Tag: yadda ake

  • Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau

    Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin gyaɗa marau-marau. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Ko kun san gyaɗa mai ɓawo ta fi bayar da kariya daga sinadarin (Aflotoxin), mai sanya cutar daji wato (cancer) a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Gyaɗa mai ɓawo
    2. Gishiri
    3. Toka
    4. Ruwa
    5. Ƙasar yashi ko toka

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A tsince dattin da gyaɗa ko mara kyau sannan a wanke ta fita.
    2. A zuba gyaɗa da gishiri cikin ruwa a dafa, kamar na munti 5-6. Sai a tace.
    3. A ɗora tukunya mai zurfi, idan toka ta ɗau zafi sai a saka wannan dafaffiyar gyaɗar a yi ta juyawa har sai ta yi.
    4. Idan ta yi, sai a juye domin shan iska.

    Domin koyar Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri

    Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin soyayyiyar gyaɗa mai gishiri. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Ko kun san soyayyiyar gyaɗa na saurin narkewa a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Gyaɗa rabin mudu (ɓararriyar gyaɗa/mara ɓawo).
    2. Ƙasa (kamar kofi biyu). Yashi ko toka.
    3. Gishiri chokali uku

     Yadda Ake Haɗawa.

    1. A tsince gyaɗa mara kyau, ko a bakace gyaɗar, domin fitar da marasa kyau. Sannan a wanke gyaɗar ta fita fes.
    2. A cikin roba mai zurfi a zuba ruwa, ɗan gishiri da kuma gyaɗar, sai a bar ta kamar na awa 3-4 bayan awannin, sai a tace a busar da shi a inuwa ko rana.
    3. A zuba ƙasa a cikin tukunya mai zurfi idan ƙasar ta yi zafi sai a zuba gyaɗar cikin ƙasar a yi ta juyawa, har sai gyaɗar ta gasu da kyau.
    4. Sai a sauke a raba gyaɗar da ƙasa, sannan a bar ta ta sha iska.

    Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Taliya danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Soyayyiyar Taliya

    Yadda Ake Soyayyiyar Taliya

    Soyayyiyar taliya samfarin abinci ne, da ake yi da taliya a maimakon a ci da miya ko dafa-duka. To wannan samfarin ma akwai shi da sauƙi wurin haɗawa kuma da daɗi wurin ci.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Taliya
    2. Tumatur
    3. Nama
    4. Kaza
    5. Karas
    6. Koren wake
    7. Peas
    8. Magi
    9. Curry
    10. Tafarnuwa
    11. Citta
    12. Albasa

    Yadda Ake Haɗawa

    A ɗora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sannan a zuba taliya da gishiri kaɗan. Idan ta yi tafasa ɗaya, sai a tsame. A ɗora man gƴaɗa a wuta, sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attaruhu. A tafasa nama, sannan a yayyanka shi ƙanana sannan a zuba.

    A zuba magi, kori da garin tafarnuwa da citta, sannan a ɗauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa kaɗan, sannan a rufe bayan mintuna biyar a sauke.

    A tafasa kaza, ta yi laushi haɗe da magi da kayan ƙamshi, sannan a soya da man gyaɗa. A soya tumatir da attaruhu da albasa. A zuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan sun soyu, sannan a ɗauko kazar a cakuɗa shi a ciki, sannan a ɗora a kan wannan soyayyiyar taliyar.

    Domin karanta Yadda Ake Macaroni 2 danna koren rubutu.

  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Ayaba da Kwakwa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Ayaba da Kwakwa

    Abubuwan da ake buƙata domin haɗa ƙunun gyada mai Ayaba da Kwakwa ba su da yawa; kunun gyada mai ayaba da kwakwa yana da matuƙar daɗi sosai musamman a ce an kula da tsafta a lokacin da ake haɗa sa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Kayan haɗi
    2. Gyaɗa
    3. Madara
    4. Ayaba
    5. Kwakwa
    6. Suga
    7. Shinkafar tuwo

    Yadda Ake Haɗawa:

    Ki samu gyaɗa, ki gyara ki wanke ki jiƙa, idan ta jiƙu, sai ki sabule ɓawan duka.
    Ki samu shinkafar tuwo ki jiƙa, idan ta jiƙu, ki haɗa da gyadar ki markaɗa, sannan ki tace ki ɗora a kan wuta.
    Ki ta juyawa saboda kar ya yi gudaji, idan yai kauri yadda kike buƙata, sai ki matsa lemon tsami ki sauke, idan ya ɗan sha iska.
    Sai ki zuba a kofi ki sa madara da suga, dama kin goga kwakwa ki zuba a kai; sai ki yanka ayaba ita ma ki jera a sama, shi kenan sai sha.

    Domin karanta Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga ko Yadda Ake Kunun Zaƙi danna koren rubutu.

  • Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

    Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

    A duk lokacin da ka samu kanka cikin wani hali na matsi a rayuwa, to ka tuna daman can Allah yana jarrabar bayinsa da masifu daban-daban.

    Allah Ya ce:

    “Wallahi sai mun jarraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawayar dukiya, da asarar rayuka da na kayan marmari, kuma albishir ga masu haƙuri”.
    (Baqara:115).

    Ka ga tunda mun fahimci kowane irin tsanani daga Allah ne; To, ka ga mun san babu mai yaye mana, sai Allah Maɗaukakin Sarki.

    Mene ne abin yi kenan?

    Abin yi shi ne mu rungumi wannan ƙaddara, da yin haƙuri, da koyi da yadda Annabi (S.A.W) ya ce mu yi.

    Jarrabawa na iya zama mabambanta a tsakaninmu. Wani rashin iyaye, wani cuta, wani talauci, wani rashin ‘ya’ya da dai sauransu.

    Wani lokacin kuma, ya zama Annoba ce da Allah ya jarrabi dukkanin al’umma. Wato kamar ciwon sarƙewar numfashi (Corona).

    Shi Musulmi duk abin da ya same shi na sharri da wahala ba za ka same shi yana raki ba. Kuma yai ta mita ko laƙanawa wani shi ya ja masa. Koda yake rauni irin na ɗan Adam ba a hana mutum baƙin ciki ba. Amma dai zai zama mai dogaro ga Allah.

    Matakan cin jarrabawar bala’in da yayi tsanani

    • Mu ƙasƙantar da kawunanmu. Mu tuba, mu yi nadama. Mu yawaita istigfari.
    • Mu yawaita karatun Ƙur’ani.
    • Mu bincika tsakaninmu da iyayenmu mu gyara. Mu dinga kyautata musu.
    • Ma’aurata su gyara tsakaninsu.
    • Mu yawaita sadaka.
    • Mu yawaita addu’a Allah Ya yaye mana. Ya kawo mana mafita.
    • Mu yawaita: Hasbunallahu wa ni’imal wakeel.
      Lahaula wala quwwata illa billah.
      La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimn.

    A ƙarshe mu sani, mai sauƙi ne a wajen Allah ya yaye mana kowanne irin bala’i. Saboda haka, mu gaggauta gyara tsakaninmu da Mahaliccinmu. Sannan kuma ga dukkanin jarrabawa irin ta Annoba; Mu bi shawarar malamai, da shugabanni, da ma’aikatan lafiya.

    Da bin waɗannan in sha Allahu sai ka ga mun yi nasara. Mun ci jarrabawar bala’in da ya tsananta cikin sauƙi.

    Wallahu A’alam.

    Duba Yadda Ake Tsaftace Baki

  • Yadda Ake Faten Wake Da Doya

    Yadda Ake Faten Wake Da Doya

    Barkanmu da  kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake faten wake da doya. Tare da ni Hafsat Shettima.

    Abubuwan haɗawa:

    • Wake (½ kofi)
    • Doya peeled and washed (gwargwadon buƙata)
    • Attaruhu Jajjagaggen 5 (ko gwargwadon buƙata)
    • Jajjagaggen Tattasai 2
    • Jajjagaggen Albasa 2
    • Kifi busasshe
    • Cray fish niƙaƙƙe
    • Manja
    • Ogu leave Yankakken
    • Maggi
    • Curry
    • Jajjagaggen Tafarnuwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a dafa wake ya nuna sai a ajiye a gefe.
    2. A cikin wata tukunya mai zurfi, a saka manjan, sannan a yanka albasa ya ɗan fara soyuwa, sai ki zuba kayan miyanki, maggi, curry da tafarnuwa idan ya soyu, sai ki zuba ruwa ya ɗan tafasa.
    3. Sai ki zuba doya da ogu da kifi sannan a rufe ya yi kamar minti 10-15 ko kuma idan doyar ta yi laushi, sai ki zuba wake a juya. A yi a hankali wurin juyawa kar waken ya farfashe.
    4. A bar shi na minti 4-5 sannan a sauke.
    5. A ci da fanke ko a haka.

    Domin koyan Yadda ake farfesun kayan ciki a sauƙaƙe danna wannan koren rubutun

  • Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe

    Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe

    Barkan mu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa; A yau za mu koyi yadda ake farfesun kayan ciki a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettima.

    Farfesun kayan ciki na mutum 3-4

    Abin da ake buƙata

    • Kayan ciki (Na rago, shanu, ko akuya)
    • Albasa yankakken matsakaita 2s
    • Jajjagaggen Tumatir matsakaita 1
    • Attaruhu Jajjagaggen (to taste)
    • Jajjagaggen Tattasai madaidaita 2
    • Sinadarin ɗanɗano (Maggi, Knorr, onga, etc.)
    • Sinadarin ƙamshi (Garlic, gyaɗar miya, curry, etc)
    • Ruwa kofi 3 da rabi

    Yadda ake haɗawa

    1. A wanke kayan ciki sosai su, fita tsaf.
    2. Cikin tukunya mai zurfi a zuba kayan ciki da rabin albasa, kayan ƙamshi da kofi biyu ruwa, da Sinadarin ɗanɗano.
    3. Idan ya dahu sai a saka markaɗaɗɗen kayan miya da saura kayan ɗanɗano, a ɗan bar shi kamar minti 4-5, sai a juye raguwar ruwa a bar shi ya ci gaba da dahuwa na minti 10-15.

    Domin koyan Yadda ake Farfesun Ganda na musamman danna wannan koren rubutun.

  •  Yadda Ake Farfesun Ganda Na Musamman

     Yadda Ake Farfesun Ganda Na Musamman

    Barkanmu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa; A yau za mu koyi yadda ake farfesun ganda. Tare da ni Hafsat Shettima.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Ganda
    • Jajjagaggiyar albasa matsakaita 2
    • Tumatir  Jajjagaggen matsakaita 2
    • Jajjagaggen Attaruhu (to taste)
    • Tattasai Jajjagaggen madaidaita 2
    • Sinadarin ɗanɗano (Maggi, Knorr, onga, etc.)
    • Sinadarin ƙamshi (Garlic, gyadar miya, curry, etc)
    • Ruwa kofi 3 da rabi

    Yadda ake haɗawa:

    1. Asa ganda cikin pressure cooker a dafa, har sai ta yi laushi.
    2. Cikin tukunya mai zurfi, a sa ganda da kayan ƙamshi, da markaɗaɗɗen kayan miya da saura kayan ɗanɗano kofi biyu ruwa.
    3. Idan ya dahu sai a saka, a ɗan bar shi kamar minti 4-5 sai a sauke.
    4. Za a iya ci da French bread ko kuma as starter. Wannan shi ne yadda ake farfesun ganda.

    Domin koyan Yadda ake danderun nama sabon salo danna wannan koren rubutun

  • Yadda Ake Danderun Nama Sabon Salo

    Yadda Ake Danderun Nama Sabon Salo

    Abubuwan haɗawa

    1. Nama
    2. Albasa
    3. Attarugu
    4. Yaji
    5. Maggie
    6. Gishiri
    7. Mai
    8. Spice da kike so, ko kike da shi (na yi amfani da black pepper, nut meg da coriander powder)
    9. Seasoning da kike so
    10. Tafarnuwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Za ki wanke namanki, sai ki ajiye a gefe.

    2. Ki daka nutmeg da black pepper in ba ki da dakakkiya.

    3. Ki nemi roba ki sa mai, attaruhu, albasa, yaji, Onga classic, tafarnuwa, maggie, spice and seasoning.

    4. Sai ki zuba su nutmeg naki da kika daka a cikin bowl ɗin, ki haɗa su.

    5. Ki ɗauko namanki ki sa wuƙa, ki ɗan tsatstsaga ta.

    6. Sannan ki ɗauko marinate naki, na roban ki shafa ko’ina a jikin naman kowane lungu da saƙo.

    7. Bayan kin gama marinating, sai ki nemi tukunya ki sa ruwa, sai ki sa murfin kwano a ciki sannan ki sa denderun naki.

    8. Ki nemi paper foil/ko normal paper ki rufe naman naki. Ki bar shi a kan wuta ya nuna.

    Ƙarin Bayani

    1. Ba a juya danderu haka nan zai nuna a low temperature.

    2. Mafiya yawa a sallah (Eid Kabir), muna yi da daddare, mu bar shi a ƙasan garwashi, har gari ya waye.

    3. Yawanci ana amfani ne da wuyan rago ko side na rago ko kuma cinyar rago wajen danderu.

    4. Idan danderu ya nuna, kina taɓawa za ki ga naman na barin jikin ƙashin, alamun ya yi kenan.

    5. Kisa enough kayan haɗi, gun yin danderu su Maggie da sauransu. Akwai wani abu ɗaya da danderu in ba ki sa enough maggie ba, in ya nuna za ki ji taste din ya koma baya, to maggi bai jiba. Saboda Haka, ki sa Maggi da seasonings su ji, amma kuma kada ki sa sosai.

    Danna koren rubutu domin karanta Yadda Ake Onion Sauce

  • Yadda Ake Kunun Zaƙi

    Yadda Ake Kunun Zaƙi

    Kunun zaƙi

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Gero
    2. Kanunfari
    3. Girfa
    4. Citta
    5. Sugar
    6. Ruwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Ki samu gero ki sa ruwa ki wanke, sai ki jiƙa ta, kamar na awa biyu
    1. Sai ki raba shi kashi biyu, kashi ɗaya ki ɗaura ruwa a kan wuta, in ya tafasa, sai ki zuba a kai ki juya. Kashi ɗayan kuma, ki zuba ruwan sanyi akai, sai ki haɗa da ɗayan, ki juya su duka.
    1. Idan ya yi kaurin da kike so, shi kenan inda buƙatar ƙara ruwa, sai ki ƙara. Sannan ki samu abun tata ki tace, sai ki sa suga.

    Ki nemi gora ki ɗura a ciki, sannan ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha.

    Domin karanta Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo danna koren rubutun nan.