Peptic Ulcer Diseases

0
322

Ciwon olsa  ta zama ɗaya daga cikin manyan cutuka da suke damun al’ummah a ƙasar mu ta Najeriya.

Peptic Ulcer Disease : (Gyambon Ciki) general name ne na ulcern ciki gabaki ɗaya.

Ita Peptic ulcer (gyambon ciki ko ciwon ulcer) ya kasu kashi uku kamar :

1- Gastric Ulcer (Gyambo wadda ke kama Fatar ciki ciki)

2- Duedenal Ulcer (Gyambo wanda ke kama hanji)

3- Esophagus Ulcer  (Gyambon maƙogwaro)

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Ciwon Olsa na zuwa da alamomi da yawa, ga su kamar haka: 

1- Ƙonawar zuciya

2- Ciwon Ciki

3- Rashin cin abinci

4- Tashin Zuciya 

5- Amai

6- Ciwo har a gadon baya

7- Kashi da jini  ko baƙin kashi

8- Kumburin ciki

9- Ciwon ciki

10- Ɗaukewar numfashi.

Me yake kawo ciwon Olsa ?

* Ƙwayar cutar bakteriya mai suna H- pylori shi yake kawo ciwon Olsa. Haka kuma yawan shan maganin ɗauke  ciwo kamar su  Aspirin, Shan taba (sigari) da kuma shan giya suna taimakawa sosai wajen kawo ciwon Olsa.

Sannan yana da kyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

Ta Wacce Hanya Ake Ɗaukan Ƙwayar Cutar Olsa ?

  • Mutum yakan iya ɗaukan wannan ƙwayar cutar ta hanyar musayar yawu (saliva) ko lokocin kiss.
  • Mutum yakan iya ɗaukan wannan ƙwayar bakteriyan  ta hanyar ruwan sha da kuma abinci 

Idan ruwan sha ko abinci ya gurɓanta da bayan gida ko fitsarin mai ciwon, wanda hakan yana faruwa ne ta hanyoyi da yawa.

Me Yasa Ita Ciwon Olsa Ba A Warkewa Da Wuri?

Ba ba a warkewa ba ne, ana warkewa daga cutar Olsa ko wacce iri amma abinda yake faruwa shi ne:

1- Rashin shan magani yadda ya kamata, yau an wayi gari shan magani barkatai ya zama ruwan dare a Najeriya, mafi yawa ƙwayoyin cutar an saba musu da wannan maganin har ya zama suna jurewa.

2- Za ka ga mutum ana ba shi maganin wata ɗaya ko sati biyu, a ranan da ya fara shan maganin idan ya ji sauƙi shi kenan ya rabu da maganin sai lokocin da alamomin cutar ya sake zuwa zai cigaba da shan magani. 

3- Misali a ce ƙwayar cutar ana samun shi daga gurɓataccen ruwa, to ana shan magani kuma ana cigaba da shan gurɓataccen ruwan ka ga babu maganar warkewa .

4- Rashin bin ƙa’idojin likita na gaba gaba wajen hana warkewan wannan ciwo na Olsa.

5- Shan magunguna barkatai ba tare da Izinin likita ba musamman magungunan olsa da sunan zai warkar maka da olsa, da kuma amfani da magunguna na gargajiya wanda ba a san kanta ba.

Shawara Ga Masu Ciwon Olsa:

1- A ƙauracewa waɗannan Abinci :

– Abinci mai yaji

– Abinci mai ɗaci

– Abinci Mai tsami

– Abinci masu Gas

– Abinci masu ɗauke da Acid kamar tumaturi.

2- A daina amfani da hayaƙi ko wacce iri ko tabar sigari, wiwi ko shisha sabida suna daga cikin abubuwan da suke haddasa olsa Kuma suna tsananta olsa.

3-  A daina amfani magungunan ɗauke ciwo irinsu Aspirin, Ibuprofen, cataflam, Naproxen, Feldene, da sauransu.

4- A rage shan giya domin yawan shan giya yana daga cikin abubuwan da suke kawo olsa kuma suke tsananta Olsa.

5- A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da ake da kokwanto a kai kafin amfani.

6- A yawaita amfani da kayan lambu musamman cabbage (kabeji) yana taimaka wajen daƙile ciwon olsa.

7- Sai Kuma zuwa ga likita domin tabbatar da cutar da kuma ba da magani.

Domin karanta Damar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata Danna nan

labarin da ya wuceGangliyon Sist [Ƙarin Mahaɗar Ƙashi]
Labarin na GabaTaminal Lusiditi (The Surge)