Matsayin Malamai Kan Kashe Husaini (Radiyallahu Anhu)

0
14

Malamai sun kasu gida uku dangane da kashe Husaini (Radiyallahu Anhu); biyu a gefe ɗaya a tsakiya:

1. Ɗayan na gefe: suka ce an yi dai-dai da aka kashe shi, saboda ya fito ne dan ya raba kan musulmai, Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Duk wanda ya zo yana son ya raba kawunanku, alhali kuna bin wani shugaba guda ɗaya, ku kashe shi”. Suka ce Hussaini ya zo ne ya raba kan mutane, alhali suna ƙarƙashin shugaba ɗaya.

2.Ɗaya gefen kuma suka ce shi Husaini shi ne shugaban Musulmai a lokaci wanda ya wajaba a yi wa biyayya, kuma imani ba ya cika sai da yarda shi ba za a yi sallar jam’i ko jama’a ba sai a bayan wanda ya naɗa, kuma ba za a yi jihadi ba sai da izininsa.

3. Su kuwa waɗanda suke a tsaka-tsaki su ne Ahlussuna, ba su goyi bayan waɗannan ɓangarori biyu ba, abinda suke cewa Husaini an kashe shi ne bisa zalunci, kuma ya yi shahada, amma a lokacin ba shi ne shugaba ba, shi kuma wannan hadisi (Na ‘yan tawaye) bai shafi Husaini ba. Saboda lokacin da ya sami labarin kashe ɗan baffansa Muslim bin Akil, sai ya bar maganar halifanci ya nemi a ba shi dama ya tafi wurin Yazidu, ko ya tafi jihadi ko ya koma gida, amma suka ƙi, suka ce sai dai ya yarda a kama shi, yin hakan kuwa bai zama wajibi ba a kansa.

Ya ɗan uwa musulmi mai neman gaskiya ka ga dai matsayin Ibn Taimiyya a kan wannan mas’ala shin ina alamun ƙin Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma) ko goyon bayan abinda aka yi wa Husaini da iyalansa a cikin waɗannan bayanai?

Ya kamata duk wanda ya ce maka Ibn Taimiyya ya ce kaza, to ya kawo maka littafin kuma a karanto maganar tun daga farkonta har ƙarshenta, ba wai a ciccizgo maganganun nan da can ba. Yaa Allah ka fahimtar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta. Ka ba mu ikon yin adalci ga wanda muke so da wanda ma ba ma so, ka fitar da gaba da riƙo daga zukatan mu. Amin.

Yanzu kuma ga maganganun wasu fitattun ɗaliban Ibn Taimiyya:

Shamsuddin Bn Kayyimul Jauziyya Rahimahullah (A.H.S 691 Y.M.S 751)

Shi kuwa kuwa shaihin malami Ibnul Ƙayyim Muhammad Ibn Abubakar, babban almajirin lbnu Taimiyya (Rahimahullah) ga abinda yake cewa:

Yana daga cikin hadisan ƙarya, hadisan falalar sa kwalli da yin ado, da yalwatawa iyali da yin wasu salloli ranar ashura da wasu falaloli da ake faɗa, waɗanda ko hadisi ɗaya bai inganta ba a kansu.

Abinda kawai ya inganta shi ne yin azumi a ranar banda shi sauran duka ƙarya ne. Hadisi mai ɗan dama-dama a kan wannan shi ne hadisin yalwatawa iyali a ranar ashura (cika-ciki) shi kuma Imam Ahmad Rahimahullahu ya ce bai ingata ba”.

Amma hadisin falalar sa kwalli da shafa mai da sa turare ranar ashura, haƙiƙa maƙaryata ne suka ƙirƙire su, sai kuma wasu (‘yan bidi’ar) suka ƙirƙiri nuna alhini da ɓacin rai domin su ƙalubalance su, duka su biyun ‘yan bidi’a ne, sun saɓawa sunna.

Su kuwa ahlussunna, suna aikata abinda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi umarni da a aikata a ranar, suna nisantar bidi’o’in da shaiɗan ya yi umarni da su’.

Ibn Rajab Al-Hambali (Rahimahullah) A.H.S 735 Y.M.S 795

Babban malami Zainuddin Abul Faraj Abdurrahman Ibnu Rajab Al-Hambali ya Ce:

“Dukkanin hadisan da aka rawaito a kan falalar sa kwalli da yin ƙunshi da wanka ranar ashura, ƙarya ne ba su inganta ba” amma an rawaito daga Abdullah ɗan Amr Ibnul As ya ce: “Wanda ya yi azumi ranar ashura za a ba shi ladan azumin shekara guda, wanda ya yi sadaka a ranar za a ba shi ladan sadakar shekara guda” Abu Usa Al-Madini ne ya fitar da shi.

Maganar cika-ciki kuwa an tambayi Imam a kan wannan hadisin ‘sai ya nuna cewa bai inganta ba. Sai da Ibnu Uyaina yace shekararsu hamsin suna jarraba yalwatawa iyali ranar ashura, kuma suna ganin buɗi. Amma dai hadisin bai inganta ba.

Amma ɗaukar ranar a matsayin ranar baƙin ciki da zaman makoki kamar yadda Rafilawa (‘yan shi’a) suke yi saboda a ranar ce aka kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) wannan aiki ne na ɓatattu amma suna ganin dai-dai suke yi; saboda Allah da Manzonsa ba su yi umarni a mayar da ranar da musibu suka afkawa annabawa ko ranar mutuwarsu ranar makoki ba, ballantana, waɗanda suke ƙasa da su”.

Al-Hafiz Abul Fida Ibn Kasir (AH.S 701 Y.M.S 774)

Babban malamin hadisi, malamin tafsiri kuma malamin tarihi; Al-allama lbn Kasir (Rahimahullah) shi kuma ga abinda yake cewa:

“Ya kamata dukkanın musulmai su yi baƙin ciki da kashe Husaini (Radiyallahu Anhu). Saboda shi yana daga cikin shugabannin musulmai, kuma yana cikin sahabbai malamai, ga shi jikan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) na wurin ‘yarsa mafi daraja, kuma shi mai yawan ibada ne jarumi karimi.

Amma duk da haka, abubuwan da ‘yan shi’a suke yi suke yi a ranar ashura na nuna raki da baƙin ciki wanda wani abin ma feleƙe ne kawai da riya, ba shi da kyau, a shari’ance. Saboda babansa (Sayyidina Ali Radiyallahu Anhu) shi ma kashe shi aka yi a ranar Juma’a 17 ga watan Ramadan a shekara ta 40 daga hijra ya fito zai tafi sallar Asuba, amma ba su mayar da ranar, ranar makoki ba.

Haka kuma Sayyidina Usman (Radiyallahu Anhu) wanda a wajen ahlussunna ya fi shi. Tsare shi aka yi aka hana shi fita daga gidansa tsawon kwanaki, a cikin kwanakin aikin hajji a shekara ta 36 daga hijra, amma ba a mayar da ranar juyayi ba.

Ga kuma Sayyidina Umar (Radiyallahu Anhu) wanda ya fi Usman da Ali (Radiyallahu Anhuma) daraja, yana sallar asuba yana tsaye yana karatun Al-ƙur’ani a masallacin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) aka kashe shi, amma ba a yin komai idan ranar takewayo. Su kuma dukkan su Sayyidina Abubakar (Radiyallahu Anhu) ya fi su falala, amma ranar mutuwarsa ba a mayar da ita ranar makoki ba.

To kuma ɗungurungum shugaban taliƙai (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya koma ga Allah kamar yadda annabawan da suka gaba ce shi suka koma ga Allah, amma ba a aikata bidi’o’in’ da ‘yan shi’a suke aikatawa idan ranar kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) ta kewayo. Kuma babu wani wanda ya ce a ranar rasuwarsu waɗansu abubuwan mamaki na keta al’ada sun faru kamar yadda rafilawa suke cewa wai sun faru ranar mutuwar Husaini (Radiyallahu Anhu).

Abu dai mafi kyau shi ne duk lokacin da aka tuna waɗannan musibu da makamantansu sai a ce; “lnna lillallahi wa Inna ilaihi raji’un” kamar yadda shi Husaini ya rawaito daga kakansa (Salallahu Alaihi Wa Sallam) cewa: “Duk wanda ya tuna wata masifa, komai tsawon lokacin faruwarta, ya ce: “Inna lillallahi wa inna ilaihir raji’un.” Za a ba shi ladan kamar a ranar masifar ta faru. Imam Ahmad da lbn Majah ne suka rawaito wannan hadisin. Kuma Ibn Kasir (Rahimahullah) ya ce:

“Kuma a zamanin daular banu Buwaihe (daular ‘yan shi’a, a tsakankanin shekaru na ɗari huɗu daga hijra, Rafilawa sun kasance a ranar ashura a Bagdad suna fitowa tituna suna ta kaɗe-kaɗe, suna watsa toka da ɓuntu a kan hanyoyi da kasuwanni, suna maƙala ƙyallaye a jikin rumfuna, Suna koke-koke, wasu ma a daren ba sa shan ruwa, wai suna kwaikwayon ƙishirwar da Husaini ya sha ranar da aka kashe shi.

Haka matansu ma suke fitowa, fuskokinsu a bayyane, ƙafafuwansu ba takalma, suna kururuwa suna marin fuskokinsu, suna dukan ƙirajensu, da dai bidi’o’i munana, wai kawai don su baƙantawa banu Umayya saboda a zamanin mulkinsu ne aka kashe Husaini (Radiyallahu Anhu).

A gefe guda kuma waɗansu masu adawa da Ahlul Baiti (Nawasib) a Sham su kuma a ƙoƙarinsu na su ƙalubalanci ‘yan shi’a. sai su yi girke-girke a ranar, su yi wanka, su sanya sababbin kaya, su sa turare, su yi ta nuna farin cikin kamar ranar salla, wai don su ɓatawa ‘yan shi’a rai.

Waɗansu sun yi tawili dangane da kashe Husaini da aka yi suka ce ai yana ƙoƙarin rarraba kan mutane ne, da yi wa shugaban da mutane suka zaɓa tawaye, wannan kuwa abu ne da manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya hana ya faɗi irin azabar da za a yi wa mai aikata hakan kamar yadda ya tabbata a Sahihu Muslim, to wannan tawili ne na jahilci, kuma bai kamata a y kisa a kansa ba. Da tun farko sun yarda da ɗayan abu uku da ya nuna a yi da shikenan, amma suka ƙi suka kashe shi.

To kuma wannan ba zai zama hujjar da za ta sa a yi ta la’antar gaba ɗayan al’umma ba; saboda laifin wasu ‘yan tsiraru marasa kirki. Saboda mafi yawancin shugabanni sun yi tur da abinda ya faru tun wancan lokaci har ya zuwa yau. Babu wanda ya goyi bayan kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) sai wasu ‘yan tsiraru daga mutanen Kufa; waɗanda su ne suka gayyato shi amma da suka ga abin duniya suka yi watsi suka rabu da shi; wasu ma daga cikinsu suka koma bayan masu yaƙarsa.

Kuma koda a cikin wannan runduna ba dukkansu ne suka goyi bayan kashe shi ba. Kai koda shi Yazid ɗan Mu’awiyya (Radiyallahu Anhu) bai goyi bayan kashe Husaini (Radiyallahu Anhu); a bisa kyakkyawan zato da shi ne ya kama shi, da ya masa afuwa, kamar yadda shi da kansa ya faɗa. Sannan kuma har tsinewa Ibn Ziyad ya yi, amma kuma duk da haka bai tsige shi daga kan muƙaminsa ba bai kumayi masa komai ba Allah shi ne masani.

Har ila yau shaihin malami Ibn Kasir (Rahimahullahu) ya yi bayanin matsayi da darajar Husaini (Radiyallahu Anhu); da kuma kyakkyawar alaƙar da take tsakaninsa da Abubakar da Umar da Usman da kuma Mu’awiyya (Radiyallahu Anhuma); inda yake cewa:

“A taƙaice dai Husaini ya yi rayuwa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma sun rabu lafiya; sai dai yana ƙarami lokacin wafatin Manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wa Sallam).”

Bayan nan Sayyidina Abubakar da Umar da Usman (Radiyallahu Anhuma) suna mutuƙar girmama shi. Ya rayu tare da mahaifinsa (Sayyadina Ali Radiyallahu Anhu) kuma ya yi riwaya a gurinsa; ya kasance tare da shi a dukkanin yaƙe-yaƙen da ya yi na Jamal da Saf’in. Sannan ya masa biyayya har zuwa lokacin da aka kashe shi.

Lokacin da ɗan uwansa Hasan (Radiyallahu Anhu) ya zama halifa ya yi nufin yin sulhu da Mu’awiyya; ya nuna rashin amincewarsa, shi yana ganin gara a yi ta yin yaƙi. Shi kuwa Hasan (Radiyallahu Anhu); ya nuna ɓacin ransa ga wannan matsayi na ƙaninsa har ya yi barazanar ɗaure shi a kurkuku.

A lokacin halifancin Mu’awiya (Radiyallahu Anhu) Hassan Da Husaini (Radiyallahu Anhu) suna yawan zuwa wurinsa; yana kuma matuƙar girmama su, yana yi musu kyauta ta girma; akwai ma ranar da a lokaci guda ya ba su dinarai dubu biyu har yace; “ku karɓa daga ɗan Hindu kyautar da ba ku taɓa samun irinta ba, haka kuma ba za ku sake samun irinta ba”, shi kuma Husaini sai ya ce; “kai ma ba za ka sake yin kyauta ga waɗanda suka fi mu daraja ba, kuma ba za ka taɓa yin irinta ba’.

Bayan rasuwar Hasan (Radiyallahu Anhu) Husaini (Radiyallahu Anhu) ya ci gaba da zuwa wurin Mu’awiya; kuma Mu’ awiya ya cigaba da girmama shi da yi masa kyauta ta karamci. Yana ma daga cikin mujahidan da suka yi yaƙin Kustantiniyya a shekara ta hamsin da ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Yazidu’.

To ɗan uwa ka ga fa yadda ‘ya ‘yan asali tsarkaka suka yi mu’amala ta mutunci da girmamawa da Mu’awiyya da sauran sahabbai; amma a yau masu cewa tafarkinsu suke bi ba su da aiki sai ƙin jini da La’antar waɗannan sahabbai waɗanda su ne abokai; aminai, surukai, mataimaka na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da ‘ya ‘yansu da jikokinsa (Ahlul Baiti Radiyallahu Anhuma).

‘Yan uwa a sake tunani a yi biyayya ta gaskiya da koyi na gaskiya ga Ahlul Baiti da sahabbai. Raditallahu Anhum Ajma’in) Allah ka ganar da mu.

Imamuzzahbi Abu Abdullahi (A.H.S Y.M.S 748)

Imamuz Zahabi MashahurIn masanin ilimin hadisi ne da tarihi da sauran fannoni; ga irin yabo da kirari da ya yi ga Imamu Husaini (Radiyallahu Anhuma) inda yake cewa; “Shi ne shugaba, sharifi kamili, Jikan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kuma abin ƙamshinsa; abin ƙaunarsa a duniya, baban Abdullahi ɗan sarkin Muminai baban Hasan Aliyu ɗan Abu Talib; ɗan Abdulmuttalib. ɗan Hashim, ɗan Abdul Munaf, ɗan Kusayyu, Bakuraishe, Bahashime”.

Kuma yana cewa: Shugabanmu Aliyu yana cikin halifofi shiryayyu; waɗanda aka yi wa albishir da aljanna, muna matuƙar ƙaunarsa; amma ba za mu ce shi ko Abubakar Siddik ma’asumai ne ba. ‘Ya’yansa Hasan da Husaini jikokin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne; kuma su ne shugabannin samarin aljanna, sun can-canci halifanci.

Bayan haka, ga kuma Imamus Suyuti wanda kowa ya yarda da shi, saboda ɗimbin iliminsa da tsoron Allah.

Imam Jalaluddin Assuyuɗi (A.H.S 849 Y.M.S. 911)

Imamus Suyuti Rahimahullahu ya ce; yana daga munanan bidi’o’i abinda wasu yan bidi’a suke aikatawa ranar ashura na ƙin shan ruwa; da nuna ɓacin rai da nuna alhini, abubuwan da Allah bai shari’anta su ba. Haka ma Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), ko wani daga magabata ko a cikin Ahlul Baiti, ko a waninsu; saboda kisan Husaini (Radiyallahu Anhu) wata musiba ta faru tuntuni kuma ta wuce.

Kuma abinda ya wajaba shi ne a karɓeta da faɗin; “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” da kyakkyawan haƙuri kamar sauran musibu; amma ba a nuna raki da azabtar da kai ba, da yaɗa labaran ƙarya; da cin mutuncin sahabbai waɗanda ba su ji ba ba su gani ha, kamar dai yadda ‘yan bidi’a suke yi.

Ibn Majah ya rawaito daga shi kansa Husaini ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma) ya ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce; “duk wanda ya tuna wata musiba da ta same shi, (sai ya sake mai-maita) “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’ un”; Allah zai ba shi lada kamar a lokacin musibar ta faru komai daɗewa kuwa da ta yi da faruwa”.

Amma ɗaukar ranar ashura a matsayin ranar makoki da ɓacin rai; wannan sam ba musulunci ba ne ya mafi kusa da maguzanci. Kuma su masu yin wannan bidi’ar suna yi wa kansu asarar lada da falalar da ke cikin yin azumin wannan ranar.

Waɗansu kuma sai suka ƙirƙiri bidi’o’i saɓanin na waɗancan su ne na yin wanka, da ƙunshi; da sanya kwalli da gaggaisawa da juna, wannan munanan bidi’o’i da aka gina su kan wani hadisi na ƙarya. Abinda kawai ya tabbata a sunna shi ne a yi azumi a ranar. Hadisin da aka rawaito wanda yake bayanin falalar yalwatawa iyali ranar ashura rarraunan hadisi ne.

Tana yiwuwa masu wuce iyaka wurin girmama ranar ashura; suna yin haka ne domin ƙalubalantar ‘yan shi’a to yin hakan dai ba dai-dai ba ne; saboda shi shaiɗan burinsa dai ya ga ya ɓatar da mutum ta kowane hali. Ya kamata dai ‘yan bidi’a su guji bidi’a kawai ba wata Magana”.

Ya ɗan uwana mai neman gaskiya; ka dubi wannan hadisi mai girma wanda shi da kansa Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu) ya rawaito shi daga kakansa. Ka ga duk masoyinsa mai goyon bayansa ya wajaba ya yi aiki da shi ta hanyar faɗin; “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” a duk lokacin da ya tuna da shahadarsa a Karbala illa iyaka; ba wai ya yi ihu da zage-zage ba. Allah ka ganar da mu.

Shin mai imamai suka ce?

A wannan gaɓa ina so mu yi nazarin maganganun da suka fito kai tsaye daga bakin shugabannin Ahul Baiti; waɗanda ake cewa saboda su ne ake yin ibadu da bukukuwan ashura domin mu tantance tsakuwa da tsaba; mu san gaskiyar addinin da suka koyar da kuma saɓaninsa.

Da farko bari mu fara da shi kansa Imamu Husainni (Radiyallahu Anhu); mu ji wasiyyar da ya yi wa ‘yar uwarsa Zainab (Radiyallahu Anha) dab da zai yi shahada:

Domin karanta cikakken bayani a kan Wasiyyar Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama
Labarin na GabaWasu Daga Fitattun Malaman Alƙur’ani A Kurfi