Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad

0
1105

Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad – Suratul Ikhlas; ita ce sura ta (112) a jerin surorin Alƙur’ani mai girma, a wasu lokutan ana kiran ta da Ƙulhuwallahu Ahad, wato ana ambaton ta da ayar farko da ta fara da ita.

Wannan sura mai albarka, tana cikin surorin da aka saukar a Makka, kuma ayoyinta (4) ne; kamar haka:

Bismillahir Rahmanur Rahim
Ƙulhuwallahu ahad(1), allahusamad(2), lamyalid walamyulad(3), walamyakullahu ƙufuwan ahad(4).
Ka ce: shi Allah ɗaya ne (tak)(1). Allah wanda ake nufa da buƙata(2). Bai haifa, kuma ba a haife shi ba(3). Kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi(4).

An saukar da wannan sura ne don tabbatar da:

1. Ɗayantakar Allah ta zati da siffa da kuma aiki.
2. Sanar da bayi wadatuwar Allah daga komai, tare da buƙatuwar komai zuwa ga falalarsa da jinƙansa.
3. Rushe aƙidar danganta wa Allah uba ko kuma ɗa.
4. Kore daidaita wani bawa da Allah.

Domin Karanta cikakken bayani a kan Falalar Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

FALALARTA: 

An karɓo hadisi daga Abu Sa’idil khudri Allah ya yarda da shi ya ce: Ɗan ‘uwana Ƙatada ɗan Nu’uman ya ce: 

Haƙiƙa wani mutum ya yi tsayuwar dare a lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam), sai ya yi ta karanta ƙulhuwallahu Ahad (Bayan Fatiha), bai ƙara wata sura ba, da gari ya waye sai ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambata masa tsayuwar daren da ya yi da ƙulhuwallahu Ahad, yana ganin kamar surar ta yi kaɗan. 

Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: 

“Na rantse da wanda raina yake hannunsa tabbas tana daidai da ɗaya bisa uku (1/3) na Alƙaur’ani”. (Wato wajen samun lada). Bukhari ne ya rawaito shi. 

Kuma an Karɓo daga Anas ɗan Malik, Allah ya yarda da shi ya ce: Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ina matuƙar son wannan sura: “Ƙulhuwallahu Ahad”. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “son da kake yi mata ya shigar da kai Aljanna”. Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi. 

Sannan an karɓo wani hadisin daga Buraida ɗan Husayyib Allah ya yarda da shi ya ce: “Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa: 

“Ya Allah ina roƙon ka, ina mai tabbatar da na shaida tabbas kai kaɗai ne abin bauta, babu wani abin bautawa (na gaskiya) sai kai kaɗai, ɗayan da ake nufa da buƙata, wanda bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi”. 

Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Tabbas ka roƙi Allah da sunansa wanda in har aka roƙe shi, to zai bayar da abinda aka roƙa, kuma idan aka kira shi da shi, to zai amsa”. Imam Ahmad, Abu Dawud, Tirmizi da wasunsu ne suka rawaito shi.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

MUHIMMANCIN ƘULHUWALLAHU AHAD DA BAYANIN GURAREN DA MANZON ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) YAKE KARANTA TA: 

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni da karanta ƙulhuwallahu Ahad, kuma shi ma ya kasance yana 

karanta ta a gurare daban-daban, saboda muhimmancin da take da shi. 

  1. Ya yi umarni a karanta ta bayan idar da sallar Farilla, kamar yadda Abu Dawud Tirmizi, Nasa’i da wasunsu suka rawaito daga Uƙbatu ɗan Amir, Allah ya yarda da shi. 
  2. Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana karanta ta a wuturin sallar dare da yake yi. Kamar yadda Imamul Nasa’i, da waninsa suka rawaito. 3. Kuma yana karanta ta a raka’a ta biyu ta nafilar da yake yi kafin Sallar Asuba (Wato Raka’atal Fajri), kamar yadda Imam Muslim ya rawaito. 
  3. Sannan kuma yana karanta ta a raka’a ta biyu bayan kammala ɗawafi. Muslim ya rawaito. 
  4. Sai kuma a raka’a ta biyu ta bayan sallar Magariba. Tirmizi ya rawaito. 6. Kafin kwanciya bacci yana karanta ta tare da Falaƙi da Nasi ya shafe jikinsa sau uku. Bukhari ya rawaito. 
  5. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce wanda ya karanta ƙulhuwallahu Ahad sau goma (10), Allah zai gina masa ƙerarren gida a Aljanna. Ahmad da wasunsu ne suka rawaito. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

To ‘yan uwa Musulmai, duk mai son ya ribaci alhairan da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da sahabbansa suka ribata daga wannan sura ta ƙulhuwallahu Ahad, to ya yi koyi wajen yin amfani da ita a guraren da suka yi amfani da ita , Allah dai ya ce idan har muka bi Manzo za mu shiriya. Duba suratul Nur, aya ta (54).

Ya ‘yan uwa Musulmai ku sani cewar da ake yi a rubuta ƙulhuwallahu sau ɗari kaza da sha kaza, na tsawon sati a riƙa wanke wa ana sha bai da asali, domin kuwa ba koyarwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba ce. 

Kuma babu wata madogara ingantacciya game da cewa ayi laya da ƙulhuwallahu Ahad a saka a kwalaba a binne a kusurwoyin gida ko ofis ko rumfar kasuwa a matsayin maganin sata. Da sauran abubuwa makamantan waɗannan marasa dalili, don haka, mu lura da kyau mu yi hattara mu sani ɓata ba zai taɓa yin daidai da shiriya ba. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceHalaye Da Siffofin Shugaba Nagari
Labarin na GabaFalalar Ƙulhuwallahu Ahad