yi sallah) Isha’i a cikin Lailatul ƙadri (Ai a cikin ranakun da ake sa ran ganinsu), haƙiƙa ya riski daren lailatul ƙadri.

    Haka kuma Ibin Abdulbarri yace, wannan ba zai iya kasancewa ba, sai kawai ra’ayi ne, sannan ba zai riƙi komai ba, sai  dai neman dacewar Allah (Subhanahu wata’ala) a cikin wannan ranar.

    Saboda haka malamai sun ƙarawa junansu sani a kan daren Lailatul ƙadri, saɓanin mai yawa, daga cikin su akwai maganar baban malamin nan Al-araki, saboda ita (Lailatul ƙadari) ba ta yi dai-dai da sauran shekaru ba ko ranaku.

    Ma’ana ganin wannan daren sau ɗaya ya taɓa faruwa a zamanin Manzon Allaah (Sallallahu alaihi wasalla), sannan kuma an faɗa a wata maganar, wannan daren yana kewayawa ne a kowace shekara, a wata faɗar kuma an ce Lailatul ƙadri tana cikin rabin watan Sha’aban, sannan kuma wasu sun ce, A a an keɓance ta ne a cikin watan Ramadan.

    Sannan za a iya samunta a cikin kowanne dare (Ramadan), Bugu da ƙari kuma Sheikh Sabkiyu ya yarinjar da shi, amma malam Sarkhisu ya faɗa a cikin sharhin ‘’ Hidayatu’’. Maganar Abi-Hanifa yace za mu same ta (daren Lailatul ƙadri) an ciro ta ne a cikin dukkanin Ramadan, haka nan ma abokinsa ya faɗi haka sauransu.

    Haka ma an ruwaito daga Ibin Abi-Asim daga Anas yace, babu wanda ya sani daga cikin mu (ranar ganin Lailatul ƙadri), sai wani malami daga cikinsu yace, A a, Lailatul ƙadri, tana cikin rabin watan Ramadan, sai kuma wani mutum yace, A a tana cikin daren goman sha shida ne, na Ramadan.

    Sai kuma wani yace, A a tana cikin daren goman sha bakwai, sannan sai wani yace, A a tana cikin daren goma sha takwas, sai kuma wani ya ƙara cewa, A a tana cikin daren goma sha tara ne, sai kuma wani ya sake cewa, A a tana cikin daren ashirin ga watan Ramadan,

    Haka kuma sai wani yace, A a ita Lailatul ƙadri abar so ce, sannan kuma tana cikin goman tsakiyar watan ramadan, sai kuma wani yace A a ita kuma abin so ce, sannan tana cikin goman ƙarshe.

    Sai kuma wani yace, A a, Lailatul ƙadri tana cikin daren ashirin da biyu na watan Ramadan har zuwa daren talatin ga watan Ramadan, sannan kuma wasu suka ce Lailatul ƙadri, tana cikin goman tsakiyar watan Ramadan, wasu kuma suka ce tana cikin goman ƙarshen.

    Amma a cikin mazahabar Imam shafi’i jamhurum Sahabbai (mutanan mu) suka ce, haƙiƙa ita Lailatul ƙadri tana goman ƙarshe watan Ramadan, sannan kuma abar so ce a kan mu, sai dai ita abar ayyanawa ce a kan wannan al-amari, sannan kuma wannan daren na Lailatul ƙadri ba za ta gushe ba, har zuwa ranar lahira, kowanne ranaku goman ƙarshe (na wata) abar ɗaukakawa ce.

    Daga ƙarshe kuma,mazahabar imam shafi’i sun rinjayar da daren ashirin da ɗaya shi ne daren Lailatul ƙadri, sannan kuma dukkanin mazahaban nan guda huɗu sun yi bayani a kan kwanakin sa ran ganin Lailatul ƙadri.

    A takaice, alamomin daren lailatul ƙadri suna da yawa, amma dai idan ana cikin tsananin zafi ko sanyi, to a ranar daren za a samu sauƙi, idan kuma garin akwai duhu, to za a samu haske a garin da sauransu.

    Domin karanta Falalar Gaggauta Shan Ruwa danna nan 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Gama Alwala

    Addu’ar Gama Alwala

    Addu’ar da mutum zai yi bayan ya gama Alwala

    اَشْهَدُ اَنْ لا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُه

    اللّهُمَّ اجْعَلْنِي مِنَ التَّوَّابِينَ وَاجْعَلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّرِينَ

    Ash hadu alla ilaha illallah, wahdahu la sharikalah, wa ash hadu anna muhammadan ‘abduhu wa rasuluh. Allahummaj ‘alni minat tawwabina waj ‘alni minal muta tahhirin.

    Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi Kaɗai, kuma ba shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne.

    Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkake ka.

    Danna nan don karanta Adu’ar Buɗe Sallah

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Buɗe Sallah

    Addu’ar Buɗe Sallah

    Addu’ar Buɗe Sallah (wato Bayan An yi Kabbarar Harama)

    اللَّهُمْ بَاعِدْ بَينِي وَبَيْنَ خَطاياي كما باعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبُ ، أَللَّهُمْ نَقْنِي مِنْ خَطاياي كما يُنقى الثوبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدنس ، اللهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بالثلج والماءِ وَالبَرَد

    Allahumma ba’id baynee wabayna khatayaya kama ba’adta baynal-mashriki walmaghrib, allahumma nakkinee min khatayaya kama yunakkath-thawbul-abyadu minad-danas, allahummagh-silnee min khatayaya biththalji walma’i walbarad.

    Ya Allah! Ka nisanta tsakanina da laifuffukana kamar yadda Ka nisanta tsakanin gabas da yamma; Ya Allah! Ka tsarkake ni daga laifuffukana kamar yadda ake tsarkake farar tufa daga dauɗa, Ya Allah! Ka wanke ni daga laifuffukana da ƙanƙara da ruwa da raɓa.

    Domin karanta Addu’ar Daren Lailatul ƙadri danna nan 

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Ittikafi

    Ittikafi

    Ittikafi:  shi ne dauwama a masallaci, domin yin ibadah, Salloli da tasbihi haɗi da tahlili, takbiri da salatin annabi da karatu alƙur’ani mai girma da sauransu a cikin masallacin Juma’a.

    حدثنى يحي عن مالك عن إبن شهاب عن عروة بن الزبير عن عَمْرَةَ بِنْتُ عَبْدُالرَّحْمَنْ عَنْ عَائِشَةُ زَوْجِ النَّبِيُ صَلَى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهَا قَالَتْ :كَانَ رَسول الله صلى الله عليه وسلم إِذَا عْتَكَفَ يُدْنِى إِلَى رَأْسَهُ فَأُرَجِّلُهُ ,وَكَانَ لاَ يَدْكُلُ الْبَيْتَ إِ لاَّ لِحَاجَةِ الإِ نْسَانِ .

    An rawaito daga Yahaya daga Malik daga Ibin Shihab daga Urwata bin Azzubairu daga Amrata binti Abdulrahman daga Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ita ce tace “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) ya kasance, idan yana ittikafi, yana kusanto  kan sa kusa da ni (ma`ana sai annabi ya miƙa kansa ta taga, saboda gidansa  yana kusa da masallaci ne) sai ta tsattsefe (tatacewa) masa kansa, sannan (annabi) ya kasance ba ya shiga gida, don buƙatar wani mutum”.  Idan yana ittikafi.

    Saboda haka mai ittikafi ba zai shiga gida ba, don buƙatar wani mutum daban, Haka ma mai Ittakafi ba zai fita cikin masallaci ba, sai don buƙatar kansa kamar su, rashin lafiya, abinci, idan babu mai kawo masa abinci da sauransu.

    Bugu da ƙari kuma,  mai Ittakafi ba zai tafi ziyarar maƙabarta ba, ba zai tafi zance ba ko gurin ɗaurin aure, ba zai kwana a gidansa ba, sai dai idan a cikin masallaci ne, ba zai yawaita yawan surutu ba, sannan kuma dole ne a kan mai Ittikafi ya nisanci dukkanin abin da ya kamata ya nisanta. Misali kamar su kasuwanci, labaran duniya, kallon tsaraici, maganganun batsa ko kwarkwasa da sauransu.

    Haka kuma mai Ittikafi ba zai tafi gida ba, idan an ga wata (shan ruwa), har sai ya dawo daga masllacin idi kamar yadda ya zo a cikin wannan hadisin na annabi Muhammad  (Sallallahu alaihi wasalla), sai dai idan akwai wani dalili mai ƙarfi.

    حدثنى يحي عن زياد عن مالك : أنه رأى بعض أهل العلم إذا عتكفوا العشر الأواخرين من رمضان ,لا يرد إلى أهاليهم حتى يشهدوا الفطر مع الناس .

    An ruwaito daga Yahaya daga ziyadi daga Malik (yace), haƙiƙa shi ya ga sashin ma’abota Ilimi, idan suka yi Ittikafi na kwanaki goman ƙarshen watan Ramadan, ba sa dawowa gidan su (wajan iyalansu), har sai sun halarci masallacin Idi tare da musulmai.

    Sannan kuma babu laifi a kan mace ta yi Ittikafi kamar namiji, idan mace tana Ittikafi, sannan sai hailarta ta same ta a cikin wannan hali (Ittikafi) me za ta yi?, Amsa idan mace hailarta ta same ta a wannan hali za ta koma gida ne, idan ta yi tsarki, sai ta dawo masallaci ta gina ko ta ɗora a kan abin da ya wuce na Ittikafinta, kamar macen da akwai ramuwar azumi wata biyu (60) a kanta, kuma waɗanda ake jera su, sai ta fara ramuwar azumin da ake binta, sai kuma hailarta ta zo mata, sai ta tsaya da yin azumin, idan ta ɗauke mata,  sai ta ɗora a kan abin da ta yi na azuminta.

    Hakan kuma babu laifi a kan mai Ittikafi yin aure ko Aure, matuƙar ba zai fita cikin masallaccin ba, sannan kuma ba zai sadu da matar ba, har sai bayan ya fito daga masallaci. Bugu da ƙari kuma, an hana saduwa da iyali ga mai Ittikafi da safiya ne ko  daddare ne, har sai bayan ya kammala Ittikafinsa.

    Sannan kuma babu laifi ga mai azumi, idan yana da mataye ko `yan uwa, sai su kawo masa ziyara cikin masallacin, amma kuma ba za su yi maganar wasa ba ko kwarkwasa.

    Har ila yau, mafi alherin Ittikafi kwana goma, ƙarancinsa kwana ɗaya da yini, haka kuma ba a yin  Ittikafi sai da azumi, kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗa a cikin Baƙara ayata (187)

    Sannan kuma mai Ittikafi ya shagaltul da karatun Alƙur’an ko nafilfili ko Istigifari ko ambaton Allah (S.W.A) dare da rana. Haka ma ya dage da neman kusanci ga Allah da mazonsa haɗi da neman addu’ar ci gaban addinin musulunci da musulmai da kuma kare su daga sharrin maƙiya da mahassada, domin alfarmar annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla). Bugu da ƙari kuma, babu laifi a kansa idan yana da wasu buƙatu ya roƙi Allah (S.W.A).

    Saboda haka Ittikafi yana ɗaya daga cikin manya-manyan Ibada masu girman gaske, sannan kuma shi Ittikafi riba biyu ce ko ma uku, na farko Ibadah ce mai girma, na biyu ga samun ƙarin girma a wajen Allah da manzonsa, matuƙar ya cika sharaɗan Ittikafi, na uku ga samun lada mai yawa haɗi da biyan buƙata da kuma samun farin jini a wajen al’umma da sauransu. Haka ne ma yasa ba kowa ba ne yake iya samun yin Ittikafi, saboda falalar dake cikinsa, saboda duk wanda zai aikata abin da zai nisanta shi daga shiga wuta, sai shaiɗan ya ɗora masa kasala da gajiya, wajen ya ga ya hana shi aikata haka.

    Bugu da ƙari ma yana hana su yin aikin alheri kamar su kyauta, sadaka, ciyarwa, nafilfili da sauran su. Saboda haka sai ka ga mutane sun ƙi shiga Ittikafi, har sai ka ga masu shiga Ittikafin sun kammala, sun dawo suna zama tare da su, ka ga su, sun aikata Ibadah mai girma, sannan kuma sun dawo suna zama tare da su.

    Daga ƙarshe kuma, ina kira ga waɗanda ba su samu ikon shiga Ittikafi ba, to su samu binci ko abin sha ko kayan marmari, su ba masu yin Ittikafi da sauransu, domin samun falalar da suke cikin, saboda duk wanda ya ciyar da mai azumi, Allah (S.W.A) zai ba shi lada kwatan-kwancin wanda ya yi azumi, ballantana ma a ce ka ba mai yin azumi kuma wanda yake cikin Ittakafi.

    Saboda haka ina ba da shawara ga waɗanda suke zuwa Umarah duk shekara, ga wata falala mai ɗimbin yawa, wanda ya kamata su dinga aikatawa, saboda kuɗin da suke kashewa a ƙalla zai iya ciyar da mutane abinci haɗi da nama na mutane guda  dubu ɗaya, saboda haka yaya kake tunanin a cikin kowane gari a samu mutane guda goma su aikata haka, mutane dubu nawa ne za a taimakawa, a maimakon su dinga zuwa umrah duk shekara.

    Sannan kuma duk abin da mutum ya ciyar da wani mutum, to Allah (S.W.A) zai riɓanya masa sau ɗari bakwai (700) ko ma fiye da haka, sannan kuma ga samun zaman lafiya a tsakanin mawadata da talakawa haɗi da yabo na karamci da addu’o`i a gare su da sauransu. Muna roƙon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ba mu ikon aikata wannan Ibadah ya kuma sa mu dace, Ameen, domin alfarma annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla), sannan kuma mutum ya guji yin ƙarya a lokacin da yake yin ittikafi, saboda dukkanin wanda ya yi ƙarya ko kasuwanci ko saduwa da mace ko catin da waya (WhatsApp ko Facebook) ko yawan surutu, to ittakafin sa ya baci, sai ya sake wani, matuƙar ya shagaltu da aikata haka. Wasu malamai suka ce kuma a a, ittikafinsa yana nan, sai dai ya rage ma kansa lada”.

    Danna nan don karanta Azumin Watan Ramadan

    Edita:@rumasau-kallamu

     

  • Addu’ar Daren Lailatul Kadri

    Addu’ar Daren Lailatul Kadri

    Nana Aisha (R.A) tace, Ya Manzon Allah (S.A.W) shin kana ganin idan na gane wane dare ne na Lailatul kadri, me zan ce a cikinsa? sai yace ki ce:

    “اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي”

    “Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa’afu anni”

    MA’ANA: “Ya Allah kai mai afuwa ne kuma kana son afuwa, to ina roƙon ka yi mini afuwa” (Tirmidhi da Ibn Majah)

    Edita:@rumasau-kallamu