Hausawa Da Al’adunsu

1
6968

MATASHIYA

     Al’ummar Hausa dai, al’umma ce dake zaune a arewa maso yammacin Tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin Jamhuriyyar Nijar. Al’umma ce mai dimbin yawa, sun bazu a cikin kasashen Afirka da kasashen Larabawa, kuma a al’adance masu matukar hazaka, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin wadanda harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A tarihi, Hausawa na tattare a salsalar birane. Hausawa dai sun samu kafa Daularsu tun daga shekarun 1300, lokacin da suka samu nasarori da dauloli kamar daular Mali, Songhai, Borno da kuma Fulani.

  A farko-farkon shekaru na 1900, a lokacin da Hausawa ke yukurin kawar da mulkin aringizo na Fulani, sai Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya suka mamaye Arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa karkashin mulkin Birtaniya,’yan mulkin mallaka sai suka marawa Fulani baya na ci gaba da manufofin aringizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin-gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne ya yi kane-kane a arewacin Nijeriya .

      Koda yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da zuwan Addinin Musulunci da kuma karbarsa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bamban.

Ginshikan al’adun Hausawa na da mutukar jarumta, kwarewa da sanayya fiye da sauran al’ummar dake kewayenta. Sana’ar noma ita ce babbar sana’ar Hausawa, saboda ingancin noma; Hausawa ke wa sana’ar noma kirari da cewa, “Na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Akan samu kimanin watanni shida babu ruwan sama.

To wannan yanayi ne ya ba wa Hausawa damar rinka fita daga wurarensu zuwa wasu wuraren domin yin wasu sana’o’i da ayyuka na musamman, irin wannan fita ce Hausawa suke ambata da cirani. Ana yin wannan fita ce don a cinye tsayi na rani, sai ka ga ba za a dawo gida ba sai alamun damina sun fara bayyana (Gusau, 2008: 5 – 6).

Akwai kuma wani nau’i na tafiya da Hausawa suke yi wanda kai tsaye ya shafi fatauci inda suke daukar kaya da jakuna daga wani wuri zuwa kasuwanni daban – daban. Masu wannan fatauci su ne ake kira fatake (Falke: tilo). Shugaban fatake kuwa shi ne Madugu (Madugai: jam’i). haka kuma a irin wannan tafiya akwai ‘yankoli. (Gusau, 2008:6).

A takaice, za a iya cewa akwai Hausawa mazauna kasar Hausa daban – daban wadanda suka hada da manoma da mafarauta da mayaka da madugai da fatake da masunta da masaka da makera da majema da maharba da madinka da malamai da masarauta da makada da mabusa da dillalai da kuma ‘ya’ya da bayi da sauransu. (Gusau, 2008:6).

Harshen Hausa shi ne mafi girma da sanayya a nahiyar Afirka, harshe ne da ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman Larabci sannan kuma harshen na tafiya tare da yanayi na zamani bisa al’adar cude-ni in-cude-ka.

Harshen Hausa ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama’a da ba Hausawa ba ne a nahiyar Afirka.

Bugu da kari, akwai cinciridon al’ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacin Afirka da kuma yankunan cinikayyar al’ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar su ta zuwa aikin Hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun Ajami da aka buga tun kafin zuwan Turawa ‘yan mulkin mallaka na Birtaniya.

Hausawa sun yadu a kasashe da yawa a cikin Afirka da kasashen Larabawa, cikin wadannan kasashe akwai: Sudan, Saudiya, Libya, Aljeriya, Burkina faso, Kameru, Aljeriya, Benin, Cadi, Gambiya, Ghana, Togo, Gine-Bisau, Mali, Sierra Leone, Gabon, afirka ta tsakiya, Libya, Ethiopia, Kwango.

ASALIN KASAR HAUSAWA

Masana tarihi sun ambaci cewa, akwai mutane tun lokaci mai tsawo da ya shude a wadannan garuruwa na Kasar Hausa, kuma babu wanda zai bugi kirji ya ambaci daga inda suke, koda yake dai wasu kuma sun ambaci cewa ana kyautata zaton asalin Hausawa barbarar yanyawa ne tsakanin mazauna kasar da baki da suka yiwo kaura daga kasashen Asiya zuwa kasashen Afirka.

Dalilin wannan kaurar kuwa, an ce wai juyin mulkin da ya faru ne a tsakanin Banu Abbas da Banu Umayyah a Bagadaza, shi ya sanya wasu suka yiwo kaura, daga nan ne suka bazu cikin Afirka ta Yamma, musamman ta fuskar kasuwanci. Sai dai kuma an ce, yayin da suke yin wadannan kaurace-kauracen ne, kamanninsu da harshensu da al’adunsu suka canja saboda auratayya da canjin yanayin rayuwa.

Har ila yau an kara da cewa, ana zaton mutanen sun fi dadewa a Daura da Kano, ba don komai ba kuwa sai don su ne aka gwada kuma aka ga akwai dadadden tarihinsu da yadda mutanen suka rayu a wadannan wurare. (Adamu, M.T. 1997:21 – 22).

Akwai masu ra’ayin cewa, tun asali Hausawa a garuruwansu na kasar Hausa Allah ya yi su, ba wai sun yiwo hijira ba ne daga wani wuri suka zo nan din. Malaman suna da hujjoji masu yawa a kan hakan, daga ciki suna kafa hujja da maganar babban Malamin nan Sheikh Nasiru Kabara, kamar yadda yake cewa jirgin kwale-kwalen Annabi Nuhu (AS) yayin da ruwan Dufana ya dauke ya tsaya ne a wani gari mai suna ‘Yandoto, wanda yanzu garin yana cikin Jihar Zamfara ta nan kasar Hausa.

A wajen masu wannan ra’ayi, wannan nahiya tun asali ana kiran ta da shi wannan suna ne da aka santa da shi wato “Hausa”.

Yawan kare-kare a wasu shiyyoyi na Kasar Hausa, da karancinsu a wasu wuraren shi ne babban dalilin da za a jinginu da shi. A cewar masu wannan ra’ayin duk inda kare- karen suka tattaru a dan kankanen wuri, to a nan aka haifi harshen. Idan kuma ka ga harshe ya yadu bai daya a kasa mai fadi, to ba a nan aka haife shi ba ya zo ne daga wata kasa.

(T/Wazirchi, 2009:17 – 18). Bunza, yana da irin wannan ra’ayi cewa “Hausa ba daga wani wuri ta zo ba Nahiyar Gobir nan ce mahaifar Hausa”. (T/Wazirchi, 2009): 18). Sannan su ma mafi yawan mawakan baka, musamman wadanda suka fito daga yankin Sakkwato, Zamfara da Kabi suna ambaton wannan nahiya “Hausa”.

Idan muka koma ga gurbin kasar Hausa, wato taswirarta ta faro ne daga yammacin Afirka, yankin kudancin Sahara kuma arewa da Kurmi inda Larabawa ke kira Biladul Sudan, wato kasar bakar fata. Yanki ne da ya kunshi kasashe da dauloli da dama a cikinsu har da kasar Hausa.

Wadda ta kafu a Yammacin Sudan, tsakanin Tafkin Cadi daga Gabas, da guiwar Kogin Kwara daga Yamma, da hamadar Sahara daga Arewa, da kuma dazuzzukan gabar Tekun Atilantika daga Kudu. Dangane da kasashe da kabilu da kasar Hausa ta yi iyaka da su kuwa, a Gabas ta yi iyaka da Kanem-Borno, a shiyyar Kudu, kuma ta yi iyaka da kwararrafa (Kasar Tibi, Nufe, Gwari, da sauran tsirarun kabilu).

A yamma kuma ta yi iyaka da tsohuwar Daular Songhai, daga shiyyar Arewa kuma kasar Hausa ta yi gaba da garuruwan Buzaye (Agadas) na cikin kasar Nijar. (T/Wazirchi, 2009: 11 – 12). A yanzu haka idan muka duba taswira, za mu ga Kasar Hausa tana Arewacin Nijeriya ne da kuma wani sashi na Jamhuriyar Nijar (T/Wazirchi, 2009: 12).

A cikin kabilu mazauna yankin Sabannah, wato kasa mai karancin itatuwa, ko mai itatuwa jefi-jefi, Hausawa su ne suka fi mamayar wurin zama mai fadin gaske. Wannan wuri shi ne aka fi sani da kasar Hausa. (Gusau, 2008: 2).

ASALIN KALMAR HAUSA DA MA’ANARTA

Akwai maganganu da yawa dangane da asalin kalmar Hausa, inda suka bayyana a matsayin ra’ayinsu. Daga cikin maganganun akwai:

Nil Skinner (1968) cewa ya yi, “Asalin kalmar Hausa, an samo ta daga Songhai. A ganinsa, akwai dadaddiyar dangantaka tsakanin Hausawa da su mutanen Songhai, har ta kai Hausawa suna aron kalmomin Songhai domin a nasa binciken cewa, kalmar Hausa an samo ta ne daga ‘Assa’ sunan da suke kiran mutanen da suke Gabas da su, su kuma Hausawa suka aro suka lakaba wa kansu.

Malam Aminu Kano kuwa, ya bayyana cewa an samo kalmar Hausa daga kalmar Habasha, wai don a cewar sa asalin Hausawa mutanen Habasha ne, kuma a maimakon a rinka cewa Habasha din sai ake cewa Hausa. (Adamu, M.T. 1997:19).

A nasa tsinkayen, Mr. C.R. Niben (1971) cewa ya yi, an samo asalin kalmar Hausa ne daga Buzaye, domin kuwa haka suke kiran mutanen dake zaune a arewacin Kogin Kwara, wato Hausa. (Adamu, M.T. 1997: 19).

Shi kuwa mai Martaba Sarkin Ningi; Alhaji Haruna Wakati, cewa ya yi an samo kalmar Hausa ce daga labarin zuwan Bayajida garin Daura, a lokacin, da ya isa da daddare ya sauka a gidan wata tsohuwa ‘Ayyana’ ko kuma ‘Wayre’, inda ya bukaci ruwan sha a wurinta, da cewar ba ta da ruwa ya tambaye ta ina zai samu, ita kuma ta sanar da shi babu inda zai samu sai ya je rijiya, kuma matsalar ba a diban ruwa sai sati-sati ake zuwa a debo ruwa; saboda wata macijiya mai suna sarki.

Daga nan sai ya bukaci ta ba shi guga, ta nuna mai inda rijiyar take ya je ya zura guga ya fara debo ruwan, sai wannan macijiyar ta biyo igiyar gugar, shi kuma ya sa takobi ya sare kanta. Inda labari ya bazu a gari har Sarauniya Daurama ta samu labarin abin da yake faruwa, ta sa a nemo wanda ya kashe macijiyar don a yi masa kyautar bajintar da ya yi. Ana ta neman wanda ya kashe amma ba a same shi ba.

Sai aka tambayi tsohuwa, wanda ya kashe ta ba a same shi ba. Sai ta ce musu “Ai ya hau”. Hau-sa maimakon ta ce ya hau doki tunda ita ba ta taba ganin doki ba. To wai wannan ‘Ya hau-sa’ ne aka hade kalmomin ne suka koma ‘Hausa’.

Haka kuma a wata fadar an ce, da can Larabawa da suka zo harkar cinikayya Arewa zuwa Kurmi, lokacin da suka zo suka ga kalmomi da dabi’u irin nasu, sai suka ce wadannan mutane sun so su yi kama da mu, amma sun dan karkace. To shi ne idan za su zo sai su ce: “Za mu Hawasa”, wato za su garin karkatattu. (T/Wazirchi, 2009:14).

Masu ra’ayin Harshe suna ganin cewa kalmar Hausa a wurin su ‘Bahaushe’ ma’anar ta “harshe”, domin idan ka yi magana da wani harshe daban, bahaushe yakan ce ” Ya ji ana wata Hausa”, wato a nan Hausa sunan harshe ne ba na kabila ba, kuma al’ummomin da suka taru suke magana da wannan harshe su ne Hausawa. (T/Wazirchi, 2009: 16).

A takaice dai, Kalmar Hausa tana nufin harshe, tana kuma nufin mutanen da suke magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa, kamar yadda kuma take nufin kasar da su wadannan al’umma ta Hausa suke zaune. Saboda haka ne ake kiran harshen da cewa “Harshen Hausa” a kuma ce “Bahaushen Mutum” sannan a cewa mazauninsu “Kasar Hausa”.

SIFFOFIN BAHAUSHE DA HALAYENSA

Bahaushen mutum baki ne amma ba baki kirin ba irin wadanda Turawa ke kiran su Negroid, domin su bakin su wankan tarwada ne. Bahaushe ba shi da dogon gashin kai irin na mutanen Songhai, amma kirar jikinsa da kamanninsa daidai yake da na al’ummar Aryaniyawa (Aryan), wadanda da suke zaune a tsakanin kasashen Turai da Asiya, kafin su yi hijira su watsu wurare daban-daban a duniya. Game da halayensa kuwa, halaye ne na nagarta wadanda ya shahara das u, kuma yana daya daga cikin shahararrun kabilun da ake girmamawa a Afirka. Wadannan halaye na Bahaushe su suka daga shi har ya yi fice aka san shi a duniya ta da, da ta yanzu fiye da sauran kabilun bakar fata a Afirka ta Yamma. (Kantoma, 2011:16-17).

SHUGABANCI A WURIN HAUSAWA

Shugabanci na nufin rikon ragamar al’umma da ba su umarni da yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da sasanta tsakaninsu, da makamantan wadannan. Shugaba shi ne kololuwa a tsakanin al’umma, wato shi ne yake saman kowa, umarninsa ake bi, shi ne mai zartar da hukunci a tsakanin al’umma. A Kasar Hausa kuwa, akan samu sarki a matsayin shugaba, sai kuma ‘yan fadarsa wadanda su ne masu taimaka masa wajen tafiyar da al’amuran jagorancinsa.

Shugabanci ta bangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga tsarin zaman iyali inda maigida yake kamar sarki a gidansa, wanda shi ne babba, daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko fiye da haka akan zabi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jaruntaka da dauriya. Wasu dalilai kamar halin kunci a cikin gida ko bukata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya, kan sa maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani wuri na daban, kamar gona ko garke. Ta haka ne iyali kan yadu su yawaita su hada wani kauye. Saboda haka ne sai a kara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan kauye. Wannan shi ya haifar da mukamin Mai Unguwa kuma shi zai rinka tsara musu dokoki.

Kauye yakan bunkasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka sai a kara zabar wani mutum a matsayin Maigari (Fagaci) domin kula da wannan gari. Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka kara yawaita sai aka samar da mukamin Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Maigari akalla guda biyar don ya kula da su. Da tafiya ta yi tafiya, sai aka samar da mukamin Sarki, inda ake hada wa Sarki masarautar Hakimai akalla biyar ko fiye domin ya shugabance su ya kuma shimfida musu dokoki domin zaman lafiya.

DOKA A KASAR HAUSA

Game da ma’anar Doka kuwa, Neil Skinner (1980), ya bayyana cewa “Doka wata tsararriyar hanya ce da akan gindaya ta ga mutanen gari, da kuma horo ga duk wanda ya ketare ta don samar da tsaftatacciyar rayuwa ga wannan al’umma”.

RABE-RABEN TSARIN DOKA A KASAR HAUSA

Dangane da rabe-raben doka kuwa, masana sun raba su zuwa gida uku kamar haka;

  1. Doka a bangaren cikin gidan Hausawa.
  2. Doka a bangaren shugabanni.

iii. Doka a bangaren masu sana’o’in gargajiya.

Wadannan su ne manyan rukunai ko azuzuwan da doka ta kasu gare su. Ga yadda bayanansu yake.

DOKA A BANGAREN CIKIN GIDAN HAUSAWA:

A gargajiyance gidan Bahaushe yakan kunshi maigida da matansa, da ‘yan’uwansa, da kuma ‘ya’yansa. Iyali shi ne ainihin ginshikin da aka kafa al’ummar Hausa a kansa. Daga iyali ne jama’a kan faru, har su zama ‘yar kungiya, daga nan kuma su hadu su samar da ‘yar unguwa, wadannan unguwoyi suke haduwa su kafa kauye, daga nan kuma sai garuruwa su samu.

A zaman iyalin Bahaushe, babba ne kan yi kokarin sadaukar da kansa, ya kyautata wa na kasa da shi. Shi kuma karami ya yi masa biyayya, da kauce wa duk wani abu da ka iya kawo raini ga na gaba. To akasari za ka tarar irin wannan gida, gida ne na gado, wato wanda aka gada tun kaka da kakanni kuma ba a raba shi ba. Sau da yawa irin wannan gida a tukunya guda ake girka abincin da za a ba wa kowanne.

A wani bangare kuwa, Kaka na wajen uwa ko na wajen uba, shi ne mai yin hukunci na farko a tsakanin danginsa, kuma shi ne zai fadi abin da za su yi. Idan ka ga an jingine Kaka, to ya tsufa ne ko kuma ba shi da cikakkiyar lafiya, ko ta Allah ta kasance a kansa (ya mutu).

A wannan bangare ana yin amfani ne da Doka ta ina gaba da kai, don haka dole abin da na umarce ka shi za ka bi, ki da so. A lokacin da maigida ba ya nan, wansa ko kaninsa shi zai zama a makwafinsa, kuma ko mahaifi (Maigida) yana nan zai iya zama a makwafinsa, misali zai ce “Kai wane mun samu labari kana neman auren ‘yar gidan wane, ba za ka aure ta ba”.

Shi kenan ba ka da ta cewa, don yana cikin masu fada a ji a cikin danginku. Kuma sannan wadannan ‘ya’ya ba za su zama manya ba ko da kuwa an yi musu aure, har sai sun hayayyafa. Kun ga kenan na gaba yana wucewa na baya na maye gurbinsa, shi ma wancan kakan a da jika ne na wani, ya zama da, ya zama uba, kana ya zama kaka. Don haka Kaka shi ne tsani na farko da za a taka wajen bin Doka ta cikin gida.

Idan muka juya bangaren aure kuwa, Hausawa suna da al’adar wanda duk aka ba wa yarinya ta bayu, ko tana so ko ba ta so, dole ne su zauna tare. Haka shi ma mijin ba kasafai ake bari ya zabi wacce yake so ba, yana yin uhn! Za a ce “Kai! Da ubannika za ka yi jayayya?.

Ko kuwa wannan ba kanin ubanka ba ne? Wato ba shi da iko a kan ka kenan?”. Haka nan a kan dole zai zauna da wannan mata, in da rabo ma sai ka ga sun hayayyafa. Su ma idan suka tashi aurar da ‘ya’ansu irin wancan auren da aka yi musu (na zumunta) za su yi wa ‘ya’yansu.

DOKA A BANGAREN SHUGABANNI

Shugabanci a Kasar Hausa ya danganci rikon ragamar al’amuran jama’a, wanda ya hada har da ba su umarni, da kafa musu doka, da sulhunta tsakaninsu da sauran hakkokinsu na yau da kullum. A karkashin wannan aji na bangaren masu mulki muna da Sarki da Hakimi, da Dagaci (Fagaci) da kuma mai unguwa. Ga bayanin yadda kowanne daga cikinsu ke zartar da Doka a bangarensa.

  1. MAI UNGUWA:

Shi ne sabon shugaban da talakawa suka zaba a yayin da suka fuskanci sun soma yawa, dole tafiyar sai da jagora, daga baya ne abin ya zama gado. To shi Mai unguwa yana cikin masu kafa Doka a bi dole, ko ya hana don karfin mulkinsa, sai fa idan abin ya fi karfinsa ne zai tura shi gaba.

  1. DAGACI (FAGACI):

Shi ne mutumin dake mulkar unguwannin dake karkashin masu unguwanni kamar biyar ko fiye, ana kiran sa Maigari saboda yankinsa ya fi karfin unguwa. To shi ne mai zartar da hukuncin da ya gagari masu unguwannin dake karkashinsa.

  1. HAKIMI:

Ya samu wannan suna ko mukami ne a yayin da aka samu ci gaba, kuma garuruwa suka kara yawaita. Sai aka ba wa Hakimi garuruwan Fagaci akalla guda biyar don ya kula da su. To shi ma Hakimi idan abu ya daure masa kai, yakan tura shi kai tsaye ga shugaban kasa na gargajiya (Wato Sarki).

  1. SARKI:

Shi ne shugaban koli ga dukkan mahukuntan da aka yi bayaninsu a baya, shi ya sa ma wasu ke yi wa sarki kirari da “Bango madafar bayi”

DOKA A BANGAREN MASU SANA’O’IN GARGAJIYA:

Al’umma tamkar jikin dan’adam take, wanda baya ga aikin da tilas ne kowace gaba ta yi don tabbatar da rayuwarta cikin inganci, akwai kuma gudunmawar da take ba da wa don kasancewar dan’adam din jiki guda. Ga kuwa sauran aikace-aikace da suke da muhimmanci fiye da saura, wadanda in ba a yi su ba, sai ta kai ga katsewar rayuwa. Wannan siffa ta al’umma, ta tilasta wa kowa daga cikin jama’arta yin wani aiki, domin tabbatar da wanzuwar al’ummar, ba ya ga wasu aikace-aikace da suka zama dole ga kowa, domin rayuwarsa shi kansa.

Sarakuna a kowanne gari, sun bai wa shugabannin sana’o’i da manyan bokaye, da jarumai har ma da dattijan gari matsayi na musamman wajen gudanar da mulkinsu. A hakika ma, bincike ya tabbatar da cewa wadannan rukunonin jama’a ne suka zamo mataimakan Sarki, wajen tafiyar da mulkin yankinsa.

Don haka a gargajiyance ana zabar dattijo da ya fi kowa yawan shekaru da kwarewa a kan sana’ar da mazauna wurin suke yi. Irin sana’o’in da ake da su a wancan lokaci sun hada da Noma, Kiwo, Kira, Jima, Saka, da sauransu.

Bisa ga tsarin zama na gargajiya, Hausawa sun amince da zaman cude-ni-in-cude-ka. Kowanne mai sana’a, yakan yi la’akari da cewa kamar yadda yake bukatar wasu abubuwa don nasarar sana’arsa, haka ma wasu ke bukatar wani abin daga gare shi. Wannan fahimtar tasa kowanne mai sana’a yakan yi fiye da abin da yake bukata, ta yadda zai iya amfana daga abin da ya saura, don mallakar wasu abubuwa da ba zai iya yi da kansa ba.

Misali, Manomin dake bukatar wuka, ko fartanya, ko lauje, sai ya dauki hatsinsa ya kai ga Makeri. Haka shi ma makerin zai ba da garma ko takobi don a yi masa yabbe ko jinka ko dinki. Da haka sai ka ga kowa ya samu biyan bukatarsa kuma rayuwa ta saukaka, wannan, nau’in ciniki shi ake kira cinikin furfure.

Amma ko ba a fada ba, irin wannan rayuwa, tana bukatar kowa ya yi aiki tukuru, tare da nusar da mutum zuwa ga yin tsimi da tanadi na abin da ya yi saura don gaba. Wannan ya sa tsarin tattalin arzikin Hausawa ya ginu a kan sana’o’insu.

To idan kuma ya kasance a bangaren sana’a kamar ga Mahauta ne, wani ya ci bashin dabbar wani ya ki biya, to shi wanda aka ci bashin nasa ba zai ja wancan da rigima ba, a’a sai ya tafi wajen Sarkin Fawa ya yi kararsa. Shi kuma Sarkin Fawa zai tura daya daga cikin fadawansa su yi kiran wanda ya ci bashin, a nan za a kashe rigimar, ko Sarkin Fawa ya biya, ko a yi wa wanda ake bi bashi lamuni ya kawo. To haka ma abin yake ga sauran masu sana’o’in gargajiya da suke da sarakuna.

ADDINI DA BAUTA A WURIN HAUSAWA

Addini hanya ce ta bauta, wadda tilas dukkan dan’adam ya bi. Allah (S.W.A) ya ce “Ban halicci mutum da aljani ba sai don ya bauta Mini”. Amma kuma ya ba su na su bauta wa Allah da ya hallicce su. Ko kuma su bauta wa waninSa. Abin da kawai dan’adam ba zai samu ba, shi ne ya zauna bai yi bauta ba, ko ba komai ya bauta wa cikinsa, ko wani ra’ayi nasa. Allah ya tsare mu, amin.

A matsayinsa na hanyar bauta addini shi ne yake daidaita tunanin dan’adam da dukkan al’amuransa na rayuwa, ko da kuwa kowanne addini mutum ya zabi ya yi, to kuwa za ka tarar addinin nasa yana da kwakkwaran tasiri dangane da yadda yake tafi da harkokin rayuwarsa.

Idan kuwa muka koma dangane da bauta, addinin Hausawa na gargajiya za mu tarar yana da dokoki, da tsare-tsare da mabiyansa ke bi. Misali ga alama ‘Kan-Gida’ shi ne abin bautar kowanne iyali na Hausawa. Dodo kuwa, abin bauta ne na jama’ar gari, kowanne gari suna da Dodon da suke bautawa, za a iya cewa Tsunburbura ita ake bautawa a Kano. Daura kuwa, suna bauta wa macijiya. Zariya kuwa suna bauta wa dodanni da ake kira ‘MADARA’ Da ‘KUFE’.

Shi kuwa Bori addini ne da Hausawa suke bautawa ‘ubangiji’ ta hanyar iskoki. Shi kansa addinin bori, duk da cewa ya yadu a Kasar Hausa, ba kowa da kowa ne ya karbi addinin yake bi ba. Ma’ana ba kowane Bahaushe ne dan bori ba, sai wanda ya yarda da addinin, kuma shugabanni addinin na bori suka karbi yardar tasa, suka yi wasu al’adu na shigar da shi addinin nasu.

Misali, mutumin da ya zabi ya bautawa kare, za ka same shi yana kaffa-kaffa da karen tare da yin dukkan abin da kare ke so, da kuma barin dukkan abin da karen ba zai so ba. Haka za ka samu wannan mutum ya cika da bakin ciki a duk lokacin da wani ya saba wa karen, ko ya sa shi fishi, sannan ya yi farin ciki da wanda duk ya kyautata wa karen ko ya gan shi cikin koshin lafiya da annashawa, dan haka duk wata harka da ba ta shafi karen ba bai damu da ita ba. Karen nan ya sani, shi ya tsare aikinsa ke nan hidimar kare. Dan haka ba ya sake da duk wata doka da ya kafa wa kansa game da karen.

TUFAFIN HAUSAWA NA GARGAJIYA

Dangane da sutura, masana da dama sun yi bayani kan suturun Hausawa na gargajiya wato. Misali, Alhassan da Musa (1980), cewa suka yi, “Galibi adon namiji na Hausa ba ya wuce riga gare da wando musamman tsala, da takalmi faɗe ko kafa-ciki da hula kube. ko ɗanƙwara, ko dara. Idan kuwadattijo ne, yakan sa rawani. Adon mata kuwa zani ne da gyauton yafawa, watau gyale da kallabi da taguwa da ‘yan kunne da dutsen wuya watau tsakiya”. Magaji (1986) kuwa cewa ya yi, “Idan aka ga mutum da babbar riga da ‘yar ciki da wando za a sa a rai cewa Bahaushe ne, koda mutum ɗin kuwa ba Bahaushe ba ne ba.

Bisa haka, masana suka bayyana riga Aska-Takwas, Girken-Gwandu, Binjima, Kwaƙwata, Riga mai kwaɗo, Sace, Riga mai barrage, ‘yar madaka, Bulla fara da baƙa dukkaninsu kaya ne na maza. Mata kuwa kan sanya tufafi inrinsu: Zanin Gwandai, Duhun-saki, Bakurde, Adikko da sauransu.

TASIRIN ZAMANANCI AKAN SUTURA

Dangane da tasirin baƙin al’adu kan suturar Hausawa, A’ishatu (1991) tana cewa; Hausawa sun ɗauki tsarin suturun Turawa domin kuwa a yanzu suturun Turawa sun yi yawa a wajen Hausawa musamman matasa waɗanda su ne madogarar al’umma, kuma manyan gobe. Wannan shi ya sa suturun Hausawa na gargajiya suke neman ɓacewa wurin Hausawa matasa sai na Tarawa. Misali, yanzu in ka lura da Hausawa musamman matasa duk inda suke, sai ka tarar ko dai tsarin suturunsu tsarin ɗinkin Turawa ne ko kuma yadin ainihin saƙar, Turawa ne. Ɗinkin Hausawa ko yadinsu sai ƙalilan ne ake samu wajen Hausawa. Maimakon tsarin wadatattun suturun Hausawa da aka san su da su sai matsattsu irin na Turawa da yadinsu sun mamaye na Hausawa na gargajiya. Mai karatu na iya duba matsayin maganin gargajiya a wurin Bahaushe.

  Bayan baka, baƙin al’adu da suka shafi sutura sun kawo tufafi irinsu kwat, shat, siket da nek tayal, waɗanda ba su dace da al’adunmu ko yanayinmu ko addininmu ba (Zaruk, da wasu (2001). Akwai suturun maƙwabtanmu na kusa da na nesa waɗanda suka yi tasiri akan Hausawa. Daga cikinsu akwai tazarce, da agbada, da ashoke. Mata ma ba a bar su a baya ba, wajen sabuwar bakin tufafi, domin su ma sun samu tufafi iri-iri wadanda suka hada da: Sitella, Short play, Play, Follow me gayu, Baba na isa aure, Jahannama ga fasinja, Sa hannunka masoyi, Easy to rich, Fish, Tazarce, Kerewa, In ka isa duba, Kai ka kula, da dai sauransu.
MAGUNGUNAN GARGAJIYA NA BAHAUSHE

Maganin gargajiya shi ne yin amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle, don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata. Wannan sana’a ta magani ta bunƙasa a ƙasar Hausa, don haka ma da wuya a sami gari ko ƙauye wanda ba mai magani a cikinsa. Waɗanda suka fi shahara da wannan sana’a su ne malamai da bokaye.

Maganin gargajiya sana’a ce mai amfani don haka wasu sukan yanke mata saƙa, kamar bokaye da ‘yar maiganye, da ungozoma, da maharba, da malamai tsabibai. Wani lokaci, likitocin zamani ma sukan nemi taimakon waɗannan masu magani na gargajiya. Magungunan da suke yi kuma suna da yawa. Ga bayanin wasu daga cikinsu.

  1. Tsimi: Maganin da ake haɗa itatuwa ko kaucinsu musamman ko a yi garinsu ko sassaken jikinsu, ko a tsima su, ko a dafa su, a yi maganin cututtuka iri-iri da su kamar maganin ‘yar maiganye.
  2. Sassaƙe-Sassaƙe: Maganin da ake shiryawa don maganin shawara, da daji, da maganin dafi, da na hauka, da na tauri, da na hangun, da na ciwon hakori (haure), da ɗan kakkarai, da ciwon mata, kamar mele, da tunjere, ko ɗan birni, da ciwon bututu, da cirar gashi, da tunjiɓini, da tantanau, da gumurdu, da tottojiɓo, da sauransu.
  3. Turare: Maganin da ake turarawa, wanda ake haɗi da wasu itatuwa da hakukuwa, ko tsumma, ko gashi, ko sansami. Kuma ana yin turare don maganin fitar da maciji daga kogo, ko daga gida ko daga rami. Kuma da irinsa ake maganin hana maciji cizo, ko kunama ko munu-munu, da kamun namun daji. Kuma da irinsa ake kau da miyagu, da sauran irinsu.
  4. Kulle-Kulle da Tofe-Tofe: Maganin da ake yi da ƙulleƙkulle da tofe-tofe, da zare ko da tsirkiya, ko da jijiya, ko da gashi ko da ɓawon itace, da rataya su ga wuya, ko a kafaɗa. Kuma akan yi ƙulle-ƙulle da tofe-tofe a kafa a cikin gona, ko a gida, ko a ɗaki, ko a kasuwa, ko a yi ɗaurin ruwa, ko daji, ko ma mazakuta, ko wanin waɗannan.
  5. Tofawa da Shafawa: Maganin da ake haɗawa da tambaya da tofi da shafe-shafe, kamar maganin dori, ko ciwon kai, ko maganin haƙarƙari ko ta-ƙauye ko faɗuwar zuciya ko haƙora ko ƙarangashewar wani abu ga wuya ko ma ciwon farfaɗiya.
  6. Gashi: Maganin da ake yi da wuta ko da ƙarfe ko da ƙasa, kamar lalas, da ruwaye, da ƙyasƙyastu ko sakiya ko tuwon ƙasa ko kamun ta-ƙauye, da haƙarkari, ko kafi.
  7. Jiƙe-Jiƙe: Maganin haihuwa kamar maganin zaƙi ko faɗuwar uwa da saukin gwiwa da na ƙarfin jiki da na jini da maganin jinjiri saboda lafiyarsa.

Bayan haka ana yin magani gama-gari tahanyar jiƙe-jiƙe. Misali ana jiƙa toka don ɗankanoma da ɓacin ciki, Ana jiƙa kanwa, ko filasko, don ciwon ciki da wanke ciki. Kuma ana jiƙa maɗaci, da tsamiya, da lemun tsami da kayan yaji, don ƙarin mazakuta da maye, ko don ƙarin matuntaka da maganin ƙazuwa da ‘yan rani da kirci da ciwon hangun da sauransu.

  1. Jifa: Maganin ɓata wa wani rayuwarsa don son ran wani, kamar magani don a fitar da kishiya, ko don a naƙasar da wani, ko a karɓe amfanin gonar wani, ko a ɓata sarauta, ko ciniki, duka ta hanyar mugun dabo.
  2. Ajiya da Rataya: Maganin tsaraka kamar sa fure a cikin nono ko dawo don samun kasuwa ko a maƙala wani abu, don neman farin jini ko bashi, ko bi-ta-zai-zai, ko gamaɗiɗi, ko ƙifit.
  3. Siddabaru: Maganin siddabaru kamar maganin maita da ɗaukar abu mai nauyi da cika soro, da taɓo rufin shigifa da ƙafa, da rikiɗa kura ko mage ko maciji ko taiki, ko barin hannu, ko ɗora hannun da ya karye kamar wajen wasan kwaraya.
  4. Shashatau: Maganin shashatau, kamar ɓatar da abin noman wani, da mayar da mutum biri, da ɓatar da kan jinjiri, ko mazakuta; ko wanin waɗannan.
SANA’A DA MUHIMMANCINTA A WURIN BAHAUSHE

Sana’a, kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take ɗaukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance. Misali, sana’ar ƙira .

A gargajiyance, Bahaushe yana da sana’o’in da yawansu ke da wahalar ƙididdigewa. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai manya akwai kuma ƙanana. Sannan kuma masana sun kasa su zuwa kashi uku da suka haɗa da sana’o’in maza, sana’o’in mata da kuma sana’o’in haɗaka ko gamayya.

  1. Sana’o’in Maza

Sana’o’in maza su ne sana’o’in da maza zalla ne suka fi yinsu. Koda an samu mata a ciki to yawansu bai kai a misalta ba. Misali, sana’ar ƙira, fawa , da sauransu.

  1. Sana’o’in Mata

Sana’o’in mata kuma su ne sana’o’in da mata ne kawai suka keɓanta da yin su. Idan aka ga namiji a ciki irin waɗannan sana’o’i akan kira shi da ɗan’daudu. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai sana’ar kitso , dafe-dafen abinci, da sauransu.

iii. Sana’o’in Tarayya

Sana’o’in tarayya kuma su ne sana’o’in da maza da mata suka yi tarayya a ciki. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai kiwo , roƙon baka da sauransu.

NAU’O’IN SANA’O’I A KASAR HAUSA
  1. Sana’ar Wanzanci. 2. Sana’ar Kiwo.   3. Sana’ar Gini.    4. Sana’ar Dukanci.             5. Sana’ar Sussuka.         6. Sana’ar Fawa.    7. Sana’ar Noma      8. Sana’ar Sassaƙa.            9. Sana’ar Saƙa.             10. Sana’ar Kitso.     11. Sana’ar Ƙira         12. Sana’ar Jima.
  2. Sana’ar Rini. 14. Sana’ar Ginin Tukwane. 15. Sana’ar Arkomanci. 16. Sana’ar Farauta.       17. Sana’ar Su.
BUKUKUWAN HAUSAWA

Biki taro ne da ake yi a Kasar Hausa domin taya juna, ko wani, ko wasu murna wanda ake gudanar da shi a nishanɗance ta hanyar kaɗe-kaɗe, raye-raye, waƙe-waƙe, tanɗe-tanɗe, da lashe-lashe. Kenan, duk wani taro da ya haɗe waɗannan abubuwa guda huɗu ko wasu daga ciki, to kai tsaye za a iya kiransa da biki.

Akwai bukukuwa da dama da ake gudanarwa a Ƙasar Hausa. Amma waɗanda aka fi sani su ne; bikin aure, bikin suna, bukukuwan salla, bikin mauludi, bikin takutaha da sauransu.

Ɗangambo (1984), ya raba bubukuwan Hausawa zuwa rukunai guda biyu, wato akwai bukukuwan da suka shafi addini, da kuma bukukuwan da ba su shafi addini ba.

  1. Bukuwan da suka shafi addini

Waɗannan bukukuwa su ne bukukuwan da ake yi a lokutan da ake gudanar da wata hidima ta addini. Daga cikin irin waɗannan bukukuwa akwai bikin sallah ƙarama da sallah babba, bikin mauludi, bikin takutaha, bikin maukibi, bikin sallar gani da sauransu.

  1. Bukukuwan da ba su shafi addini ba

Waɗannan su ne bukukuwan gargarjiya na Bahaushe waɗanda suka haɗa da bikin aure, bikin suna, bikin shan kabewa, bikin naɗin sarauta, bikin hawan daba, bikin kaciya da sauransu.

BIKIN AURE A KASAR HAUSA

Aure alaƙa ce ta halascin zaman tare tsakanin namiji da mace (Habib, Usman, da Rabi’u, 1982). Ana yin aure domin abubuwa da dama, daga ciki akwai kariya daga zina, samun nutsuwa da kwanciyar hankali, samawa abin haihuwa (abin da aka haifa wato ɗa ko ‘ya) mutunci, da sauransu.

Akan samu bambance-bambancen al’adu daga yanki zuwa wani yanki a ƙasar Hausa . Amma akwai gama-garin abubuwa, waɗanda ko’ina ana yinsu.

Idan muka koma ta fuskar matsayi kuwa, aure a wurin al’ummar Hausawa abu ne mai matukar muhaimmancin gaske, ko ma a ce wajibi ne, domin kuwa babban abin kunya ne a ce mutum ya kasa yin aure ko aurar da dansa ko ‘yarsa.

A wurin kowane uba bai wuce a ce ya ga jikokinsa ba, kamar yadda iyaye mata suke da wannan buri, wannan ta sanya suke fara tanadin auren ‘ya’yansu mata tun yayin da suka fara tasowa, ma’ana alamun budurci suka fara bayyana a gare su.

Irin wannan muhimmancin ne ya sanya mata kan yi wasiyya da cewa, “Idan Allah bai kaddara kai ni ganin auren wance ba, to ga abu kaza a ba ta”.

A wurin maza kuwa, duk wanda ya isa aure amma ya ki yi, to ana kiran sad a ‘Tuzuru’, wanda ya taba yin aure kuwa amma wani sanadi ya kawo rabuwarsu, to shi ne ‘Gwauro’. Wannan ya sanya da zarar Bahaushe ya manyanta ya kai yin aure, to yake yin aure, domin gudun kiran sa da wadancan sunayen, ko kuma sauran tsokana da ake masa a tsakanin abokai da dangi. Daga cikin irin tsokanar da ake yi wa Gwauro, akwai wakar nan:

Na jej je ni gidan Gwauro,

An bab ba ni tuwon dusa,

Ban karba ba ina tsoro,

Tsoron me? Tsoron wani abu jan baki,

Jan baki sari koto, koton me?

Koton gidan Baraje,

Barajen da wa yake?

Yanko hannu mu je mu,

Mu je mu wacce rana?

Ranar yakin Kalele,

Kalele barbadin kuka,

Tumba masaki tumba haske.

IRE-IREN AURE A KASAR HAUSA

Al’ummar Hausawa na da ire-iren aure wadanda masana suka kasafta su ta hanyar la’akari da yadda ake gudanar da su. Cikin su akwai: auren fari, auren zumunta, auren sadaka, auren kisan-wuta, auren dauki-sandarka, auren takalmi, auren je-ke-da-kwarinka, auren buta.

MATAKAN AURE A KASAR HAUSA

Bah aka kawai ake kulla aure a Kasar Hausa ba, dole sai an bi wadansu matakai na al’adu da addinin da al’ummar Hausawan ke bi. Kafin a kai ga wadannan al’adun ma, dole sai an samu ma’aurantan guda biyu wanda su kuma a al’adance akan hadu ne a dandali, ko kasuwa, ko gidan ‘yan’uwa, ko gidan kawa, ko a yawon talla, ko a gidan biki, ko a wurin kalankuwa ko bukukuwan sallah da sauran wuraren da al’ada ta yarda mace za ta iya haduwa da da namiji. Daga cikin matakan da al’ummar Hausawa ke bi sun hada da:

  1. Bayyana soyayya. A nan akwai hanyoyi da dama, amma mafiya shahara a ciki su ne: Hanya ta farko ita ce saurayi ya ga budurwa yana so. Idan haka ta faru to ba shi zai yi mata magana kai tsaye da kansa ba, zai samu babban abokinsa wanda suka amincewa juna ya sanar da shi, idan shawararsu shi da abokin nasa ta yi daidai, to shi abokin nasa ne zai yi wa budurwar magana.

Ko kuma wani daga cikin su (saurayin ko abokin nasa), ya samu ƙawar budurwar ya gaya mata ita kuma ta isar da saƙon zuwa ga wacce ake so. Idan aka samu dacewa a tsakaninsu, to shi ke nan.

Hanya ta biyu kuma ita ce ta hanyar kamu: Kamu a neman aure shi ne idan iyayen yaro sun ga wata yarinyar da aka san gidansu mutanen kirki ne, sai su ce muna kamu ko mun yiwa wane kamu. Ta irin wannan sigar ce ake samun abokai maza ko ƙawaye mata su haɗa ‘ya’yansu aure.

Haka zalika, budurwa ma kan so saurayi, sai dai bisa al’ada ba za ta iya furta masa ba saboda kunya irin ta ‘ya mace.

Tare da haka, suna da wasu hanyoyi nasu na al’ada domin nuna soyayyarsu ga wanda suke so, wato ta hanyar wakoki a dandalin ko a gaban mai kalangu, sukan saki baki su bayyana abin dake cikin zukatansu. Daga cikin ire-iren wakokin akwai: Tama ta yi tama, da Iye Nanaye da sauransu.

  1. Kyauta, ita ce mataki na biyu a cikin neman aure. Ita wannan kyauta shi mai nema ko iyayensa ne ke kai kyautar gidan matar da za a nema. Irin kyaututtukan nan da ake byarwa suna da yawa, amma a dunkule wasu na kiran su ‘toshi’. Akwai toshin sauri, na gani ina so, kayan jin kira da toshin sallah.
  1. Gasa, bisa ga al’ada, duk budurwar da take da saurayi fiye da daya; to mai farin jinni ce, kuma samun hakan abin alfahari ne a kanta da danginta. Su kuma samarin da suka yi tarayya wajen son budurwa daya sukan yi kishi wanda hakan yakan haifar da gasa tsakaninsu.

Daga cikin irin gasar da suke yi akwai rawar kalangu a lokacin da makadi ko wani ya daure budurwa, kuma bisa al’ada bat a da ikon tashi daga gabansa. Ta wannan hanyar ce, wani cikinsu zai kunce ta da naira biyar, wani kuma y ace ya kara daure tad a naira goma, haka dai za a yi ta yi har sai wanda ya fi kudi ne zai fanshe tad a kudin da kowa ya gagara kunce ta ko daure ta.

  1. Fitowa, ita ce saurayi ya nuna wa iyayen yarinya da sauran jama’a cewa lalle yana sonta, wato ya turo magabatansa gidansu a yi magana. Akan tura wani cikin dangin saurayi kamar baffansa ko kawunsa domin ya je nemar masa auren. Haka akan tura mata ma kamar gwaggonsa, ko kakarsa, ko yarsa domin yin wannan magana. A irin wannan, akan hadawa da wasu kayayyakin kwalliya kamar: turare, man shafawa, hoda, jan-baki, gazal, takalma, zobe, warawarai, kamfai, ‘yan kwalaye, sai kuma ‘yan kudade kadan, wasu kuma kawai kudi suke kaiwa.
  2. Baiko, shi ne tabbatarwa da wanda za a bai wa yarinya aure cewa an bashi. Akan raba ɗan abin masarufi kamar irin su alewa da sauran su ga jama’a; musamman makusantan saurayin da budurwar, domin su sheda cewa an tsayar wa da yarinya mijin aure.
  3. Ada’a, ita ce godiyar da iyayen saurayi kan yi wa iyayen budurwa bayan an yi baiko, a nan akan tura wasu cikin dangin saurayi domin yin wannan godiyar. Bisa al’ada, akan je gidansu budurwar dauke da goro da wasu ‘yan kudade ba masu yawa ba; domin nuna murna da farin ciki.
  4. Saka Rana ko Tsayar da Rana, ita ce fitar da tsayayyiyar rana da za a daura auren saurayi da budurwa. Bisa al’ada mata ne ke sanya rana a Kasar Hausa, wato za a hadu da dangin saurayi da na budurwa a gidansu yarinya ko wata gwaggonta, a zauna ana kallon-kallo, karshe dai dangin saurayi su fara magana. A yayin sa-rana ma, akan hadowa da wasu ‘yan kaya kamar goro, alawa (minti), tabarma, kuɗi, da sauransu waɗanda kan bambanta daga wuri zuwa wuri.
  5. Tsirance, a nan saurayi ne zai gayyaci budurwa gidansu domin su kwana suna hira, wato hirar tsakar dare, amma sai bayan an sa-rana. Hausawa na yin haka ne domin a samu kyakkyawar dangantaka tsakanin saurayi da budurwa da kuma samun karin kauna. A irin wannan hira, babu wani abu da yake shiga tsakaninsu face wannan hira. Amma a yanzu wannan al’ada ta mutu a ko’ina a Kasar Hausa saboda dalilai na addinin Musulunci da kuma karancin gaskiya da rikon amana.
  6. Lefe, kayayyaki ne da ake haɗawa da suka shafi tufafi da kayan kwalliwa gwargwadon ƙarfin mai nema, a zuba su cikin lefe, daga baya ya koma fantimoti, ko kwalla ko akwatu. A wannan zamanin na yanzu kuma akwatu mai taya, a kai gidan su yarinyar da ake nema. Yawanci mata daga ɓangaren mai nema su suke kai waɗannan kayayyaki.

A zamanin baya, akan tara waɗannan kayan lefe na mutane da yawa, gwargwadon farin jinin yarinya. Daga ƙarshe kuma sai a zaɓi mutum ɗaya a aurar da ita gare shi.

  1. Ɗaurin Aure, shi ne babban ginshiki kuma kololuwa a harkar neman aure, wato daga an yi shi, komai ya kare sai ‘yan sauran guntattakin al’adu da ake yi a yayin wannan biki. Kafin zuwan addinin Musulunci a Kasar Hausa, akan daura aure ne ta hanyar taruwa maza da mata ana kade-kade da tulunan giya da kuma abinci. Bayan an ci an sha sai a kawo akuya a matsayin sadaki, da gishiri a raba wa dangi a matsayin shaida. Dagan an sai a ci gaba da kida; saurayi da budurwa su fito su taka rawa, ana cikin haka sai kawun budurwa ya shigo tsakiyar fili ya kama gefen zanin buduewa da gefen rigar saurayi ya daure, daga nan aure ya dauru.
       Amma zuwan addinin Musulunci, sai aka samu sauyi inda za a tara jama’a a ƙofar gidan mahaifin yarinya ko kuma waliyinta a daura, sannan a tanadi abubuwa kamar haka:
  1. Sadaki, kuɗi ne waɗanda iyayen yarinya ke ayyanawa a bisa ƙa’idar aure.
  2. Waliyyai, mutane ne guda biyu da ɗaya ke tsayuwa a ɓangaren yarinya (walin ‘ya mace), ɗayan kuma ke tsayuwa ta ɓangaren ango (walin ɗa namiji), waɗanda ke a matsayin wakilan ango da na amarya.
  3. Shaidu, su ne jama’ar dake taruwa don su zama shaidar cewa daga wannan rana wance ta zama matar wane.
  4. Siga, wato furucin bayarwa da na karba.

Har wa yau, akan kawo goro ana rarrabawa dukkan jama’ar da suka taru a wannan waje ne. Su kuma kuɗin akan ba wa walin ‘ya mace, malamai masu addu’a, da kuma abokan wasanta maza.

HANYOYIN TARBIYANTARWA DA WASANNIN HAUSAWA

              Kamar yadda al’ummar Hausawa take da tsare-tsarenta tun fil’azal wato ta fuskar shugabanci, auratayya, zamantakewa, bukukuwa da sauran al’amuransu haka suke da irin wannan tsari ta fuskar tarbiyyantar da yaransu da kuma wasannin su na yau da gobe wadanda suka rika a matsayin hanyoyin nishadi. Daga cikin hanyoyin tarbiyyantarwar akwai; tatsuniya da camfi.

1.Tatsuniya: – Tatsuniya wata al’ada ce ta Hausawa kanyi tatsuniya idan dare yayi daga an gama cin abincin dare. Yahaya da wasu (1992:7) sun bayyana tatsuniya da cewa, “Wani tsararren labara ne mai dan tsawo na hikima da nuna kwarewa da ya kunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilimin zaman duniya, sannan das aka nishadi da kuma cinye lokaci”. Tatsuniya tamkar makaranta ce a wurin al’ummar Hausawa, domin tana daga cikin hanyoyin da suke amfani da su wajen dasa gaskiya da rikon amana da jarumta a zukatan yaransu.

Hausawa sukan dasa kyawawan akidu da tarbiyyantar da yaransu da koyar da su muhimman al’amuran duniya da sanya musu jarumta a zukata duk a cikin tatsuniyoyi. Wannan ya sanya aka samu tarbiyya, hakuri, tausayi, kauce wa kwace da zamba da sata da gulma, biyayya, halaye nagari, wayo da dabara, nishadantarwa da sauransu duk a matsayin muhimman jigon tatsuniyoyin Hausa.

Masana sun bayyana game da inda ake yin tatsuniya, inda suka ce ana yin ta a gidan sabuwar amarya ko gidan wata tsohuwa, musamman lokacin wani aiki, ko kuma a tsakanin ‘yan mata ko yara. Akan yi tatsuniyar ce da daddare bayan an gama cin abincin dare. A wurin Bahaushe, ba a yin tatsuniya da rana, domin duk wanda ya kuskura ya yi, to zai yi makuwa ya kasa komawa gida. Amma idan ta kama sai an yi, to sai a daure gizo.

Ire-iren Tatsniyoyin Hausawa

Tatsuniya a wurin Bahaushe suna ta tara, domin yana da tatsuniyoyi mabambanta suka kasa su zuwa rukunai biyu kamar haka:

i.Tatsuniyar Gizo, irin wadannan tatsuniyoyin sun shafi labaran Gizo ne da matarsa Koki, wanda galibi Gizo kan fitowa a matsayin tauraro, wani lokacin cikin kyakkyawar siffa, wani lokacin kuwa mummuna.

  1. Sauran tatsuniyoyi, su ne dukkanin dangogin tatsuniyoyin da suka shafi mutane, dabbobi, tsuntsaye, aljanu, dodanni da sauransu.
  2. Camfi: – Masana sun yi bayani game da ma’anar camfi, misali: El-shamy (1976) ya ce “Camfi yarda ne ko amincewa, ko yin imani da wani abu a matsayin an gaskata shi tare da abubuwan da ya ƙunsa”.

Scott (1976) shi kuma cewa ya yi “Camfi shi ne, yarda ko amincewa da wani abu, ko aiwatar da wani abu, da aka gada, kaka da kakanni cikin duhun jahilci, saboda tsoro, ko nuna fargaba da abin da ba a amince da shi ba”.

Ɗangambo (1984:38) ya ce “camfi shi ne mutum ya ɗauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to ya gaskanta wani abu zai faru, sakamakon haka”.

Bunza (2006:58). Cewa ya yi “Camfi wata daɗaɗɗiyar al’ada ce da Hausawa suka tarar tun kaka da kakanni. Kuma masana da manazarta Hausa sukan yi wa camfi kallo ta fuskoki biyu, wasu na kallon camfi, al’ada ce kawai kamar irin kowace al’ada; a ganin wasu kuwa, abin ya wuce haka, ya kai matsayin addini daga cikin addinin gargajiyar Bahaushe”.

Hausawa sun dauki camfi irin yadda suka dauki tatsuniya, wato suna amfani da ita wajen cusa kwazo da jarumta da tarbiyya a tsakanin ‘ya’yansu. Daga cikin misalan camfin dake cusa tarbiyya a tsakanin Hausawa akwai:

1 Idan aka doki maciji da karan rama, za a ga kafafunsa, amma za a mutu.

  1. Idan yaro na cin ƙwai zai yi sata.
  2. Cin kan kifi na sa dushewar basira.
  3. Idan mace mai ciki ta tsallake rafi to za ta yi ɓari.
  4. Ketarar wando na sa mata yawan mafarki
  5. Kallon majigi ga mai ciki, kan sa a haifi yaro mahaukaci.
  6. Yin shara da dare na kawo tsiya (talauci).
  7. Idan mace mai ciki ta ɗebi ruwa a rafi da daddare, aljanu za su musanya ɗanta da nasu.
  8. Idan mutum ya yi hamma bai rufe baki ba, aljanu za su tokare bakin ya kasa rufewa.
  9. Idan fitsarin kwado ya taba mutum zai yi ciwon kuturta.
  10. Zama a turmi ko murhu yana karya magani.

Idan aka dubi waɗannan misalan, za a ga cewa camfe-camfen da aka kawo suna dauke da wasu sakwanni dake nuni ga tarbiya ko adana al’adu da nuna halayen kiwon lafiya a gargajiyance da rigakfi ko wanin wadannan.

WASANNIN HAUSAWA NA GARGAJIYA

Wasanni su ne dukkanin nau’o’in shagugula da ake gabatarwa a wani dandali na musamma ko kuma a gida domin samar da nishadi da karsashi a jika ko kuma sanya annashuwa. Akwai wasanni da dama da al’ummar Hausawa suke aiwatarwa a lokuta mabambanta, misali; Wasan Gauta, Wasan Kalankuwa Wasan Dambe, Wasan Kokawa, Wasan Waza, Wasan Tashe, Langa, Wasan ‘yartsana da kuma sauran wasannin da yara ke yi da daddare da kuma wanda ‘yan mata ke yi.

Shfin farko

labarin da ya wuceYadda Ake Faɗar Ina Ƙaunar ki/Ka A Soyayya.
Labarin na GabaASALIN ƘASAR HAUSAWA

SHARHI ƊAYA

An rufe yin sharhi