Tag: Waƙoƙin Hausa

  • Ma’anar Yabo

    Ma’anar Yabo

    Yabo na nufin ba da shaida mai kyau game da mutum bayan ya yi wani abin a yaba; na burgewa ko kuma ana so ya aikata abin na burgewa ko na a yaba.

    Misalin Yabo:

    Jagora: Ka ji waƙa tana fita,
    Gurin ɗan Bafillatana,
    Abu kamar harsashi,
    In na yi hushi harsashin ɗin me?
    In dai waƙa ce,
    Allah ya yarda. (Gusau, 2009:350).

    A nan, za mu fahimci yabo da cewa wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen bayyana zahirin yadda mutum yake, shin waɗannan kalmomin da aka ambata ƙarya ce ko kuma gaskiya ce.

    Domin akan yabi mutum ta hanyar faɗar abin da yake ba gaskiya ba ne, an dai yi ne kawai domin a faranta masa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammd Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

  • Hanyoyin Tattara Waƙoƙi da Bayanai

    Hanyoyin Tattara Waƙoƙi da Bayanai

    Wannan nazari ya sami tagomashin kammaluwa ta hanyar sauraren waƙoƙin da aka yi wa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau;

    Sannan sai aka ga dacewar rubuce su, wanda kafin a rubuta su ɗin, sai aka sami wasu a rubuce; sannan aka tantance su, sai aka tsamo yabon da aka yi masa.

    Bayan wannan, an yi ƙoƙarin bibiyar ayyukan masana waɗanda suka shafi wannan aiki, da kuma tuntuɓar masanan da bibiyar rubuce-rubucen da aka yi a game da Farfesa Gusau da nazarin waƙoƙin baka na Hausa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi; Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammd Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ma’anar Roƙo Take danna nan

  • Muhallan Da Ake Waƙoƙin Fiyano Na Hausa

    Muhallan Da Ake Waƙoƙin Fiyano Na Hausa

    Muhallan da ake waƙoƙin Fiyano na Hausa su ne wuraren da mawaƙan Hausa masu amfani da fiyano suke rera waƙoƙinsu.

    Muhallan Fiyano su ne kamar haka:

    1. Fina-finan Hausa

    Wato irin fina-finan da ake yi a ƙasar Hausa, ko kuma Hausawa suke yi, ko kuma ake yi da harshen Hausa; To a cikinsu akan samu kaɗe-kaɗe na fiyano; da kuma waƙoƙin da aka yi amfani da fiyano wajen aiwatar da su.

    2. Tarukan Siyasa

    A nan ya shafi dukkanin wani dandazon mutane da za a tara a dalilin siyasa, wanda a wannan wuri akan samu waƙoƙin da aka rera da kiɗan fiyano, a wasu lokutan ma akan samu makaɗan fiyano a wurin.

    3. Bukukuwa

    Dukkanin wani nau’i na biki, sawa’un bikin suna ne ko aure ko wanin waɗannan. A nan, za a iske waƙoƙi da dama da aka rera su ta hanyar amfani da fiyano. A wani lokaci kuma, akan samu makaɗan fiyano a wuraren bukukuwa domin yin kiɗan fiyano.

    4. Majalisi

    Wannan kuwa ya shafi wuraren yabon Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da halifofinsa da sauran mutanen kirki. A wannan muhalli ma, akan yi amfani da fiyano wajen yin kiɗa ga waƙar da aka yi ta yabo.

    5. Tallace-Tallace

    Dukkanin wani nau’i na tallace-tallace, sawa’un tallar magunguna ne ko wasu abubuwa ne, kamar robobi da kayan abinci da yaduna da sauransu. To a nan, su ma akan yi musu waƙoƙi ta hanyar amfani da kiɗan fiyano

    6. Kafofin Yaɗa Labarai

    Wannan ya shafi kafofin sadarwa kamar gidajen radiyo da talabijin, domin sukan yi amfani da kiɗan fiyano a yayin da wani shiri ya ƙare kuma suna son sanya wani. Haka zalika, sukan yi amfani da shi domin tallata wani abu da wani kamfani zai ba su.

    7. Yabon Masoya

    Ma’abota soyayya tsakanin maza da mata sukan yi amfani da fiyano wajen yabon junansu, wato za a iske budurwa ta yi wa saurayinta waƙa, kuma ta je an yi mata kiɗan fiyano, ko kuma shi ya mata waƙa, kuma ya je an masa kiɗa da fiyano.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta bayani a kan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan

    Domin karanta bayani akan Misalan Waƙoƙin Hausa Na Fiyano danna nan

  • Misalan Waƙoƙin Hausa Na Fiyano

    Misalan Waƙoƙin Hausa Na Fiyano

    Zainab (2009:84) ta ce “Waƙoƙin fiyano na Hausa su ne waƙoƙin da suka samu canje-canje; daga kayan kiɗa na gargajiya zuwa kayan kiɗa na zamani; kamar fiyano da jita da sauransu”.

    Kamar yadda aka ambata a sama, yawancin mawaƙan wannan zamani suna amfani da fiyano ne wajen kaɗe-kaɗen waƙoƙinsu, don haka kenan waƙoƙin da suka samar na kiɗan fiyano ne.

    Cikin irin waɗannan waƙoƙin akwai:

    • Sakarkari ta Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa)
    • Rayuwa tana faruwa ta Fati Musa Ƙofar Wambai
    • Gatana ta Malam Nafi’u Nguru
    • Ku Ɗinka Hijabi ta Malam Ibrahim Lalula Nguru
    • Bulaliya ta Abubakar Sadiq Suwa’ilu
    • Rawa-rawa ta Naziru M. Ahmad
    • Almajiri ta Muhammad Sani Aliyu
    • Ƙarshen Tika-tika Tik ta Aliyu Auta Masani, Nguru
    • Ku Yi Haƙuri ta Jibrin Muhammad Jalatu
    • Waƙar Rigar ‘Yanci ta AbdulAziz Abdullahi Ningi

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Muhallan da Ake Waƙoƙin Fiyano na Hausa danna nan

    Domin karanta bayani akan Ire-iren Kiɗan Fiyano danna nan