Wannan al’amari ya kasu nau’i biyu, akwai wanda a iya cewa larura ce ke haddasa shi, akwai wanda kuma lafiya lau yakan faru babu larura.
Wanda yake ba na larura ba shi ne wanda yake ba kullum kullum ake samun kai cikin fitar sa ba, kurum yanayi ne na gari ko gurin ƙwanciya ya yi tasirin fitar sa, kamar an yi ruwan sama gari ya ɗau sanyi, iska amintacciya na kaɗawa, kun ga wannan daɗin barci ne ya jawo shi ba rashin lafiya ba ne.
Hakazalik akwai mutane da dama waɗanda wata halayyar salon ƙwanciyarsu ke jawo wa, wato wanda za ga ka suna bacci amma baki a buɗe hanhai maimakon a rufe, kuma su suka fi samun wannan matsala ta jiƙa matashin kai ka ji har ɗoyi yake saboda bacteria ɗin da ke cikin bakunan mu da tarin kemikals, musamman mutane masu ƙiba.
Domin karanta Cewa Uwa Za ta Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa Danna nan
Su waɗanda ke rufe baki lokacin bacci ko miyau ya taru hadiye shi suke ko sun sani ko ba su sani ba, domin a lokacin bacci hatta numfashi da haɗiya, da duk sauran ayyukan da ke gudana ƙwaƙwalwa ce ke ɗaukar nauyinsu ba tare da mun sani ba, Su kuma waɗanda ke sakin baki buɗe miyau ɗin gangarowa yake ba tare da sun sani ba wannan shi ne bambancin.
Akwai kuma wanda larura ne, ta yiwu wasu magunguna suke sha da ke sa su rasa control ɗin miyau ɗin, kamar magunguna irin na cutar farfaɗiya, depression, anxiety, ko larurar taɓuwar ƙwaƙwalwa, wanda idan mutum na shan irin su wani zai iya samun yawan taruwar miyau a bakinsa.
Sai Kuma cuttukan dakan shafi baki da haƙora, kamar ƙuraje, laurorin tonsils, ko kuma rashin tsaftar haƙora baki ɗaya, domin koda kana brush idan ba ka iya yinsa yadda ya dace ba ba za ka daina fuskantar matsalar ba, yayin brush har harshe ake haɗawa ba iya haƙora ba, haka kuma akwai salon yadda ake goga brushes ɗin da duk sai an koya.
Domin karanta bayani akan Larurar Sarƙewar Numfashi Da Ake Kira (Asthma) Danna nan
Illa iyaka duk wannan dai dama yana faruwa ne yayin bacci, babbar matsalar ita ce idan babban mutum na yawan samun dalalar miyau a farke ba lokacin bacci ba, amma ko shi wannan a ƙananan yara wannan ba matsala ba ce, domin su ko a farke suna dalalar da miyau, musamman a watannin da suka fara fitar haƙora.
Matakan Da Ya Dace A Ɗauka Su ne:
- Yawan goge baki kafin a kwanta da man goge haƙora ko asuwaki, yayin kwanciya da bayan an farka, hakan zai iya rage ƙarfin yawan yadda sinadaran bakin ke sarrafa miyau ɗin, kuma ya rage zubar sa.
- Canza yanayin salon kwanciya wato “sleeping position”maimakon kwanciya a hannu hagu ko dama, ko kuma ruf da ciki, ya zamto mutum ya komo yana kwanciya akan bayansa, wato fuskarsa na kallon sama, sannan ya sami pillow yasa ƙasan gwiwoyin ƙafarsa domin cikinsa ya yi relaxing, uwa uba magance larurar mura domin wasu toshewar hanci ke haddasa musu hakan.
- Amfani da pillow madaidaici wajen ta-da kai, hakan na taimakawa, kuma ake kula da tsaftar rigar pillow ɗin da ta zanin gado, a ƙalla duk sati a canza wata ko a cire pillow da zanin gadon a wanke su, har turare a koyi shafawa jikin pillow, ko zanin gado yana inganta bacci.
- Riƙa shan wadataccen ruwa kowanne yini, wato ya zamto kana shan ruwa yadda ya kamata a ƙalla kofi 5 zuwa 12 a yini, ka zamo hydrated, kuma ake wanka kafin a kwanta tare da sanya tufafin me laushi a jika mara nauyi.
- Idan duk hakan ya ci tura toh sai a riƙa amfani da takunkumin baki yayin kwanciya bacci wato “Mouth guard” da in an ga masana a fannin lafiyar haƙora “Dentist” suke dubawa su ba mutum shawarar neman dai-dai da bakin sa.
- A wasu matsalar munsharin bacci tare da gurnani wato sleep apnea wanda galibi a masu ƙiba ko teɓa ko mashayan taɓa sigari hakan ya fi faruwa dole su yi ƙoƙarin rage nauyi da ƙiba, me shan taba ya yi ƙoƙarin bari domin irin wannan munsharin na sanya kasala lokutan da gari ya waye mutum ke aikin yau da kullum wanda wannan yawan amma da kasalar na haddasa wannan zubar miyau ɗin yayin bacci.
- Magance matsalar ƙwarnafi wacce ita ma na taka rawa wato GE Reflux, wanda hakan ne ke sanya mutum ya riƙa jin kamar wani abu ya kakare ko ya tsaya masa a wuya na lump, amma ba komai ɗin ba ne kurum sphincter ɗin maƙogoro ce ta tsuke, magance wannan zai sa mutum ba zai ke buƙatar buɗe baki ba wajen bacci, wanda galibi magungunan ciwon ulcer ne ke magance wannan matsalar.
- Matakin shan magani, bayan abin ya ci tura an je an ga likita an tabbatar babu mura ko ƙwarnafi, ko matsalar ƙiba ko munshari, to akwai rukunin magunguna da akan ɗora mutum ya riƙa sha, akan sami sauƙi sosai. Sannan idan ma akwai wata larurar a baki akan haɗa duk ai maganin ta, musamman rashin wankin baki, duk wata shida ya dace a je a yi Mouth scaling and polish, a lalace ka riƙa yi duk shekara, wannan ya sha bamban da teeth brush, ko kana wanke haƙora da makilin hakan bai hana ka buƙatar scaling, kai da kanka za ka ji bakin ya ƙara santsi da daɗi, Infact kama fi jin taste ɗin komai ya ƙaru.
- Abu na ƙarshe still akwai wani mai da akan sayar a super market da guraren sai da kayayyaki irin wannan da akan kira “EUCALYPTUS OIL” ni da Hausa ban san sunansa ba. Amma dai kamar bishiyar ce ake ce mata dogon yaro! Wata me tsayi da ake falwaya da ita, to idan aka samo man aka ɗiga a jikin auduga sai a sa a kafar hanci a shaƙe shi har ya ratsa kai, haka za a yi a kowacce kafar hanci koda sau biyu a yini, insha Allahu shi ma yana magance matsalar, wasu ma ganyen suke tafasawa su riƙa sha kuma su kurkure baki tare da sirace da shi.
Domin karanta bayani akan Idan Ka ji Tamkar Wani Abu Ya Tsaya Maka A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] Danna nan
Edita:@rumasau-kallamu