Babahabu49
NA
MUHAMMAD ABUBAKAR
GABATARWA
Magana da harsuna biyu wani al’amari ne da ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan Nijeriya. Wannan wani abu ne da ke muna tsarin jin harsuna masa yawa a tsakanin al’ummar Nijeria. Yawan harsuna a Nijeriya abu ne da masana suka daɗe suna nazari a kai, kuma sun tabbatar da cewa Nijerya ƙasa ce mai yawan ƙabilu masu magana da harsuna daban-daban.
Masana ilimin harsuna sun bayyana cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya 22 da ke da al’ummu masu magana da harsuna mabambanta. Sakamakon binciken Ethnologue ya tabbatar da cewa Nijeriya na da harsuna 510 waɗanda ƙabilu daban-daban ke amfani da su kuma suke mu’amala a tsakaninsu. Wani abin sha’awa shi ne, duk da yawan waɗannan harsuna da ake magana da su (waɗanda harshe ne na uwa), ana kuma amfani da wasu harsuna baƙi kamar Ingilishi da Larabci da Faransanci da sauransu.
Harshen Ingilishi shi ne harshe na biyu a Nijeriya, sannan kuma akwai gargaliyyanci (pidgin) da al’umma ke amfani da shi sakamakon haɗuwa da kuma hulɗa (contact) tsakanin harshen Ingilishi da harsunan na gida. A wannan aiki za a nazarci yadda harsuna biyu ko fiye ke haɗuwa su yi mu’amala da juna (language contact), tare da bayyana yadda wannan haɗuwa ke samar da wani nau’i na harshe a cikin al’umma, wato yadda a sakamakon hulɗar ake samun wani harshe ya tsiro sakamakon haɗuwa ko hulɗa tsakanin harsuna ‘yan gida da kuma baƙi.
MA’ANAR HARSHE
Yakasai (2012);
“Wata hanya ce ta bayyana kai da kuma hulɗa tsakanin juna wadda dabbobi basu da irin ta.” (Yakasai, 2012).
ILIMIN WALWALAR HARSHE
Holmes (1971) ya bayyana ma’anar da cewa ;
“Fage ne na zari da kan nazarci hanyoyin da ake sarrafa harshe domin tantance kima da matsayin mutane cikin zamantakewa”.
Yakasai (2012) cewa ya yi ;
“Wani ɓangare ne daga fannin nazarin harshe da kuma yadda ake sarrafa shi” (Yakasai, 2012: 24).
ME AKE NUFI DA HAƊUWAR HARSHE (LANGUAGE CONTACT)?
Domin amsa wannan tambaya bari mu kalli abin da masana da manazarta harshe ke cewa cikin bincike-bincikensu. Dada (2007) ya bayyana cewa:
“A duk lokacin da al’ummomi masu magana da harsuna biyu ko fiye suka cuɗanya ko suka yi mu’amala da juna sakamakon da ake samu shi ne haɗuwa tsakanin harsuna da al’adun waɗannan al’ummu wanda kan haifar da wani sabon harshe. Haɗuwa ko hulɗa ko kuma mu’amalar harshe shi ne yadda ake samun harsuna biyu mabambanta da jama’a ko al’umma ke amfani da su.”
Yusuf (1999) na da ra’ayin cewa:
“Ana iya kallon haɗuwar harshe (language contact) a matayin wata hanya ta samar da wani harshe sakamakon mu’amala tsakanin ƙabilu masu al’adu mabambanta, wanda hakan kan kasance sakamakon mulkin mallaka, ko yaƙe-yaƙe, ko kuma ƙaura da makamantansu.”
Crystal (1997) ya bayyana cewa:
“Da zaran wani mutum ko al’umma ta haɗu kuma ta yi cuɗanya da harshen wata al’umma to abin da ke faruwa shi ne wannan al’umma ko mutum zai kasance mai jin harsuna biyu (bilingual).”
A taƙaice, haɗuwar harsuna (language contact) wani al’amari ne da ke faruwa a yayin da wani mutum ko wata al’umma ta cuɗanya da wata kuma a sakamakon haka sai wannan mutum ko al’umma su riƙa magana ko sadarwa a tsakaninsu cikin waɗannan harsuna biyu wato harshen asali da baƙon harshe. Masana ilimin harshe sun tabbatar da cewa irin wannan haɗuwa na harsuna kan samar da wasu abubuwa da yawa duk ta sanadiyar wannan haɗuwar.
ABUBUWAN DA HAƊUWAR HARSUNA KE HAIFARWA
Akwai wasu abubuwa da wannan haɗuwar harshen ke haifarwa a tsakanin al’umma, waɗannan abubuwa kuwa sun haɗa da:
- Hawa biyu (diaglossia)
- Aron kalmomi (language borrowing)
- Magana da harsuna biyu (bilingualism)
- Sirki (code switching)
- Hargitsa balle (code mixing)
- Matsawar harshe (language shift)
- Haihuwar harshe (language birth)
- Harshe na cikin hatsari (language endangerment)
1. Hawa biyu (diaglossia) shi ne haɗuwar harsuna biyu wanda za su dinga gogayya da juna wannan na nema ya danne wannan wannan na nema ya danne wannan amma dole sai ɗaya ya fi ɗaya ƙarfi kuma ko wanne da amfaninsa daga haka ne ɗaya harshen sai ya fara aron kalmomi daga wanda ya fi ƙarfinsa. Misali kamar Hausa da Turanci idan muka ɗauki Kano harsuna biyu ne suka yi fice wato Hausa da Turanci to za ka ga suna so su danne juna amma duk da haka Turanci ya danne Hausa, Turanci ana amfani da shi a ma’aikatu da ofisoshi da makarantu shi kuma harshen Hausa a gida da wasu wurare ake amfani da shi.
2. Aron kalmomi(language borrowing) shi ne haɗuwar al’umma masu magana da wasu harsuna daban su zauna tare da juna ta sanadiyyar wannan zaman da suka yi tare sai kuma su fara aron kalmomi a tsakaninsu. Misali Hausa sun aro tarin kalmomi/ daga harsuna mabanbanta tun daga na cikin gida har zuwa baƙi.
3. Mai jin harsuna biyu (bilingualism) shi ne mutumin da ya yi cuɗanya da wani harshen har ya iya magana da shi kuma yake jin duk wani abu da aka faɗa a wannan harshen, misali kamar haɗuwar Hausawa da Turawa tun Hausawa suna aron kalmomi daga Ingilishi har suka zo suka fara magana da wannan harshen Turawan sai ya zamana suna jin harsuna biyu.
4. Sirki (code switching) wani yanayi ne da mutum mai magana da harsuna ko fiye kan yi amfani da shi lokaci ɗaya. Wato mutum yana magana da wani barshe sai a ji can ya koma ya yi da wani harshen daban. Misali: Ana iya samun Hausawa suna gudanar da kasuwanci a kudancin Nijeriya, babu mamaki kwatsam sai ka ji suna magana da Turanci ne sai ka ji sun koma yin magana da Hausa.
5. Hargitsa balle (code mixing) yana faruwa a lokacin da mutum yake amfi da wani harshe tare da shigar da sigogin wani harshe a cikin wani harshe yayin da yake magana. Misali mutum ya fara gina kalma da Hausa ko Turanici ko Larabci amma sai ya rufe da wani harshen daban.
6. Matsawar Harshe(language shift) wannan wani yanayi ne wanda kan faru a lokacin da al’umma majiya harsuna biyu suka haɗu da juna suka zauna tare a hankali sai ɗaya ya bar amfani da nasa harshen ya ari na wani yana amfani da shi ko dai don martabar wancan harshen ya fi nasa ko kuma wani dalili na duban. Bayan wani lokaci sai ya watsar da nasa harshen ya koma yin amfani da wancan gaba ɗaya.
7. Haihuwar harshe (language birth) haihuwar harshe wani al’amari ne da ke faruwa a yayin da wani mutum ko wata al’umma ta cuɗanya da wata kuma a sakamakon haka sai wannan mutum ko al’umma su rinƙa magana ko sadarwa a tsakaninsu cikin waɗannan harsuna biyu wato harshen asali da kuma baƙon harshe. Misali buroka (pidgin), a nan Nijeriya a wajajen kudancin Nijerya haɗuwarsu da harshen Ingilishi ya haifar da wani harshe daban.
8. Harshen da ke cikin hatsari (language endangement) shi kuma harshe da masu magana da shi idan sun haɗu da wasu mutane sai su rinƙa ƙyamar magana da nasu harshen sai su koma suna magana da wani harshen, kuma ba su koya ma ‘ya’yansu ba masu tasowa ya zama idan an haifi yaro ba za a ko ya mai wannan harshe na farko ba, sai dai kawai su koya mai wani harshen daban.
KAMMALAWA
Duba da waɗannan bayanai da suka gabata tun daga kan ma’anar harshe da ma’anar ilimin walwalar harshe tare kuma bayani game da haɗuwar harshe (Language contact) na fahimci abin da ake nufi da haɗuwar harshe. Aikin bai tsaya a nan ba, sai da ya kawo wasu abubuwa waɗanda haɗuwar harshe ke haifarwa a tsakanin al’umma tare da ɗan taƙaitaccen bayanin kowanne.
MANAZARTA
Crystal, D. (1997): English as a Global Language. Cambrige.
Dada, S (2007); Language Contact and Language Conflict: The Case of Yoruba-English Bilingualism.
Holmes J. And Pride J.B (1971) : Sociolinguistics, Penguim Book Ltd.
Yakasai, S. (2012), Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Garkuwa Media Services LTD Sokoto Nigeria.
Yusuf, Y. (1999): An Introduction to Linguistics.
http//www.google.com
Domin karanta Jin Harsuna Biyu Ko Fiye Da Biyu danna nan
Edita@rumasau-kallamu