Illar Shan Ampiclox Ba Bisa Ƙa’ida Ba

0
28

Ampiclox: Wannan wani magani ne da ya shahara wanda mutanen mu sun bude ido dashi matuƙar zaka samu koya mutum ya sami rauni kurum zai tafi chemist yace abashi Ampiclox haka zaizo yaita sha… bai sama ƙa’idojin shansa ba ko kadan.

Haka zaita faman dirkawa cikinsa, idan yaga ankwana biyu babu canji a ciwon ya kuma komawa yace abashi wanda yafi kowane karfi wato BEECHAM…. saboda kurum damuwarsa yaga ciwon ya warke kota halin yaya.

Wannan magani ba abun wasa bane. Broad spectrum antibiotics ne, ko da matsalarka ta shafi antibiotics ba likitan dake dora mara lafiya kan Broad spectrum antibiotics masu karfi irin haka nan take… mu kan mu da narrow spectrum muke fara treatment sai abun yaci tura.

Duk ma’aikacin lafiyar dake dora mara lafiya akan broad spectrum kai tsaye toh baima san me yake ba. Ballantana kuma kai kanka da sunan kurum ka rike.

Yana dakyau kuranta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)

Akaf bayanin maganin AMPICLOX ka duba kowacce irin journal a duniya bazaka taɓa ganin anrubuta cewa wannan maganin yana taimakawa wajen ƙamewar ciwo ba, ko kuma yana magance rauni (wound) ba, bazaka taɓa gani ba. Amma mutanen mu kunƙi ku gane duniya anwaye. Komi kunfison shi ai muku kuna daga kwance bazaku asibiti ba. Shyasa cuttuka sukafi yiwa mutanen kisan wulakanci,abunda bai kamata yai ajalin mutanen mu bama yanzu kashemu yake.

Inbanda Nigeria ba ƙasar da zakaje chemist ko pharmacy store kace abaka ANTIBIOTICS batare da prescription sheet na likita tare da license number dinsa ba ajiki abaka…. Wannan kuma shike cutar da jama’a dinmu domin kuna yiwa kanku illa baku damu kusan kunayi ba.

Antibiotics ana amfani dasu wajen magance ciwon da ƙwayoyin bacteria suka haddasa, kai ciwo kurum kaji inda abunda kafi bukata baifi Vitamins supplement ba da zasu taimakawa Clotting factor dinka a lokacin jini ya zamto ya tsaya. 

Ana ƙarawa mutum da antibiotics ne idan a ka ga ciwo ya nuna alamun infection ma’ana ƙwayoyin cuta sun hau kai, kila har ya fara ruwa, ko ya fara wari…. kuma ko a irin wannan halin AMPICLOX bashi ne magani a zaɓin farko ba. 

Likitoci matakin farko sai mun duba yama immunity dinka yake, shin baka da Allergy ma da irin wannan antibiotics din, sannan muyi nazari muga shin wacce irin bacteria ce tafi kusa da kama wannan sahin jikin naka inda ciwon yake.

Bayan mun auna wannan abu nagaba, shine ita bacteria wacce irice? Wanne jinsi take (Gram+ve ko Gram -ve), shin me sakin guba ce (toxins) ko kuwa? shin tana son iska (aerobic) ko bame rayuwa a inda iska take bace (anerobic)? ko kuwa takan iya rayuwa walau da iska ko ba iska (microerophilic) shin tana da jijiya ko bata da jijiya (cell wall)? shin kwana nawa takanyi kafin ta mutu? shin magani bactericidal me kisa, ko kuwa antimicrobials me rage mata karfi ya dace mu fara amfani dashi……. Da sauran abubuwa masu yawa da basai na lissafa muku su baki daya ba. Wannan shine matakin farko

Domin karanta bayani akan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure) Danna nan 

Sannan in munzo rubuta magani, sai mun duba tsakanin mace da namiji nan ma akwai bambanci,nauyinka nan ma abun dubawa ne, shin yaya baka da hypersensitivity, bayan wannan shin baka da ciwo da kake shan maganinsa wanda bai bukatar agaurayashi da wannan antibiotics misali maganin hawan jini, malaria, ciwon koda, ciwon suga, asthma da sauransu.

Sannan maganin awa nake yaje rabin rayuwarsa ajika (half life), DOSE nawa ya dace dakai bisa nauyinka da shekarunka acikin jikinka, shin a ina ma ake narkar dashi wannan magani da muke shirin baka? shin baka da matsala ta gurin da ake narkar dashi ko ake tacesa ya fita (Excretion)? metabolism (huhu, hanta, koda ko hanji) duk gurare ne da magunguna daban daban ake iya metabolism dinsu.

Sannan shin abincin da kake ci ma ya dace ahadasa da irin wannan maganin ko kuwa? shin kafin aci abinci ko bayan anci abinci ya dace asha ko kuwa?, shin baka ma da ulcer a ciki ko yaya? duk wadannan abubuwa ne da muke nazarinsu kafin dora mutum akan magani, shi yasa da wuya mutum yaje ga likita kaga ciwo yaci gaba da lalalatashi.

Yana dakyau ku karanta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)

Idan kuwa muka baka maganin da muke tunanin shine amma bawani canji toh a irin wannan ne sai mun turaka ga LAB SCIENTIST sun dau sample din ruwan dake fita agurin domin suyi CULTURE AND SENSITIVITY su gano mana wacce irin ƙwayar cuta ce, sannan wanne magani ne zai halaka ta. Ba daka muke ba amma kowa kurum yaji ciwo ba ruwansa AMPICLOX… toh bari kuji illolin hakan

  • Shan wannan maganin dakayi kasani kangarar da jikinka kake gaba kiri kiri Antibiotics zaizo yaki aiki ajikinka! abunda muke kira resistance.  Saboda ka saba abusing din antibiotics any how duk randa wani ciwon ya kamata koda maganin da ake baka shine zai warkar dakai toh zakaita sha kuwa kaqi warkewa… zakaci wahala.
  • Wannan ita tasa da yawa cikin mutane sai kaji mutum yazo yana surutun yaje asibiti anbashi magani amma sai sha yake shi bawani canji… likitan ma baisan me yake ba. Kaine bakasan me kakeyi ba….. Saboda bakasan cewa kai kaima kanka da kanka illar ba ta hanyar shan maganin antibiotics abaya daka wanda ka sabawa kanka, kaga ko ai dole kaci wahala
  • Kana lalata lining din cikin uwar hanjinka ne, ana nan zaka hadu da pseudomembranous colitis watarana! wato hanjinka zai taɓu ka rika fama fa zafin ciki koma kaji shiru ka dauka komi normal sai rana tsaka aji ance wane ya mutu ba ciwo ba komi.

A domin me? Sanine ba aiba, kaine kaima kanka illar da a hankali hanjinka yakai ga hujewa…. kashinka wanda yake kunshe da milyoyin bacteria ya zuba cikin kayan cikinka ya haddasa sepsis wanda hakan yakai ga  peritonitis ka mutu nan take… 

Akasashen da akaci gabane da suka damu susan abunda ya kashe mutum da ake kawomana gawa mui AUTOPSY bayan mun bude kayan ciki mukan iya gano irin abun ya faru kenan da mutum har ya mutu. Mu kuwa saidai a tafi a hargitse mutum a cikin kasa shikenan tasa ta ƙare kuma.

  • Duk randa amai da gudawa suka kama me irin shan antibiotics din toh nan ma ka kuka da kanka… kafi kowa saurin chance din mutuwa
  • Zaka iya haduwa da lalacewar fata.
  • Zaka iya haduwa da ciwon hanta… wanda sai akarshe zai bayyana. Nasha fadamuku ba iya hepatitis virus ne ke haddasa ciwon hanta ba, hatta paracetamol ya shahara wajen haddasa ciwon hanta
  • Zak aiya haduwa da farfadiya sanadiyyar hakan wato (seizure) in ka zamo addict 
  • Duk da AMPICLOX antibiotics ne akwai antibiotics din da ba a haɗashi dashi asha… shiyasa nafadamuku ko likita sai ya auna kafin rubutashi. 
  • Ko jira jirai da kananun yaran da akewa allurar rigakafin BCG ba a basu AMPICLOX a tsakanin… hantarsu na iya taɓuwa ko su hadu da zagwanyewar ɓargo
  •  Ba’a  hada shan AMPICLOX da Ja da yellow,ampiclox ba’a hadashi da wadannan magungunan” (BCG vaccine, cholera vaccine, demeclocycline, doxycycline, azithromycin, Allopurinol, minocycline, tetracycline, typhoid vaccine
  • Yana iya bakinka ya rika kwailewa yana jini akai akai 
  • Yana iya lalata lafiyar aikin koda (kidney) da sauransu

Don haka ku hankalta, mutum ya kiyayi shan antibiotics daka bama sai AMPICLOX ba. Kai magani ma baki dayansa ka kiyayi shansa duka guba ne kaje wajen wanda yasan magani ya dubaka ya baka shawarar abunda ya dace.

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

labarin da ya wuceMagungunan Na Aiki Ta Hanyar Daƙile Azarbabin Sinadarin Isar Da Sakon Zafi A Jijiya Zuwa Ga Ƙwaƙwalwa.
Labarin na GabaNausea (Tashin Zuciya)