Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci

0
554

Ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa dangane da waƙafi a matsayinsa na sadaka; wacce ladan ta yake ɗorewa har bayan rayuwar wanda ya yi ta. Kamar yadda ya zo a cikin faɗin Allah Maɗaukakin Sarki; “Kuma ku tsayar da sallah kuma ku bayar da zakka kuma abin da kuka gabatar; domin kanku daga alheri za ku same shi a wurin Allah, lalle ne Allah ga abin da kuke aikatawa mai gani ne”. (Baƙara aya ta 110).

Haka kuma ya zo a hadisin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa; a lokacin da ɗan Adam ya rasu dukkan ayyukansa sun tsaya in ban da abubuwa guda uku; sadaka mai gudana (waƙafi), ko wani ilmi da ake amfana da shi; ko ɗa nagari da yake yi masa addu’a.

Haka nan fassarar abin da ake nufi da sadaka mai gudana ta zo a wani hadisi da Ibn Majah ya ruwaito; wanda a cikinsa ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa; “Lalle abin da kawai zai cigaba da iske mumuni na kyawawan ayyukansa bayan mutuwarsa. Shi ne wani ilimi da ya yaɗa ko ɗa na ƙwarai da ya bari ko wani Alƙur’ani da ya bar gadonsa; ko wani masallaci da ya gina ko kuma gida da ya gina don (amfani) matafiya.

Ko wata ƙorama da ya tona take gudana ko kuma wata sadaka da ya fitar daga cikin dukiyarsa; a lokacin da yake da lafiya sanda yake raye wacce ladanta zai ci gaba da riskarsa har bayan rayuwarsa”.

Haka nan kuma ya zo a cikin littattafan sirah cewa; a lokacin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi Hijira daga Makka ya sauka birnin Madina. A duk faɗin birnin, babu wata hanya ta samun ruwan sha mai daɗi, sai wata rijiya da ake kira rijiyar Rumah, wacce a wancan lokaci mallakar wani marowacin mutum ce; wanda yake tsawwalawa mutane wajen sayen ruwanta.

Ganin haka sai Ma’aiki Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwaɗaitar da sahabbansa da cewa; “Wane ne zai sayi rijiyar Rumah (ya sadaukar da ita) Allah ya biya shi da mafiticinta a gidan Aljannah wanda nan take kuwa Sayyidina Uthman ya saye ta dirhami dubu talatin da biyar, kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi “Ka sadaukar da ita ga musulmai, Allah zai ba ka lada, shi kuwa bai yi wata-wata ba ya aikata hakan.

Haka nan Bukhari da Muslim sun ruwaito daga sayyidina Umar ɗan Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) cewa; ya ce da ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na sami wata gona a Khaibara; wacce ban taɓa samun wata dukiya da ta kai darajarta a tsawon rayuwata ba”.

Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Idan ka ga dama kana iya riƙe asalinta ka sadaukar da amfaninta da Sayyidina Umar. Ya ji haka sai ya sadaukar da ita bisa sharaɗin cewa, ba za a sayar da ita kanta gonar ko a kyautar da ita ko a ci gadonta ba; tare da sadaukar da duk wani amfani nata ga talakawa, da ‘yan uwa, da bayi; da hanyoyin ɗaukaka addinin Allah, da baƙi, da kuma matafiya.

Babu laifi ga masu kula da ita su ci ‘ya’yan itatuwanta; su kuma yi kyauta ga abokansu gwargwadon yadda aka sani a al’adance ba da sayarwa ba.

Wannan al’amari na waƙafi ya watsu matuƙa a cikin sahabban Ma’aikin Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bayan kwaɗaitarwar da ya yi da aikata hakan. Domin kuwa sun yi waƙafi na abubuwa daban-daban da suka haɗa da masallatai da gonaki; da rijiyoyi da kayan jihadi don ɗaukaka kalmar Allah.

Ya tabbata cewa adadi mai yawa na sahabban Ma’aikin Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun yi waƙafi. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Khalid ɗan Walid, da Jabir ɗan Abdullah, da Sa’ad ɗan Ubadah; da Ukbat Abdullahi ɗan Zubair, da Sa’ad ɗan Abi Waƙƙas, da uwar muminai Sayyidatina A’isha; da kuma Asma’u yar Abubakar – Allah ya yarda da su gaba ɗayansu.

Babu wani mai hali daga cikin sahabban Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; wanda bai yi waƙafi ba, Haka kuma an rawaito daga Imam ash-Shafi’iya na cewa; “Labari ya ishe ni cewa mutum tamanin daga cikin sahabban ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; ‘yan Madinah kowanne a cikin su ya yi waƙafi” .

Domin karanta cikakken bayani a kan Manufofin Waƙafi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan

Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma. Wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceManufofin Waƙafi
Labarin na GabaMa’anar Waƙafi