Tag: yadda ake

  • Hukuncin Tsotsar Al’aura A Musulunci

    Hukuncin Tsotsar Al’aura A Musulunci

    Hukuncin tsotsar farji (cunnilingus) ko azzakari (fellatio) a Musulunci ya kasance cikin lamuran da malamai suka yi iƙhtilāf (ra’ayi daban-daban) a kai, saboda babu ayar Qur’ani ko sahihin Hadisi da ya bayyana lamarin a fili. Amma ga bayani da ra’ayoyin malamai:

    1. Ra’ayin da ya halatta shi da sharaɗi:

    Wasu malamai sun halatta shi, idan ba a haɗiye wani najasa ba, kuma ya kasance tsakanin ma’aurata da yardar juna. Misali:

    •Idan miji ya tsotsi farjin matarsa ba tare da hadiye ruwa ko wani najasa ba, hakan ba haramun ba ne a ra’ayinsu.
    •Haka kuma, idan mace ta yi wa mijinta hakan da nufin soyayya ko nishaɗi tsakanin su an halatta shi, musamman idan hakan yana ƙara ƙaunar aure.

    2. Ra’ayin da ya hana shi gaba ɗaya:

    Wasu malamai sun haramta hakan gaba ɗaya saboda:
    •Ƙarancin ladabi da girmamawa ga gabobin jiki.
    •Yiwuwa a haɗiye najasar da ke fitowa daga gabobi.
    •Imitation (kwaikwayo) na ayyukan alfasha irin na film ɗin batsa (pornography).

    3. Ra’ayin matsakaici:

    Wasu malamai sun ce:
    •Makruhi (abin ƙyama) ne amma ba haramun kai tsaye ba, sai dai idan an haɗiye ruwa ko najasa, to hakan ya haramta.
    A taƙaice:
    •Halal ne tsakanin ma’aurata idan babu najasa kuma da yardar juna.
    •Haramun ne idan zai kai ga shan maniyyi ko wani abu najasa.
    •Makruhi ne idan ba a samu tsafta ko tsafta ba.

    Shawara:

    A guji irin wannan abu idan zai kawo rashin girmama juna ko saɓawa da al’ada, ko kuma idan yana kawo tunanin film ɗin batsa. A maimakon haka, a ƙarfafa soyayya da nishaɗi cikin tsafta da girmamawa.
    HukunciDomin karanta Saduwar Aure A Musulunci danna nan
    Edita@rumasau-kallamu
  • Yadda Ake Saduwar Aure A Musulunci

    Yadda Ake Saduwar Aure A Musulunci

    Yadda ake saduwa da mace (jima’i) cikin halal ya danganta da matakin aure da tsafta, kuma yana da kyau a yi da niyyar samun lada da ƙarfafa soyayya tsakanin ma’aurata. Ga yadda ake saduwa da mace cikin tsarin Musulunci:

    1. Halal ne kawai idan kuna da aure:

    Saduwa da mace ba ta halatta ba sai tsakanin miji da mata da aka ɗaura auren su cikin shari’a.

    2. Niyya da addu’a kafin saduwa:

    Ana so miji ya fara da addu’a kafin saduwa:
    “Bismillahi, Allahumma jannibnash-shaitana wa jannibish-shaitana ma razaƙtana.”
    Ma’ana: “Da sunan Allah, ya Allah ka nesanta shaiɗan daga gare mu, da daga abin da za Ka azurta mu da shi.”

    3. Tsafta:

    Mace da miji su kasance a cikin tsabta. Idan mace na cikin haila ko jini bayan haihuwa, haramun ne a sadu da ita sai ta wanke jikinta (wato ta yi wanka).

    4. Saduwa da ladabi:

    •Ana son ma’aurata su yi fara’a da juna kafin jima’i (romance), kamar runguma, magana mai daɗi, shafawa da sauransu.
    •Ana saduwa ta gabanta (farji), ba ta dubura ba domin hakan haramun ne.
    •Ana iya canza salo da matsayi (position) kamar yadda Qur’ani ya ambata:
    “Mata naku gonakinku ne, ku zo gonarku yadda kuka so…” (Surah Al-Baqarah: 223)

    5. Bayan saduwa:

    •Dukkan ma’aurata su yi wanka na janaba kafin su yi sallah ko karanta Al-Qur’ani.
    •Ana son miji da mata su nuna kulawa da juna bayan saduwa, su gaishe da juna cikin farin ciki.
    Don Karanta Lefe A Auren Hausawa danna nan
    Edita@rumasau-kallamu
  • Tarihin Mahiru Sharif Bala

    Tarihin Mahiru Sharif Bala

    An haifi Gwani Sharif Bala ɗan Sharif Musɗafa ɗan Sharif Muhammad a shekarar 1345; wadda ta yi dai-dai da shekarar 1934 a Unguwar Gabari cikin garin Kano.

    Mahiru Sharif Bala ya taso a gidan ilimi da wadata da karamci a inda ya yi karatu a wurin mahaifinsa tare da ɗan uwansa Sharif Ahmad. Mahiru Sharif Bala ya rubuta Alƙur’ani sau uku tun yana ɗan shekara goma sha takwas; kuma a dai-dai wan nan lokaci ne aka yi masa auren fari. Mahiru Sharif Bala ya kutsa fannonin ilmi inda ya karanci tafsiri da Hadisi da Fiƙhu a Unguwar Makwarari.

    Wani abin mamaki game da rayuwar Mahiru Sharif Bala ya yin neman Alƙur’ani shi ne: bai taɓa zuwa ko’ina ba kamar yadda abin yake wajen mafi yawan makaranta. Babbar baiwar da Mahiru Sharif ya shahara da ita baya ga ƙarfin tilawar Alƙur’ani, shi ne gwanintar rubutunmu na Magribi.

    Kwanciyar baƙaƙen AIƙur’ani irinsu “Kaulasan” da Lam’ara da tsaiwar Bayala shaida ce ga ficen da Mahiru Sharif Bala ya yi a wannan fage. Saboda irin baiwar rubutunsa da irin karɓuwar da yake da ita tsakanin makaranta Alƙur’ani ba a ƙasar Kano ba kawai; har ma da wasu sassa na Afrika ta Yamma; ta sa Mahiru Sharif Bala ya juyi littattafai a sassan ilman Musulunci da hannunsa irinsu:-

    – Asshifa
    – Dala’ilul Khairati
    – Ishriniyya
    – Alburda
    – Hamziyya
    – Risatul Anwar
    – Igasatul ibad
    – Risala
    – Iziyya da sauransu

    Babu shakka wannan ya sauƙaƙawa makaranta tsangaya waɗanda ba su saba da rubutun sharƙiyya ba, damar kutsawa fannoni ilmi.

    A taƙaice za mu iya cewa hannun Mahiru Sharif Bala da tasirinsa a tsarin tsangaya ya zama “hantsi leƙa gidan kowa”; domin kuwa ya ratsa kowane loko da saƙo na makaranta.

    Ma’ana dai, in almajiri bai je gabansa ya yi karatu ba to kuwa ya kwaikwayi irin salon rubutun hannunsa; tun daga kan Juzi’i biyar ko goma har zuwa ashirin.

    Yaɗuwar da Alƙur’anin Mahiru Sharif Bala ya yi ya zarta yaɗuwar mafi yawan Alƙur’anan da aka rubuta da hannu; domin kuwa ya rubuta Alƙur’ani hamsin da hannunsa. An buga bakwai daga cikinsu, kuma an ɗabba’a su fiye da sau dubu ɗari biyu: waɗanda duk sun yi fice da fitar da harji da meram da falalar kowace sura.

    Game da taimakon yin magani da ayoyin Alƙur’ani kuwa, Mahiiru Sharif Bala ya rubuta Alƙur’ani don sha fiye da sau ɗari; Suratul Yusuf sau dubu ɗaya, Bisimilla da Wallahu ya ‘asimuka da Sanuƙ’ri’uka sama da miliyan guda.

    Farin jinin rubutunsa da baiwar da Ubangiji yai masa ta sa an buga:-

    i- Asshifar da ya rubuta da hannunsa sama da dubu talatin
    ii- Dala ilul khairati sama da dubu ɗari
    iii- Ishiriniya sama da dubu ɗari biyar
    iv- Alƙur’ani ɗan izu ashirin sama da dubu ɗari biyar
    v- Alƙur’ani ɗan izu goma sama da miliyan biyu
    vi- Alƙur ‘ani ɗan izu biyar sama da miliyan biyu
    vii- Ƙawa’idi sama da miliyan biyu
    viii- Ashmawi sama da dubu ɗari biyar
    ix- Risala sama da dubu goma
    x- Iziyya sama da dubu goma
    xi- Alburda sama da dubu goma
    xii- Ira’atul biladi sama da dubu goma.

    Har zuwa yanzu, Mahiru Sharif Bala bai gushe ba yana ba da karatu da ilimi a shahararriyar makarantarsa; tare da mataimaka sama da talatin da almajirai yara da manya, maza da mata sama da dubu biyar. Ubangiji Maɗaukaki Ya ƙara masa lafiya ya kuma sanya masa kyawawan ayyukansa a mizani.

    Tsokaci

    Akwai wasu malamai na Alƙur’ani fitattu a Kano da yawa – da ya kamata na gutsurawa mai karatu wani abu daga tarihin rayuwarsu, amma hakan ba ta samu ba.

    Cikinsu akwai Malam Na Mai Ganji da Malam Giwar Takwasa da Malam Husaini Ɗangurai da Malam Ɗangidimoni; da Malam Ɗayyabu Mai Saje da Malam Yahaya Malammadori da Gwani Tata Bunkure da Malam Ɗan Ringim; da Malam Mai Hafizai da ma waɗanda ban ambata ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Daga Malamai a Katsina danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Lalurar Rashin Jin Ƙamshi, Ko Wari (LOSS OF SMELL)

    Lalurar Rashin Jin Ƙamshi, Ko Wari (LOSS OF SMELL)

    Akan sami wani kaso na mutane masu wannan matsalar ta LOSS OF SMELL wato rashin iya tantance komai ta hanci, takan kasance ko dai rashin sense of smell ɗin kwata-kwata [anosmia] ko kuma ya zamto mutum na ji amma ba can da ƙarfi ba, sai ƙamshi ya yi ƙamshin ko ɗoyi ya yi ɗoyi sannan su ji wato [hyposmia] ko waɗanda wani lokacin jin smell kan ɗauke, ba a ji amma ya kan dawo daga baya [intermittent], ko kuma sai in sun kara abin dab da hanci.

    RABE-RABEN DALILAN LARURAR

    Irin wannan matsalar dalilanta sun kasu kashi 5:

    1]. Akwai wanda haka mutum ya taso ya sami kanshi, wacce mukan kira CONGENITAL ANOSMIA. Tun a yayin goyon ciki matsalar ta samo asali, domin cikin ƙwaƙwalwar mutum duk wani abu da yake toh akwai jijiyar da ita ke sarrafa wa ta taimaka abin ya yiwu, wanda idan ta sami naƙasu tun a ciki ba tare da tai girma tare da jikin mutum ba, ko sakamakon mahaifiya ta sha wani magani ko jiƙe-jiƙe yayin goyon cikin wanda kuma maganin ya je yai illa ga wannan sashin jijiyar cikin rashin sanin cewa me ciki ba ta shan maganin toh shi ne akan ga an haifo mutum ya zo da matsalar wannan jijiya da ba ta iya yin aikinta yadda ya dace, kama daga:

    – Jin wari ko ƙamshi wanda jijiyar da ake kira OLFACTORY NERVE ke samarwa, idan ita ce ta sami matsala sai a ga mutum ya zo ba ya jin komi tun haihuwarsa walau ƙamshi, wari, bashi ko wani abu.

    – Akwai OPTIC NERVE in wannan ta sami matsala tun a ciki shi ne jariri kan zo a makaho tun haihuwa har girma ba ya gani.

    – Akwai OCULOMOTOR, TROCHLEAR & ABDUCENT NERVES in suka sami matsala shi ne za a ga mutum ya zo da harara garke idonsa ba ya tsayawa cak, shi in yana magana abinda yake nunawa daban amma in kana kallon idon za ka ga inda yake kallo daban.

    – Akwai VASTIBULOCOCHLEAR NERVE da in ta sami matsala shi ne mutum kan zo a kurma tun haihuwa.

    Da dai sauran irin waɗannan jijiyoyi.

    Don haka samuwar tangarɗa jikin kowacce ke nuna matsalar da mutum ka iya fuskanta. Don haka in tun haihuwa mutum bai san wari ba, bai san ƙamshi ba toh olfactory nerve ɗin sa ce ba ta aiki. Wannan kuma bai nuna mutum zai haɗu da wata matsala ba, kurum dai sai haƙuri, wasu kuma in tafiya tai tafiya sukan wayi gari daga baya suna ɗan jin ƙamshin bayan shafe shekaru ba sa ji.

    Har mutane kan camfi a da cewa: wai wanda ba ya jin ƙamshi ko wari duk randa ya ji toh mutuwa ta kusanto masa, ko kuwa wani babba zai mutu a gidan. Amma duk camfi ne. Wannan kenan game da congenital anosmia.

    2. Sai kuma External cause wanda yake dalilin ƙila an taɓa yi wa mutum tiyata a gurin da yake hanyar jijiyar OLFACTION ne, ko aikin ƙwaƙwalwa, ko dalilin tsiro a cikin hanci wato nasal polyp, ko hatsari na wani abu da ya taɓa bugun fuska.

    Haka zalika in da girma abin ya samu mutum yana yin sana’a ko muhalli musamman ta’ammali da magunguna irin na ƙwari da sauran solvents, ko cuttukan mura.

    3. Amfani da wasu rukunin magunguna ma ka iya jawo daukewar ƙamshi, irin su antibiotics, magungunan cutar damuwa antidepressants, magungunan cuttukan zuciya, ko radiation ga masu wani nau’in cutar cancer, mutane masu shaƙar koken, duk suna iya sa ba ma ƙamshi ba hatta ji da gani ma ka iya yin rauni.

    4. Wasu cuttukan jiki, walau mutum ya taɓa cutar ƙyanda yana yaro, ko sanƙarau, ko ciwon mantuwa Alzheimer’s, cutar yunwa tamowa ko Malnutrition, ko cutar kyarma da mutum kan iya kasa tsayawa cak, hannun sa ya riƙa kyarma wato (parkinson), ds.

    5. Sai kuma rashin daidaiton sinadaran halitta wato HORMONALS IMBALANCE wanda wasu kan sami abinda muke kira KALLSMAN Syndrome. Za ka ga ko balaga ta ƙi zuwa musu, ba sa jin wari ko ƙamshi, kuma a haka ga shekaru amma balaga ta ƙi zuwa gabansa babu alamar gashi kamar ta yara abar tasa, in namiji ne, babu karyewar murya, babu girman maraina, haka in mace ce babu girman nono, ba haila, ba wani alamu na ta girma ta balaga duk da gashi ta kai shekarun sosai. Wasu duk hakan kan samu amma sai daga baya ba sanda aka saba ganin yawanci maza da ‘yan mata da abin ba. Haka na faruwa sakamakon karyotype da ke damaging ɗin sassan sarrafawa da samar da hormones ɗin a ƙwaƙwalwa wato Hypothalamus.

    Wannan shi ne taƙaitaccen bayani a game da ɗaukewar ƙamshi ko wari, Maganin kowanne ya danganta da abinda binkice ya nuna.
    Amma galibi wanda suke congenital ba abinda za su yi haka suke kurum natural, wasu kuma ana iya gano lesion ɗin ai aiki a cire idan tsiro ne a ƙwaƙwalwa, wasu kuma in mura ce su yi maganinta, wasu kuma in kallsman ai musu hormonal therapy yadda balagar za ta zo in aka yi sa’a komi ya daidaita.

    Amma dai galibi kowa ya kwan da sanin ƙarfin jin ƙamshi ko wari yana kamawa ne ka’in da na’in in an kai shekara 30 zuwa 60. Daga 60 dama naturally wannan na raguwa, komai ma na jiki ya fara saki.

    Domin ganin likita kan matsala ana iya samun duk wani ƙwararren likita a fannin kunnuwa, hanci da maƙogoro wato (ENT Physicians) ko Head & Neck surgeons. Suna nan a dukkan manyan asibitoci.

    Don karanta Harara-Garke danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma)

    Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma)

    Daga hadisan da suka gabata, za mu fahimci cewa ranar Ashura sananniya ce tun kafin bayyanar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma azumin ranar shi ma an daɗe ana yin sa tun zamanin yahudu da nasara har zuwa lokacin larabawan jahiliyya.

    To amma akwai waɗansu masu da’awar Son Ahlul Bait (Radiyallahu Anhuma), da bin tafarkinsu su ba sa yin wannan azumin; suna ko ganin ƙirƙirarsa aka yi kawai wai don nuna farin ciki da goyon baya; kan kashe Sayyidina Husaini (Radiyallahu Anhu) da aka yi a ranar ashura shekara ta 61 hijiriyya.

    Wannan yana nufin tun ɗaruruwan shekaru kafin a haifi Husainin aka fara murnar za a kashe shi; ɗan uwa ka yi tunani, a hankalce haka za ta yiwu?

    To amma mu duba mu gani shin su Ahlul baiti (Radiyallahu Anhuma); ya ya suka ɗauki ranar ashura da kuma azumin ranar? Ga amsa daga bakinsu:

    Sayyidina Ali (Radiyallahu Anhu): An karɓo daga Al-As-wad IbnYazid ya ce; “Ban ganin wanda ya fi Sayyidina da Ali da Abu Musa yawan umartar mutane da yin azumin ashura ba.

    An karɓo daga Abu Abdullahi daga babansa (Alaihis Salam) ya ce haƙiƙa Ali (Alaihis Salam) ya ce; “Ku yi azumin ashura da tasu’a saboda yana kankare zunubin shekara guda 2.

    Daga Abul Hasan (Alaihis Salam) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi azumi ranar Ashura”3)
    JA’AFARU SADIK (Radiyallahu Anhu)

    An karɓo daga Assadik (Radiyallahu Anhu) ya ce wanda zai iya azumtar watan Muharram gaba ɗayansa ya yi; zai tsare mai yin sa daga dukkan saɓo”.

    Daga Abu Ja’afar (Alaihis Salam) ya ce: “Jirgin ruwan Annabi Nuhu (Alaihis Salam) ya tsaya a jikin dutsen jude ranar Ashura, sai ya umarci gaba ɗayan mutane da aljanu da suke taře da shi da su yi azumi a ranar.

    Wannan kaɗan ne daga maganganun Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma) kan falalar azumin ashura, saboda wani babban malamin shi’a mai suna Radiyuddin Abul Ƙasim Aliyu bin Musa Ibn Ja’afar Ibn Tawus ya ce: Hadisai da yawa sun zo kan bayanin zaburarwar kan azumin ranar Ashura”.

    Mai karatu ka ga yadda maganganun Ahlul Baiti (Alaihis Salam) suka dace da maganganun kakansu (Sallallahu Alaihi Wasallam) da na sauran musulmi kan azumin Ashura da falalarsa da tarihinsa tun zamanin Annabi Nuhu (Alaihis Salam).

    Sai dai kuma su Kulaini da Ɗusi da ire-irensu sun yi fatali da waɗannan maganganu na gaskiya da hadisai ta yadda suka Rago waɗansu maganganun suka jingina su ga Ahlul Baiti saɓanin waɗanda suka gabata.

    A irin waɗanan maganganu sai suka ce wai Abu Ja’afar da Abu Abdullahi sun hana yin azumin ashura; kuma yin sa bidi’a ne, kuma wai iyalan Ziyadu ne da banu Umayya suka ƙirƙiro domin murnar kashe Husaini; kuma duk wanda ya yi to zunubinsu ɗaya da waɗanda suka kashe Husaini, da sauran maganganu.

    To abin tambaya a nan shi ne, shin su ma Imaman da ma Annabi Nuhu da Ahlul Kitabi har ma da shugaban halitta (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) banu Umayya ne? Kuma wannan wacce irin tufka ce da warwara daga Imamai? Anya suna baki biyu? Ko kuwa dai akwai wata a ƙasa?

    Kuma su Ɗusi da Sadik da Hurrul Amili, da Nuri Attabrasj da Ibn Tawus da suka rawaito falalar azumin; suna yaɗa sunnar banu Umayya ke nan? Ɗan uwa ka yi tunani.

    Daga ƙarshe ya kamata a sani cewa ruwayoyin da suke tabbatar da falalar ranar ashura da yin azumi a ranar ingantattu ne a wurin malaman Shi’a; amma waɗanda suke hani da sukar azumin raunana ne! Kamar yadda shaihunsu Alhaj Assayyid Muhammad Rida Alhusaini Alha’iri ya faɗa a littafinsa mai suna; “Najatul Umma fi lkamatil aza’i ala! Husaini wal a’ imma shafuka na 145, da 147, bugun binin Ƙum na Iran shekara 1413.

    Gaskiyar Magana

    Daga abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa gaskiyar magana game da ranar ashura da azuminta ita ce; Ranar Ashura rana ce mai daraja da ake yin azumi a cikinta tun kafin bayyanar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).

    Dukkanin musulmai tun daga annabawa har Ahlul Baiti sun yarda da haka. Duk abinda ya saɓawa abin da ya gabata ƙarya ne.

    Ya Allah ka ganar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ba Su Inganta Ba Game Da Ashura danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Malaman Mabera A Sakkwato

    Malaman Mabera A Sakkwato

    Malaman Mabera A Sakkwato Waɗanda Ke Tara Almajirai A Tsarin Tsangaya

    Waɗannan sun haɗa da Malam Mai Kaɗa da Malam Shehu da Malam Balarabe da Malam Nadaniya da Malam Giro. Makarantunsu sun shahara da tara almajirai da gardawa daga cikin Sakkwato da maƙwabtanta.

    Dukkan almajirai na haɗa Alƙur’ani ne da kuma Ɓangaren ilmin Furu’a a irin waɗannan tsangayu da ke Sakkwato.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Daga Malaman Alƙur’ani A Jihar Zamfara danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Takaitaccen Bayani A Kan Jihar Kano. danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Istimna’i (Masturbation)

    Istimna’i (Masturbation)

    Istimna’i (masturbation) shi ne mutum, mace ko namiji, ya yi amfani da hannuwansa ya riƙa wasa da al’aurarsa ko kuma wani sashi na jikinsa domin ya motsa sha’awarsa, har ya kai ga fitar da maniyyi ga namiji ko kuma ruwan saduwa ga mace. Sa’annan ana yin istimna’i da wasu kayan saduwa na roba ko na ƙarfe waɗanda turawa suke ƙerawa da ake kira “sex toys” ko “dildos”, kamar azzakarin roba, ko farjin roba, ko na’urar jijjiga (vibrator), da sauransu.

    Masu yin istimna’i suna yin sa ne domin tsananin sha’awar saduwar aure da suke da ita, amma ba su da abokan zama na aure waɗanda za su biya musu buƙatar.

    Wani lokacin kuma ana samu masu aure ma suna yin istimna’i, domin ba su zama wuri ɗaya da iyalinsu, ko akwai rashin ƙauna a tsakaninsu da iyalinsu, ko an sami rashin jituwar da ta sanya suna wuri ɗaya amma ba su hulɗa da juna.

    Musulunci ya yi hani mai ƙarfi daga yin istimna’i. Haka nan turawa da yahudawa su ma da ba su ɗauki istimna’i a matsayin laifi ba, amma suna ɗaukarsa abin kunya, domin ba su buƙatar a gansu suna yin sa.

    A likitance kuma, istimna’i yana da illoli kamar haka:

    1. Haddasa rashin haihuwa (infertility).

    2. Haddasa rashin isasshen ruwa a jiki (dehydration).

    3. Rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai a jiki (hormonal imbalance).

    4. Rage kaifin gani (loss of vision).

    5. Rage girman mazakuta ga namiji (decreased penile size).

    6. Cututtukan sanyin mara ga mata (pelvic inflammatory diseases).

    7. Rage ƙarfin mazakuta (erectile dysfunction).

    8. Rashin sha’awar saduwar aure tsakanin mata da miji (loss of libido).

    9. Fitar ƙuraje a jiki (body acne).

    10. Rashin isasshen ruwan maniyyi (low sperm count).

    11. Fitar gashi a tafin hannu (hairy palm).

    Ga waɗanda Istimna’i ya haifar masu da matsaloli ko rashin haihuwa matakin farko da ya kamata su ɗauka shi ne su je asibiti mafi kusa da su, idan so samu ne su je teaching hospital a ɓangaren family and reproductive health. A nan za a je a yi musu bayanin komai ba tare da ɓoye-ɓoye ba. Sa’annan a bi dukkan ƙa’idojin da zai gindaya na aune-aune da magunguna.

    Allah SWT ya yafe mana kurakuranmu, kuma ya yi mana mafita daga matsalolinmu, amin.

    Don karanta Hucewar Zazzaɓi danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Su Wanene Matasa?

    Su Wanene Matasa?

    Ya kamata kafin mu je ko’ina mu fara bayyana shin su wane ne matasa wato matashiya ko matashi. Akwai ra’ayoyi daga masana daban-daban game da batun matashi ko matashiya, kuma an karkasa su kashi-kashi mun kawo su kamar haka:

    Akwai matakin yarinta, wanda ya soma daga shekara uku zuwa goma sha biyu. Masana ilimin tarbiyya sun karkasa wadannan matakan shekaru zuwa shekara biyu zuwa biyar a matsayin lokacin fara girman yaro ko yarintar farko. Sai kuma shekara shida zuwa takwas a matsayin matsakaiciyar yarinta.

    Sannan kuma akwai shekara tara zuwa goma sha daya a matsayin lokacin yarinta na ƙarshe.Yara ba sa gushewa a cikin matakin yarinta har sai lokacin da suka zama baligai ta hanyar sha’awar jinsi wanda yake faruwa daga shekara goma sha ɗaya ga da namiji ko shekara goma sha uku ga ‘ya mace.

    Akwai shekarun yarinta wanda ya kama daga shekara bakwai zuwa goma sha biyu, lokacin da ake kula da mutum wajen yin ibada, musamman salla, kafin ya kai ga balaga.
    Sannan akwai kuma ayyamul murahaƙa, wato wanda bai balaga ba amma yana dab da balaga a tasakanin shekara goma sha huɗu zuwa goma sha bakwai (ya danganta da yanayin jikin mutumin ko saurin balaga ko kuma rashin balaga da wuri).

    Don haka ana ɗauka wannan ne lokacin da za a kira na tasawa (matasa). Ko kuma dab da balaga zuwa shekara ashirin da  biyar. Ana iya ɗaukar su a matsayin matasa wato muhariƙ d Larabci, wato matashi kenan.

    A addinance za mu iya ɗauka cewa, matasa su ne waɗanda suka balaga daga nan har zuwa shekara ashirin da biyar. Alwai kuma shekarar gwarzantaka wato lokacin da mutum ya kai shekara arba’in, sanda ya kai matsayin cikakken mutum.

    A binciken da aka gudanar wanda aka sanya a kundin ƙidayar al’umma na duniya za mu ga cewa waɗanda suka faɗo cikin wannana ƙwarya da ake cewa matasa su suka fi yawa a cikin al’ummar duniya baki ɗaya. Bayan haka kuma, hukumomi da masana sun yi ta bayyana su wanene matasa, kuma daga shekara nawa zuwa nawa ne za a iya ce wa mutum matashi, kamar yadda za mu gani a nan gaba, irin fassarori ko ma’anoni da aka bayar na zama matashi ko matashiya.

    Hukumar UNESCO ta bayyana matashi ko matshiya da cewa waɗanda shekarunsa suka tashi daga goma sha biyar zuwa ashirin da huɗu su ne matasa. A cikin ƙamus Oxford Dictionary, bugu na shida wanda aka buga a cikin shekara ta dubu biyu miladiyya (2000AD) kuwa, an bayyana matasa a matsayin lokacin yarinta zuwa girma.

    A kundintsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999 kua, tsarin mulkin ya ce waɗanda suka kama daga shekara goma sha takwas zuwa talatin da biyar su ne matasa. Idan muka yi la’akari da waɗannan mabambantan bayanai za mu gane su wane ne matasa. Amma a ƙasar Hausa abin ba haka yake ba, domin akwai bambancin matashiya mace da matashi namiji wajen shekara, domin a ƙasar Hausaba za a taɓa kiran mace ‘yar shekara arba’in a matsayin matashiya ba, sai dai mu ce daga shekara goma sha biyar zuwa talatin za a iya kiran ta matashiya.

    Masana halayyar dan Adam da rayuwarsa kuwa sun nuna cewa masu shekara tsakanin sha biyar zuwa arba’in, ko ka ce daga balaga zuwa shekara arba’in, su ne jinsi na matasa. A tsakanin waɗannan shekaru ne mutum yake kammala gina jikinsa da hankalinsa. Kuma a tsakanin waɗannan shekaru ne, kamar yadda masu sanin yanayin jikin ɗan Adam suka tabbatar cewa, jiki zai ta bunƙasa,a inda gaßobi kan ƙara tohuwa, kuma tunani na ƙara yawa har ya zuwa lokacin da ɗan Adam ya kai shekara ashirin da uku ko da biyar.

    A wannan lokaci ne tsawo ko girman ƙasusuwan ya ƙare, sai dai wataƙila tsoka ta ci gaba da ƙaruwa ga wanda Allah ya sa yana motsa jiki da kuma yanayi da abincin da mutum yake ci. Idan mjka yi nazari za mu ga cewa, waɗannan su ne shekaru na yin tunani, na gina menene mutum zai yi a rayuwuwarsa. Su ne lokuta na neman ilimi, lokuta na sassaƙa burace-burace na zan yi kaza zan yi kaza, na zan haifar da kaza.

    Lokaci ne da ake tunanin yin aure domin fara samun ‘ya’ya da makamantansu, lokaci ne na sha’awace-sha’awacen rayuwar duniya, domin a tsakanin waɗannan shekaru ne ake samun matasa suna sha’awar su zama masu kuɗi, suna sha’awar zama masu ilimi, suna sha’awara zama shugabanni da kuma sha’awar zama manyan ‘yan kasuwa.

    Duk waɗannan tunane-tunane da sha’awace-sha’awace suna zuwa ne a cikin waɗannan shekaru. Lokaci ne na jin ƙarfin jiki da zafin kai da na zuciya saboda sannan ne ake jin ƙarfi da kuzari, sannan ne ake da lafiya isasshiya. Saboda haka wajibi ne mu fahimci cewa, waɗannan shekaru ne masu muhimmancia rayuwar kowace irin al’aumma, kuma idan aka yi watsida yi wa jinsi na wannan al’umma saiti, to, ba yadda za a sami al’umma ta gari.

    Kamar yadda muka sani, matasa su ne ƙashi bayan ci gaban kowace al’ummaba tun yanzu batun lokacin rayuwar annabi mai tsira da amonci da sahabbansa. Haka nan a wannan lokaci da muke ciki su ɗin ne kan gaba a kowace sabga ta ci gaba da kuma bunƙasar rayuwar al’umma.

    Misali mu dubi irin gudunmawar da matasa suka bayar kamar irin su Abdullahi ɗan Umaru da Abdullahi ɗan Abbas da Ammar ɗan Yasir da Zaidu ɗan Harisata da Sabit ɗan Ƙais da Hisham ɗan Urwa da Abdullahi ɗan Salim da Sa’ada ɗan Abi Waƙƙas da kuma Mua’ab ɗan Umair waɗanda aka yi yaƙi da su, kuma wasunsu har hadisai sukan rawaito. Kuma duk shekarunsu sun fara daga ashirin ne zuwa ashirin da biyar.

    Mus’ab ɗan Umair ɗan masu kuɗi ne amma ba musulmi ne ba, ya yarda ya dawo musulunci ya haƙura da dukiyar gidansu ya amshi musulunci ya zo ya kasance tare da Annabi mai tsira da aminci.

    Haka kuma akwai mata matasa a zamanin Annabi (S.A.W) waɗanda suka taimakawa addinin musulunci, irin su Nana A’isha ɗiyar sayyadina Abubakar wadda aka rawaito hadisai sama da dubu huɗu daga gare ta. Haka ma Nana Hafsa ‘yar Umar ɗan Khaɗɗab wadda ajiye Alƙur’ani a wajenta da Asma’u ‘yar Abubakar Saddiƙ da sauransu, duk sun ba da gudunmawa a addinin musulunci.

    Sannan in muka dawo Nijeriya, Nana Asma’u ‘yar Shehu Usman Ɗanfodiyo ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin addinin musulunci don ta rubuta waƙoƙi masu yawan gaske da Hausa da Fillanci da kuma Larabci, sannan kuma ta fassara wasu waƙoƙin Shehu Usman Ɗanfodiyo, kuma ta koyar da mata a fannin addini da sana’o’i da zamantakewa.

    Danna nan do karanta Waye Bahaushe

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Domin ƙarin bayani, tuntuɓi gidandabino@yahoo.com

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Wasu Daga Malamai A Katsina

    Wasu Daga Malamai A Katsina

    Malam Sani Hafizi Katsina

    An haifi Malam Sani a shekara ta 1916. Ya fara karatun Alƙur’ani tun yana yaro ƙarami. An kai shi gabas (Maiduguri) don ya sami ƙwaƙƙwarar tilawa. Ya zauna a Nguru a inda ya haddace Alƙur’ani sannan ya tafi katagum yankin Guddiri daga bisani kuma ya isa Maiduguri. Ya zauna wurin Malam Ɗan kutama a Bazamfareri a inda ya Gyara tilawarsa.

    Malam Sani ya koma Katsina a shekarar 1994, wato shekarar guda Bayan rasuwar sarkin Katsina Muhammad Dikko. Malam Hafizu ya kafa tsangayarsa kusa da babban Masallacin juma’a da ke Katsina.

    Malam Salisu Gidan Liman Kurfi

    Malam Salisu ya shaharar da karatun Alƙur’ani a garin kurfi. Makarantarsa na karɓar baƙuncin ɗaruruwan almajirai a inda suke hadda ce Alƙr’ani. Mafi shahara daga ɗalibanta su ne Liman Ɗayyabu da Malam Daudu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Daga Fitattun Malaman Alƙur’ani A kurfi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Wasu Daga Fitattun Malaman Alƙur’ani A Kurfi

    Wasu Daga Fitattun Malaman Alƙur’ani A Kurfi

    Waɗannan Malamai sun haɗa da:

    Malam Umar Saulawa da Malam Sule Unguwar Maraɗi da Malam Yahaya Tsoho da Malam Abdu ƙofar Igi da Malam Ibrahim ƙofar Fada da Malam Dauda da Malam Sa’idu Nasarawa da Malam Musa Mahaddaci da kuma Malam Jume.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Malaman Ƙasar Zariya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.