Zainab (2009:84) ta ce “Waƙoƙin fiyano na Hausa su ne waƙoƙin da suka samu canje-canje; daga kayan kiɗa na gargajiya zuwa kayan kiɗa na zamani; kamar fiyano da jita da sauransu”.
Kamar yadda aka ambata a sama, yawancin mawaƙan wannan zamani suna amfani da fiyano ne wajen kaɗe-kaɗen waƙoƙinsu, don haka kenan waƙoƙin da suka samar na kiɗan fiyano ne.
Cikin irin waɗannan waƙoƙin akwai:
- Sakarkari ta Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa)
- Rayuwa tana faruwa ta Fati Musa Ƙofar Wambai
- Gatana ta Malam Nafi’u Nguru
- Ku Ɗinka Hijabi ta Malam Ibrahim Lalula Nguru
- Bulaliya ta Abubakar Sadiq Suwa’ilu
- Rawa-rawa ta Naziru M. Ahmad
- Almajiri ta Muhammad Sani Aliyu
- Ƙarshen Tika-tika Tik ta Aliyu Auta Masani, Nguru
- Ku Yi Haƙuri ta Jibrin Muhammad Jalatu
- Waƙar Rigar ‘Yanci ta AbdulAziz Abdullahi Ningi
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.
Domin karanta cikakken bayani a kan Muhallan da Ake Waƙoƙin Fiyano na Hausa danna nan
Domin karanta bayani akan Ire-iren Kiɗan Fiyano danna nan