Tag: Waƙoƙin Hausa

  • Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun
    Waƙoƙin Baka na Hausa

    Adamu Rabi’u BAKURA1, Abu-Ubaida SANI
    Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria

    Tsakure: Rubuce-rubucen nazari da aka yi game da waƙoƙin Hausa sun fi shurin masaƙi. Duk da haka, mafi yawan rubuce-rubucen sun karkata ne kan zaƙulo fasahohi da ke cikin waƙoƙin tare da nuna yadda suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Wannan takarda na da fahimtar cewa an bar wani babban giɓi wanda shi ne nazarin fanɗare wa dokokin addini cikin waƙoƙin Hausa.

    Maƙalar nan na da manufar binciko muhallan da ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa suka keta
    dokokin da Allah ya shimfiɗa wa bayinsa. An tattara bayanai ta hanyar sauraron waƙoƙin da tsamo misalan ɗiyan waƙoƙin da abin ya shafa, tare da ciro hukunce-hukuncen da suka yi bayani kansu daga Alƙur’ani da hadisan manzon Allah.

    Binciken ya fahimci cewa, akwai tarin misalan fanɗare wa addini a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Daga ƙarshe an ba da shawarwarin da suka haɗa da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ire-iren waƙoƙin ba su yi tasiri wajen gurɓata tarbiya nagartacciya ba.

    Fitilun Kalmomi: Waƙoƙi, Addini, Musulunci, Fanɗarewa

    GABATARWA

    Musulmi ba a bar shi kara zube ba. An kafa masa sharuɗɗan tafiyar da rayuwa dukkanta. Ire-iren waɗannan sharuɗɗan suna ƙunshe cikin littafin Allah (Alƙur’ani) da Hadisan Annabi S.A.W. Daga cikin dokokin akwai na tilas, wato abin da Musulmi mai hankali ba zai iya rabuwa da shi ba, komai tsanani.

    Akwai kuma abubuwan ƙi, wato waɗanda ba a so Musulmin ya aiwatar da su ba. Haka akwai haramun, waɗanda aka hana mutun ya aikata su. Idan dukkannin rayuwar mutum ta kasance cikin ɗa’a, kuma ya nisanci saɓo, babu shakka ya kiyaye dokokin Allah Maɗaukakin Sarki.

    A gefe guda kuwa, kamar yadda Chiromawa, (n.d. p. 5-10) ya bayyana, ko da addinin Musulunci ya iso ƙasar Hausa ya tarar da al’ummomi da dama suna aiwatar da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe nau’i-nau’i da suka haɗa da:
    i. Kiɗan sana’a
    ii. Kiɗan jawo hankali
    iii. Kiɗan lallashi (rarrashi)
    iv. Kiɗan faɗakarwa

    v. Kiɗan zaburarwa
    vi. Kiɗan ƙarfafa zuciya
    vii. Kiɗan jaruntaka
    viii. Kiɗan farin ciki
    ix. Kiɗan ibada

    Duk ire-iren waɗannan kaɗe-kaɗe akan haɗa su ne da waƙe-waƙe. Kasancewar addinin Musulunci, addini ne mai sauƙi da sauƙaƙa wa mabiyansa, bai haramta waɗansu daga cikin nau’ukan kaɗe-kaɗe ba. Ya dai kawo gyare-gyare domin kare mutunci da martabar
    mabiyansa. Ya haramta shi ne yayin da aka aiwatar da abin da Allah ya haramta a cikinsa.

    Hasali ma akwai wuraren da Musulunci ya sunnanta kiɗa da waƙa, kamar a lokuttan ɗaura aure, tamkar yadda Imamu Buhari ya bayyana a “Babin Kaɗa Ganha” a ranar aure da walima. Bayan haka, akwai ranar kai amarya ɗakin mijinta, da ranar idi da ranar suna, da ranar zuwan wani shugaba da ranar komawarsa, da ranar kaciya (kugunu/kuidu).

    Akwai hadisai waɗanda Buhari da Muslim da Tirmizi da Hakimu da Nisa’i suka rawaito da ke nuni ga halaccin kiɗa da waƙa a babin aure da sallar idi. Halaccin kan tabbata ne matuƙar bai haɗa da alfasha ko motsawa zuwa ga saɓon Allah ba. A bisa wannan ne, maƙalar ta ƙuduri aniyar yin ƙwarya-ƙwaryar bincike a muhallan da makaɗan baka na
    Hausa suka keta ƙa’idojin da Allah ya shata ta hanyar kauce musu.

    Duk wasu ɗiyan waƙa da makaɗi ya yi za a yi ƙoƙarin kawo shi tare da auna shi da ma’aunin shari’a da aka ciro daga nassin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. domin tabbatar da hasashen. Ana iya samun ɗiyan waƙoƙin da ke ƙunshe da gurbin fanɗara a waƙoƙin makaɗan sarauta, da na jama’a da na maza da sauransu, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.

    Dabarun Gudanar Da Bincike

    Kadadar wannan bincike ta taƙaita ne ga waƙoƙin baka na Hausa a farfajiyar koyarwar addinin Musulunci. A ɓangaren waƙoƙin an ɗauko ɗiyan waƙoƙi da aka tattauna kansu kai tsaye ta hanyar sauraron odiyoodiyo da kallon bidiyoyinsu.

    A ɓangaren hukunce-hukuncen addinin Musulunci kuwa, an ɗauko su kai tsaye daga cikin Alƙur’ani mai tsarki da hadisan Manzon Allah (S.A.W.) ingantattu. An kuma nazarci rubuce-rubucen masana da manazarta a wannan fannin inda suka haska hanya ga binciken.

    Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Zambo

    Makaɗan saurauta sun shahara wajen yin zambo, domin ƙawata waƙoƙinsu. Masana da dama sun bayyana ma’anar zambo gwargwadon fahimtarsu. Gusau, (1984 p. 37) ya tafi kan cewa “Akan yi zambo don adanta waƙa da muzanta wanda ke hamayya da wanda ake yi wa waƙa.” Abba da Zulyadaini, (2000 p.63) sun bayyana zambo da cewa: “… nau’i ne na muzanta mutum ta hanyar ƙasƙantar da shi, ko wulaƙanta shi, domin a baƙanta masa tare da dusashe masa kwarjini a idon jama’a.

    Mawaƙan sun fi shahara da zambo don su aibanta duk wani ɗan sarki da ke ja da ubangidansu. Muhammad, (2005) kuwa na da ra’ayin cewa zambo zagi ne kai tsaye,
    … saboda akan ba da hoton wanda ake yi wa tare da bayyana cikakkiyar sifarsa ta hanyar ambaton duk wani abu da ya dace da shi. A lokacin da aka yi ma wani zambo akan fito da hotonsa ne zahiri, ta yadda duk wanda ya san shi zai gane cewa da shi ake. Muhammad, (2005 p. 28)

    A taƙaice kenan, zambo yana ƙunshe da ma’anar ƙaga wa mutun magana wadda za ta muzanta shi ta ɓata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. A dubi misalin zambon da Alhaji Musa Ɗankwairo ya yi wa wani ɗan sarautar Tsafe:

    Kun san zamanin ga ya canza,
    Ga wani ɗan sarki da kandaye,
    Ya shaho hoda kamar Delu.
    (Ɗankwairo: Waƙar Sarkin Tsahe).

    Wannan zambon da Ɗankwairo ya yi wa ɗan sarki ya kai matuƙa wajen aibanta ɗan sarkin ta hanyar kamanta shi da ɗan daudu. Hakan ba ƙaramin muzantawa da dushe masa kima ya yi a idon al’umma ba. Tabbas kuwa hakan ya saɓa wa dokokin addinin Musulunci. An umurci Musulmi da ya tsare (kame) harshensa da yin furucin abin da bai halatta ba, kamar keta mutuncin ɗan uwansa Musulmi ba tare da wani abu mai wajabtawa ba na shari’a. Allah na cewa:

    Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da ba wa ma’abocin zumunta kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana yi muku gargaɗi ko da kuna tunawa. (Surar Nahli: 16:90).

    Idan aka dubi wannan ayar za a tarar ta yi hani ga yi wa wani mugun baki (mugun fata), sannan ta yi hani ga alfasha. Ya kuma yi umurni da tausayawa tare da yin abu bisa gaskiya. Daga ƙarshe ta yi hani a kan ha’intar wani ta kowane ɓangare. Wannan na iya
    kasancewa ta hanyar lafazi ko a aikace. Ta la’akari da wannan ɗiyar waƙar, za a tarar mawaƙin ya kauce wa dokar da Allah ya ɗora masa.

    Annabi S.A.W. Ya Ce: Haƙiƙa, mafi sharrin mutane a matsayi wurin Allah a ranar alƙiyama shi ne wanda mutane suka ƙyale shi don ƙiyayyar alfasharsa. (Muslim ya ruwaito). Wanda duk wani mawaƙi ya yi wa zambo, to zai guje shi tare da yin kaffa-kaffa da al’amarinsa.

    Sau da yawa akan ba su kyauta ne bisa tilas don gudun zambonsu. A irin wannan yanayin idan aka nazarci hadisin, za a ga a nan ma sun kauce wa koyarwar Annabi
    S.A.W. A wani Hadisin kuwa Annabi (SAW) cewa ya yi: “Mumini bai kasancewa mai yawan suka ba ko yawan la’anta ko yawan alfasha, ko mai sakin harshe” (Tirmizi
    ne ya ruwaito shi).

    Wannan hadisin ya fito ƙarara ya bayyana mana cewa, duk mawaƙin da ya ba da gaskiya
    ga Allah da ranar lahira da manzancin Annabi S.A.W., zai kasance mai bin dokokin Musulunci kamar yadda suke. Hakan kuwa zai sanya ya guji yi wa Musulmi zambo.
    Akwai misalan wuraren da makaɗan jama’a suka yi wa abokan hamayyarsu zambo ta hanyar zagi kai tsaye.

    A irin wannan lamari ne mawaƙin jama’a kan fito da halayen mutun a fili, sannan ya zage shi. Misali, a waƙar “Gagara Badau,” Alhaji Mamman Shata cewa ya
    yi:
    Shata: Allah ya tsine ma tsohon mazinaci,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Allah ya tsine ma da kai da iyalinka.
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Yanzu babban ɗan bai gani,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Babban jikanshi kuma yana kama agwaginmu,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Gida ya lalace.
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

    Dubi yadda Shata yake zagin wani basarake tare da nuna ɗansa ya makance, ya kuma kira jikansa ɓarawon agwagi. Wannan ba ƙaramar fanɗarewa ba ce, domin a shara’ar Musulunci an umurci Musulmi da ya kiyaye da yin zance da bai halatta ba, kamar ƙarya, da zage-zage da keta mutunci Musulmi. Allah na cewa: “…Kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana muku gargaɗi ko da kuna tunatuwa.” (Alƙur’ani,
    Suratul Nahl, 16:90).

    Fanɗare Wa Koyarwar Musulunci Ta Hanyar Habaici

    Habaici ko gugar zana salo ne ko azancin yi da wani a kaikaice ta yadda sai wanda ya san shi kuma ya san abin da ake magana game da shi ne kaɗai zai iya ganewa. Habaici wata hanya ce da makaɗan baka suke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin ƙara musu
    armashi, ta hanyar ƙasƙantar da wani mutun ko kuma muzanta shi ko su zage shi ko kuma su soka masa wata magana a kaikaice. Misali, a cikin waƙar Mai Dubun
    Nasara Sardauna, Alhaji Musa Ɗankwairo yana cewa:

    Ga kare ga kura kowane ya hangi wani,
    Ga aura ya koma,
    Wagga nan hanya ba mu ga wurin wali ba.
    (Alhaji Musa Ɗankwairo, Waƙar Mai Dubun Nasara, ta Sardauna).

    Yayin da aka dubi ɗiyar wannan waƙar za a ga yadda Ɗankwairo ya siffanta Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kura. Ya yi hakan ne domin bayyana irin ƙarfinsa kamar yadda kura ke da shi. Wannan kuwa ya shafi yadda take iya tauna ƙashi da kuma kwarjini da waibuwarta na sanya rashin kuzari ga halittar da ta tunkare ta.

    A gefe guda kuwa, sai ya kira wanda yake yi wa habaici da kare, saboda ba sa zama
    inuwa ɗaya da kura. Hasali ma kare ba ya hangen nesa sosai, kuma mai gidansa yakan yi amfani da shi ne wajen farauta. Kiran mutun kare ba ƙaramin ƙasƙantarwa ba ne
    a al’adance. Wannan ne ya sa makaɗan baka sukan siffanta waɗanda suke son wulaƙantawa da kare saboda nhalayyarsa da ɗabi’unsa.

    Musulunci ya hana keta mutuncin Musulmi ko wulaƙanta shi ko zagin sa ko laƙa masa munanan sunaye, ba tare da haƙƙin shara’a ba. Allah na cewa: “… kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye” (Alƙur’ani, 49:11). Idan muka dubi wannan ayar, za mu ga cewa ta hana a kira Musulmi da sunan da zai kasance tamkar zagi ne gare shi. Yin haka kuma fanɗare wa umurnin Ubangiji ne.

    Annabi S.A.W. ya ce: “Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙar sa kafirci ne” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi). Idan aka dubi wannan hadisin cikinsa da
    wajensa, aka kuma nazarci ɗiyar waƙar da ta gabata, za a tarar cewa, makaɗin ya kauce wa faɗar Annabin S.A.W., ya yi gaban kansa. Yin haka fanɗarewa ne ga dokokin addinin Musulunci.

    Bin dokoki da ƙa’idojin Musulunci kuwa dole ne, inda har Allah ke cewa: “Kuma abin da Manzo ya zo muku da shi, to ku riƙe shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu” (Surah Al-hashr, 59:9).

    Fito-Na-Fito Da Koyarwar Muslunci

    Akwai misalan inda mawaƙa ke amfani da wasu kalmomin da suka kauce wa ƙa’idojin addinin Musulunci. Akan samu irin wannan fito-na-fito a fannonin da suka shafi sahihan aƙidojin da suka danganci ranar lahira, da matsayin mala’ikun Allah da makamantansu. Ya kuma haɗa da dokoki da ƙa’idojin addinin Musulunci ta fuskar hani da horo. Wannan
    ɓangare na aikin zai mayar da hankali wajen zaƙule irei-ren waɗannan misalai:

    Izgilanci

    Izgilanci ga abubuwan da addini ya zo da su nanuni ga halin ko-oho ga lamarin addinin. Musulunci kansa ya tsawatar da riƙo da dokokin da ke ƙunshe cikinsa ba tare da wargi (wasa) ba. Duk da haka, akan samu wuraren da mawaƙa suka yi izgilanci ga lamarin
    addini. Alhaji Muhammadu Ɗan’anace a waƙar Shago yana cewa:

    Jagora: In da lahira ana kasa dambe…
    ‘Y/Amsohi: Da Walakiri ya ji ƙwal ga gaba nai.
    Jagora: Duk wanda bai yi kallon Shago ba,
    Aradu yana da sauran kallo,
    Ya zaka duniya kamar bai zo ba,
    Kamar zuwan kare ga aboki,
    Tamkar mutum ya mari budurwa,
    Ko ya mutu ba a gafarta mai.

    In aka dubi wannan ɗan waƙar, za a tarar cewa, wannan makaɗin ba ƙaramar kasada ya yi ba. Ya nuna rashin jin tsoron aukawar wani haɗari (hatsari) ko shiga cikin abin da bai san sakamakonsa ba. Allah na cewa: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi a kansa.” (Surar Isra’i, 17:36).

    Idan muka nazarci wannan ayar, za a ga yadda Mahaliccin sammai da ƙassai ya faɗakar da masu imani da su yi kaffa-kaffa ga dukkan lamarin da ba su san haƙiƙanin yadda yake ba. Ko bayan batu kan abin da mutum bai sani ba, batutuwan da ke ƙunshe cikin ɗiyar
    waƙar na tattare da izgilanci ga abin da ya shafi imani da mala’iku da ranar ƙiyama.

    Goyon Bayan Karuwanci

    Kalmar karuwa, suna ne na mace. Jam’i kuwa shi ne karuwai. Karuwa na nufin mace mai zaman kanta wadda mazan banza ke neman ta su ba ta kuɗi domin saduwa (zina) da ita. Zina kuwa tana nufin saduwa (jima’i) da matar da ba ta halatta ga mutum ba ta hanyar aure, wato wadda ba matarsa ba. Tun kafin bayyanar Musulunci a farfajiyar
    ƙasar Hausa, Bahaushe ya ƙyamanci zina.

    Don haka karuwanci bai samu bagiren zama ba, balle a yi zina. Duk da kasancewar akwai al’adar tsarance, a inda saurayi kan gayyaci budurwarsa ta je ɗakinsa har ma ta kwana. Sakamakon irin wannan al’adar ce, ya sanya su amfani da al’adun tsafi domin tabbatar da amarya ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba (zina) kafin a yi mata aure. A irin
    wannan al’adar ce, idan yarinya ta san maza kafin a yi mata aure, za ta kunyata a cikin jama’a.

    Idan kuma ta ɓoye ba ta faɗa ba, ta mutu, kamar yadda Ibrahim, (1985 p. 5) ya nuna.
    Yayin da addinin Musulunci ya bayyana, sai ya haramta zina. Hasali ma ya sanya ta cikin manyan laifuka, bayan kafirci, wato haɗa Allah da wani da kashe ɗan Adam. Allah yana cewa: “Kuma kada ku kusanci zina, lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Alƙur’ani; Suratul Isra’i, 17:32)

    Haka kuma Musulunci ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da za ta iya zama sanadin aikata zina ta hanyar wajabta wa mata sanya hijabi. Sanya hukuncin jefe mazinaci da mazinaciya har su mutu a bainar jama’a, idan sun yi aure, ko a yi musu bulala idan ba su taɓa yin aure ba, na nuni da girman zunubin. Duk da wannan umarni na Ubangijin talikai da kuma uƙubar da aka tanadar wa mazinata, sai aka sami wani mawaƙi da ake kira Habibu Sakarci ya yi wa wata karuwa waƙa.

    A cikin ɗiyan waƙar yana cewa:
    Jagora: Shehuwar mata Safiya Kano, Ta gidan ‘Yajja
    Safiya Kano.
    Jagora: ‘Yan birni roƙo suke, Allah ba mu jaka bakwai,
    Mu gano ɗakin Safiya Kano.
    Jagora: Direbobi ma roƙo suke, Allah ba mu jaka
    bakwai, Mu gano ɗakin Safiya Kano.
    Jagora: Mutan birni yanga suke, Domin darajar Safiya
    Kano.

    Yayin da aka nazarci ɗiyan waƙar, za a ga cewa Habibu Sakarci yana tallar wannan karuwa ta hanyar bayyana ta a matsayin ƙasaitacciyar karuwa. Har ma ya nuna ‘yan birni da dirobobi na burin Allah ya ba su kuɗi masu yawa, don su tafi ɗakinta. Hasali ma ya bayyana ta fi sauran karuwan birnin kyau. Wannan ba ƙaramar fanɗara ba ce da keta dokokin Allah.

    Ya zo cikin hadisi
    Annabi S.A.W. yana cewa: Lalle ana rubuta wa ɗan’adam rabonsa daga
    zina, kuma lalle mai risker sa wancananka ne babu makawa. Idanu zinarsu ita ce kallo, kunnuwa kuwa zinarsu ita ce sauraro, harshe kuwa zinarsa ita ce zance. Hannuwa kuma zinarsu ita ce damƙa, ƙafa kuma zinarta ita ce taku, zuciya kuwa saƙa soye-soyenta ne, kuma tana guranta su, farji yana gaskata wancananka ko ya ƙaryata (Buhari da Muslimu ne suka ruwaito hadisin).

    Duk da irin waɗannan nassoshin Alƙur’ani da hadisan Annabi S.A.W., sai ga ya makaɗa na fanɗare musu ta hanyar gayyatar al’umma zuwa ga aikata fasiƙanci. Shi ma Alhaji Mamman Shata ya yi makamanciyar wannan waƙar, a inda ya yi wa wata mata da ake kira Karo Oma:
    Jagora: Duk ɗan birnin da ya riƙa,
    Ni kar ya yi mini yanga,
    In yana so ya isa
    In gan shi gidan Kara Oma.
    (Alhaji Dakta Mamman Shata: Waƙar Kara Oma)

    A nan Shata ya fito ƙarara ya tura ‘yan birni su tafi gidan wannan karuwa idan har sun isa. A ɗaya ɓangaren kuwa cicciɓa ta ya yi da cewa, sai manyan mutane wayayyu ne kawai suka isa su yi hulɗa da ita. Wannan waƙar ba abin da ya raba ta da fanɗare wa
    dokokin Allah da ya shata wa Musulmi.

    A shara’ar Musulunci, an san Musulmi da kunya. Hasali ma kunya tana cikin halayensa, kuma tana daga cikin Imani. Imani kuwa shi ne aƙida da rayuwar Musulmi. Manzon Allah yana cewa: “Kunya da imani suna zozozo da juna. Idan babu ɗayansu, ɗayan ma ba za
    a same shi ba” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

    Goyon Bayan Shan Giya

    Giya, kalmar suna ce da ke cikin jerin sunaye jinsin mata. Ita kuma nau’i ce da ake yi da hatsi ko alkama ko inibi wadda ake sha a yi maye. Ana kuma kiranta barasa, kamar yadda ƙamusan CNHN (2006 p.168) ya nuna. Shan giya a tsakanin al’ummar Larabawa kafin bayyanar Musulunci abu ne sananne. Shi ne ƙashin bayan doron ginin tattalin arzikinsu, kuma giya na daga cikin kayan fataucinsu.

    Har matansu sun kasance shahararru wajen haɗa ta. Hasali ma kowane gida akan
    same ta. Wannan ya sa har suna yabon giya a cikin waƙoƙinsu. Su ma al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba, domin sun mayar da shan giya musamman a lokuttan
    bukukuwan aure da na haihuwa tamkar ƙawa. Yayin da suka samu rabauta na karɓar addinin Musulunci, sai suka guje ta a sakamakon hanin da addinin ya yi gare su.

    Kasancewar Musulunci addini ne mai sauƙi da ke ƙunshe da dabarun magance abubuwan da ke haifar da fitsara da ta’addanci a tsakanin al’umma, sai ya fara bayyana wa muminai rashin kyanta. Daga nan kuma ya hana kusantar wurin ibada yayin da aka sha ta Daga ƙarshe ne kuma ya sauƙar da hani kai tsaye game da shan giya inda aka ce:
    “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku sani cewa, giya da caca da gumaka da ƙyaurayen duba ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nisance su don ku rabauta
    (Alƙur’ani; 5:90).

    A wannan ayar an bayyana wa masu imani munanan ayyuka da ake buƙatar mumini ya nisance su. Kuma duk al’ummar da ta rungume su za ta faɗa cikin masifa da rashin kwanciyar hankali. Ayar ce kuma ta zo da haramcin shan giya kai tsaye. Akwai hadisai da dama da suka tabbatar da haramcin shan giya da kuma abin da ake kira da giya.
    Annabi S.A.W. yana cewa: “Duk abin da ke bugarwa giya ce, kuma kowace irin giya haramun ce” (Muslim ne ya ruwaito shi).

    A Wani Hadisin Kuwa Cewa Ya Yi: Allah ya tsine wa giya, masu shan ta, da waɗanda suka zuba ta, da waɗanda suka sai da ita, da waɗanda suka saye ta, da waɗanda suka tatso ta, da waɗanda suka ɗauki kayan da ake tatsarta, da waɗanda suke ɗauke ta, da waɗanda aka kai wa ita, da waɗanda suka samu kuɗi a gare ta” (Abu Dawuda, da Al-Hakem a isnadi ingantacce, suka kawo shi)

    Yayin da aka dubi waɗannan nassoshi, za a tarar cewa, ƙin bin su sau-da-ƙafa keta shara’ar Musulunci ne, wato fanɗarewa faɗar Allah da annabinsa ne. Duk da haka, an ci karo da waƙoƙin da suka yi kira da a sha gida. Alhaji Mamman Shata Katsina ya waƙe giya. Har ma cewa ya yi:

    Jagora: Ka ji karatun masu bugun ruwa, Waɗanda…
    ‘Y/Amshi: Ke zikiri a Kuloniya, A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: A nan muke sallarmu ta Juma’a, Mu tattara kayanmu mu kai Neja, Ku sha ruwan nan…

    Y/Amshi: Ba laihi ba ne, A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Ruwa na kwalba ba laihi ba ne, Ai kun ga…
    ‘Y/Amshi: Alhaji Shata sha yake. A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Yara mu koma wasa Kuloniya, Mu tashi kana
    mu koma Neja,
    ‘Y/Amshi: Nan ne muke zikirinmu na Juma’a. A sha
    ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Malam ka sha ai ba laihi ba ne, Ga taka ga tau…
    ‘Y/Amshi: Kowa ya aje. A sha ruwa ba laihi ba ne.

    Idan muka nazarci waɗannan ɗiyan waƙar za a ga yadda mawaƙin ya yi fito-na-fito da dokokin Allah da Manzonsa. Allah ya haramta, shi kuma ya halatta. Dubi yadda mawaƙin ya ce a sha giya ba laifi ba ne, bayan Annabi S.A.W. ya ce kada a sha, a inda yake cewa:
    “Kada ku haɗa fulawa da dabino gaba ɗaya, kuma kada ku haɗa busasshen tafarnuwa da dabino sam-sam, ku bar su idan an niƙa su.”

    Yayin da aka niƙa su, nan take suna bugar da wanda ya sha su. Don haka ne Annabi ya umarci masu imani da kada su sha a haɗe yayin da suke niƙe, kamar yadda Munhajul Muslimu Jadawali na uku: Abinci da Abinsha ya nuna. Hasali ma mawaƙin ya bayyana cewa shi ma yana shan giyar tare da yaransa. Akwai hadisai da dama da suka nuna haɗarin Musulmi ya mutu yana shan giya, ko da bai halatta ta ba.

    To ina ga wanda ya halatta shan ta? Daga cikin ire-iren waɗannan hadisai akwai wanda
    Ibni Abbas ya ce: Manzon Allah S.A.W. ya ce: Duk wanda ya mutu yana cikin ɗabi’ar shan giya bai tuba ba, zai tarar da Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki tamkar wanda ya bauta wa gumaka (Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin).
    A wata waƙar ta mawaƙin da ake kira Horo/Horu, an ga baitukan da suka nuna ba laifi ba ne shan giya da ma cin mushe. Mawaƙin na cewa:

    Jagora: Arnaaa ku sha giya ku ci mushe, Aljanna mai rabo zai sama.

    A wani wuri kuwa, har ya nuna ma kashi ne ga mutum ya sha giya ‘yar kaɗan kuma ta wahalshe shi. Yana cewa:

    Jagora: Kowa ya sha giya yai yi amai, Ba ɗan halas ba ne, shege ne!
    Jagora: Su wane ‘yan giyan ƙarya ne, Shegu, kwalba guda take ka da su.

    Don karanta Tarihin Garin Rimin Gado danna nan

    Goyon Bayan Sata

    Abubakar (2015, p. 431) ya bayyana cewa, sata “tana nufin ɗaukar abin wani ba da saninsa ko izinin ba. ”Sata na nufin ɗaukar wani abu da hukuncin shari’a ko hankalin tuwo bai mallaka wa wanda ya ɗauka ba, tare da amfani da shi ko musanyensa da wani abu mai daraja kwatankwacin na kuɗi ko kuma mai amfanarwa, ba tare da izinin wanda ko waɗanda ke da mallakin abun ba.

    Sata ta kasu zuwa nau’uka daban-daban. Sun fi danganta da salon yadda aka gudanar da satan. Fitattu daga cikinsu sun haɗa da:
    i. Cuta
    ii. Damfara
    iii. Fashi
    iv. Fizge/Wabce/Fauce
    v. Ƙwace
    vi. Sane

    Sata babbar abar ƙyama ce a farfajiyar Hausa da Hausawa, tun ma kafin bayyanar addinin Musulunci. Sauyawan al’amurra da cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu sun wanzar da taɓarɓarewar tarbiyya da ƙoƙarin neman tara abin duniya ido rufe. Ta kai ga
    fanɗararru marasa kishin kansu cikin al’umma sun tsunduma a fagen wannan ta’addanci.
    Yayin da addinin Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa, sai ya ƙara ƙarfafa wa Hausawa ƙyamar wannan muguwar sana’a.

    Musulunci ya zo da dokoki domin kawar da duk nau’o’in sata. Allah na cewa:
    Ɓarawo kuma da ɓarauniya sai ku yanke hannayensu ya zama sakamako ne na abin da suka aikata, (wannan horo ne) daga Allah. Allah kuwa mabuwayi ne Gwani. (Alƙur’ani, 5:38). A addinin Musulunci ta kowace fuska ana ƙoƙarin kare dukkanin al’umma ta yadda za a zauna cikin aminci game da dukiyoyi da rayukan al’umma.

    Ita kuwa sata, mugun hali ce da ke haifar da rashin kwanciyar hankali da salwantar rayuwa a tsakanin al’umma. Don haka ne shari’a ta tanadar da hukuncin yanke hannun
    ɓarawo wanda zai hana watsuwar irin wannan muguwar ta’asa a tsakanin al’umma [14]. Allah na cewa: “Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar cuta ”(Alƙur’ani, 2: 188).

    Ayar tana tabbatar wa masu imani cewa, cuta haram ce. Ba ya halatta ga Musulmi ya yi zalunci ta hanyar zaƙin baki ko dabara. Haka kuma, bai halatta ya yi jagora don a cuci wani ba. Duk da irin waɗannan dokokin da Allah Maɗaukakin Sarki ya shimfiɗa domin samar da kyakkyawan zamantakewa da aminci a doron ƙasa, an samu gungun mawaƙa da ke jayayya da dokokin cikin lafuzzan waƙoƙinsu.

    Bunza, (2014) ya kawo baituka da dama daga bakin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada.
    Gambo ya bayyana ƙarara cewa:
    Jagora: Don Waɗanda ka sata nay yi ganga, Ba do wani sarki mai naɗi ba.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Tsoho Tudu)
    A cikin waƙarsa ta Nazaƙi kuwa, an ga yadda hirarsu ta gudana da Nazaƙi bayan ya tuba daga sata.

    Sannu a hankali har Gambo ya sake zuga shi yadda har sai da ya dawo satan. Gambon da kansa ya bayyana cewa:
    Ɓarawo in ina kusa ba tuba yakai ba,
    Ko ya aje gemu, ko ya yi saje,
    Ko ya fidda farin gashi ga kaina,
    In Gambo na kusa ba tuba yakai ba,
    Ba ko batun shegantaka ba.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Nazaƙi)

    A wannan ɗiyan waƙa, sai da ya jaddada cewa, batunsa ba “batun shegantaka” ba ce kawai. Wato dai haƙiƙanin gaskiya yake faɗa cewa idan yana kusa ɓarawo ba ya tuba domin kuwa zai ziga shi ya hana shi tuban. Wasu makaɗan sukan yi waƙoƙin yabo ne ga
    ɓarayin. Misali Alhaji Mamman Shata ya yi wa wani ɓarawo mai suna Mamman Ɗan’yarbayye waƙa, a inda yake cewa:

    Jagora: Mai hannun taɓa ƙofa in an bacci,
    Masu samame baƙon Ɗanmani.
    Na faɗa maka Mamman.
    In dai ka ɗauko sa’a,
    Har ka buɗe ƙofa,
    Ka tarar an bacci,
    To zari akwati tsakiyar shi ya fi kaya.
    Na saman hoto ne,
    Na ƙasan maganin ƙwari ne.
    Tafi zari akwatin tsakiyar shi ya fi kaya.
    Na Abdu ƙyale dangi sai an bacci,
    Iyalin Mamman, waɗanda ba su so a yi haske,
    Su sun fi so a tabka duhu da ruwa yaf-yaf-yaf.
    Wani don ya taka kara bai mai ƙara ba,
    Sannan ganyen ganji duk ya bi ƙasa.
    (Alhaji Dakta Mamman Shata: Mamman
    Ɗan’yarbayye)

    A waɗannan ɗiyan waƙar, mawaƙin ya yabi ɓarawon tare da ba shi shawarar yadda zai gudanar da sana’arsa ta sata. Wannan ya haɗa da yi masa ishara ga irin lokuta da yanayi da dabarun da zai bi wajen yin satar, da kuma nau’in abin da zai sata da ya fi saura daraja.

    Hakan kuwa karan-tsaye ne ga dokokin addini. Hadisin Manzo (S.A.W.) ya bayyana cewa: “Ɓarawo ba ya sata a lokacin da yake da imani” (Buhari ne ya ruwaito
    hadisin). Allah Maɗaukakin Sarki ya kawo nau’in hukuncin da ya dace a zartar wa masu fashi da makami, a inda yake cewa:

    Ba wani abu ne sakamakon waɗanda suka yi wa (Musulmi masu bin) Allah da manzonsa fashi ba, kuma suke tafiya a bayan ƙasa da ɓarna ba, sai kawai a kashe su ko kuma a tsire su ko a yanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe, ko kuma a kore su daga ƙasa. (Yin) wancan ƙasƙanci ne a gare su a duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma. (Alƙur’ani, 5:33).

    Allah ya bayyana mana cewa masu yin fashi da makami suna ƙoƙarin ɓata tsarin Allah da Manzonsa ne, saboda aiwatar da fashi ya kauce wa hanyar gaskiya da adalci, waɗanda Musulunci ke ƙoƙarin tabbatar da su a doron ƙasa. 3.5 Goyon Bayan Kisan Kai Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa:

    Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya
    tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur’ani, 4:93).

    An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago, yana cewa:
    Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,
    Ba kukan tuwo ba, Ba na hura ba…
    ‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi, Suna kirarin banza.
    Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin
    ‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake….
    A wani wuri yana cewa:
    Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma. Ɗan Abdu…
    ‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:
    i. Kusheyi
    ii. Lahira a kai miki gawa
    iii. Lahira tana yin baƙo
    iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

    Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:
    Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,
    Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,
    In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,
    Don wagga ba sata ta ba Gambo.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

    A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    Goyon Bayan Kisan Kai

    Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa: Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur’ani, 4:93).

    An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago, yana cewa:
    Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,
    Ba kukan tuwo ba, Ba na hura ba…
    ‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi, Suna kirarin banza.
    Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin
    ‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake….

    A wani wuri yana cewa:
    Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma. Ɗan
    Abdu…
    ‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:
    i. Kusheyi
    ii. Lahira a kai miki gawa
    iii. Lahira tana yin baƙo
    iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

    Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:
    Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,
    Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,
    In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,
    Don wagga ba sata ta ba Gambo.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

    A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    Hani Ga Bautar Ubangiji

    Ko bayan kira zuwa ga aikata ɓarna da fasadi, akwai misalan ɗiyan waƙoƙi kuma da ke kira ga barin bautar Ubangiji. Na biyu a cikin shika-shikan Musulunci ita ce salla. Tana da matuƙar muhimmancin da har ya kasance kadarko tsakanin mutum da kuma shirka da
    kafirci. Duk da haka, sai ga ɗiyan waƙa da ke hani ga yin salla:

    Bayarwa: Ɗan Abdu ban da sallas swahe,
    ‘Y/Amshi: Domin yawan sallan nan yana rage maka ƙarhi.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Sakamakon Bincike

    Ta la’akari da nassoshin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. da kuma ƙumshiyar wasu waƙoƙin baka na makaɗan Hausa, za a a iya cewa, mawaƙa na wuce gona da iri a waɗansu lokuta. Yawanci hakann na faruwa ne yayin da suka yi ƙoƙarin adanta waƙoƙin nasu domin burge wanda aka yi wa waƙar da kuma sauran masu nsauraro.

    A haka ake samu ɗiyan waƙoƙin sun yi wa dokokin Musulunci karan-tsaye. A wannan nazarin an fahimci cewa duk wani aikin da ɗan’adam ya aikata wanda Allah da manzonsa
    suka yi hani da shi, yin haka nau’i ne na fanɗare wa dokokin Allah. Ya zama tilas kowane Musulmi ya nemi ilimin duk wani lamarin da ya shafi rayuwarsa, (kamar yadda mai Ahalari ya bayyana) don gudun auka wa fushin Ubangiji.

    An kuma fahimci cewa, a Musulunci kowane irin al’amari an ɗora shi a kan mataki-mataki. Wannan ne ya wajabta wa kowane Musulmi ya yi umurni da aikata alheri da kuma hani ga mummunan aiki gwargwadon ƙarfin ikon mutun.

    Kammalawa

    Yin fice da waƙoƙi suka yi wurin ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa, ba shi ke nuna ba a samun fanɗarewa a cikinsu ba. Nau’ukan fanɗarewa da ake samu cikin waƙoƙin Hausa sun shafi ziga zuwa aikata abin da Ubangiji ya hana, ko izgilanci ga
    abubuwan da Musulunci ya zo da su, ko kuma hani ga abin da Ubangiji ya yi umarni da a aikata.

    Abu ne mai kyau manazarta su riƙa zaƙulo ire-iren fanɗarewa da ake samu a cikin waƙoƙi domin faɗakar da al’umma da su kansu mawaƙan. Malamai da ke jagorantar nazarcenazarcen waƙoƙi a makarantu kuwa, ya kamata su mayar da hankali wajen yin shiri na musamman na faɗakar da ɗalibai ta fuskokin da suka dace yayin da aka ci karo da ire-iren baitukan fanɗarewa a cikin waƙoƙin da suke nazarta.

    Gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa ma na da rawar takawa wajen samar da ƙa’idoji da tsaretsaren tace waƙoƙi kafin sakinsu. Haɗakar waɗannan za su tabbatar da al’umma ba ta rinjayu da kiraye-kirayen waƙoƙin fanɗara ba zuwa taɓewa.

    MANAZARTA

    • Abba, M., & da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan
    waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Corporation Limited.
    • Abubakar, A. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa.
    Zaria: Northern Nigeria Publishing Company LTD.
    • Al-Munajjid, M. S. (2004). Muharramat: Forbidden
    matters same people take lightly. International
    Islamic Publishing House, Saudi Arebia.
    • Bunza, A. M. (2014). In ba ka san gari ba saurari
    daka: Muryar nazari cikin tafashen Gambo Elkods
    Printing Hausa.
    • Chiromawa, U. A. U. (n.d.). Dalilin kiɗa a cikin
    Alƙur’ani da hadisi.
    • Gusau, S. M. (1984). Nazarin zaɓaɓɓun waƙoƙin
    makaɗan baka na Hausa, littafe na ɗaya.
    • Ibrahim, M. S. (1983). Kowa ya sha kiɗa. Longman
    Nigeria Limited.
    • Magaji, A. (2016). Kassu Zurmi da waƙoƙinsa.
    Spectrum Books Limited.
    • Muhammad, Y. M. (2005). Adabin Hausa. Ahmadu
    Bello University Press Limited.
    • Sani, A. U., & Jaja, M. B. (2019). Zamani Riga:
    Akalar Magungunan Gargajiya a Hannu Addini da
    Zamani. In The Nasarawa Journal of Humanities, 7,
    (1-2), 257-268. ISSN: 1118-6887.
    • Shehu, M., & Sani, A. U. (2019). Intra-Religious
    Conflicts within the Hausa Hausa-folk. In EAS
    Journal of Humanities and Cultural Studies, 1(3),
    145-150. ISSN: 2663-0958 (Print) & ISSN: 2663-
    6743 (Online) Available at:
    https://www.easpublisher.com/get-articles/344.
    • Umar, M. B. (1987). Dangantakar adabin baka da
    al’adun gargajiya. Kamfanin “Triumph” Gidan
    Sa’adu Zungur

    Danna nan don karanta Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Musa Ɗanƙwairo A Koyo Da Biyayyar Waƙa

    Musa Ɗanƙwairo A Koyo Da Biyayyar Waƙa

    Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya tashi, ya girma a gidansu; ya tarar da ana harka ta kiɗa da waƙa. Magabatansa tun daga Kaka Maiganga da mahaifinsa dukkansu makaɗa ne na noma; da yaƙi da kuma Sarauta da suka aiwatar da kiɗa da farar ganga da kuma gangar kotso.

    A bisa ɗabi’a ta gadon gida, mutum zai koyi abin da ya tarar ana gudanarwa a gidansu. Hausawa sukan ce, gadon gida alala ga rago, a yayin da Musa Ɗanqwairo ya fara tasawa, sai ya karkata wajen koyon abubuwa na hukunce-hukuncen addinin Musulunci da kuma hidimomin kiɗa da waƙa waɗanda suka shafi wasu harkoi na zamantakewar Hausawa.

    Musa Ɗanƙwairo ya fara biyayya ta sanin makamar waƙar baka tun a wajen mahaifinsa, Makaɗa Usman Ɗankwanagga24. A wajen mahaifin nasa ya koyi kaɗa kanzagi da karɓin waƙa da jajircewa a karin waƙa da samar da rauji na waƙa (Gusau, 2019: sh. 10-11).

    Haka kuma Musa Ɗanƙwairo ya daɗa gwangwajewa a zuba ɗiya na waƙar baka a biyayyar da ya yi a yayin Halifantakar da ya yi wa wansa Abdu Kurna. Domin himmar Musa Ɗanƙwairo da ƙwazonsa da basirarsa, wansa Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Abdu Kurna, ya naɗa shi ya zama Daudun Kiɗa kuma Ɗangaladimansa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Musa Ɗanƙwairo a Gayaunar Waƙa danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Waƙar Shawara Ga Mai Bilicin danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Kiɗa Da Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo

    Kiɗa Da Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo

    Kiɗa da waƙa ta baka wani fage ne wanda yawancin makaɗa masu tunani da ƙwaƙwalwa da fasahar shirya kalmomi; musamman ta fuskar zaɓensu da baiwa ta hangen nesa da furuci mai cusa tarbiyya ta ruhi da ta gangar jiki suke aiwatarwa ga al’ummominsu.

    Wasu ladubban waƙoƙin baka sun haɗa da bayanai na tarbiyyatarwa da faɗakarwa da jan hankali; zuwa ga kyawawan ayyuka da halaye na gari, musamman waɗanda al’umma da addinin al’umma suke aiki da su.

    Domin haka, waƙar baka ta ƙunshi wasu matakai da sigogi na aiwatarwa wato shiryawa da ƙullawa; da kuma rerawa tare da sadar da ita ga al’umma. Kuma waɗannan su ne suke ɗaukar hankalin al’umma wajen sauraron waƙoƙin baka da aiki da su.

    Makaɗin baka yakan zama tilas ya san waɗannan ladubban waƙar baka; waɗanda Allahu yake yi masa ilhama da su ta hanyoyin koyo da biyayya ko jibilliyya ko bisa wata buƙata ta rayuwa.

    Domin karanta cikakken bayani akan Musa Ɗanƙwairo a Koyo da Biyayyar Waƙa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mawaƙan Da Ake Yi Wa Kiɗan Fiyano danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Wasu Waƙoƙin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    Wasu Waƙoƙin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    2.1 Sanƙiran Aliyu Gadanga (Ibrahim Imo) :
    ‘Ali Ɗan’agunda Jikan Jama’a.’
    Kirarin Sanƙira na Aliyu Gadanga da na S.M. Gusau :

    2.2 Aliyu Gadanga Gusau :

    ‘Sai na zo mu Taya shi Murna,
    Mu zo mu ga Farfesa Sa’idu.’ 

    2.3 Babangida Kakadawa Gusau 

    ‘Farfesa Sa’idu Muhammad.’
    Waƙar Babangida Kakadawa ta ‘Baban ɗan Ƙasa na
    Ƙasar nan’ 
    ‘Furofesa ne Sa’id’
    Waƙar Babangida Kakadawa ta ‘Furofesa ne Sa’id’

    2.4 Aminu Ladan Abubakar, Alan Waƙa, Baharun Waƙa :

    ‘Ga ka Farfesa ga ka Katibi kan Adabi,
    Sannu Farfesa Sa’idu ɗan Muhammad na Gusau.’ 
    ‘Ga ka Farfesa ga ka Katibi kan Adabi,
    Sannu Farfesa Sa’idu ɗan Muhammad na Gusau.’ 
    ‘Gangaran ka fi Gwani Shehu Adibi na Gusau,
    Mashahurin Malami Sa’idu Muhammad na Gusau.’ 
    ‘Shehin Adabi da Al’ada,
    Sa’idu Gusau Furofesa Mafakar Mazaje.’ 

    2.5 Sarfilu Umar Zarewa Ɗanbaiwa, Maiwaƙa 

    ‘Sannu Furofesa Gusau,
    Sa’idu Muhammad na Gusau,
    Ko an ja Maka za a sau,
    Maka a Fannin Ilimi.’ 

    2.6 Ibrahim Bello, Billy’O 
    ‘Furofesa Gusau Gaisuwa Muka zo,
    Za mui maka.’ 

    2.7 Maryam Fantimoti, Sarauniyar Waƙa ta Sarkin Kano :

    ‘Furofesa Sa’id Muhammad na Gusau,
    A gai da Babban Malami a Harshen Hausa
    Ɗan Ƙwarai.’

    2.8 Muftahu Umar Muhammad Maiwaƙa, Kano 

    ‘Da Madubin Adabi Sannu Turka ta ilimi,
    Yau Furofesa Sa’idu Muhammad na Gusau Muke
    Waƙewa.’ 
    ‘Prof. Gusau Madalla Shehu Sa’idu ɗan Babba,
    Ga Gwani Adibin Shehi ɗan Muhammadu Ɗankullum.’ 

    2.9 Shehu Ajilo Ɗanguzuri, Kaduna

    ‘Baba Furofesa nau,
    Sa’idu Mamman Gusau.’ 
    ‘Sa’idu Muhammad,
    Na gode Sa’idu Furofesan Hausa.’ 

    2.10 Abdul Jos Maiwaƙa na Sarkin Waƙa Naziru 

    ‘Farfesa Baba Sa’idu Muhammad Gusau sha Kallo,
    Sashen Hausa na Jami’ar Bayero,
    Ƙumdum Kamarka ba a yo ba.’ 

    2.11 Abba Abdulƙadir Shu’aibu (Abban Baba)

    ‘Sannu Jarumi Furofesa Sa’idu Muhammad Gusau,
    A gai da Katibi jan Zaki Baba Tushen Hausa’ 

    2.12 Rubutawa: Sulaiman Ahmad Usman (Baba Sule) :

    Rauji da Rerawa: Sarfilu Umar Zarewa Ɗanbaiwa Maiwaƙa,
    G/Waƙa: ‘Babban Gijin Jami’ar Bayero,
    Farfesa Sa’idu mai Gaskiya’ 

    2.13 Alhaji Imamu Muhammad Sanusi, Ɗanƙwairon Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman

    ‘Furofeso Sa’idu Gusau,
    Ɗan Muhammadu ka Buwai Arna’ 
    ‘In ga ɗan Muhammadu Ɗankullum,
    Sa’idu Furofesa ne kai’ 
    ‘Furofesa Sa’idu Gusau ɗan Muhammadu,
    Ka buwai Arna’ 

    2.14 Rubutawa: Fatima Uba Adamu 

    Rauji da Rerawa: Sarfilu Umar Zarewa Ɗanbaiwa
    G/Waƙa: ‘Baba Sa’idu Gusau Furofesa,
    Mai Zurfin Ilimin Sanin Harshen Hausa,
    Babban Furofesa’ 

    Domin karanta cikakken bayani a kan Waƙoƙin Fada Da Wasu Waƙoƙi Game-Gari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i Na Biyar (Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka); wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Nazarin Yabo Daga Cikin Waƙoƙin Ala

    Nazarin Yabo Daga Cikin Waƙoƙin Ala

    Jigon yabo baduniyen jigo ne da ke yaba mashahuran mutane irin su; sarakuna da shugabanni da attajirai da ma’aikata da manyan malamai da masu ilimi ko ba na addini ba ne.

    Irin waɗannan waƙoƙi sun fara samun tagomashi bayan zuwan Turawan Mulki, kuma sun haɓaka daga wajen 1950 zuwa yau. Waƙoƙin yabo suna taimakawa wajen ƙara wa waɗanda aka yi wa yabo gwuiwa don sun ƙara hoɓɓasa kan irin gudunmawar da suke bayarwa, domin yaba musu kamar ƙaimi ne wato ke nan an ga fa’ida da muhimmancin abin da suke yi.

    Waƙoƙin kuma sukan zama kamar matashiya ga wasu daban domin; sukan sa wasu mutanen su ma su tashi tsaye su yi hoɓɓasan da su ma; wasu mawaƙan za su gani su ma su yi musu irin waɗannan waƙoƙin yabo don yaba musu (Abdulƙadir, 2014: xx).

    Makaɗan baka na zamani sun yi waƙoƙin yabo da zuga daban-daban ga malaman Hausa musamman waɗanda suke jami’o’in ƙasar nan, inda waƙoƙin nasu suka fi karkata ga farfesoshi.

    A wannan gaɓa, za a bayyana wasu muhallai da aka yi irin wannan yabo ga wasu manyan malaman Hausa; sannan a yi ƙoƙarin yin sharhin wannan yabo a taƙaice.

    1. Salon Yabo ga Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir

    Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir yana cikin jerin malamai, masana kuma manazarta harshen Hausa ‘yan Ƙasa na farko, masanin harshe da adabi da al’adun Hausa ne. Gudumawarsa ba ɓoyayyiya ba ce; musamman a fagen waƙa.

    Makaɗi (Dr) Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya yi wa Farfesa Ɗandatti waƙa, inda a cikin waƙar ya yabe shi a wasu baituka. Ga yabon da ya masa:

    G/Waƙa : Ɗandatti Dattijo Abdulƙadir Furofesa,
    Ka ji masu umarni da hani bisa sha’anin Allah,

    Misali na I

    Jagora : Ka ji masu umarni da hani bisa sha’anin Allah,
    Ɗandatti Dattijo Abdulƙadir Furofesa,
    Yau gida na malanta na taho za na yi wa ƙasida,
    Yau jinin sarakai zan waƙe in rubuta nashida,
    Bahari na taso in wa yabo masani na al’ada,
    Bahari na fannonin adabi na gama da al’ada,
    Ɗan Abdulƙadir Abdulƙadir ku min shaida,
    Baitukan na yo wa ne atafa ko in ce farar tsada,
    In zubo ɗiyan waƙa wane dirhami fagen tsada,
    In yabon Furofesa Abdulƙadir a ƙasida,
    Datti masu umarni da hani bisa sha’anin Allah.

    Idan aka dubi matashiyar wannan waƙa, za a ga Makaɗin ya buɗe waƙarsa da wannan ɗiya; wanda hakan ɗaya ne daga cikin salon da Alan Waƙa ke bi yayin buɗe waƙoƙinsa musamman waɗanda suka shafi yabo. A wannan ɗiya, ya yi yabo ga Farfesa Ɗandatti ta amfani da kalmomi da dama. Misali, ya ambace shi da “masu umarni da hani”, a nan sai ya yabe shi da wata kyakkyawar sifa ta koyarwa. Sannan ya ambace shi da “masanin al’ada”, da “bahari a fannoni”, ma’ana mutum ne wanda yake da ilimi a ɓangarori da dama, inda har ma ya keɓanci wasu ɓangarori, wato masanin adabi da kuma al’ada.

    Misali na II

    Jagora : Gaisuwa gurin Allah arraziƙi mai azirtawa,
    Mai aro na ilhama hikima kyauta gurin bawa,
    Taimake ni min lamun na zo a gare ka don ƙwawa,
    Zan yabon wurin jigon adabi mai hali na madalla.

    A wannan ɗiya na farko, bayan ya yi gaisuwa ga Allah da roƙon lamuni. Sai ya bayyana zai yi yabo ga “jigon adabi”. Jigo a nan, na nufin ginshiƙi, wato ginshiƙin adabi. Shi kuwa adabi sanannen abu ne ga masu nazari da ɗalibai.

    Misali na III

    Jagora : In ana dara dangi ai fid da uwa ake gefe,
    Yau uban iyaye ne na tashi yabo fa zan tsefe,
    In ana batu na sani Abdulƙadir ku kai gefe,
    Bahari fa kogi ne na masu iyo fa don Allah.

    A wannan ɗiya na uku, ya yabe shi ta hanyar ambatarsa da ‘uban iyaye’ da ‘kogi’. Uban iyaye na nufin kakan jikoki amma a fuskar ilimi. Sannan ya ambace shi da kogi, wato iliminsa yalwatacce ne ta yadda ganin ƙarshensa akwai matuƙar wahala.

    Misali na IV

    Jagora : Rukunin dukkan daraja da ke ɗaga martabar bawa,
    Ilimi da sarauta sai alatu halin bawa,
    Ka haɗa mu’amilla yakana mai izo gurin bawa,
    Babu wanda ɗan Audu bai taka ba ibadul Lah

    A wannan ɗiya na huɗu kuwa, ya yabe shi ta hanyar amfani da rukunan da suke sanyawa a yabi mutum, wato ilimi ko sarauta ko dukiya ko kuma wata kyakkyawar mu’amala ga mutane. To a nan, sai yake ƙoƙarin nuna cewa duk waɗannan dalilai da suke sanyawa a yabi mutum, to fa Farfesa Ɗandatti ya haɗa su.

    2. Yabo ga Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo

    Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo yana cikin rukunin ‘yan Ƙasa rukuni na uku a fagen Hausa, fitaccen masani ne a ɓangaren adabi da al’adu, musamman yadda ya zama manazarci mai son ganin an haɗa hanyoyin nazarce-nazarce su tafi bai ɗaya. Farfesa ya taimaka wajen samar da hanyar fiɗar waƙa, sannan ya fassaro kalmomin nazari tare da ƙirƙiro wasu. (Gusau, 2008: 56).

    (Dr.) Alan Waƙa ya gwangwaje Farfesa da waƙoƙi, cikin waƙoƙin an bibiyi guda ɗaya, sannan aka zaƙulo yabon da ya yi ga Farfesa.

    G/Waƙa : Garkuwar Adabin Hausa sannu Farfesa,
    Sannu Ɗangambo na taho in gaishe ka.

    Misali na I

    Jagora : Za ni hau sarari na yabo da baitukka,
    : In yabanta gwani turmi ma-sha duka,
    : Nemi Ɗangambo ka ji rairayar waƙa,
    : Rariyar adabi ce matankaɗar waƙa

    A wannan ɗiya, ya yabe shi da kalmar ‘gwani’, wato ƙwarrarre a kan abu, sannan kuma mai juriya. Har wa yau, ya yabe shi ta hanyar gwarzantawa wajen nuna cewa dukkanin abin da ya shafi adabi, to shi yake tantancewa.

    Misali na II

    Jagora : Maliyar malala dole sai fa an sha ka,
    : Ko cikin birni ko a sha a ƙauyuka,
    : Ga ni nai girshe ginshiƙi fa zan waƙa,
    : Matsirar masana Hausa sai fa labbaika.

    A wannan ɗiya, Makaɗin ya yi ƙoƙarin amfani da salon kambamawa ga Farfesa a yayin yabo, sannan sai ya ƙara bayyana cewa shi Farfesa Ɗangambo tushe ne na masana Hausa. A taƙaice a nan, ya yabe shi da kasancewarsa mai yalwar ilimin Hausa, sannan kuma tushe ga dukkanin wani masani ga Hausa.

    Misali na III

    Jagora : Na kira ka daƙu a fagen nazar naka,
    : Hausa dai wannan sai in ce a kalle ka,
    : Za a gan ta tafe a ƙasan ƙafafunka,
    : Godiya Bakano ke ta yi da samun ka.

    A nan kuwa, ya yabe shi ne ta hanyar kwatantawa, inda a layin farko na ɗa, sai ya ambace shi da ‘daƙu ‘. To a fagen ilimi ma ya ambace shi da ya san komai ko ya taɓa kowane ɓangare na ilimi.

    Masali na IV

    Jagora : Bishiyar rimi ko na nesa ya ganka,
    : Mai firirita sai in ce ki yai kanka,
    : Haka nan Jamus na ga ɗalibai naka,
    : Da na je Oxford na ga ɗalibai naka.

    A wannan ɗiya ma, sai ya sake yabonsa ta hanyar kwatantawa, inda ya kamanta shi da ‘Bishiyar Rimi’. Rimi wata ƙatuwar bishiya doguwa mai kamar kuka, tana da ‘ya’ya da ake samun audugar da ake katifa da matashin kai da ita (CNHN, 2006: 372).

    Domin ya bayyana faɗaɗuwar ilimin Farfesa Ɗangambo da yadda ya kewaya ko’ina ta yadda kuma kowa na iya kwankwaɗa daga ciki, sai ya kwatanta shi da wannan bishiya. Abin nufi, duk yadda mutum yake son bincike a ɓangaren Hausa, a ko’ina yake, to fa sai ya ci karo da ilimin Ɗangambo a wannan fage. Domin ya tabbatar da abin da ya faɗa, sai ya bayyana cewa a Jihar Oxford ma ya ga ɗaliban da Farfesa Ɗangambo ya koyar.

    Masali na V

    Jagora : Malami tammi masani na fannoni,
    : A adon harshe zai zame maka tsani,
    : A fagen tarke ka biyo shi ladani,
    : Ya faɗa ka faɗa ya sanar ka allonka.

    Jagora : Yadda Jami’atu ke alam ya shaide ka,
    : Ba ka satifiket wanda ke alamta ka,
    : Haka nan Ala ke alam na shaidarka,
    : In kiraye ka gwargwadon nagartarka.

    Jagora : Ɗauraya ta fadon feɗiya a kan waƙa,
    : Ka yi rabbe-rabben Adabi na Hausarka,
    : Kai Kitsen Rogo ƙirƙira ta kwanyarka,
    : Godiya wannan ya ci ai yi ma waƙa.

    A waɗannan ɗiya uku da suka gabata, Makaɗin ya yi masa yabo ta hanyar tabbatar da ilimi da nagartarsa, ta yadda har Jami’a ta ba shi shaidar yabo ta satifiket, wanda samuwar wannan satifiket ne ya sanya shi kuma Makaɗin ya yabe shi gwargwadon wannan nagarta tasa. Sannan sai ya bayyana wasu ayyuka cikin muhimman rubuce-rubucensa da ya yi.

    3. Salon Yabo ga Farfesa Ahmadu Bello Zaria

    Farfesa Ahmadu Bello Zariya shi ma na cikin ‘yan Ƙasa rukuni na uku a Hausa, masani ne kuma manazarci a ɓangaren Harshe. Farfesa Ahmadu Bello ya yi rubuce-rubuce da dama a ɓangaren harshe; waɗanda suka fi karkata ga Nahawu da ƙa’idojin rubutun Hausa da Arulin Hausa da kuma kare-karen harsuna.

    Makaɗi (Dr.) Alan Waƙa ya yabe shi musamman kasancewarsa ƙwararre a fagen Arulin Hausa. Ga wasu baituka da ya masa a wata waƙa.

    G/Waƙa : Ahmadu Bello Farfesa kai ne mizanin Arulinmu,
    A.B.Z Furofesa tartibi na awo a waƙenmu.

    Misali na I

    Jagora : Ahmadu Bello Farfesa ABZ babban kadarkonmu,
    Ahmadu Bello Farfesa gwadabe ɗoɗar na sani namu,
    :Farfesa hanyar ilimi ne a waƙenmu,
    :Farfesa alfijiri mai haska harkarmu,
    ABZ Furofesa mudu na awon sha’irai namu,
    :hanyar gane dukka lagonmu,
    :hanyaar turke a ƙasidarmu,
    :hanyar fiɗar abbiyat namu.

    Makaɗi Alan Waƙa ya buɗe wannan waƙa tasa da waɗannan ɗiya, inda a cikin su ya yi amfani da wasu kalmomi domin yabo na sani da maƙura a ilimi ga Farfesa Ahmadu Bello. Kalmar ‘kadarko’ na da ma’anoni biyu, amma a nan mun kalli ma’anar wata ‘yar ƙaramar gada wadda yawanci ake yi da katako a kan hanya don kwararar ruwa (CNHN, 2006: 223). To a nan, an yi amfani da ita ga Farfesa Ahmadu Bello a matsayin babba duk da cewa ƙarama ce, mai makon ruwa da take kwarararwa, to a wurin Farfesa sa kuwa hanya ceta kwararar da ilimi.

    Ambatarsa da gwadabe ‘godabe’ kuwa, an siffanta shi da babbar hanya ta sani ga ilimin waƙa. Sannan Makaɗin ya ƙara yabon shita hanyar siffanta shi da alfijir, wanda alfijir wani haske ne da ke fara fitowa domin yaye duhu. To haka shi ma hasken ilimi ne da yake yaye duhun jahilci. A wannan ɗiya dai, duk ya yabe shi da ilimi da sani a tsarin waƙa.

    Misali na II

    Jagora : Ya Jabbaru Ƙahharu mai ikon duka lammura namu,
    : Ban hikima da tarbiyya za ni yaba wa gwaddabe namu,
    : Za ni yabon Imaminmu Limamin da ya zamma gatanmu,
    : Shehun Shehunai namu Ahmadu Bello qafar sani namu,
    : Madalla da jagora mai fitilar haskawa dubanmu.

    A wannan ɗiya kuwa, ya ambace shi da imam, wato ja-gaba. Sannan ya ba shi babban suna na malamin malamai, wanda idan aka ce ‘shehi’ babban malami ne, to shi kuma sai ya ambace shi da ‘shehun shehunai’.

    Misali na III

    Jagora : Amma na sani tunda na yi tawassil gunsa mai iko,
    : Zai fisshe ni jin kunya inda na yo lam’a da mamako,
    : Baiwa ta Jibulliya ba ta tsumayi ba ta yin dako,
    : Allah ba ni ilhama lamunce Ka saka ni nai ƙarko,
    : Za ni yabon madubinmu masanin waƙa har irin tamu.

    A wannan baiti na huɗu, ya yabe shi da kalmar madubi masani. ‘Madubi’ na da ma’anoni da dama, amma a nan za mu ɗauki ma’anarsa ta ‘ƙarau da aka shafa wa wani abu mai ɗaukar ido da yake nuna surar duk abin daya bayyana a gabansa; mutane kan yi amfani dashi domin duba fuskokinsu’. To shi ma Farfesa a fagen ilimi, an siffanta shi da madubi ta yadda suke duba zuwa ga rumbun iliminsa a game da waƙa.

    Misali na IV

    Jagora : Na yi shiru na tsahirta na gyaɗa kai wayyo ni wayyo ni,
    : Ya zan su fahimce ni na ga kamar malam suka riƙe ni,
    : Mai nazari da mai waƙa ba ɗaya suke ba ko a mizani,
    : Ba lalle ga mai waƙa yai nazari balle ya hau tsani,
    : Ko bishiyar Galadanci sai Ahmadu AB madubinmu.

    Bishiyar Galadanci, ita ce bishiyar li’irabi ta jimla a Hausa. Wannan bishiya aba ce mai matuƙar muhimmanci a tsarin jimlar Hausa. Akan ɗauki jimla a yanka, a feɗe ta sannan a rataye ta a bishiyar. Farfesa M.K.M Galadanci ɗaya ne cikin malaman Farfesa Ahmadu Bello Zariya, wanda ya yi littafin kan wannan tsari na bishiya, duk da wahalar hawanta. To Farfesa Ahamdu ya naƙalci hawa wannan bishiya domin rataye jimla.

    4. Salon Yabo ga Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    Farfesa Sa’idu Gusau na cikin ‘yan Ƙasa rukuni na huɗu, masani ne manazarci da ya yi rubuce-rubuce a kan abin da ya shafi adabi da al’adu, sai dai ya fi karkata zuwa waƙar baka. Farfesa Gusau ya bayar da gagarumar gudumawa a fagen waƙar baka, ya fito da hanyoyin nazarin waƙar baka, ba ya ga gata da ya mata na bincike da lalubo tushenta.

    Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya yi wa Farfesa Gusau waƙoƙin yabo da dama, amma a wannan takarda an bibiyi waƙa guda ɗaya sannan aka zaƙulo wurin da ya masa yabo, wato waƙar ‘Shehin adabi da al’ada’. Ga wasu ɗiya da ya yi yabo a cikin su:

    G/Waƙa : Shehin adabi da al’ada,
    : Sa’idu Gusau Furofesa mafakar mazaje

    Misali na I

    Jagora : Malam na Gusau kadarko ne,
    ‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaji,
    Jagora : Tsanin ilimi adibi ne,
    ‘Y/amshi : Namijin mazaje,
    Jagora : Kambin adabi na ilmi ne,
    ‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
    Jagora : A yau a fage karimi ne,
    ‘Y/amshi : Namijin mazaje,
    Jagora : Ya zam fitilar adibbai ne,
    ‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
    Jagora : Farfesa Gusau gadon bai ne,
    : Mabiyar mazaje.

    A wannan ɗa, Makaɗi Alan Waƙa ya yi wasu kalmomi ga Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, waɗanda kalmomi ne da suka bayyana yalwar ilimi da yadda shi Farfesa Gusau ya zama mai yi wa ilimi hidima a kowane ɓangare. Cikin kalmomin da ya yi amfani da su wajen wannan yabo akwai kalmar ‘kadarko’.

    Kalmar ‘kadarko’ na da ma’anoni biyu, amma a nan mun kalli ma’anar wata ‘yar ƙaramar gada wadda yawanci ake yi da katako a kan hanya don kwararar ruwa (CNHN, 2006: 223). A nan, Alan Waƙa ya yi amfani da kalmar, maimakon ruwa da take kwarararwa, to a wurin Farfesa Gusau hanya ce ta kwararar da ilimi.

    Har wa yau, ya sake yabon shi ta hanyar kambama iliminsa da cewa ‘Tsani ilimi’.

    Tsani shi ne wani abu da za ka taka domin ya sada ka da wani abu; wanda ba za ka iya kai wa gare shi ba, dole sai ta wannan hanya. A nan, sai ya yabe shi ta hanyar kwatantawa, inda ya nuna Farfesa Gusau tsani ne ga wanda yake son ilimi, wato duk wanda ke son ilimi, to ga wanda zai haxa shi da ilimi, ma’ana zai karantar da shi ilimi.

    Kambi na nufin hula ta zinare da sarakunan Turai kan sa. Ko kuma wata lamba ta girmamawa (CNHN, 2006: 229). A nan, sai ya kwatanta Farfesa da kambi, amma a fagen ilimi, domin a fagen ilimin, wani mutum ne da ake girmamawa.

    A ci gaba da yabon, sai ya bayyana shi da ‘karimi’, wato mutum mai yawan kyauta.
    Alan Waƙa, ya ci gaba da yabo, inda ya ambaci Farfesa Gusau da ‘Fitilar adibbai’. ‘Fitila’ na nufin abar da ake haskaka wuri ko ɗaki da ita (CNHN, 2006: 143). A nan, sai ya bayyana Farfesa Gusau da cewa fitilar adibbai ne, wato shi ne ke haskaka wa duk wani adibi domin ganin hasken ilimin adabi.

    Domin ƙara fito da wani nauyi na ilimi da ke kan Farfesa Gusau, sai Makaɗin ya ambace shi da ‘Gadon bai’. A nan, kalmomi guda biyu ne aka mayar da su ta hanyar samar da harɗaɗɗen suna, wato ‘gado’ da ‘baya’. Amma a ginin kalmar, sai aka yi gutsirewa, wanda sanannen abu ne a tsarin nazarin kalma ko ilimin kalma, wato maimakon a ce ‘gadon baya’, sai a ce ‘gadon bai’, ko dai don shi mai waƙa ya sami kalmar ta shiga waƙarsa, ko kuma domin taƙaita kalmar. Gadon bai da ya ambace shi da shi, yana nufin shi sha-nauyi ne a fagen ilimi.

    Misali na II

    Jagora : Ruhin adabi da al’ada,
    ‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
    Jagora : Ƙigon adabi da al’ada,
    ‘Y/amshi : Namijin mazaje,
    Jagora : Jigon adabi na al’ada,
    ‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
    Jagora : Domin ka a yau muke tsada.

    Domin bayyana ƙarfin ilimin Farfesa Gusau a ɓangaren adabi da al’ada, sai ya yabe shi da ‘ruhin adabi da al’ada’, wato rai ne shi a adabi da al’ada, ta yadda idan babu shi; to babu waɗannan abubuwa biyu. Sai kuma ya yi masa kirari da irin kirarin da ake yi wa sarki ko ango, amma shi ya keɓanta shi da adabi da al’ada, wato ‘ƙigon adabi da al’ada’. Sannan kuma sai ya yabe shi ta hanyar ambaton sa da ‘jigon adabi na al’ada’. Imma dai jigo da ma’anar shugaba, ko kuma jigo da ma’anar itatuwan da ake kafawa su tallabi gugan ban ruwa (CNHN, 2006: 216). To amma shi a nan, shi ake kafawa domin a tallafi ilimi, ma’ana tsayuwarsa ce ke samar da wannan ilimi.

    5. Salon Yabo ga Farfesa Salisu Ahmed Yakasai

    Farfesa Salisu Ahmed Yakasai sanannen masani ne a ɓangaren harshe, ya yi rubuce-rubuce da dama waɗanda suka fi karkata ga kare-karen harshen Hausa, harsunan da ke maƙwabtaka da Hausa. Haka zalika ya yi rubutu a ɓangaren tatsuniya. Makaɗi (Dr.) Aminuddeen Ladan Abubakar ya yi wa Farfesa waƙoƙi, cikin waƙoƙin mun nazarci waƙa guda, inda muka ciro yabon da ya yi masa. Ga irin yabon nan biye:

    G/Waƙa : Jagoran ilimi Salisu ɗan Amadu Furofesa,
    : Darajar ilimi Salisu jigo na walwalar harshe.

    Misali na I

    Jagora : Ga ruhin ilimi Salisu in dai ana batun harshe,
    : Ga rayin ilimi Salisu tsari na sautukan harshe,
    : Ga gidan ilimi al’umma sauti na samuwar harshe,
    : Ginshiƙin ilimi Salisu gado na sarrafar harshe,
    : Falsafar ilimi Salisu na ɗaufare a kan harshe,
    : Dakata ka jiya Salisu yau zan rawa rawar harshe,
    : Ka yi min uziri Salisu rumbunka zan shige harshe,
    : Zan yi ma tage Salisu jigo na walwalar harshe.

    Kamar yadda ya gabata a bayanan sama, mafi yawa ire-iren waɗannan waƙoƙi Makaɗi Alan Waƙa kan buɗe su da wasu ɗiya, sannan daga baya gindin waƙa da amshi ya zo. A wannan matashiya, ya buɗe da yabon Farfesa Salisu Ahmed Yakasai inda ya bayyana shi da ‘ruhin ilimi’, da ‘rayin ilimi’ wanda dukkaninsu ma’ana ɗaya suke ɗauka. Sannan sai ya ambace shi da ‘gidan ilimi’ da ‘ginshiƙin ilimi’.

    A waɗannan yabo da ya yi ta hanyar gwarzantawa, ya yi ƙoƙarin bayyana fagen da Farfesa Yakasai ya fi shahara, wato fagen ilimin harshe. Sannan a layi na ƙarshe, sai ya bayyana shi da ‘jigo na walwalar harshe’. Wannan sai ya ƙara fito da fagen da Farfesa Salisu Yakasai ya fi shahara.

    Misali na II

    Jagora : Jami’a na nufa aradu wanshekare batun harshe,
    : Jami’ar ilimi zan je ga tushe maɓuɓɓugar harshe,
    : Jami’ar su Kware autansu jika ga Shehu kau reshe,
    : Ga Baba Gwani Salisu Amadu maigidan harshe,
    : Walwala nika so Salisu za mu yi a kan batun harshe.

    A wannan ɗiya kuwa, ya kira shi da ‘Baba’ da kuma ‘gwani’. Wato uba ne a ɓangarensa na harshe, sannan gwani ne ta yadda ya san wannan fage sosai da sosai.

    Misali na III

    Jagora : Sanadin su uba Salisu ɗan Amadu Furofesa,
    : Daraja tasa ce ta hana Ala ya rinƙa Ingausa,
    : Sababin ilimi wanda nake bibiya a rumbunsa,
    : Daraja tasa ce ta hana Ala ya rinqƙa Arausa,
    : Vurbushin ilimi ya ba ni dama ta walwalar harshe.

    Domin ya ƙara nuna gogewar Farfesa Salisu Yakasai a wannan fage na harshe, sai ya bayyana wa duniya ta hanyar yabo cewa, shi kansa idan ba domin Farfesa Salisu ba, da ba zai rinƙa tafiyar da waƙarsa da tatacciyar Hausa ba, sai dai ya rinƙa haɗawa da Ingausa, wato ya rinƙa ɗaukar wasu kalmomi na Turanci yana kiran su da Hausa, ko kuma Larausa, shi ne Hausantar da kalmomin Larabci. To amma albarkar karatun da ya samu a rumbun Farfesa Salisu, sai ya san abubuwa da dama, kuma ya iya tantance kalmomi.

    Misali na IV

    Jagora : Zan yabon ka gwani ko da a kan bishiya a kan reshe,
    : Zan yabanta gwani ba zan amai ba balle fa in lashe,
    : Ko in na sarari ko ko ina a hukunce ga harshe,
    : Za a ji ni da kai Salisu ƙaunarka na cikin tushe,
    : A jinni take ma Salisu tun fil’azal cikin tushe.

    Duk domin dai gwarzanta Farfesa Yakasai, sai ya ci gaba da yabonsa da kuma bayyana cewa ko a ina zai iya yabon sa, sannan ƙaunarsa daman can akwai ta tun a tsatso.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Masana A Bakin Makaɗa: Nazarin Yabon Masanan Hausa A Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Alan Waƙa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa danna nan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Ƙungiyar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ta Kiɗa

    Ƙungiyar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ta Kiɗa

    Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya samar da ƙungiya ta aiwatar da kiɗa mai zurfin tunani wadda kuma ta amsa sunanta. A wannan ƙungiya Ɗanƙwairo shi ne Jagora, kuma yana ba ‘Y/Amshi nasa damar yin ƙari da ajewa da sauka da saukar sauka da takidi da rakiya ko karɓeɓeniya, wani bi ma da bayayyeniya, sannan da yin takidi na G/Waƙa.

    Haka kuma a rera wasu waƙoƙi Alhaji Musa Ɗanƙwairo yakan tafi da Sanƙirori da wasu hadiman waƙa duk a ƙungiyar kiɗa ta Musa Ɗanƙwairo.

    Da kansa Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya nuna yadda yake aiwatarwa da ƙullawa da rerawa da sadar da ɗiya a waƙoƙinsa a wannan ɗa na waƙarsa ta ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu II, mai G/Waƙa:

    Shirya kayan faɗa mai gida Tsahe:

    Jagora: Duk Makaɗan da at Tsahe nai jam’i,
    : Hab baƙi ha ‘yan gida su duka,
    ‘Y/Amshi: Babu mai shirya waƙa kamat tawa,
    Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla wuƙatai,
    ‘Y/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,
    : In nuk ƙulla waƙa a ƙara man,
    : Mu haɗu duk azanci gare mu,
    : Shin a a mutum guda za ya radde mu,
    : Shirya kayan faɗa mai gida Tsahe,
    : Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.
    Jagora: Ga mu hwa! Ga mu hwa!!

    (Ɗan’ƙwairo, Waƙar Musa Ɗanƙwairo ta ‘Yandoton Tsahe Aliyu & Gusau, 2003: sh. ɗi)

    Domin haka, Musa Ɗanƙwairo yana ƙullawa da rera ɗiya na waƙoƙinsa a yayin sadarwa kamar haka:
    +Ƙungiya
    + Jagora (+Ƙulli)
    + ‘Y/Amshi (+Ƙari +ajewa +sauka +saukar sauka +takidi +rakiya +karɓeɓɓeniya +/-Bayayyeniya +ciko ko maimaita ko takidin G/Waƙa)
    + Sanƙira (Mai Kalato Ƙarin Bayanai)
    + Hadiman Waƙa

    Ƙungiyar Makaɗa Musa ƊanƘwairo Maradun ta Kiɗan Kotso ta haɗa da:

    i) Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun = Jagora

    ii) Muhammadu, Daudun Kiɗa na Farko, Ya rasu = Kiɗa da Amshi

    iii) Garba, Zawacin Kiɗa, Marafan Kiɗa,
    Daudun Kiɗa na Biyu (2), Ya rasu = Kiɗa da Amshi

    iv) Audu, Wakilin Kiɗa = Kiɗa da Amshi

    v) Ali, Sabon Kiɗa (ɗan Sa’idu Shayi, Wani Ƙanin Musa Ɗanƙwairo) = Kiɗa da Amshi

    vi) Sani, Zaƙin Murya, Marafan Kiɗa, Ya rasu = Kiɗa da Amshi

    vii) Abubakar (Garba), Ciroman Kiɗa (ɗa), Ya rasu = Kiɗa da Amshi

    viii) Ibrahim Sarkin Fada (Ƙane) = Kiɗa da Amshi

    ix) Muhammadu Jikka (Jikka, Halifa 3) = Kiɗa da Amshi

    x) Sani (Jika) = Kiɗa da Amshi

    xi) Muhammadu Gambo (Bara) = Kiɗa da Amshi

    xii) Malam (Bara) = Sanƙira, Kwandon Ɗanƙwairo

    xiii) Ƙanƙahu (Bara) = Tsaron Kaya

    xiv) Sada (Bara) = Sanƙira

    xv) Rabo (Bara) = Kiɗa da Amshi

    xvi) Nabuba (Bara) = Kiɗa da Amshi

    xvii) Bucaca ‘Yarkohji (Bara) = Kiɗa da Amshi

    xviii) Amadu Bakura (Bara) = Sanƙira

    xix) Sallah Kwana (Bara) = Hadimin Gidan Ɗanƙwairo

    xx) Daudu Ɗangaladima (Bara) = Kula da Doki da Gona

    Domin karanta cikakken bayani akan Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Dangantakar Harshe da Waƙa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yin Waƙar Baka ko Sarrafa Waƙar Baka

    Yin Waƙar Baka ko Sarrafa Waƙar Baka

    A lokacin da makaɗi ya zo yin waƙar baka tun a ƙwaƙwalwarsa da tunaninsa yake fara tsara ta. Wannan tsari shi ne na baɗini, wanda yake a rattaɓe a zuciyarsa kuma a cikin jumlolinsa.

    To, tun daga wannan lokaci ne ya riga ya yi waƙarsa ta baka ta bin waɗannan matakai:

    – Matakin Ƙullawa
    – Matakin Kiɗa
    – Matakin Rauji
    – Matakin Kalmomi
    – Gindin Waƙa
    – Layuka ko Saɗaru a Ɗiya 
    -Nuna Farin Ciki
    – Nuna Baƙin Ciki
    -Faɗakarwa
    -Gargaɗi
    -Ilmantarwa
    -Nasihantarwa
    – Isharantarwa
    -Yabawa
    -Yin Zambo
    -Yin Habaici

    Da Sauransu Kamar Kalmomin Azancin Magana

    Matakin Ƙullawa

    Makaɗan baka sukan ƙulla waƙoƙinsu ta azanci da fasahar da suke da su.
    Ma’anar ƙulli ta ƙamus:

    A ƙamus na Hausa-English (Awde, 1996: 102) ya nuna Ƙulli shi ne (1) to knot (2)to plan (3) to conspire; wato (1)ya ƙulla (2) ya shirya ko ya yi dabara (3) ya haɗa kai. Shi kuma Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 285) cewa ya yi ƙulla, ita ce ɗaura ko ƙudura.

    Ma’anar Ƙulli ko Ƙulla ko Ƙullawa ta isɗilahi wato ta fannin ilimin waƙar baka. Ita ce:

    Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya faɗi yadda yake ƙulla waƙarsa a inda yake cewa:

    Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,
    ‘Y/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,
    Jagora: In naƙ ƙulla waƙa a ƙara man,
    ‘Y/Amshi: Mu haɗu duk azanci gare mu,
    : Shin a a mutum guda za ya radde mu,
    : Shirya kayan faɗa Maigida Tsahe,
    : Ali ɗan Iro bai ɗauki reni ba.

    (Ɗanƙwairo, Waƙar ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu II (1960-1991)

    Ƙullawa ta waƙoƙin makaɗan baka tana da matakai biyu. Akwai ƙullawa ta makaɗan ƙungiya, sannan akwai ƙullawa ta makaɗan kaɗaita. Ga su kamar haka:

    i) Ƙullawar Makaɗan Ƙungiya

    Waƙoƙin baka na Hausa waɗanda ake ƙullawa ta ƙungiya, waƙoƙi ne waɗanda ake tunaninsu ta tsakanin Jagora da kuma ‘yan amshinsa. Ita ƙungiya ita ce wadda ta ƙunshi Jagora da kuma yaransa masu yi masa amshi na waƙar baka da kuma yin kiɗa.

    Har wa yau, ƙungiya ta ƙunshi ‘yan ma’abba ko san-ƙirori ko masu kirarin baki. A wannan lokaci, za a haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin Jagora da ‘yan amshinsa, a dinga tunanin yadda za a shirya waƙa, musamman ta kawo jumloli da yadda za a tsara saɗaru ko layuka, sannan ana yi ana dakatawa ko lumfasawa. Wannan shi ne ƙulla waƙa ta makaɗan ƙungiya.

    Su kuwa makaɗan kaɗaita, su ne waɗanda Jagororinsu kawai za su dinga ƙulla kalmomi da jumloli, amma yaransu, za a sami waɗanda suke yin amshi wato +ciko kawai, sai dai ba su yi musu kowane irin ƙari a waƙa. Akwai wasu jagororin da ba a ce musu ko ƙala, Jagora ne zai ƙulla waƙarsa kuma ya ƙare ta shi kaɗai. Irin wannan ƙulli jagora ne kawai zai yi tunanin waƙa a baɗininta idan ya gama ƙulla ta sai ya zo cikin yaransa ya rera ko ya je wani wuri ya sadar da ita. A irin wannan waƙa, Jagora ne kawai ake jin muryarsa yana rera waƙa, yana sadar da ita ga jama’a.

    A bisa waɗannan matakai ne ake bi, ake ƙuƙƙulla, waƙoƙi na gargajiya ko waƙoƙi na zamani na baka da Hausawa suke yin tunaninsu a baɗini, daga baya su rera su a yayin da suke sadar da su.

    Matakin Kiɗa

    A Ƙamusun Hausa an nuna kiɗa yana nufin bugun ganga ko kalangu ko abun bugawa ko bugun ƙwarya ko goge ko garaya ko taushi ko kotso da hannu ko da makaɗi ko da wani abu (CNHN, 2006: 243).

    A ilimin fannin waƙar baka, kiɗa yana nuni ne da wani amo ko sauti da ake samarwa ta gwama ko haɗa abubuwa biyu kamar dutsi + dutsi ko tafi + tafi ko baki + ƙahon dabbobi ko ganga + gula (makaɗi) ko wani abu + wani abu ko sauransu. Kiɗa kuma yakan zama wani amo ne wanda yakan shiga jikin mai sauraro, ya sa masa karsashi har ya dinga rausayawa, yana tattakawa ko jujjuyawa.

    Gusau (2008: 54) yana ganin kiɗa shi ne wanzar da amo mai shiga jiki wanda kuma ake aiwatarwa ta haɗa abubuwa biyu ta matakin busawa ko tafawa ko bugawa ko kaɗawa ko gogawa ko girgizawa ko kuma wasun waɗannan.

    Akwai kayayyakin kiɗa da dama. Wasu na gargajiyar Hausawa ne, wasu kuma na baƙin wasu al’ummu ne waɗanda Hausawan suka aro, suna amfani da su. A wajen Hausawa akwai kiɗa zallarsa kawai, ba tare da haɗawa da waƙa ba, ko kirari ko kaɗa take. Akwai kuma kiɗa ta amfani da kayan kiɗa wanda ake haɗawa da waƙa, wanda kuma ake yi wa waƙoƙin da makaɗan baka suke yi.

    Kiɗa a wajen Hausawa ya rarrabu zuwa: Kiɗa

    -waƙa +take -take +waƙa
    -Waƙoƙin Gaɗa
    -Waƙoƙin Samartaka
    -Waƙoƙin Manyan Mata
    -Waƙoƙin Manyan Maza
    -Waƙoƙin Makaɗa

    A wajen aiwatarwa ta waƙar baka akan gwama ta da amon kiɗa wanda za su dinga tafiya a tare tsakanin muryar makaɗi da sautin gangar da makaɗin yake amfani da ita. Bisa mahangar makaɗa, akwai wasu hanyoyi da ake ɗora kiɗa na waƙoƙinsu na baka domin su yi daidai da yadda ake sadar da su. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da:

    – sadar da kiɗa daidai da nauyi na muryar makaɗi da kuma raujin da aka zaɓa wa matanin waƙa;
    – Dacewar amon kiɗa da gaɓoɓin murya bisa gurabunta na hawa da sauka da kuma faɗuwa;
    – Ƙarfafa madirar gaɓoɓi;
    – Wani bi a kaurara amon kiɗa;
    – Wani bi a sassauta amon kiɗa;
    – Wani bi a ja amon kiɗa;
    – Wani bi a matse ko a tauye amon kiɗa;
    – Wani bi a qwairanta amon kiɗa;

    Sannan kuma yanayin kiɗan yana iya zama:

     Mai diri
     Mai ƙarfi
     Mai kauri
     Mai zaƙi
     Mai kumbura
     Mai kaurara
     da sauransu

    Matakin Rauji

    Ƙamus na Hausa a ɓangaren Hausa-English (Awde, 1996: 131) ya bayyana kalmar rauji da clapping wato yin tafi ko ban tafi (Awde, 1996, 131 & 210). A kuma littafin Ƙamus na Keɓaɓɓun kalmomi wato Hausa Metalanguage ya fassara Rauji da Ingilishi da Rhythems wato Kari ko karin murya (Awde, 1996:361).

    A fannin ilimin waƙar baka kuwa, rauji wani sauti ko amo ne wanda yake tashi a sama ko ya sauka ko ya faɗi. Rauji yana iya zama murya ta wata halitta mai rai ko sautin wani abu maras rai kamar ƙara ko doka ƙafafu a bisa ƙasa ko wani tsando ko sauti daga kukan tsuntsaye. Har wa yau kuma akwai rauji mai ɗaɗi, mai zaƙi da kuma rauji maras daɗi, mai-ta-da-hankali, kamar kukan kanari (rauji mai zaƙi) da kuma kukan jaki (rauji maras zaƙi, mai ɗaukar hankali).

    Wata ma’anar isɗilahi kuma, rauji na iya zama masaukar murya a gaba.

    A yayin da aka gwama rauji a waƙar baka ta Hausa ana ɗora shi bisa muryoyi na gaɓoɓi na kalmomi ne waɗanda akan sarƙa su a tayar da saɗara a ɗa na waƙa. Rauji wanda aka zaɓa, aka ɗora wa saɗara ko layi a ɗa na farkon waƙa, shi ne zai dinga daidaita rauji a dukkan layuka da ake ƙullawa a ɗiya na waƙar.

    Nauyin rauji a waƙar baka ta Hausa gajere ne, shi ya sa yake tafiya bisa gaɓoɓi na kalma gwargwadon hawansu da saukarsu da faɗuwansu. Matakai waɗanda ake bi a wajen samar da rauji a waƙar baka ta Hausa sun haɗa da:

    – Rauji mai dogon zango
    – Rauji mai gajeren zango
    – Rauji mai matsakaicin zango

    Sannan gaɓa ta rauji za ta iya zama mai nauyi wadda za ta ƙunshi [bww] ko [bwb], ko kuma ta zama mai sauƙi wadda za ta iya zama gaɓa mai [bw] kawai.

    A wajen furta rauji na waƙar baka ana yi masa waɗannan abubuwa kamar haka:

    – Kaurara gaɓa mai nauyi;
    – Jan gaɓa mai nauyi ko mai sauƙi;
    – Daidaita amsa-amon kari (hawa ko sauka ko faɗuwa) a ƙarshen kowace saɗara ko layi.

    Haka kuma ana yin rauji ne na waƙar baka daga karin murya (na hawa da sauka da faɗuwa) da kuma amon kiɗa tun daga tunanin makaɗi a zuciyarsa. Domin haka, ana samar wa waƙoƙin baka rauji ne ta waɗannan hanyoyi:

     Karin murya daga makaɗin waƙar;
     Amon kiɗa daga kayan kiɗan da makaɗi yake amfani da su, ta la’akari da madiransu na hawa da saukar amo ko kuma faɗuwarsa.
     Daga nan sai a fitar mata da raujinta;
     Rauji zai samar wa waƙar baka wani amo wanda zai fitar da ita kaɗai daga sauran waƙoƙin baka na makaɗin.

    Matakin Kalmomi

    Kamar yadda aka nuna a baya, idan makaɗin baka ya tashi aiwatar da wata waƙa ta baka, yakan fara aiwatar da waƙar ne a cikin zuciyarsa da kuma ƙwaƙwalwarsa tun kafin ya furta waƙar a waje. Haka kuma tunanin makaɗi na kalmomi da yadda zai sarrafa su cikin azanci da hikima shi ne wani abu da zai biyo biyo baya a aiwatar da waƙar baka.

    Sannan kuma dukkan makaɗi na ƙungiya da kuma makaɗi na ƙire duk suna yin aiwatarwa a wajen daidaita waƙoƙinsu da tsawaita su. Matakin kalmomi yakan bambanta dangane da kalmomi da makaɗi ya yi tunaninsu ko kuma ya zaɓo su wajen tsawaita waƙar da zai yi. Wasu daga cikin kalmomi da ake zaɓa a shirya waƙar baka sun haɗa da:

    Kalmomin Shirya Gindin Waƙa

    Gindin waƙa furuci ne na wasu kalmomi masu ma’ana masu nauyin saƙo, masu hikima da balaga da azanci waɗanda ake shiryawa don a gabatar da waƙar baka. Ta gindin waƙa ne ake rarrabe ɗa da ɗa a waƙar baka. Waƙoƙin baka sun kasu kashi biyu. Akwai waɗanda ake yi wa Gindin Waƙa kamar waƙoƙin Alhaji Abdu Karen Gusau. Sannan kuma akwai waƙoƙin da ba a yi wa Gindin Waƙa kamar waƙoƙin Alhaji Babangida Kakadawa.

    Ga Misali na Gindin Waƙa:

    G/Waƙa: A lula ɗan haya,
    : Mai gyaran kekuna.
    (Abdu Karen Gusau; Waƙar Alhaji Alula Ɗanhayar Kekuna, Fagge, Kano)
    Har wa yau kuma, Gindin waƙa yakan bayyana abin da waƙa take nufi tun kafin a shiga cikinta. Gindin waƙa wani ginshiƙi ne ko babban matangali na ginin waƙar baka. Wani kuma harsashe ne ko majingini na farko a waƙar baka, inda duk bai zauna ba, waƙa ba za ta ba da sha’awa ba, balantana har ta yi wani armashi.

    Idan makaɗi ya sami zaunuwar Gindin waƙa, to, zai sami haske ya buɗu a gare shi, ya sami walwala ta zaɓo kalmomi waɗanda suka dace ya saka a waƙa waɗanda za su ba shi damar samun sauran ɗiyan waƙar. Makaɗin baka yakan yi tunani a zuciyarsa idan kuma wanda suke a ƙungiya ne sukan haɗa ƙarfi da azama su samo kalmomi zaunannu kuma mafi girkuwa a waƙar da suke shiryawa ta baka su samar da Gindinta.

    A wajen shirya Gindin waƙa makaɗa sukan yi amfani da waɗannan matakai:

    Yawanci Gindin waƙa bai shige layuka biyu (2) zuwa huɗu (4) ba;
    – Yakan ƙunshi kalmomi masu nauyi da ake sarrafa su cikin azanci da hikima;
    – Gindin waƙa yakan ƙunshi sunan mai waƙa ko laƙabinsa ko alkunyarsa ko wata ƙarina da ke nuna Mai waƙa;
    – Sannan ana wakiltar Gindin waƙa da harafin [X] na ABCD;
    – Ana kuma wakiltar adadin saɗaru ko layuka a Gindin waƙa da alkalumma na [1,2,3,4] kamar haka: [X1] ko [X2] ko [X3] ko [X4] da sauransu;

    – Ga misalai:

    i) Gindin Waƙa; (mai layuka huɗu (4)
    X1: Ka bawai maza,
    X2: Na Magajin Gari Bubakar,
    X3: Kai ad da yanzu,
    X4: Allah ya ba ka Sarkin Kabi.
    (Mamman Inyaga Argungu; Wakar S/Kabi Muhammadu Mera. Wato kalmomin nuna farin ciki).

    ii) Gindin Waƙa; (mai layuka biyu (2)
    X1: Tankwafau namijin zaki,
    X2: Sa’idu bai taɓa tsoro ba.
    (Idi Ɗangiwa Zuru: Waƙar Sarkin Sudan Sa’idu, Kwantagora. Wato kalmomin nuna farin ciki)
    – Yawancin kalmomi masu nauyin ma’ana da hikimar zance da makaɗa suke tsarawa a Gindin waƙa sun ƙunshi na nuna farin ciki ko na nuna baƙin ciki. Misalin Gindin waƙa na kalmomin nuna baƙin ciki:
    G/Waƙa: X1: Gagarabadon namiji tsayayyen ɗan kasuwa
    (Shata: waƙar ‘Gagarabadau, Mp3)

    – Kuma wani Gindin waƙar yakan ƙunshi kalmomin yabawa ko na zambo ko na habaici da na zugugutawa da makamantansu. Misali:

    G/Waƙa: X1: Ya ci maza ya kwan yana shirye,
    X2: Gamda’aren Sarki Tudu Alu.
    (Narambaɗa, Waƙar Tudu Alu; Kalmomin zuga da kururantawa da yabawa).
    Akwai kuma a wani G/Waƙa:
    X1: Madogara na Malam,
    X2: Iro Uban Bawa,
    X3: Maigida Shinkahi.
    (Narambaɗa, Waƙar Magajin Garin Shinkahi, Ibrahim; Kalmomin zuga da yabawa).

    – Haka kuma wani Gindin waƙar yakan ɗauki kalmomin faɗakarwa ko gargaɗi ko ilimtarwa ko isharantarwa ko nasihantarwa da sauransu. Misali:
    G/Waƙa: X1 “Yan Nijeriya sai Hausa
    (Abdu Karen Gusau; waƙar Harshen Hausa-kalmomin kishin Hausa da na gargaɗi da na ilimantarwa. Gusau, 2015: 64-75).

    G/Waƙa: X1 Mu kama sana’a ‘yan Nigeriya,
    X2 Zaman banza ba namu ne ba.
    (Abdu Karen Gusau, Waƙar Gargaɗi kan riƙo da sana’a – kalmomin gargaɗi da na faɗakarwa da na isharantarwa, Gusau, 2015: 75-78).
    G/Waƙa: X1 Shegiyar ƙafa ke kika saba da gulando,
    X2 Ki tallafe ni, ɗaukar ni ƙafa kar ki gaza ni.
    (Abdu Karan Gusau, Waƙar Shegiyar ƙafa – Kalmomin faɗakarwa da na gargaɗi da na isharantyarwa. Gusau, 2015: 96-97).

    Layuka ko Saɗaru a Ɗiya

    Layuka jam’i ne na layi (tilo). A Ƙamusun Hausa (CNHN, 2016 206-304) an faɗi ma’anarsa kamar haka: (i) Miƙaƙƙen zane (ii) miƙaƙƙiyar hanya ta cikin gari, ko jerin rumfunan kasuwa ko wani abu (iii)majalisar alƙalai ko kotu ko ɗakin shari’a. Amma kuma a ƙamus (Hausa-English) na Awde (1996:106) ya bayyana Layi (p/layuka) da harshen Inglishi da Line. A kuma ɓangaren ƙamus ɗin na English-Hausa, Awde

    (1996: 295) ya fassara line da noun=n=: (1) layi (2) Baiti (3) Telephone line wato waya. Ta Fuskar Saxaru (Jam’i); saɗara (tilo) kuwa – Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 381) ya fassara ta da layi cikakke na rubutu.

    A cikin layuka ne ko saɗaru waƙar baka take shirya saƙonni tun a ƙwaƙwalwa, sannan ta rera su, ta sadar da su ga al’umma; ta amfani da mataki na kalmomi waɗanda suka haɗa da nau’o’i daban-daban.

    Kuma har gami da kalmomi na maganganun habaici da isharantarwa da gargaɗi da ilimantarwa da tunasarwa da faɗakarwa da makamantansu da yawa.

    A waƙoƙin baka na Hausa akan shirya layuka ko saɗaru masu sauƙi a ƙagi ɗa na waƙar baka wanda zai ƙunshi saƙo ɗaya kawai. Akwai kuma layuka ko saɗaru da ake shiryawa masu tsauri, waɗanda za su haɗu su tayar da ɗa ɗaya na waƙar baka. Shi ɗa ɗaya mai tsauri yakan ƙunshi saƙonni da yawan gaske kamar guɗa huɗu (4) ko ma fiye da haka waɗanda ake wakiltarsu kamar haka:

    Ɗa ɗaya mai tsauri:
    A1:
    A2:
    B1:
    B2:
    B3:
    C1:
    C2:
    C3:
    C4:

    Da sauransu. Za a ba da misali na ɗan waƙa mai sauƙi (Mai saƙo guda ɗaya kawai) kamar haka:
    A1: Ni kam lafiya nit taho salla,
    A2: Lafiya ni ishe Sarki,
    X1: Amadun Bubakar gwarzon Yari,
    X2: Dodo na Alƙali.
    (Narambaɗa, waƙar Sarkin Gobir Ahmadu Bawa (1935-1975).

    Shi kuma ɗan waƙa ɗaya mai tsauri (mai Saƙonni da yawa fiye da ɗaya), ga wani misali kamar haka:

    A1 Na Magaji mai Martaba ɗan Mu’azu,
    A2 Irin assabad Bubakar baba yay yo,
    A1.1 Na Magaji mai Martaba ɗan Mu’azu,
    A2 Irin assabad Bubakar baba yay yo,
    B1 Tsarin gaskiya Bello kai Shehu yac ce,
    B2 Bari masu son duk su maishe ka yaro,
    B 1.1 Tsarin gaskiya Bello kai Shehu yac ce,
    B2 Bari masu son duk su maishe ka yaro,
    B3 Da kyauta da ilimi da neman dalili,
    B4 Da gode ma Allah da istingfari,
    B5 Da su Bello ɗan Shehu yat tsarmo kowa,
    B6 Ka kai kamar Bello ka gadi Moyi,
    B7 Saura ka kai inda mai Hausa yak kai,
    B6.1 Ka kai ka mar Bello ka gadi Moyi,
    B7 Saura ka kai inda mai Hausa ya kai,
    X1: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,
    X2: Sarki Kudu Macciɗo ci maraya.

    (Sa’idu Faru, waƙar Muhammadu Macciɗo lokacin yana a matsayin Sarkin Kudun Sakkwato, ya rasu a 1995 yana Sarkin Musulmi).

    A layi na ɗan waƙa ana wakiltar sa da alƙalumma na [1-0], da haruffa na ABCD ban da [X] kamar yadda aka gani a misalan da suka gabata. Har wa yau kuma ana iya wakiltar ɗan waƙa ta jan layuka kawai. Misali:

    Ɗanwaƙa mai layuka biyu ko uku
    Xa: 1 ____________________
    2 _______________________
    3 _______________________
    X1 ______________________
    X2 ______________________

    Ko ɗa mai layuka biyu
    Xa: 1 ____________________
    2 _______________________
    X1 ______________________
    X2 ______________________

    Saƙonni a ɗa na waƙa, bisa yawanci ba su shige layuka guda biyar (5). Misali: A1, B1, C1, D1, E1, wato saɗo na ɗaya (1) zuwa na biyar (5).

    A layuka ne kuma ko saɗaru ake tunani a zuciya a gina saƙo na farin ciki ko na baƙin ciki ko na faɗakarwa ko na tunasarwa ko na gargaɗi ko na ilimantarwa ko na isharantarwa ko na yabawa ko na zambo ko na habaici ko na wani saƙo da makaɗi yake son ya gaya wa al’ummarsa a harshen waƙar baka.

    Alalmisali:

    Jarora: Yara farau-farau farar tabarma,
    : Farin cikin mai baƙunta,
    Y/Amshi: Gagarabadon namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    (Shata, Gagarabadau; Gusau, 2018:20)
    Akwai kuma
    Jarora: Ga wani ya yi ilimi babu hankali,
    : Ga dai ilimi babu nutsuwa,
    : An kira shi Dabtan ya amsa,
    : Da ganin ƙurji sai ya yaɓa wuƙa,
    Y/Amshi: Na gode wa Amadun Gaya.

    (Shata, Waƙar Amadun gaya; Gusau, 2018: 23)

    A lokacin da makaɗa suke yin tunanin baɗini na wata waƙa da za su shirya sukan bambarta a wajen yin wannan tunani da kuma samo kalmomi na waƙa.

    i) Wasu makaɗan sukan zauna a ƙarƙashin wata inuwa kamar ta wata bishiya, su kwanta su lulluɓe kansu, suna tunanin wata waƙa. Alalmisali, Alhaji Ibrahim Narambaɗa, idan yana tunanin waƙa har zana tunanin nasa yake yi a ƙasa, ya dinga shata wani zani ko zane-zane kamar zai zana wani hoto na musamman. Zai dinga zanawa a ƙasa a cikin layuka, ya dinga yin zane-zane, yana tsara saɗaru na waƙa.

    ii) Wasu kuma makaɗan sukan dinga jefo wasu kalmomin suna sarƙawa suna kuma zubar da wasu, suna warwarewa, har su haɗa kalmomin da suke buƙata na waƙar. Wasu makaɗan, kamar Salihu Jankiɗi, har tattaka ‘yan amshinsa yake yi, suna zazzaune, idan sun jefo wasu kalmomi da ba su dace ba.

    Ta haka dole ɗan amshi ya yi taka-tsantsan da abubuwan da yake ba da tasa gudummawa.

    iii) Wasu makaɗan, musamman makaɗan ƙire (kaɗaita) sukan sami saulin yin tunani ne a yayin da ‘yan amshinsa suke maimaita kiɗa, su kuma makaɗan sukan yi shuru, suna numfasawa. A lokacin da kuma sanƙirorinsu suke ba da tasu gudunmawa, su kuwa makaɗan (Jagororin) suna yin shuru, suna saurarensu. Da sauran halayen makaɗan kaɗaita. A duk lokacin da makaɗan suka yi shuru suna tunani ne a kan abubuwan da za su ƙara ƙulla waƙoƙinsu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sadarwa a Waƙar Baka danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita, RMK

  • Yabo A Waƙoƙin Baka

    Yabo A Waƙoƙin Baka

    Ba wannan aikin ba ne farau da yake ɗauke da yabo a cikin waƙoƙin baka na da ko na zamani; an yi ayyuka da dama da suke da kamanceceniya da wannan nazari.

    Misali: Yakawada (Babu shekara) ya yi wani aiki mai taken “Nazarin Jigon Yabo da Zuga A Kirarin Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina”. 

    Inda a wannan aiki nasa, ya yi ƙoƙarin hakaito wasu cikin yabon da aka yi wa Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina.

    Shi ma Bello (1976) ya yi makamancin wannan rubutu; inda ya bibiyi waƙoƙin Hausa ya zaƙulo yabo da zuga da kuma zambo.

    Yakawada (2001:68-85) ya maimaita wani aiki, amma a aikin, ya kalli tubalan ginin yabo ne inda ya kevanci nazarin ga waƙoƙin iko (sarauta) ne kawai.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi; Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

    Domin karanta Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa danna nan

  • Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka

    Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka

    Makaɗan baka na zamani sun yi waƙoƙin yabo da zuga daban-daban ga malaman Hausa musamman waɗanda suke jami’o’in Ƙasar nan; inda waƙoƙin nasu suka fi karkata ga farfesoshi.

    A wannan gaɓa, za a bayyana wasu muhallai da aka yi irin wannan yabo ga ɗaya daga cikin malaman Hausa; wato Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau;

    Inda aka keɓance wasu waƙoƙi guda biyar daga bakunan makaɗa biyar cikin ɗimbin makaɗan da suka yi masa waƙa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo Daga Waƙar Aminu Alan Waƙa danna nan

  • Yabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti

    Yabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti

    Kamar Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa); Zabiya Maryam Sale Fantimoti ita ma ba a bar ta a baya ba, ta yi waƙoƙin yabo da dama ga mutane mabambanta; cikinsu kuwa har da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau.

    A wannan ɓangare, an ɗauko ɗaya daga cikin waƙoƙin da Maryam Fantimoti ta yi masa, inda aka zaƙulo muhallan da ta yi wannan yabo domin fito da su fili.

    G/Waƙa: Furofesa Sa’idu Muhammad na Gusau,
    A gaida Babban Malami a harshen Hausa
    Ɗan ƙwarai.

    Jagora: Akwai adabi gare shi sashi-sashi,
    A fannin Hausa sai na ce ga shi,
    Idan ya tsaya yana bayani ma’ishi,
    Sai in ce

    ɗalibai maqoshi.
    Sa’idu Muhammad Gusau ɗan gayya ɗan ƙwarai.

    Jagora: Nauyin ba ya sa ka ka makara,
    Domin ɗalibanka kar sai ta jira,
    Ga ka da alƙawar kamar tattabara,
    Idan ka faɗa za ka yi shi ka tara,
    Za ya zuba ya ba wa kowa ya sha ɗan ƙwarai.

    Jagora: Ga ka da halinka mazaje na jiya,
    Idan an gano ka za a tuna jiya,
    Sannan laffazin da duka za aka biya.

    Taƙaitaccen Tarihin Zabiya Maryam Sale Fantimoti

    An haife ta a shekarar 1977 a unguwar Gyaɗi-gyaɗi ta Kanon Dabo, sannan ta yi karatu tun daga Islamiyya har zuwa Sakandare.

    Game da waƙa kuwa, ta fara tun tana ƙarama, kawo yanzu ta yi waƙoƙi da dama, wanda har ta kai ga duniyar Adabi ta san ta, kuma har ta kai ga zama Sarauniyar Waƙa ta Sarkin Kano (Gusau, 2016:244-245).

    Fantimoti shi ne sunan da ake yi mata alkunya da shi.

    Jagora: Duk wani ɗalibi ya zauna ya iya,
    Du’a’i ne muke wa Baba na Baba ɗan ƙwarai.

    Jagora: Ka zama dattijo mai haɗa kowa,
    Lallashi gare ka mai tausawa,
    Koyarwarka Baba ta isa a yi wa,
    Duk wani ɗalibi mu je zakka zuwa,
    Hallata zamaninka Ubanmu ɗan ƙwarai.

    Yabon Da Zabiya Maryam Fantimoti Ta Yi Wa Farfesa

    Zabiya Maryam Fantimoti ta yi yabo ga Farfesa ta hanyar ambatar bayyana faɗin ilminsa, inda ta nuna shi a matsayin ‘masanin sassan adabi’. Shi kuwa adabi, daman ya kasu zuwa gida biyu a jimlace, wato adabin baka da adabin zamani , amma kowane ɓangare yana da nasa rassan.

    To a nan, sai Zabiya Fantimoti ta yabe shi ta hanyar nuna cewa yana da ido a kowane ɓangare na adabin. Sannan sai ta ɗora ga cewa, duk yayin da ya tsaya yana bayani kan adabi ga ɗalibai, to fa za su kwankwaɗa daga kogin ilminsa har su ƙoshi.

    Sannan a baiti na gaba, sai ta bayyana yabon ta fuskar ƙwazonsa wajen rashin nawa ko kasala, ta yadda a duk lokacin da yake da darasi ga ɗalibai, to fa babu wani abu da zai sanya ya ƙi zuwa, zai bar duk wani uzirinsa ya je ya yi wa ɗalibai darasin. Saboda ƙoƙarin yabonsa ta fuskar cika alƙawari, sai Zabiya ta ambace shi da tattabara.

    Domin yabon gaskiyarsa kuwa, Zabiya Fantimoti ta bayyana shi da ‘mazan jiya’. Mazan jiya su ne mutanen da ake bayyana su da cikakkiyar kamala, gaskiya, ƙwazo, himma, riƙon amana, juriya da kuma magana ɗaya, ma’ana idan sun tsaya a kan magana, ba sa sauyawa saboda son zuciya ko wata buƙatarsu ta daban. 

    To siffanta mutum da wannan suna na mazan jiya, kai mutum ne maƙurar yabo ga kyawawan siffofi. Sannan sai ta jingina masa kalmar ‘dattijo’ wadda ita ma siffa ce da ake yabo da ita ga nagartaccen mutum mai magana ɗaya, kuma wanda ba ya saɓa alƙawari ko cin amana.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi; Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) wallafa shi.

    Domin karanta bayani a kan Yadda Ma’anar Roƙo Take danna nan