Jin rashin gamsuwa da zaƙuwa wajen jin alamar mutum kamar zai yi amai.
Dalilan Da Ke Kawo Tashin Zuciya
Za a iya samun tashin zuciya a sakamakon wata cuta ko wani yanayi da jikin ɗan Adam ka iya samu (conditions)
Motion Sickness: Yanayi da ka iya haifar da cutar a sakamakon tafiya a abin hawa.
Misali
- Tashin zuciya (Nausea)
- Rashin samun balance
- Amai (Vomiting)
Concussion: Samun rauni a ƙwaƙwalwa sakamakon duka ko naushi (blow) a kai ko girgiza kai ba bisa ƙa’ida ba
Misali
- Tashin zuciya (Nausea)
- Amai (Vomiting)
- Akan iya rasa human memory
Alcohol Abuse: Yanayin ko salon shaye-shaye ba bisa ƙa’ida ba.
Misali
- Tashin zuciya (Nausea)
- Amai (Vomiting)
- Craving ko physical defence
Morning sickness: Inda aka fi raja’a da kuma ba da sunan tashin zuciya kacokan shi ne zargin ko samun juna biyu.
Halaiyar Mu Da Ke Kawo Mana Tashin Zuciya
- Shan magunguna na ƙwaya daban-daban ba tare da an ci abinci ba.
- Yawan cin abinci a cika ciki tab.
- Ƙarancin cin abinci a zauna da yunwa.
- Yawan ƙwanƙwaɗar barasa ko shaye-shaye.
- Tsintar kai a yanayin tafiya a jirgi ko mota.
Hanyoyin Kare Kai Daga Tashin Zuciya
- Samar da wadatarciyyar iska a abin hawa jirgi ko mota.
- Cin abinci akan lokaci ko ƙa’ida ba tare da ci kaɗan ba ko cikawa.
- Rage cin abinci me maiƙo yayin karyawa zuwa ɗagawar rana.
- A yawaita karyawa da (dry food) busashen abinci kamar biscuit cabin.
- Kada a zura hannu a baki don kakaro mai.
- Samun hutawa da wadataccen bacci sannan a guji cin abinci me ɓata ciki.
- Kai ziyara asibiti dan bambance me ke kawo tashin zuciya, da ɗora mutum a kan hanyar da ta dace na shawarwari ko magani.
Domin karanta Illolin Shan Ampiclox Ba Bisa Ƙa’ida Ba Danna nan
Edita; RMK