Matsalar Zubar Yawun Bacci

0
63

Wannan al’amari ya kasu nau’i biyu,kwai wanda a iya cewa larura ce ke haddasa shi,kwai wanda kuma lafiya lau yakan faru babu larura.

Wanda yake bana larura ba shine wanda yake ba kullum kullum ake samun kai cikin fitar sa ba,kurum yanayi ne na gari ko gurin ƙwanciya yai tasirin fitar sa, kamar anyi ruwan sama gari ya dau sanyi,iska amintacciya na kaɗawa,Kunga wannan daɗin barci ne ya jawosa ba rashin lafiya bane

Hakazalik kwai mutane da dama wadanda wata halayyar salon ƙwanciyarsu ke jawo wa,wato wanda zaka suna bacci amma baki abuɗe hanhai maimakon a rufe,kuma su suka fi samun wannan matsala ta jiƙa matashin kai kaji har ɗoyi yake saboda bacteria din dake cikin bakunan mu da tarin kemikals,musamman mutane masu ƙiba. 

Domin karanta Cewa Uwa Zata Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa Danna nan

Su waɗanda ke rufe baki lokacin bacci ko miyau ya taru hadiye shi suke kosun sani ko basu sani ba,domin a lokacin bacci hatta numfashi da hadiya,da duk sauran ayyukan dake gudana ƙwaƙwalwace ke ɗaukar nauyinsu batare da mun sani ba, Slsu kuma waɗanda ke sakin baki buɗe miyau ɗin gangarowa yake batare da sun sani ba wannan shine  bambancin.

Akwai kuma wanda larura ne,ta yiwu wasu magunguna suke sha dake sasu rasa control din miyau ɗin,kamar magunguna irin na cutar farfaɗiya, depression,anxiety,ko larurar taɓuwar ƙwaƙwalwa,wanda idan mutum na shan irinsu wani zai iya samun yawan taruwar miyau a bakinsa.

Sai Kuma cuttukan dakan shafi baki da haƙora,kamar ƙuraje,laurorin tonsils,ko kuma rashin tsaftar haƙora baki daya, domin koda kana brush idan baka iya yinsa yadda ya dace ba bazaka daina fuskantar matsalar ba,yayin brush har harshe ake hadawa ba iya haƙora ba, haka kuma kwai salon yadda ake goga brushes din da duk sai an koya. 

Domin karanta bayani akan Larurar Sarƙiwar Numfashi Da Ake Kira (Asthma) Danna nan

Illa iyaka duk wannan dai dama yana faruwa ne yayin bacci,babbar matsalar itace idan babban mutum na yawan samun dalalar miyau a farke ba lokacin bacci ba,amma ko shi wannan a ƙananan yara wannan ba matsala bace,domin su ko a farke suna dalalar da miyau, musamman a watannin da suka fara fitar haƙora.

Matakan Da Ya Dace A Ɗauka Sune 

  1. Yawan goge baki kafin a kwanta da man goge haƙora ko asuwaki,yayin kwanciya da bayan an farka,hakan zai iya rage ƙarfin yawan yadda sinadaran bakin ke sarrafa miyau ɗin,kuma ya rage zubar sa.
  2. Canza yanayin salon kwanciya wato “sleeping position”maimakon kwanciya a hannu hagu ko dama,ko kuma ruf da ciki,ya zamto mutum ya komo yana kwanciya akan bayansa,wato fuskarsa na kallon sama, sannan ya sami pillow yasa ƙasan guiwoyin ƙafarsa domin cikinsa yai relaxing,uwa uba magance larurar mura domin wasu toshewar hanci ke haddasa musu hakan. 
  3. Amfani da pillow madaidaici wajen tada kai,hakan na taimakawa,kuma ake kula da tsaftar rigar pillow din da ta zanin gado,akalla duk sati acanza wata ko acire pillow da zanin gadon a wanke su,har turare a koyi shafawa jikin pillow, ko zanin gado yana inganta bacci. 
  4. Riƙa shan wadataccen ruwa kowanne yini,wato ya zamto kana shan ruwa yadda ya kamata akalla kofi 5 zuwa 12 a yini,ka zamo hydrated,kuma ake wanka kafin a kwanta tare da sanya tufafin me laushi ajika mara nauyi.
  5. Idan duk hakan yaci tura toh sai ariƙa amfani da takunkumin baki yayin kwanciya bacci wato “Mouth guard” da in anga masana a fannin lafiyar haƙora “Dentist” suke dubawa su ba mutum shawarar neman dai-dai da bakin sa,kamar yadda hoton kasa Ke nunawa.
  6. A wasu matsalar munsharin bacci tare da gurnani wato sleep apnea wanda galibi a masu ƙiba ko teɓa ko mashayan taɓa sigari hakan yafi faruwa dole suyi kokarin rage nauyi da ƙiba,me shan taba yai ƙoƙarin bari domin irin wannan munsharin na sanya kasala lokutan da gari ya waye mutum ke aikin yau da kullum wanda wannan yawan amma da kasalar na haddasa wannan zubar miyau din yayin bacci. 
  7. Magance matsalar ƙwarnafi wacce ita ma na taka rawa wato GE Reflux,wanda hakanne ke sanya mutum ya riƙa jin kamar wani abu ya kakare ko ya tsaya masa a wuya na lump,amma bakomi din bane kurum sphincter din makogoroce ta tsuke,magance wannan zaisa mutum bazai ke buƙatar  bude baki ba wajen bacci,wanda galibi magungunan ciwon ulcer ne ke magance wannan matsalar. 
  8. Matakin shan magani, bayan abin yaci tira anje anga likita… an tabbatar babu mura ko ƙwarnafi, ko matsalar ƙiba ko munshari… toh kwai rukunin magunguna da akan dora mutum ya riƙa sha,akan sami saukin sosai. Sannan idan ma akwai wata larurar abaki akan haɗa duk ai maganin ta,musamman rashin wankin baki,duk wata shida ya dace aje ai Mouth scaling and polish, a lalace ka riƙa yi duk shekara, wannan yasha bamban da teeth brush, ko kana wanke haƙora da makilin hakan bai hana ka bukatar scaling,kai da kanka zaka ji bakin ya ƙara santsi da daɗi, Infact kama fi jin taste din komi ya ƙaru.
  9. Abu na karshe still akwai wani mai da akan sayar a super market da guraren sai da kayayyaki irin wannan da akan kira “EUCALYPTUS OIL”  ni da Hausa bansan sunansa ba.l,amma dai kamar bishiyar ce ake ce mata dogon yaro! Wata me tsayi da ake falwaya da ita,toh Idan aka samo man aka ɗiga a jikin auduga sai asa a kafar hanci a shaƙesa har ya ratsa kai, haka za ai a kowacce kafar hanci koda sau biyu a yini,insha Allahu shima yana magance matsalar,wasu ma ganyen suke tafasawa su riƙa sha kuma su kurkure baki tare da sirace dashi.

Domin karanta bayani akan Idan Kaji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] Danna nan

labarin da ya wuceNakan Ji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ]
Labarin na GabaAbubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada