Tag: Kunun gyada

  • Yadda Ake Haɗa Hallaka Kwabo

    Yadda Ake Haɗa Hallaka Kwabo

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin hallaka ƙwabo ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Hallaka kwabo nau’in alawa ce da ake yi da gyaɗa wadda za a iya ajiyewa domin ba wa yara.

    Abubuwan Buƙata

    1. Gyada mai kyau
    2. Sugar
    3. Lemon tsami (a matse ruwan)

    Yadda ake haɗawa

    1. A daddaka gyaɗa, amma ba sosai ba
    2. Cikin tukunya mai tsafta a zuba ruwa, sugar da lemon tsami, a bar shi ya dahu na mintuna 18-20
    3. A zuba gyaɗa, a ci gaba da juyawa sai ya yi brown sosai
    4. A shafa mai a farantin silver sai a juye wannan hallaka kwabo a kai, a baza shi sosai
    5. Sai a yayyanka shi zuwa desired shapes

    Domin koyon Yadda Ake Biskit din Gyaɗa (groundnut cookies) danna nan

  • Yadda Ake Haɗa Lemon Gyaɗa, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake)

    Yadda Ake Haɗa Lemon Gyaɗa, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake)

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake yin lemon gyaɗa, shinkafa da dankalin Hausa (groundnut, rice, sweet potato shake) ku biyo ni a sannu, domin mu koya tare……

    Ko kun san Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.

    Abubuwan Buƙata

    1. Shinkafa ½ rabin kofi
    2. Gyaɗa ½ rabin kofi
    3. Dankalin Hausa
    4. Gyaɗa soyayyiya
    5. Siga
    6. Madara

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A wanke shinkafa a jiƙa ta, sai ta yi laushi.
    2. A fere dankalin Hausa a yayyanka.
    3. A soya gyaɗa a busar da ita.
    4. Sai a haɗe gyaɗa, dankali da kuma jiƙaƙƙiyar shinkafa a markaɗa a tace da abun tata.
    5. A raba ruwan gyaɗa biyu, a ɗora a wuta har sai ya yi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke a haɗe da ragowar ruwan gyaɗar, a saka madara da siga. Za a iya ƙara ruwa daidai kaurin da ake so.
    6. Za a iya tace shi da rariya, idan ya yi gudaji-gudaji, sai a saka a fridge ya yi sanyi.
    7. Asha lafiya.
  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida NIjeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Abubuwan buƙata

    1. Gasarar gyaɗa (groundnut butter)
    2. Gero
    3. Citta [optional]

    Yadda ake haɗawa

    1. A jiƙa gero da daddare zuwa safe, sai a saka citta a kai markaɗe, in an dawo a tace, a fitar da dusa.
    2. A ɗebo gasarar gyaɗa sai a zuba wadataccen ruwan da zai dama kunu. A juya da kyau a sa rariya a tace a cikin tukunya mai zurfi a ɗora a kan wuta.
    3. Idan gasarar gyaɗar ya tausa sai ajuye a cikin gasarar gero a juya. Sai a zuba lemon tsami, ko tsamiya ko ɗan tsami
    Domin sanin yadda ake kunun gyada danna nan
  • Yadda Ake Lemon Ardeb

    Yadda Ake Lemon Ardeb

    A yau za mu koyi yadda ake lemon ardeb, da yawan mutane ba su san me ake kira ‘Ardeb’ ba.

    Wannan ardeb dai lemo ne kamar lemon tsamiya. Kuma yana da alaƙa da mutanen Maiduguri. A irin wannan yanayi da muka shiga, ana yawan haɗa wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi, ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Tsamiya
    • Siga
    • Masoro
    • Kanamfari
    • Citta
    • Ruwa

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A samu tsamiya a wanke tsaf, ya fita sannan a jiƙata ta jiku, sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari.
    2. Sannan a ɗora tukunya a wuta, bayan ta yi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa.
    3. A ɗauko wannan jiƙaƙƙiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan;
    4. Kuma sanya shi a gidan sanyi domin ɗanɗano ya fito sosai.
    5. Daya hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace.
    6. A ɗora tukunya a wuta bayan tukunya ta yi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Haɗin ‘ardeb’ ya haɗu.

    Domin sanin Yadda Ake Tsiren Nama danna nan

  • Yadda Ake Kunun Aya

    Yadda Ake Kunun Aya

    Aya tana ƙara ƙarfin garkuwar jiki ga mai yawan amfani da ita. Aya tana inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita ƙuruciya, tana ƙarfafa yanayin gudanar jini, sannan tana ƙara kuzari na zahiri.

    Haka kuma Aya tana da amfani ga sha’anin da ya shafi ciki da hanji, tana ɗauke da sinadarin dake hana cushewar ciki da kuma kumburi. Har ila yau, tana taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral mara kyau a cikin jini.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Aya
    • Suga
    • Ɗanyar citta
    • Flavour
    • Kwakwa
    • Madarar ruwa
    • Dabino

    Yadda ake haɗawa

    1. A jiƙa aya ta jiƙu, a wanke ta, a saka kwakwa 1 da dabino kamar 7 ko 10, da citta ɗanya ko busasshiya, sai a niƙa.

    2. Sai a tace, a zuba madara a ciki, a sa suga da flavour a juya, a jefa ƙanƙara ko asa a fridge.

    Domin sanin Yadda Ake Spicy Meat danna nan

  • Yadda Ake Zoɓo Mai Cucumber

    Yadda Ake Zoɓo Mai Cucumber

    Zobo na ɗaya daga cikin abin sha wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci, sauko da hawan jini musamman ma idan aka haɗa shi da cucumber.

    Kayan da ake buƙata

    • Zoɓo
    • Cucumber
    • Bakin flavour
    • Kanunfari
    • Citta
    • Kimba
    • Sugar

     Yadda ake haɗawa

    1. A wanke zoɓon, sai a zuba ruwa a ɗora a wuta
    2. A zuba su cittar a gurza cucumber a zuba a ciki sai sun dahu sosai
    3. Sai ki sauke a tace, a zuba flavour masu daɗi da daɗin ƙamshi, in an ji zaƙin ya yi, to ba  sai an zuba suga ba.
    4. In kuma akwai bukatar a zuba, sai a zuba, sai a juya sosai, sai a ɗan ƙara ruwa daidai yadda ake so,
    5. A saka ƙanƙara a frige, sai a samu kofi mai ƙayatarwa a zuba.

    A sha lafiya.

    Domin karanta Yadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya danna koren rubutu

  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Ayaba da Kwakwa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Ayaba da Kwakwa

    Abubuwan da ake buƙata domin haɗa ƙunun gyada mai Ayaba da Kwakwa ba su da yawa; kunun gyada mai ayaba da kwakwa yana da matuƙar daɗi sosai musamman a ce an kula da tsafta a lokacin da ake haɗa sa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Kayan haɗi
    2. Gyaɗa
    3. Madara
    4. Ayaba
    5. Kwakwa
    6. Suga
    7. Shinkafar tuwo

    Yadda Ake Haɗawa:

    Ki samu gyaɗa, ki gyara ki wanke ki jiƙa, idan ta jiƙu, sai ki sabule ɓawan duka.
    Ki samu shinkafar tuwo ki jiƙa, idan ta jiƙu, ki haɗa da gyadar ki markaɗa, sannan ki tace ki ɗora a kan wuta.
    Ki ta juyawa saboda kar ya yi gudaji, idan yai kauri yadda kike buƙata, sai ki matsa lemon tsami ki sauke, idan ya ɗan sha iska.
    Sai ki zuba a kofi ki sa madara da suga, dama kin goga kwakwa ki zuba a kai; sai ki yanka ayaba ita ma ki jera a sama, shi kenan sai sha.

    Domin karanta Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga ko Yadda Ake Kunun Zaƙi danna koren rubutu.

  • Yadda Ake Koko

    Yadda Ake Koko

    Koko abinsha ne na karin kumallo na hausawa, wanda ake yin sa daga gero. Koko na da daɗin sha, ga matuƙar amfani a jiki.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    Gero
    Citta
    Barkono
    Kanunfari

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A jiƙa gero ya jiƙu sosai, sai a zuba citta, kanunfari da ɗan barkona kaɗan, sai a niƙa.

    2. Sai a tace shi da abin tata, a fitar da dusar da gasarar, sai a bar shi ya kwanta.

    3. A tafasa ruwa a kwano daban, kuma sai a ɗebi kwantacciyar gasarar nan, sai a ƙara mata ruwa a juya ta ɗan yi kauri kaɗan.

    4. Sai a sheƙa mata wannan tafashasshen ruwan zafin da sauri sai a motsa kaɗan.

    Domin sanin yadda ake burabusko danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Kunun gyaɗa na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da amfani a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan da ake buƙata;

    Farar shinkafa

    Ɗanyar gyaɗa 

    Sugar daidai misali

    Yadda ake haɗawa

    A gyara farar shinkafa sai a wanke ta, a tsane tsaf. Bayan haka, a soya gyaɗa sama-sama a murje, bayan an bushe, sai a markaɗa, bayan an markaɗa a tace.

    Sai a zuba tataccen ruwan gyaɗar a tukunya, in ya tafasa, sai a ɗauko wanna shinkafar da aka wanke aka tsane, sai a zuba ta a ciki, su yi ta dahuwa har sai ta dahu sosai.

    Don gudun kada ya tsinke, za ki iya zuba ruwan lemon tsami kaɗan. Idan kuma an ga bai yi kauri ba, sai ki ɗan ɗibi gasarar koko a dama da ruwan sanyi sai a zuba a juya sosai zai yi kauri.

    Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa danna koren rubutun nan.