Falalar Sanin Gaskiya Da Aiki Da Ita

0
304

Ya zama wajibi a kan dukkan musulmi mai neman tsira da shiriya ya zage damtse wajen neman gaskiyar magana a kan komai kuma in ta bayyana a gare shi, ya karɓe ta ko daga hannun wa ta fito.

Allah ta’ala ya yi umarni da a koda yaushe mutum ya kasance tare da masu gaskiya. Allah ta’ala ya ce: “Yaku waɗanda suka yi Imani, ku ji tsoron Allah, ku kasance tare da masu gaskiya.” (Attaurah: 119).

Kuma Allah ya bayyana falalar masu gaskiya a wurare da dama a Al-ƙur’ani, misali a taƙaice:

Masu gaskiya za su shiga Aljannah (suratu Al-Imran: 15-17).
Masu gaskiya suna tare da annabawa da shahidai da salihai ranar alƙiyama. (suratu Al-Nisa’i: 69-70)
Allah ya yarda da masu gaskiya (Suratul Ma’ida: 199)
Allah yana sauƙaƙe al’amura ga masu gaskiya (suratul Laili: 5-7).
Allah yana sanya albarka a cikin ciniki da aka yi gaskiya a cikinsa. (hadisin Bukhari, 2079 da Muslim 1532).

Sayyidina Ali (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Wanda yake yi wa mutane abu uku, za su yi masa abu uku, in yana faɗar gaskiya, yana riƙon amana, yana cika alƙawari, za su so shi, za su yabe shi, kuma za su taimaka masa (Aladabus Shiriyyah 1/29) na Ibn Muflih.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku lamunce min abu shida zan lamunce muku shiga Aljanna:

Ku rinƙa faɗin gaskiya
Ku rinƙa cika alƙawari
Ku riƙe amana
Ku kame kanku
Ku kame hannuwanku daga abin da ba naku ba”. (Ahmad 5/233/323).

Akan haka ya wajaba mu faɗi gaskiya, mu aikata gaskiya, mu yarda da abinda yake na gaskiya; mu bi addini na gaskiya, mu nemi gaskiyar labari kafin mu yaɗa shi.

Mu guji yaɗa labaran ƙarya, musamman kan abinda ya shafi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam); da iyalansa da sahabbansa da sauran bayin Allah managarta; saboda bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne.

Kuma laifin yi wa Allah da Manzonsa kan da addininsa da bayınsa nagari ƙarya ba ƙarami ba ne.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Hana Karɓar Gaskiya danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Zaman Lafiya Da Mutane danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceIdan Ina Magana Da Safe Bayan Na Ɗauki Azumi, Sai Na Haɗiye Sauro Ko Kuma Na Haɗiyi Ƙuda Da Rana Yaya Azumina Yake?
Labarin na GabaShin Zan Iya Shaƙar Maganin Shaƙa Na Masu Asma Idan Na Ɗauki Azumi Sakamakon Ciwon Asma?