Tag: yadda ake

  • Yadda Ake Egg Muffin

    Yadda Ake Egg Muffin

    Egg muffins abinci ne da ake yin sa daga ƙwai; ƙwai na da matuƙar amfani. Egg muffin yana da daɗi a karin kumallo ko tarar baƙi.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Ƙwai Dafaffe
    • Dankali Turawa
    • Dafaffafen nama
    • Koren tattasai
    • Tarugu
    • Albasa
    • Maggi
    • Curry da thyme
    • Gishiri kaɗan
    • Butter Ko mai
    • Baking power

    Yanda ake haɗawa

    1. A yayyanka nama, albasa, taruhu da dafaffen ƙwan. Amma kar a sa dafaffen dankali
    2. A kawo Curry da thyme kaɗan a sa, A ɗauko Maggi na ruwa a sa (za a iya amfani da su ne normal Maggi). Sai a juye a ajiye a gefe
    3. A sami ƙaramin kwano a fasa kwai, a ciki sai a sa baking powder sai gishiri kaɗan Sai a kara juyashi
    4. A ɗauko muffin pan a shafa mishi mai ko butter
    5. Sannan ki ɗauko Dafaffen dankali (yankakke) kisa a ciki
    6. Sai a sa a cikin oven a gasa, har sai ya gasu (ya zama golden brown)
    7. Za a iya ci haka ko kuma a haɗa shi da soyayyen dankali Turawa. A ci daɗi lafiya

    Domin sanin yadda ake potato balls danna nan

  • Yadda Ake Potato Balls

    Yadda Ake Potato Balls

    Potato Balls abinci ne wanda a Hausance ake kiran sa da Ƙwallon dankali, wanda ake yin sa da dankalin Turawa. Yana da matuƙar daɗi musamman ma idan a karin kumallo za a ci shi.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Dankalin Turawa (irish)
    2. Taruhu
    3. Albasa
    4. Kayan Ɗanɗano
    5. Man gyaɗa
    6. Ƙwai
    7. Fulawa

    Yadda ake haɗawa

    1. Farko za a dafa dankali, har ya dahu sai a bari ya huce sannan a yi mashing ɗin shi, a kwashe.
    2. A daka taruhu da albasa a zuba, a saka spices da seasoning.
    3. A saka lawashi, sai a juya ko’ina ya haɗe. A dinga ɗiban wannan mixture ana yinsa kamar ƙwallo a hannun ana ajiyewa.
    4. Sannan a barbaɗa masa fulawa. Za a kaɗa ƙwai, a sa masa gishiri, a ɗaura tukunya, a zuba mai.
    5. Idan ya yi zafi, a na ɗauko wannan haɗin da aka mulmula kamar ball, a sa cikin mai, ana soyawa.

    A ci daɗi lafiya.

    Domin sanin yadda ake cabbege sauce danna nan

  • Yadda Ake Cabbage Sauce

    Yadda Ake Cabbage Sauce

    Cabbage sauce miya ce wadda ake yinta da kabeji da jajjagen kayan miya, tana da daɗi da lafiya a jiki musamman ma idan aka kula da tsabtace da kayan girkin.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Cabbage
    2. Green pepper
    3. Peas
    4. Green beans
    5. Taruhu
    6. Tattasai
    7. Seasoning
    8. Gishiri
    9. Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. Farko za a yi granding din taruhu da tattasai da albasa a yanka lawashi a ajiye a gefe.
    2. A yanka cabbage da green pepper su ma, a ajiye su gefe.
    3. Sannan a zuba man gyaɗa a tukunya, idan ya yi zafi, sai a zuba albasa a juya.
    4. A zuba taruhu da tattasai ana juyawa.
    5. Sai a ɗan rufe na mintina biyu sai a wanke veggies a zuba, amma ban da cabbage da albasa su ne na ƙarshe.
    6. A juya, a sa seasoning a sake rufewa.
    7. Za a buɗe idan ya dahu, sai a zuba cabbage da albasa.

    Ita wannan sauce ana ci da abubuwa da yawa, tun daga farar shinkafa, da chapati, Fateera, har ma su jollof rice.

    Domin sanin Yadda Ake Moi-moi danna nan

  • Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

    Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

    Moi moi wadda muka fi sani da alala a Hausance ana yinta ne daga wake, alala ta kasance ɗaya daga cikin abincin gargajiya na bahaushe.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Wake
    2. Taruhu da tattasai
    3. Albasa
    4. Maggi
    5. Tafarnuwa
    6. Manja
    7. Sausage
    8. Ƙwai
    9. Karas

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki wanke wake a surfa, sai a zuba taruhu da tattasai da albasa a niƙa shi ya yi laushi sosai.
    2. Sannan a zuba wannan haɗin a cikin bowl a sa manja, maggi, tafarnuwa, da curry, za a iya saka cray fish ma, a juya shi sosai komai ya haɗe.
    3. A saka mai kaɗan a kan kaskon, a sa sausage da karas a yi stir frying nasu, sai a sauke. A dafa ƙwai a ɓare shi a yanka slices. Shi ma a aje a gefe.
    4. Za a kunna oven 180° sai a ɗauko parchment paper a shimfiɗa ta a kan faranti na gashi, a zuba ƙullun a saka a oven.
    5. Bayan mintina 10 in ya fara yi, sai a sauko da shi a zuba fillings ko’ina, a mayar ya gama gasuwa.
    6. Idan ya yi, za a ji ƙamshin ya haɗe ko’ina a sa toothpick a duba.
    7. Don a tabbatar ya dahu, a sauke a naɗe kaman naɗin tabarma.

    A ɗan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya.

    Domin sanin Yadda Ake Zobo Na Cucumba dannan nan.

  • Yadda Ake Zoɓo Mai Cucumber

    Yadda Ake Zoɓo Mai Cucumber

    Zobo na ɗaya daga cikin abin sha wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci, sauko da hawan jini musamman ma idan aka haɗa shi da cucumber.

    Kayan da ake buƙata

    • Zoɓo
    • Cucumber
    • Bakin flavour
    • Kanunfari
    • Citta
    • Kimba
    • Sugar

     Yadda ake haɗawa

    1. A wanke zoɓon, sai a zuba ruwa a ɗora a wuta
    2. A zuba su cittar a gurza cucumber a zuba a ciki sai sun dahu sosai
    3. Sai ki sauke a tace, a zuba flavour masu daɗi da daɗin ƙamshi, in an ji zaƙin ya yi, to ba  sai an zuba suga ba.
    4. In kuma akwai bukatar a zuba, sai a zuba, sai a juya sosai, sai a ɗan ƙara ruwa daidai yadda ake so,
    5. A saka ƙanƙara a frige, sai a samu kofi mai ƙayatarwa a zuba.

    A sha lafiya.

    Domin karanta Yadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya danna koren rubutu

  • Ladubban Addu’a A Musulunci

    Ladubban Addu’a A Musulunci

    WAƊANDA ALLAH KE GAGGAUTA AMSA ADDU’ARSU

    1. Addu’ar Annabawan Allah.
    2. Addu’ar mala’ikun Allah
    3. Addu’ar wanda aka zalunta.
    4. Addu’ar mai Ƙarfin imani da tsoron Allah.
    5. Addu’ar da mai biyayya ga iyayensa.
    6. Addu’ar mai Azumi.
    7. Addu’ar shugaba adali.
    8. Addu’ar iyaye (nagartattu) ga ‘ya’yansu.
    9. Addu’a ga ɗan uwa avbayan idonsa.
    10. Addu’ar mai jihadi.
    11. Addu’ar mai hajji ko umrah.
    12. Addu’ar mai dauwama cikin zikirin Allah.
    13. Addu’a ga mai karatun AlQur’ani.
    14. Addu’ar matafiyi (tafiya ta halal).
    15. Addu’ar mai taka tsantsan wajen haram;abincinsa,abin shansa,tufafinsa da mazauninsa.

    ABUBUWAN DA SUKE KAWO JINKIRIN AMSA ADDU’A

    1. Shirka ƙarama da babba.
    2. Ta’amuli da haram ci, sha ko tufafi.
    3. Nauyin zunubai da ƙeƙashewar zuciya.
    4. Barin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.
    5. Tafseel (Dalla-dalla) a cikin addu’a
    6. Wasa da wargi a cikin addu’a.
    7. Addu’a da zuciya gafalalliya mai shagala.
    8. Rashin ladabi a gaban Allah Jalla Wa’ala.
    9. Ta’allaƙa addu’a ga mashi’ah (In ka so)
    10. Gaggawa a cikin addu’a.
    11. Al-Istihsaar( Shi ne mutum ya bar addu’a saboda gajiya da kosawa)
    12. Rokon abin da hukuncin Allah ya gama da shi.
    13.Saja’i a cikin addu’a (shi ne mutum ya tilasta wa kansa daidaita harafin ƙarshen jumlolin addu’a )
    14. Bidi’o’i a cikin addu’a.
    15. Roƙon wani abu da ya shafi saɓon Allah ko yanke zumunta.

    Duba:
    1. TAS’HIHUD DU’A na Dr.BAKR
    2 ARRIYADUN NAZIRAH na Shk.Abdur Rahman Nasir Sa’adiy

    Domin karanta nasbar Manzo allah danna nan

  • Yadda Ake Pizza

    Yadda Ake Pizza

    Pizza abin maƙwalashe ne da ake yin sa da fulawa da wasu abubuwa na amfanin yau da kullum. Ana cin shi da shayi ko da lemo.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    · Fulawa
    · Gishiri
    · Yis
    · Olive oil (man zaitun)
    · Cheese Man shanun kanti
    · Mayonnaise
    · Kayan ƙamshi
    · Tumatir, albasa, koren tattasai
    · Tsokar kaza

    Yadda Ake Haɗawa

    1. Da farko za a jika yis da ruwan ɗumi, kamar tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun.
    2. Sannan sai ki ƙara fulawa a cikin wannan ruwan yis ɗin, ki kwaɓa har sai ya yi tauri.
    3. Idan ma kika ji shi ya yi ruwa ko laushi sosai, sai ki ƙara fulawa don ya yi tauri.
    4. Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30.
    5. Idan ya hau (kumbura), sai ki sami farantin gashi, ki juye fulawar a ciki, sannan ki sanya a cikin oven, ki gasa ki bar shi tsawon mintuna biyar.
    6. daga nan, sai ki yanka tumatir da farar albasa da koren tattasai ƙanana. Sai ki koma wurin fulawarki, ki duba idan ta gasu, sai ki fito da ita.
    7. Ki ɗauko kayan tumatir ɗin da kika yanka, sai ki zuzzuba a kai da ɗan garin kayan ƙamshi, ki barbaɓa.
    8. A sami tsokar naman kazarki, da kika yanka ƙanana, tare ki zuzzuba a kai. Sannan sai ki kawo mayonnaise ki yaryaɗa a kai.
    9. Sai ki zo ki rufe samansa da manshanun kanti (chease).
    10.  ki Mayar cikin abin gashin (oben) don ya kara gasuwa.
    11. Za ki ji yana ƙamshi sosai, sai ki fito da shi daga ciki, shi ke nan Pizza ta yi sai ci.

    Domin karanta Yadda Ake Mini Pizza ko Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa dannan nan.

  • Yadda Ake Mini Pizza

    Yadda Ake Mini Pizza

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake Mini Pizza; ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Abubuwan Buƙata:

    1. Biredi
    2. Tomato sauce
    3. Yankakkiyar albasa
    4. Yankakken Tumatur
    5. Koren tattasai yankakke

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A ɗauko biredi sai a yanka zuwa ƙawanya (round shape).
    2. Sai a shafa “tomato sauce”, a yaryaɗa albasa, tumatir da koren tattasai.
    3. A goga mozzarella cheese a saman haɗin biredi.
    4. Cikin oven mai zafi, sai a saka haɗin biredin har sai mozarella cheese ya fara narkewa.
    5. A ci lafiya.

    Domin koyon Yadda Ake Grilled Cheese And Corn Sandwich danna wannan koren rubutun.

  • Yadda Ake Grilled Cheese And Corn Sandwich

    Yadda Ake Grilled Cheese And Corn Sandwich

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin Grilled Cheese And Corn Sandwich. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Sweet corn (masarar gwangwani) ½ kofi
    2. Albasa ƙarama yankakkiya guda ɗaya
    3. Tafarnuwa babba 1
    4. Fenugreek bushasshe 1 ƙaramin chokali
    5. Attaruhu manya guda ɗaya jajjagagge
    6. Mai ƙaramin cokali 1 ɗaya
    7. Yankakken coriander leaves (ganyen coriander)
    8. Biredi yanka 4
    9. Cheese slice biyu
    10. Ƙwai 1 ɗaya

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A zuba mai a cikin tukunya mai ɗan zurfi, sannan a saka albasa da tafarnuwa a soya, sai a saka attaruhu da sinadarin ɗanɗano da fenugreek sai a fasa ƙwai shi ma, a haɗu a soya, a soya shi ya soyu, sai a sauke a bar shi ya huce.
    2. A cikin ƙaramin mazubi, a zuba butter da coriander a juya sosai shi ma, a ajiye a gefe.
    3. A ɗauki ko wani yankan biredi a shafa, wannan haɗin botar sai a ɗauko haɗin ƙwai a zuba a tsakiyar biredin, sannan a rufe da wani biredin.
    4. Sai a gasa a kan kaskon suya.

    Domin koyan Yadda Ake Hada Grilled Apple Peanut butter Sandwich danna wannan koren rubutun.

  • Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa

    Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin dafaffiyar gyaɗa. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Ko kun san dafaffiyar gyaɗa tana da sinadarai masu gina jiki, sannan kuma tana da ƙarancin calories wato kitse fiye da soyayyiyar gyada.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Gyaɗa mai ɓawo
    2. Ruwa

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A tsince gyaɗa, a gyara ta tsaf.
    2. Sai a zuba ruwa da gyaɗa cikin tukunya mai zurfi a rufe.
    3. A dafa shi na kimanin awa uku (3) sai a tace.

    Domin karanta Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau ko Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri danna koren rubutun nan.