Jerin Abinci Da Suke Ƙarawa Mata Masu Shayarwa Ruwan Nono

0
89

Abinda ya fi muhimmanci wajen samar da nono mai yawa da inganci ga mace mai shayarwa shi ne irin abincin da macen ke ci. Yana da muhimmanci mace mai shayarwa ta riƙa shan ruwa mai tsafta da abinci mai ruwa-ruwa kamar shayi da madara, kunu da sauransu. Ga  jerin abincin kamar haka: 

1- Hatsi; Hatsi yana samar da ruwan nono ga mace mai shayarwa saboda tana samarwa mata sinadaran bitamin E, B6 da B5 manganese, selenium da sauran su. Baya ga haɓaka samar da ruwan nono, yana inganta lafiyar garkuwar jikin yaro.

2- Alkama; Alkama wadda a turance ake kira Oatmeal tana da sinadarai masu gina jiki kuma ga sauƙin sarrafawa. Mai jego tana iya sarrafa alkama da madara ko da gyaɗa domin ƙara ɗanɗano. Yana samar da ruwan nono sosai.

3- Alayyahu; Alayyahu yana daga cikin manyan manyan abinci da ke ƙarawa uwa ruwan nono. Haka nan suna da wadata a cikin abubuwan antioxidant, wanda ke taimakawa tsawon lokacin shayarwa.

4- Shinkafa ta gida; Yana da kyau mai jego ta dena amfani da shinkafar da aka sarrafa ta a ƙasashen waje wanda muka fi sani da shinkafar gwamnati ta koma amfani da tamu shinkafar ta gida saboda ita ke ɗauke da sinadaran da ke taimakawa wajen inganta ruwan nono.

5- Karas; Idan mai jego na fama da ƙarancin ruwan nono sai ta dage wajen cin karas ko kuma saka shi cikin abinci ko miya. Karas na ɗauke da sinadarin vitaman A da wasu sinadaran da ke taimakawa wajen ƙara yawa da ingancin ruwan nono.

6- Tafarnuwa; Baya ga tana ɗauke da sinadarai masu amfani da yawa. A gefe guda, yana ƙara samar da nono da ma yana kare jariri daga abin mamakin ciki. Mace za ta iya ci haka ko a niƙa ta a cikin abinci.

7- Dankalin Hausa; Dankalin Hausa yana ɗauke da sinadarin potassium da kuma carbohydrate da ke matuƙar taimakawa wajen ƙara ingancin ruwan nono da kuma magance kasala. Ana iya dafa dankalin a ci da miya ko a sarrafa ta wata hanyar.

8- Nonon Saniya; Madarar shanu da ɗaya daga cikin abincin da ke ƙara yawa da ingancin nono ga mai jego. Bayan nonon sauran ababen da ake fitarwa daga nonon kamar kindirmo da man shanu ko yoghurt duk suna taimakawa su ma.

9- Kunu; Kunu yana ɗaya daga cikin abincin iyaye da kakanni kan ba wa mai jego ta sha da zarar ta fara shayar da jaririn da ta haifa musamman a ƙasar Hausa. Ana iya sarrafa shi da gero ko masara a ba wa mai shayarwa.

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  

 

 

labarin da ya wuceShan Maganin Fitar Da Zaƙi Kafin Haihuwa
Labarin na GabaFalalar Yin Aure