Baƙin ciki da kururawa da kuke da dukan jiki da waƙe-waƙen ta’aziyyar wanda ya ke kaiwa ga zagin magabata da la’antar su, alhali ba su ji ba, ba su gani ba, da karanta labaran kashe Husaini wanda yawancinsa ƙarya ce, manufar masu yin haka ita ce, haddasa da rarraba kawunan al’umma.
Saboda yin hakan ba wajibi ba ne, ba mustahabi ba ne, kai ƙirƙirar raki da baƙin ciki ga musibun da suka wuce babban abu ne da Allah da Manzo suka hana”2
MAGANGANU NA ƘARYA A KAN KASHE HUSAINI Waɗanda suka rawaito labaran kashe Husaini (R.A) da kashe Usman (R.A) da sauran yaƙe-yaƙe sun ƙara ƙarairayi da yawa a cikin labaran.
A cikin malamai da suka yi rubutu a kan kashe Husain (R.A) akwai manyan malamai irin su Albagawi da lbn Abid Dunya, amma duk da haka akwai ruwayoyin da ba su inganta ba, har ma da na ƙarya a cikin su.
Su kuwa waɗanda suke kawo labaran ba tare da wani sanadi ba, waɗannan su suka fi kawo ƙarairayi. Kamar yadda suke cewa wai ranar da aka kashe Husaini sai aka ga sama ta yi jawur, alhali wannan abu ne da ya ke faruwa tun kafin wannan lokacin, wai kuma a ranar duk dutsen da aka ɗaga sai an ga jini a ƙarƙashinsa, wai an yi wa zuri’ar Husaini (RA) tsirara an ɗora su a kan raƙuma ko sirdi ana ta yawo da su wuri-wuri, duk wannan ƙarya ne.
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
Musulmi ba su taɓa kama wata mace daga Banu Hashim ba a matsayin ribar yaƙi, sai dai masu son zuciya ba sa rabo da ƙarya.
WANE NE YA BA DA UMARNI A KASHE HUSAINI? Malamai da yawa sun tabbatar da cewa Yazidu bai bayar da umarni a kashe Husaini ba, kuma ba shi da burin haka, shi ya so ya girmama shi ne kamar yadda mahaifinsa Mu’awiyya (RA) ya yi masa wasiyya, sai dai ya sa a hana shi yin tawaye. Shi da kansa Husaini (R.A) da ya tabbatar mutanen Iraƙi sun kware masa baya sun ha’ince shi, sai ya koma gida, ko ya tafi Jihadi, amma suka ce sai dai ya yarda a kama shi a matsayin ribar yaƙi, shi kuwa ya ƙi, suka yi ta yaƙarsa har suka zalunce shi, suka kashe shi, ya yi shahada (R.A).
Kuma lokacin da Yazidu da iyalansa suka samu labarin kashe Husaini (R.A) ransu ya ɓaci kwarai, sun yi ta yin kuka, har ma Yazidu ya ce:
“Allah ya tsine wa ɗan Murjanatu, wato Ubaidullah Ibn Ziyad, wallahi da a ce Husaini ɗan uwansa ne da ba zai kashe shi ba, ai ba sai an kashe Husaini ba mutanen Iraki za su bi ni.
Sannan ya yi wa iyalan Husani goma sha biyu ta arziƙi ya sa aka mayar da su Madina. Sai dai (babban laifin Yazidu shi ne) bai ɗauki wani mataki ba a kan waɗanda suka aikata wannan ta’asa, bai sa an kashe wanda ya kashe shi ba.
Daga baya Mukhtar Ibn Abi Ubaid Assakafi ya jagoranci dakaru suka kashe Ubaidullah bin Ziyad kuma Mus’ab Ibn Zubair ya kashe shi saboda ya yi da’awar annabta.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
WANE NE YA CACCAKA KARA A BAKIN HUSAINI? Abin da ya tabbata a ingantacciyar ruwaya shi ne cewa, lokacin da aka kashe Husaini sai aka yanke kansa aka kai shi gaban Ubaidullah Ibn Ziyad da haƙoransa, wannan abu ya faru a gaban Anas Ibn Malik da Abu Barzata Aslami.
Ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari daga Anas ɗan Malik (R.A) an kawo kan Husaini a cikin tasa gaban Ubaidullah Ibn Ziyad, sai ya caccaka kara a tsakanin haƙoransa, ya yi magana akan kyawunsa, sai Anas ya ce, “Ya fi su kama da Manzon Allah (S.A.W) ya kasance ya rine furfurarsa”.
Kuma ya rawaito daga Abu Nu’aim ya ce: “Na ji Ibn Umar wani mutum ya yi masa tambaya a kan hukuncin maniyyacin da ya kashe ƙuda, alhali kun kashe jikan Manzon Allah (S.A.W) ya ce su ne kashe jikan Manzon Allah (S.A.W) ya ce su ne (Hassan da Husaini) abin kanshi na a duniya”.
An sami waɗansu ruwayoyi daga waɗansu waɗanda ba a san su ba, wai wannan abu ya faru ne a gaban Yazidu, wai shi aka kaiwa kan, kuma wai shi ne ya caccaka kara a bakinsa, to wannan abu ne da bai tabbata ba, ƙarya ne, kuma sahabban da aka ce a gabansu abun ya faru, ai a Iraƙi suke ba a Sham ba.
AN YI WA HUSAINI KISAN ZALUNCI
Babu shakka an kashe Hussani a bisa zalunci, kuma ya yi shahada, kamar yadda makamantansa da aka kashe bisa zalunci suka yi shahada, tunda dai ba da niyyar yaƙi ya tafi ba. Kuma duk wanda ya kashe shi da wanda ya taimaka aka kashe shi da wanda ya goyi bayan kashe shi ya saɓa wa Allah da Manzonsa. Kuma kashe shi babbar musiba ce ga dukkan musulmi amma shi ya samu shahada da daraja maɗaukakiya.
Shi dai ɗan uwansa Hassan Allah ya ƙaddara musa samun matsayin da. sai waɗanda suka gamu gwagwarmaya irin ta musulmin farko ba, saboda haka sai Allah ya ƙaddara mutuwar Hassan ta hanyar guba da aka sanya masa a abinci, shi kuma Hussaini (R.A) sai ya yi mutuwar shahada. A kan haka, abin da ya ke wajibi a kan musulmi shi ne, ya yi haƙuri ya yi ta faɗar Inna lillahi… a lokacin musibu.
Domin Karanta Bayani akan Matakan Zaman Lafiyar Kishiyoyi, Haƙuri Da Junansu A Kan Kurakurai Danna nan
MATSAYIN MALAMAI KAN KASHE HUSAINI (R.A)
Malamai sun kasu gida uku dangane da kashe Husaini (R.A) biyu a gefe ɗaya a tsakiya:
*Dayan na gefe: suka ce an yi daidai da aka kashe shi, saboda ya fito ne don ya raba kan musulmi, Annabi (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya zo yana son ya raba kawunanku, alhali kuna bin wani shugaba guda ɗaya, ku kashe shi”. Shi Hussaini ya zo ne, ya raba kan mutane, alhali sun ƙarƙashin shugaba ɗaya.
*Daya gefen kuma suka ce shi Husaini shi ne shugaban Musulmi a lokacin wanda ya wajaba a yiwa biyayya, kuma imani ba ya cika sai da yardar shi, ba za a yi sallar jam’i ko jama’a ba sai a bayan wanda ya naɗa, kuma ba za a yi jihadi ba, sai da izininsa.
* Su kuwa waɗanda suke a tsaka-tsaki su ne Ahlus Sunna, ba su goyi bayan waɗannan ɓangarori biyu ba, abin da suke cewa Husaini an kashe shi ne bisa zalunci, kuma ya yi shahada, amma a lokacin ba shi ne shugaba ba, shi kuma wannan hadisi (na ƴan tawaye) bai shafi Husaini ba.
Saboda lokacin da ya sami labarin kashe ɗan baffansa Muslim bin Akil, sai ya bar maganar halifanci ya nemi a ba shi dama ya tafi wurin Yazidu, ko ya tafi jihadi ko ya koma gida, amma suka ƙi, suka ce sai dai ya yarda a kama shi, yin hakan kuwa bai zama wajibi ba a kansa.
Ya ɗan uwa musulmi mai neman gaskiya ka ga dai matsayin Ibn Taimiyya a kan wannan mas’ala, shin ina alamun ƙin Ahlul baiti (R.A) ko goyon bayan abin da aka yi wa Husaini da iyalansa a cikin waɗannan bayanai?
Ya kamata duk wanda ya ce maka Ibn Taimiyya ya ce kaza, to ya kawo maka littafin kuma a karanto maganar tun daga farkonta har ƙarshenta, ba wai a ciccizgo maganganun nan da can ba.
Ya Allah ka fahimtar da mu gaskiya, ka ba mu ikon bin ta. Ka ba mu ikon yin adalci ga wanda muke so da wanda ma ba ma so, ka fitar da gaba da riƙo daga zukatanmu. Amin.
Yanzu kuma ga maganganun wasu fitattun ɗaliban IbnTaimiyya: SHAMSUDDIN BN ƘAYYIMUL JAUZIYYA RAHIMAHULLAH (A.H.S 691 Y.M.S 751) Shi kuwa kuwa shaihin malami Ibnul Muhammad Ibn Abubakar, babban almajirin lbnu Taimiyya(Rahimahullah) ga abin da yake cewa:
Yana daga cikin hadisan ƙarya, hadisan sa kwalli da yin ado, da yalwata wa iyali da yin wasu salloli ranar Ashura da wasu falaloli da ake faɗa, waɗanda ko hadisi ɗaya bai inganta ba a kansu.
Abin da kawai ya inganta shi ne yin azumi a ranar, ban da shi sauran duk ƙarya ne. Hadisi mai ɗan dama-dama a kan wannan shi ne hadisin yalwatawa iyali a ranar Ashura (cika-ciki) shi kuma Imam Ahmad Rahimahullahu ya ce bai ingata ba’.
Amma hadisin falalar sa kwalli da shafa mai da sa turare ranar Ashura, haƙiƙa maƙaryata ne suka ƙirƙire su, sai kuma wasu (ƴan bidi’ar) suka ƙirƙiri nuna alhini da ɓacin rai domin su ƙalubalance su, duka su biyun ƴan bidi’a ne, sun saba wa sunna.
Su kuwa Ahlulssunna, suna aikata abin da Manzon Allah (S.A. W) ya yi umami da a aikata a ranar, Allah (S.A. W) ya yi umarni da a aikata a ranar, suna nisantar bidi’o’in da shaiɗan ya yi umarni da su’.
IBN RAJAB AL-HAMBALI (RAHIMAHULLAH)A.H.S 735 Y.M.S 795. Babban malami Zainuddin Abul Faraj Abdurrahman Ibnu Rajab Al-Hambali ya ce:
“Dukkanin hadisan da aka rawaito a kan falalar sa kwalli da yin ƙunshi da wanka ranar Ashura, ƙarya ne, ba su inganta ba” amma an rawaito daga Abdullah ɗan Amr Ibnul As ya ce: “Wanda ya yi azumi ranar Ashura za a ba shi ladan azumin shekara guda, wanda ya yi sadaka a ranar, za a ba shi ladan sadakar shekara guda” Abu Usa Al-Madini ne ya fitar da shi.
Maganar cika-ciki kuwa an tambayi Imam a kan wannan hadisin, sai ya nuna cewa, bai inganta ba. Sai da Ibnu Uyaina ya ce shekarar su hamsin suna jarraba yalwatawa iyali ranar Ashura, kuma suna ganin buɗi. Amma dai hadisin bai inganta ba.
Amma ɗaukar ranar a matsayin ranar baƙin ciki da zaman makoki kamar yadda Rafilawa (ƴan shi’a) suke yi, saboda a ranar ce aka kashe Husaini (R.A) wannan aiki ne na ɓatattu amma suna ganin daidai suke yi, saboda Allah da Manzonsa ba su yi umarni a mayar da ranar da musibu suka afkawa annabawa ko ranar mutuwarsu ranar makoki ba, ballantana, waɗanda suke ƙasa da su”.
AL-HAFIZ ABUL FIDA IBN KASIR (AHS 701 Y.M.S 774).
Babban malamin hadisi, malamin tafsiri kuma malamin tarihi Al-allama lbn Kasir (Rahimahullah) shi kuma ga abin da yake cewa:
”Ya kamata dukkanın musulmi ya yi baƙin ciki da kashe Husaini (Radiyallahu anhu). Saboda shi yana daga cikin shugabannin musulmi, kuma yana cikin sahabbai malamai, ga shi jikan Manzon Allah (S.A.W) na wurin ƴarsa mafi daraja, kuma shi mai yawan ibada ne jarumi karimi.
Amma duk da haka, abubuwan da ƴan shi’a suke yi a ranar ashura na nuna raki da baƙin ciki wanda wani abin ma feleƙe ne kawai da riya, ba shi da kyau, a shari’ance. Saboda babansa (Sayyidina Ali R.A.) shi ma kashe shi aka yi a ranar Juma’a 17 ga watan Ramadan a shekara ta 40 daga Hijra ya fito zai tafi sallar Asuba, amma ba su mayar da ranar, ranar makoki ba.
Haka kuma Sayyidina Usman (R.A) wanda a wajen Ahlus sunna ya fi shi. Tsare shi a kai, aka hana shi fita daga gidansa tsawon kwanaki, a cikin kwanakin aikin Hajji a shekara ta 36 daga hijira, amma ba a mayar da ranar juyayi ba.
Ga kuma Sayyidina Umar (R.A) wanda ya fi Usman da Ali (R.A) daraja, yana sallar Asuba yana tsaye yana karatun Alkur’ani a masallacin Manzon Allah (S.A.W) aka kashe shi, amma ba a yin komai ba, idan dukkan su Sayyidina ranar ta kewayo Su kuma Abubakar (R.A) ya mutuwarsa ba a mayar da ita ranar makoki ba.
To kuma dungurungum shugaban Talikai (S.A.W) ya koma ga Allah kamar yadda annabawan da suka gaba ce shi suka koma ga Allah, amma ba a aikata bidi’o’in da ƴan Shi’a suke aikatawa idan ranar kashe Husaini(R.A) ta kewayo. Kuma babu wani wanda ya ce a ranar rasuwar su waɗansu abubuwan mamaki na keta al’ada sun faru kamar yadda rafilawa suke cewa, wai sun faru ranar mutuwar Husaini (R.A).
Abu dai mafi kyau shi ne duk lokacin da aka tuna waɗannan musibu da makamantansu, sai a ce “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”. Kamar yadda shi Husaini ya rawaito daga kakansa (SA.W) cewa: Duk wanda ya tuna wata masifa, komai tsawon lokacin faruwar ta, ya ce: “Inna lillallahi.” za a ba shi ladan kamar a ranar masifar ta faru. Imam Ahmad da lbnbMajah ne suka rawaito wannan hadisin. Kuma Ibn Kasir (Rahirnahullah) ya ce:
Kuma a zamanin daular Banu Buwaihe (daular ƴan Shi’a, a tsakankanin shekaru na ɗari huɗu daga Hijra, Rafilawa sun kasance a rahar Ashura a Bagdad suna fitowa tituna suna ta kaɗe-kaɗe, suna watsa toka da buntu a kan hanyoyi da kasuwanni, suna maƙala kyallaye a jikin rumfuna, Suna koke-koke, wasu ma a daren ba sa shan ruwa, wai suna kwaikwayon ƙishirwar da Husaini ya sha ranar da aka kashe shi.
Haka matansu ma suke fitowa, fuskokinsu a bayyane, kafafuwansu ba takalma, suna kururuwa suna marin fuskokinsu, suna dukan ƙirajensu, da dai bidi’o’i munana, wai kawai don su baƙantawa Banu Umayya, saboda a zarnanin mulkinsu ne aka kashe Husaini (R.A).
A gefe guda kuma waɗansu masu adawa da ahlul baiti Nawasib) a Sham su kuma a ƙoƙarinsu na su ƙalubalanci ƴan Shi’a. sai su yi girke-girke a ranar, su yi wanka, su sanya sababbin kaya, su sa turare, su yi ta nuna farin cikin kamar ranar sallah, wai don su ɓata wa ƴan Shi’a rai.
Waɗansu sun yi tawili dangane da kashe Husaini da aka yi suka ce, “Ai yana ƙoƙarin rarraba kan mutane ne, da yi wa shugaban da mutane suka zaɓa tawaye”. Wannan kuwa abu ne da Manzon Allah (S.A.W) ya hana, ya faɗi irin azabar da za a yiwa mai aikata hakan kamar yadda ya tabbata a Sahihu Muslim, to wannan tawili ne na jahilci, kuma bai kamata a yi kisa a kan sa ba.
Da tun farko sun yarda da ɗayan abu uku da ya nuna, da shi kenan, amma suka kashe shi.
To kuma wannan ba zai zama hujjar da za ta sa a yi wasu ƴan tsiraru marasa kirki. Saboda mafi yawan cin shugabanni sun yi tur da abin da ya faru tun wancan lokaci, har ya zuwa yau. Babu wanda ya goyi bayan kashe Husaini (R.A) sai wasu yan tsıraru daga mutanen Kufa, waɗanda su ne suka gayyato shi amma da suka ga abin duniya suka watse suka rabu da shi, wasu ma daga cikinsu suka koma bayan masu yaƙar sa.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
Kuma koda a cikin wannan runduna, ba dukkansu ne suka goyi bayan kashe shi ba. Kai koda shi Yazid ɗan Mu’awiyya (R.A) bai goyi bayan kashe Husaini (R.A) a bisa kyakkyawan zato, da shi ne ya kama shi, da ya masa afuwa, kamar yadda shi da kansa ya faɗa, sannan kuma har tsine wa Ibn Ziyad ya yi, amma kuma duk da haka bai tsige shi daga kan muƙaminsa ba, bai kuma yi masa komai ba, Allah shi ne masani.
Har ila yau, shaihin malami ibn Kasir (Rahimahullahu) ya yi bayanin matsayi da darajar Husaini (RA) da kuma kyakkyawar alaƙar da take a tsakaninsa da Abubakar da Umar da Usman da kuma Mu’awiyya (RA) in da yake cewa: “A taƙaice dai Husaini ya yi rayuwa da Manzon Allah (S.A.W) kuma sun rabu lafiya, sai dai yana ƙarami lokacin wafatin Manzon Allah(S .AW)”.
Bayan nan Sayyidina Abubakar da Umar da Usman (RA) suna mutuƙar girmama shi. Ya rayu tare da mahaifinsa (Sayyadina Ali R.A) kuma ya yi riwayya a gurinsa, ya kasance tare da shi a dukkanin yaƙe-yaƙen da yi na Jamal da Saf in. Ya masa biyayya har zuwa lokacin da aka kashe shi.
Lokacin da ɗan uwansa Hassan (RA) ya zama halifa ya yi nufin yin sulhu da Mu’awiyya, ya nuna rashin amincewarsa, shi yana ganin gara a yi ta yin yaƙi. Shi kuwa Hassan (R.A) ya nuna ɓacin ransa ga wannan matsayi na ƙaninsa, har ya yi barazanar ɗaure shi a kurkuku.
A lokacin halifancin Mu’awiya (R.A) Hassan da Husaini (R.A) suna yawan zuwa wurinsa, yana kuma matuƙar girmama su, yana yi musu kyauta ta isa da girma, akwai ma ranar da a lokaci guda ya ba su dinarai dubu biyu har ya ce: “Ku karɓa daga ɗan Hindu, kyautar da ba ku taɓa samun irin ta ba, haka kuma ba za ku sake samun irin ta ba”. shi kuma Husaini sai ya ce: “Kai ma ba za ka sake yin kyauta ga waɗanda suka fi mu daraja ba, kuma ba za ka taɓa yin irin ta ba”.
Bayan rasuwar Hassan (R.A) Husaini (R.A) ya ci gaba da zuwa wurin Mu’awiya, kuma Mu’ awiya ya ci gaba da girmama shi da yi masa kyauta ta karamci. Yana ma daga cikin mujahidan da suka yi yaƙin Kustantiniyya a shekara ta hamsin da ɗaya a ƙarƙashin jagorancin Yazidu.
To ɗan uwa ka ga fa yadda ƴaƴan asali tsarkaka suka yi mu’amala ta mutunci da girmamawa da Mu’awiyya da sauran sahabbai, amma a yau masu cewa tafarkinsu suke bi, ba su da aiki sai ƙin jini da la’antar waɗannan sahabbai waɗanda su ne abokai, aminai, surukai, mataimaka na Manzon Allah (S.A.W) da ƴa ƴansu da jikokinsa (Ahlulbaiti R.A).
Yan uwa a sake tunani a yi biyayya ta gaskiya da koyi na gaskiya ga Ahlulbaiti da sahabbai. Radiyallahu anhum ajma’in) Allah ka ganar da mu.
IMAMUZ ZAHBI ABU ABDULLAHI (A.HS Y.M.S 748)
Imamuz Zahabi Mashahurin masanin ilmin hadisi ne da tarihi da sauran fannonı, ga irin yabo da kirari da ya yi ga Imamu Husaini (R.A) inda yake cewa: “Shi ne shugaba, sharifi kamili, jikan Manzon Allah (S.A.W) kuma abin ƙamshinsa, abin ƙaunarsa a duniya, baban Abdullahi ɗan sarkin Muminai, baban Hasan Aliyu ɗan Abu Talib, ɗan Abdulmuttalib. ɗan Hashim, ɗan Abdu Munaf, ɗan Kusayyu, Bakuraishe, Bahashime”.
Kuma yana cewa: “Shugabanmu Aliyu yana cikin halifofi shiryayyu, waɗanda aka yiwa albishir da Aljanna, muna matuƙar ƙaunarsa, amma ba za mu ce shi ko Abubakar Siddik ma’asumai ne ba. Ƴaƴansa Hasan da Husaini jikokin Manzon Allah ne, kuma su ne shugabannin samarin Aljanna, sun cancanci halifanci.
Bayan haka, ga kuma Imamus Suyuɗi wanda kowa ya yarda da shi, saboda ɗimbin iliminsa da tsoron Allah.
IMAM JALALUDDIN ASSUYUƊI (A.H.S 849 Y.M.S. 911)
Imamus Suyuɗi rahimahullahu ya ce: “Yana daga munanan bidi’o’i abin da wasu ƴan bidi’a suke aikatawa ranar Ashura na ƙin shan ruwa, da nuna ɓacin rai da nuna alhini, abubuwan da Allah bai shari’anta su ba, hakama Manzonsa, ko wani daga magabata ko a cikin Ahlul baiti, ko a waninsu, saboda ko a cikin Ahlul baiti, ko a waninsu, saboda Husaini (R.A), wata musiba ta faru tuntuni kuma ta wuce, sannan abin da ya wajaba shi ne, a karɓe ta da faɗin.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”, kyakkyawan haƙuri kamar sauran musibu, amma ba a nuna raki da azabtar da kai ba, da yaɗa labaran ƙarya, da cin mutuncin sahabbai waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, kamar dai yadda ƴan bidi’a suke yi.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan
Ibn Majah ya rawaito daga shi kansa Husaini ɗan Aliyu (R.A) ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya tuna wata musiba da ta same shi “(sai ya sake maimaita) Inna lillahi wa inna ilaihi raji’ un, Allah zai ba shi lada kamar a lokacin musibar ta faru komai daɗewa kuwa da ta yi da faruwa”.
Amma ɗaukar ranar Ashura a matsayin ranar makoki da ɓacin rai wannan sam ba musulunci ba ne, ya yi kama da maguzanci. Kuma su masu yin wannan bidi’ar suna yi wa kansu asarar lada da falalar dake cikin yin azumin wannan ranar.
Waɗansu kuma sai suka ƙirƙiri bidi’o’i saɓanin na kwalli da gaggaisawa da juna, wannan munanan bidi’o’i da aka gina su kan wani hadisi na ƙarya. Abin da kawai ya tabbata a Sunna shi ne a yi azumi a ranar. Hadisin da aka rawaito wanda yake bayanin waɗancan su ne na yin wanka, da ƙunshi, da sanya falalar yalwatawa iyali ranar Ashura rarraunan hadisi ne.
Tana yiwuwa masu ƙetare iyaka wurin girmama ranar Ashura, suna yin haka ne domin ƙalubalantar ƴan Shi’a, to yin hakan dai ba daidai ba ne, saboda shi Shaiɗan burinsa dai ya ga ya ɓatar da mutum ta kowane hali. Ya kamata dai ƴan bidi’a su guji bidi’a kawai ba wata magana”.
Ya ɗan uwana mai neman gaskiya, ka dubi wannan hadisi mai girma wanda shi da kansa Imamu Husaini (R.A) ya rawaito shi daga kakansa, ka ga duk masoyinsa mai goyon bayansa ya wajaba ga masoyinsa mai goyon bayansa, ya wajaba ya yi aiki da shi ta hanyar faɗin “Innalillahi” a duk lokacin da ya tuna da shahadarsa a Karbala, illa iyaka, ba wai ya yi ihu da zage-zage ba. Allah ka ganar da mu.
SHIN MAI IMAMAI SUKA CE?
A wannan gaɓa ina so mu yi nazarin maganganun da suka fito kai tsaye daga bakin shugabannin Ahul baiti, waɗanda ake cewa, saboda su ne ake yin ibadu da bukukuwan Ashura domin mu tantance tsakuwa da tsaba, mu san gaskiyar addinin da suka koyar da kuma saɓanin sa.
Da farko bari mu fara da shi kansa Imamu Husainni (R.A) muji wasiyyar da ya yi wa ƴar uwarsa Zainab (R.A) dab da zai yi shahada:
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan