Shin Ko Ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗantsubbu (Mai Duba) Domin Sihirce Kishiya?

0
38

A’a, ina fa zuwa wajen boka ko ɗantsubbu (mai duba) zai halatta! Ai haramun ne a musulunce Musulmi ya je wajen boka ko ɗantsubbu (mai duba), ko da kuwa da nufin ya tambaye su ne, ballantana kuma ya yarda da abin da za su gaya masa na bokancin ko kuma duban. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Dalili kuwa Imamu Muslim ya rawaito hadisi da ka karɓo shi daga Hafsa (Radiyallahu An ha) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda yaje wajen wani mai jin yana da masaniyar abubuwa tun kafin faruwarsa sai ya tambaye shi game da wani abu,to, ba za a karɓi wata sallarsa ba har tsawon kwana arba’in.

Idan kuwa har Musulmi ya kuskura ya gasgata abin da boka ɗan duba ya gaya masa, to ya yi asarar imaninsa. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Dalili kuwa an karɓo hadisi daga Abu Huraira (Radiyallahu An hu) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “duk wanda ya je wajen boka ya gasgata shi game da abin da yake faɗa, to, haƙiƙa ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Abu Dawud, Tirmizi, Ibn Majah, Darimi da wasunsu ne suka rawaito shi. 

Sannan kuma a dangane da sihirce kishiya; akwai cutar da muminar baiwar Allah gashi kuwa Allah maɗaukaki ya ce: 

“Waɗanda suke cutar muminai maza da mata, ba tare da sun yi laifi ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayananne”.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

labarin da ya wuceAbubuwan Da Ke Sa Kishiyoyi Shiri Da Zaman Lafiya
Labarin na GabaHukunci Da Abinda Allah Ya Saukar