Muhallan Da Ake Waƙoƙin Fiyano Na Hausa

0
437

Muhallan da ake waƙoƙin Fiyano na Hausa su ne wuraren da mawaƙan Hausa masu amfani da fiyano suke rera waƙoƙinsu.

Muhallan Fiyano su ne kamar haka:

1. Fina-finan Hausa

Wato irin fina-finan da ake yi a ƙasar Hausa, ko kuma Hausawa suke yi, ko kuma ake yi da harshen Hausa; To a cikinsu akan samu kaɗe-kaɗe na fiyano; da kuma waƙoƙin da aka yi amfani da fiyano wajen aiwatar da su.

2. Tarukan Siyasa

A nan ya shafi dukkanin wani dandazon mutane da za a tara a dalilin siyasa, wanda a wannan wuri akan samu waƙoƙin da aka rera da kiɗan fiyano, a wasu lokutan ma akan samu makaɗan fiyano a wurin.

3. Bukukuwa

Dukkanin wani nau’i na biki, sawa’un bikin suna ne ko aure ko wanin waɗannan. A nan, za a iske waƙoƙi da dama da aka rera su ta hanyar amfani da fiyano. A wani lokaci kuma, akan samu makaɗan fiyano a wuraren bukukuwa domin yin kiɗan fiyano.

4. Majalisi

Wannan kuwa ya shafi wuraren yabon Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da halifofinsa da sauran mutanen kirki. A wannan muhalli ma, akan yi amfani da fiyano wajen yin kiɗa ga waƙar da aka yi ta yabo.

5. Tallace-Tallace

Dukkanin wani nau’i na tallace-tallace, sawa’un tallar magunguna ne ko wasu abubuwa ne, kamar robobi da kayan abinci da yaduna da sauransu. To a nan, su ma akan yi musu waƙoƙi ta hanyar amfani da kiɗan fiyano

6. Kafofin Yaɗa Labarai

Wannan ya shafi kafofin sadarwa kamar gidajen radiyo da talabijin, domin sukan yi amfani da kiɗan fiyano a yayin da wani shiri ya ƙare kuma suna son sanya wani. Haka zalika, sukan yi amfani da shi domin tallata wani abu da wani kamfani zai ba su.

7. Yabon Masoya

Ma’abota soyayya tsakanin maza da mata sukan yi amfani da fiyano wajen yabon junansu, wato za a iske budurwa ta yi wa saurayinta waƙa, kuma ta je an yi mata kiɗan fiyano, ko kuma shi ya mata waƙa, kuma ya je an masa kiɗa da fiyano.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta bayani a kan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan

Domin karanta bayani akan Misalan Waƙoƙin Hausa Na Fiyano danna nan

labarin da ya wuceMisalan Waƙoƙin Hausa Na Fiyano
Labarin na GabaMa’anar Kiɗa da Makaɗi