Sunayen ‘Ya’yan Manzon Allah (S. A. W)

0
3158

Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Manzon Allah Sallahu alaihi wa Sallam wanda ya haifa maza da mata, da kuma ɗan taƙaitaccen bayani a kansu. Allah ya ƙara yarda da su.

Sunayensu da taƙaitaccen bayani:

1.ALƘASIM (Radiyallahu ta’ala anhu): Saboda shi ake kiran Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) Abul Kasim, ya rasu tun yana jariri a Makkah.
2.ZAINAB (Radiyallahu ta’ala anha ): Matar Abul’ Aas Dan Rabi’a (Radhiyallahu anhu) ita ce babba a ‘ya ‘yan manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam). Ta rasu a shekara ta 8 da hijira.
3.RUKAYYAH (Radiyallahu ta’ala anha): Usman (Radhiyallahu anhu) ya aure ta, suka yi hijira tare zuwa abyssinia (Ethiopia). Ta rasu a lokacin yaƙin badar.
4.UMMU KURTHUM (Radiyallahu ta’ala anha): Usman (R.A) ya aure ta bayan Rukayyah (R.A) ta rasu  a shekara ta 9 da hijira.
5.FATIMA (Radiyallahu ta’ala anha): Ummu abiha (babar mahaifinta) ita ce wacce manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) ya fi so a yaransa, ta auri Ali dan Abi Ɗa’lib (R.A). Ta rasu bayan wata shida da wafatin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam).
6.ABDULLAHI: Laƙabinsa shi ne Taahir da Tayyib, an haife shi bayan Annabci, kuma ya rasu yana yaro a Makkah.

Domin sanin wanɗanda suke kama da manzon Allah Sallahu alaihi wasallam ko wadanda suka fi rawaito hadisi danna koren rubutu nan.

labarin da ya wuceMutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W)
Labarin na GabaYadda Ake Tuwon Shinkafa