An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An ba da umarni a yi wa wani bawan Allah bulala ɗari a cikin kabarinsa, sai ya yi ta roƙo yana addu’a a yi masa afuwa har sai da ta dawo bulala ɗaya.
Da aka shaula masa sai kabarin ya cika da wuta ya suma. Da ya farfaɗo sai ya ce: “Shin akan me kuka zane ni?” Sai ya ce: “Saboda ka taɓa yin sallah ba ka da tsarki, kuma ka taɓa wuce wani ana zaluntarsa ka ƙi ka taimaka masa”.
Abus Shaikh Ibn Hayyan ne ya rawaito shi a cikin Littafin Attaubikh.
Ƙarin Bayani
Lallai ne a taimakawa waɗanda ake zalunta a ƙwato musu haƙƙinsu, wannan nauyi ne akan hukumomi da ɗaiɗaikun mutane, kada a bar zalunci ya yi ta tafiya har ya zama jiki, sai fushin Allah da azabarsa su shafi kowa.
Shi ma azzalumi a taimaka masa ta hanyar hana shi aikata zalunci da hukunta shi da kuma toshe dukkannin ƙofofi da hanyoyin da duk dama da yake yin zaluncin.
Domin karanta cikakken bayani akan Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.
Edita; Rumasa’u M. kallamu