Mai gida shi ne mai daraja ta ɗaya a cikin gida gaba ɗaya, ikonsa ne sama da na kowa, sauran jama’ar gida mataimaka ne, kuma mabiya a gare shi.
Sannan kuma a ko da yaushe aka ambacin Kalmar: “Uwa” a cikin wani al’amari, to za ka samu ita ce jagaba mai kuma jagorancin waɗanda ke biye da ita, kamar uwar gida, uwar garke, da dai sauran su, ke nan uwar gida ita ce me daraja ta biyu a game da gudanar da al’amuran gida.
Kalmar “Amarya” kuwa suna ne da ake faɗa wa sabuwar mata; don bayanin matsayinta na sabunta game da rayuwar aure tare da miji da uwar gida.
Don haka, tsarin zamantakewar rayuwa ya tabbatar da babu yadda za a yi wanda ya daɗe cikin wani fage na rayuwa ya yi daidai da sabon shiga a cikinsa.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Bayan haka, kyawun jagora shi ne ya zama mai bibiya da tausayawa wanda yake jagoranta, har ya ga na ƙasa da shi ya kai ga samun ƙwarewa da gogewa cikin abin da ake jagorantar sa a kai.
Sannan shi kuma sabon shiga abin da ya kamace shi ya zama mai ladabi da biyayya tare da ganin girman wanda ya gabace shi, don ya koyi abubuwan da ba shi da ƙwarewa a kansu.
An karɓo hadisi daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, daga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Wanda bai tausaya wa ƙaraminmu ba, kuma bai tabbatar da matsayin babbanmu ba; to ba ya tare da mu”. (Bukhari ne ya ruwaito shi a cikin littafin Al- Adabul Mufrad).
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
Saboda haka, mai gida shugaban uwar gida da amarya ne, su kuma mataimakansa ne a kan harkokin gudanar da al’amuran gidansa.
Sannan kuma uwar gida yayar amarya ce, amarya kuma ƙanwar uwar gida ce, kuma mai taimaka mata ce.
Tsokaci: Don magidanci yana mai shugabantar al’amuran gidansa a matakin mai daraja ta ɗaya, bai hana uwar gida da amarya su ƙare shi da wata baiwa ta musamman da Allah ya ba wa ɗayarsu ko dukkansu ba, haka ita ma uwar gida zamantowar ta mai daraja ta biyu a gida, bai hana amarya ta ƙare ta da wani abin da Allah ya fifita ta da shi ba.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan