Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Manzon Allah Sallahu alaihi wa Sallam wanda ya haifa maza da mata, da kuma ɗan taƙaitaccen bayani a kansu. Allah ya ƙara yarda da su.
Sunayensu da taƙaitaccen bayani:
1.ALƘASIM (Radiyallahu ta’ala anhu): Saboda shi ake kiran Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) Abul Kasim, ya rasu tun yana jariri a Makkah.
2.ZAINAB (Radiyallahu ta’ala anhu): Matar Abul’ Aas Dan Rabi’a (Radhiyallahu anhu) ita ce babba a ‘ya ‘yan manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam). Ta rasu a shekara ta 8 da hijira.
3.RUKAYYAH (Radiyallahu ta’ala anhu): Usman (Radhiyallahu anhu) yaaure ta, sukai hijira tare zuwa abyssinia(Ethiopia). Ta rasu a lokacin yaƙin badar.
4.UMMU KURTHUM (Radiyallahu ta’ala anhu): Usman(R.A) ya aure ta bayan rukayyah (R.A). Ta rasu a shekara ta 9 da hijira.
5.FATIMA (Radiyallahu ta’ala anha): ummu abiha (babar mahaifinta) ita ce wacce manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) ya fi so a yaransa, ta auri Ali dan Abi Ɗa’lib (R.A). Ta rasu bayan wata shida da wafatin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam).
6.ABDULLAHI: laƙabinsa shi ne Taahir da Tayyib, an haife shi bayan Annabci, kuma ya rasu yana yaro a Makkah.
Domin sanin wandanda suke kama da manzon Allah Sallahu alaihi wasallam ko wadanda suka fi rawaito hadisi danna koren rubutu nan.