Haɗarin Ƙuntatawa Iyali Wajen Ciyarwa

0
27

Musulmin da Allah ya yi masa yalwar abin da zai ciyar da iyalinsa, da abin da zai tufatar da su, amma sai ya zama yana ƙuntata musu, ta hanyar ƙin wadata su da abin da zai ishe su, to, a zahirin gaskiya babu wanda yake cuta sai kansa, domin kuwa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “ya ishi mutum laifi, ya riƙa tozarta wanda yake ci a ƙarƙashinsa”. (Abu Dawuda ne ya rawaito shi). 

Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) yace: Haƙiƙa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) Yace: “Babu ranar da bayi za su wayi gari a cikinta face sai wasu mala’iku biyu sun sauko, sai ɗaya daga cikinsu ya kama cewa: “Ya Allah ka bai wa mai ciyarwa”. Sai shi kuma ɗayan yace: “Ya Allah ka haɗa matsolo da asara”. (Bukhari da Muslimu ne suka rawaito shi). Don haka, ‘yan uwa sai ayi hattara.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Bayan haka, da Allah zai datar da iyalan malam matsolo da samun wata kafa da za su riƙa ɗiban abin da zai ishesu daga cikin dukiyarsa, a shari’ance, ba su yi laifi ba in sun ɗebi abin da zai ishesu, matuƙar dai ba za su yi ɓarna ba. 

An karbo daga Aisha (Allah ya yarda da ita) tace: “Hindu ‘yar Utba matar Abi Sufyanu ta shiga wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) sai tace: “ Ya manzon Allah mijina Abu Sufyan matsolo mutum ne, ba ya bani abin ciyarwa da zai isheni, kuma ya ishi ‘ya’yana, sai in na ɗebi wani abu daga cikin kudinsa ba da saninsa ba, shin ko ina da laifi game da hakan da nake yi? Sai Annabi yace: “ki ci gaba da ɗaukar abin da zai ishe ki ya ishi ‘ya’yanku daga kuɗinsa”. Wato yin hakan ba laifi ba ne. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi). 

Sannan dai ita wannan ta’ada ta matsolanci, haɗarinta yana da yawan gaske, domin kuwa tana sa mai yinta ya rasa samun alherin da masu ɗaukar abin hannunsu su bayar suke samu: 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Na Farko: zai rasa samun addu’ar alherin da mala’ika yake yi wa masu ɗaukar abin hannunsu su bayar duk wayewar garin Allah, kamar yadda muka ji. 

Na Biyu: Ya rasa kwarjinin da masu bayar da abin hannunsu suke samu a wajen waɗanda suke agazawa. 

Na Uku: An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) yace, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: “Hannun da yake bayarwa ya fi hannun da yake karɓa. (In zaka bayar) ka fara da wanda nauyinsa ke kanka, ka ba wa babarka, da babanka, da ‘yan uwanka, sannan wanda yafi kusa da kai, sai wanda yake da kusanci da kai”. (Nasa’i da Darakudni ne suka rawaito shi, kuma Darakudni da ibn Hibban suka inganta shi).

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceNauye-nauyen Rayuwar Aure
Labarin na GabaHakkin Zaman Gidan Miji