Gabatarwa
Waken soya yana daga cikin amfanin gonar da aka ɗauka a matsayin abinci; wanda ake shukawa kuma ake sarrafawa a kowace nahiya. Ana samun nasarar shuka waken soya a jihohi masu yawa na Nijeriya ta hanyar amfani da iri ɗan kaɗan ko kuma kayan aiki.
Danna nan domin dauko cikekken littafin
Noman waken soya ya bunƙasa sakamakon amfani da yake da shi ga jikin ɗan Adam, da kuma amfani ga tattalin arziƙi, da yawan sarrafa shi a gidaje. Shi ginshiƙi ne wajen samun man girki, ana samun kashi 18 zuwa 22 na man girki a cikin ƙasa. Yana kuma ƙunshe da shi 40 zuwa 42 na sinadarin gina jiki.
Yanayi Da Ake Buƙata Wajen Noman Waken Soya
- Yanayi da nau’in ƙasa yana da tasiri wajen haɓakar waken soya. Waken soya yana yi sosai a Arewacin Nijeriya, inda yawan ruwan sama ya wuce mili-mita ɗari bakwai (700mm) zuwa dubu ɗaya (1000mm).
- Waken soya tsiro ne mai son gajeren yini sannan furensa yana buƙatar gajeren yini. Ana iya shuka shi a gona wadda ma’aunin PH ɗin ƙasar ya fara daga 4.5 zuwa 5.5. Ba a shuka waken soya a ƙasa mai tsakuwa ko gona mara nagarta domin zai sa shukar ta tsiro cikin rauni.
- Yana buƙatar yanayi mai zafi, tsakanin yanayin zafi 22 oc zuwa 35 oc.
Aikace-aikacen Da Ake Buƙata Domin Noman Waken Soya
Gyaran Gona
- Sharar gona; Za a cire dukkan ciyawa a filin, sannan a shirya gadon-shuka da hannu ta hanyar amfani da fatanya ko wani kayan aiki da aka maƙalawa shanu ko kuma motar gona (tarakta).
- Kasar da aka gyara da kyau na sanya shukar fita da kyau da rage haɗarin ciyawa. Za a iya shuka a kan kunya ko a gyararren fili.
Zaɓar Irin Shuka
Danna nan domin dauko cikekken littafin
Zaɓaɓɓun irin shuka
- Ka zaɓi irin da ya dace da yankin da kake noma.
- Zaɓen irin waken soya ya danganta ne ta wajen lura da lokacin nunar sa, da jure fari da cututtuka.
- Lokaci shi ma abin lura ne wajen zaɓen irin da ya dace da yankuna, a lura da iri mai zuwa da wuri ba mara saurin zuwa ba a guraren da suke da ƙarancin ruwa.
- A wanke iri da sinadarin (Fungiside kamar Captain, Apron plus) a yi amfani da fakiti ɗaya ga kilo takwas (8kg) na iri kafin a shuka domin kariya daga ƙwayoyin cututtuka dake cikin ƙasa.
- A yi amfani da irin shuka mai inganci na kalar da aka zaɓa. A guji irin da ya tsage ko wanda ya samu illa, a yi amfani da iri wanda bai wuce watanni 12, ba domin samun tsirao mai kyau.
- Zaɓi iri mai kyau don shuka sannan a tabbatar da babu ƙwari a cikin sa. Kada a sayi irin shuka a gama-garin kasuwa, domin babu tabbacin kyawun sa ko tsirar sa.
Shuka
Lokacin shuka waken soya: Waken soya yana yi sosai a lokaci mai faɗi, idan gurin yana da danshi; kwanakin shukar da aka amince da su domin shuka waken suya a yankuna daban-daban na Nijeriya su ne aka gabatar a Tebur na Ɗaya (1).
Tebur na Ɗaya: Lokutan da aka amince don shuka waken soya a Nijeriya
S/N | YANKI | Lokuntan da aka tabbatar don shika |
1. | Arewa ta Tsakiya | Farko kan Yuni zuwa farkon Yuli |
2. | Arewa maso Yamma | Tsakiya Yuni zuwa farkon Yuli |
3. | Sudan savanna/Arewacin-Arewa | Satin farko da na biyu na Yuli (1-2) weeks) |
- Kada a yi shukar wuri, saboda tsoron fari kan iya jawo yankwanewar shukar da kuma buƙatar sake shuka (kofi).
Yawan Irin Shuka
- Kimanin kilo 50-70 (Tiya 20-28) ake buƙata domin samun yawan tushe da ya kai (444,444) a cikin kadaɗa ɗaya na waken soya.
Tazara Tsakanin Shuka
- A shuka waken soya da hannu ko da injin shuka sannan a shuka kwaya 3 zuwa 4 a rami; a tazara sentimeta saba’in da biyar (75cm) tsakanin kunya da kunya, sannan sentimeta goma (10cm) tsakanin tushe da tushe.
Sa Takin Zamani
Taki da ake saka wa Waken Soya.
- Ya danganta ne daga gwajin ƙasa. Waken soya a matsayin sa na amfanin mai gululai a sauyarsa zai iya samar wa kansa sinadarin nitrogen ta hanyar jawowa daga sararin sama.
- Sinadarin phosphorus ne wanda waken soya ya rasa sosai. Don haka, sai a zuba takin phosphorus daidai don haɓakar yabanya. A zuba takin (SUPA) (3 x 50 kg bags) haɗe da ƙarin 2 x 50 bags na takin kamfa NPK (15:15:15).
- Yawan takin da aka aminta a zuba wa gonar waken soya:
Tebur na biyu: Yawan taki da za a saka wa Waken Soya
S/n | Yawan Taki (Kg/Ha) |
1 | Buhu biyu da rabi na (NPK(15:15:15) |
2 | Buhu uku na SSP (SUPA) |
Noma
Feshin Maganin Ciyawa:
Noman farko zai fara ne a sati na biyu (2) bayan shuka; sannan noma na biyu a sati na biyar zuwa na shida (5-6).
Danna nan domin dauko cikekken littafin
Feshin Maganin Ciyawa:
Magungunan kashe ciyawa in an yi amfani da su da kyau, suna aiki sosai wajen magance ciyawa. Akwai maganin ciyawa na waken soya da za a iya fesawa kafin tsirowar shi da kuma bayan tsirowar shuka. Idan an yi amfani da maganin kashe ciyawar, to noma ɗaya ake buƙata bayan sati biyar zuwa shida (5 -6); a goran magani a yi amfani da maganin kashe ciyawa kamar yadda aka yi bayani.
Ƙwari da Hanyoyin Magance su;
Za a iya magance kwarin waken soya ta hanyer feshi ɗaya na (CYPERMETRIN) Di-mechecate 10EC; a adadin 100ml a cikin lita goma sha biyar (15) na ruwa.
Tuge Waken Soya:
Waken soya yana isa tugewa ne a watanni uku zuwa huɗu bayan shuka; sannan yana buƙatar girbi da wuri domin kaucewa asarar yawan amfani.
Za a iya girbe waken soya a lokacin da ya kai matakin da ƙwari ba za su addabe shi ba; sanda danshi (yawan ruwa) dake cikinsa ya kai tsakanin kashi 14-16%.
Ayyukan da ake yi bayan tuge waken soya
Bugu da Shiƙa:-
- A buge waken soya da hannu ko da injin da zarar ya bushe sosai, ba tare da ɓata lokaci ba.
- An yarda a yi bugu da hannu a ƙananan gonaki. Wannan ya ƙunshi sanya waken soya a buhu da kuma bugun shi da sanda. Sannan za a sheƙe shi don a fitar da kwayar daga raugar.
- Ana iya amfani da inji wanda zai buge ya kuma cire datti cikin sauƙi.
Ajiya
- Ana ajiye waken soya ne a lokacin da ruwan da ya kai cikin ƙwayar yake kashi goma 10% ko ƙasa da haka.
- Ana iya gane bushewar ƙwayar waken soya ne sanda aka kasa gatsa shi da haƙora ko fasa shi da ‘yan yatsu, don ajiya daga wata 6 zuwa 12 sannan kuma domin dogon ajiya fiye da shekara.
- Kada a ajiye waken soya a ƙasa, asa itace ko katako idan za a ajiye shi a cikin suto ko rumbu.
- Kada a jingina shi da bango wajen ajiya.
Danna nan domin dauko cikekken littafin
Domin karatna cikakken bayani a kan Jagoran Noman Masara danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tuwon Masara danna nan.