Hanyoyin Farfaɗo Da Tsangayun Alƙur’ani

0
39

Kamar yadda muka gani a sashe na ɗaya babi na ɗaya cewa, a da tsangayun alƙur’ani suna da gata da wasu haƙƙoƙi cikin baitul malin hukuma. A lokaci guda kuma malaman alƙur’ani suna samun ayyuka a hukuma.

A lokaci guda kuma al’amarin da yaba su ƙima da yalwar rayuwar har suka bunƙasa suka yaɗu. Sai daga baya suka rasa gata a lokacin da bature ya zo ya dagula lissafin waɗannan tsare-tsare, ya kawo nasa ya dasa a matsayin kishiya bora da mowa. Ana nan har sai da tsangayu da malamansu da almajiransu suka zama abin tausayi marasa gata cikin al’umma.

Malamai da wasu masu kishin addini, kai a waɗansu lokuta ma har ƙungiyoyin turawa kan nuna damuwarsu game da irin halin da tsangayun alƙur’ani da almajirai ke ciki. An gabatar da tataunawa da tarukan ƙarawa juna ilimi a wurare daban-daban cikin mabambantan lokuta, da niyyar tsamo wasu tsangayun ko almajirai daga irin matsin rayuwar da suka samu kansu aciki.

Irin wannan yunƙuri ya haɗa da yunƙurin shirin bayar da ilimin firamare na duniya (UBE) da ƙungiyar haɓaka musulunci da ke Kano (IDN) da hukumar ilmantar da malamai (NTI) da asusun agazawa ilimi (ETF) da hukumar ilimin manya ta ƙasa (NMEC) da cibiyar binciken ilimi ta arewa da ke arewa house (NEPR) da jami’ar Ahmadu Bello zariya da wasu daga hukumomin majalisar ɗinkin duniya kamar su Hukumar kula da yara da ilmi da abinci ta Duniya (UNICEF da UNESCO).

A matakin gwmnatoci kuwa an samu wani makamancin wannan hoɓɓasa daga wasu gwamnatocin jihohi na Arewa misali jigawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina da Bauchi.

An kafa hukomomi a waɗannan jihohi don kyautata waɗannan makarantu, galibi da sunan Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Muslunci (Arabic and Islamic Education Board). A Kano kuwa abin sai alasan barka.

Duba ga irin yadda gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta rungumi makarantun Alƙur’ani da niyyar dawo musu da haƙƙoƙinsu a hukumance kamar yadda abin yake a tarihinmu. Don ƙarin haske sai a nemi ƙudirin gwamnatin Shekarau kan cibiyar ilimin addinin Musulunci “Action Plan” wadda aka ƙaddamar a ranar 23 ga watan Oktoba, 2003. Mai karatu zai iya fahimtar hanyoyin farfaɗo da tsangayu da raya su ta fuskoki biyu bisa matakai biyu cikin abin da ya gabata kamar haka:-

1. Yunƙurin ƙungiyoyi da cibiyoyi masu zaman kansu.
2. Yunƙurin wasu daga ciki gwamnatocin jihohin Arewa.

Babbar matsalar mataki ko yunƙurin farko wanda ƙungiyoyin da na ambata a baya suka yi shi ne, mafi yawa sun tafi akan lallai sai an haɗe tsarin karantu tsangaya da ilimin zamani (integration).

Wannan tunani yana da wuyar ɗabbaƙawa kuma yana da haɗari ga makomar karatun Alƙur’ani mai inganci irin na tsangaya.

Kada mai karatu ya manta da cewa mafi yawan ƙungiyoyin gwamnatin tarayya da Turai suna kallon tsangaya a matsayin tushen bautar da yara ƙanana da wulaƙanta su (Child Abuse/Child Labour) wanda ya kamata a magance ta hanyar haɗe su da makarantun firamare na hukuma. Malaman Alƙur’ani kuwa a nasu ɓangaren su ba sa son sallama makarantarsu ɗungurungum ga wata hukuma.

Irin wannan ra’ayi ne ya hana da yawansu haɗa fannonin ilmi Musulunci irin su Fiƙhu, Hadisi, da Tafsiri da karatun Alƙur’ani. Tunanin makaranta Alƙur’ani a tsarin tsangaya ya ginu bisa inkarin gwamnati da tsare-tsarenta. Saboda a ganinsu ta hanyar ta ne aka kawo karatun boko wanda turawa ‘yan mishan suka juyar da musulmi da yawa zuwan addini kirista, musammam ‘yan ƙabilar yarabawa.

Wannan yasa da yawan makaranta yin ƙaura da almajiransu zamanin turawa don kada a tilasta musu shiga tsarin karatun boko. Baya ga wannan kuma, mu ɗauka an haɗe tsangayunmu na Alƙur’ani a tsarin koyon karatu da lissafi cikin ilimin firamare.

Shin mene ne makomar irin fa’idojin da tsangaya kaɗai muke samu irin su baiwar rubutun alƙur’ani da ka da ingantacciyar tilawa? Yaya za mu yi da jama’armu musamman a karkara inda babu wadatattun makarantun boko kuma ba masu son sanya ‘ya’yansu a makarantun bokon?

A ganina in har kundin tsarin mulki zai ba wa ‘yan ƙasa damar zaɓen tsarin rayuwarsu da abin bautarsu, to mai son karatun tsangaya ya fi cancantar a ba shi dukkan tallafi ya yi karatunsa cikin yanayi mai inganci ba tare da an tursasa shi kan abin da ba ya so ba.
Su kuma gwamnatocin jihohin Arewa da suka nuna kishinsu ga wannan ɓangare na tsangaya sai mu ce sambarka.

Amma akwai sauran aiki domin kuwa in har ana son farfaɗo da tsangayun Alƙur’ani da raya su dole ne a dawo musu da martabarsu ta hanyar:-

1. Juyin-juya Hali a Ɓangaren Ilmi Jihohin Arewacin Najeriya:-

Ma’anar wannan shi ne samar da wani ƙudirin siyasar ilmi a jihohin Musulmi da ke Arewacin Najeriya Wanda zai ayyana ilmin tsangaya a matsayi ɗaya da karatun boko, tare kuma da yin doka a majalisa ko kuma ta kowace hanya da ta dace don ɗorewar ƙudirin.

2. Samar da daidaito ga Tsangayun Al-ƙur’ani Cikin Dukkan Haƙuƙuwan da Gwamnati ke ba wa Ilmin Zamani:-

Babu shakka kowace irin damuwa muka nuna game da ingantuwar tsangayun Alƙur’ani da kyautatuwar rayuwar almajirai, hakan ba zai yi tasiri ba har sai tattallin arzikinsu ya bunƙasa. Ma’ana rayuwarsu ta samu gata tabbatacce maimakon gutsura musu ɗan wani abu da bai taka kara ya karya ba.

Idan har za a daidaita tsangayu da sauran sassan ilmin zamani to dole gwamnati ta dubi dukkan fuskokin da take tallafar ilmin boko, tun daga albashin malamai da gina sababbin makarantu, da gyara waɗanda suka lallace da kuma irin ciyarwar da ta ke yi wa ‘yan makarantar kwana da irin kayan aikin da take ba su.

Jimillar waɗannan kuɗaɗe su ya kamata a duba wajen ba wa tsangayu buƙatunsu na rayuwa. Wani abu mai ban sha’awa shi ne ma’abota tsangayu mutane ne da abin duniya bai shamakance idanuwansu ba. Matuƙar hukuma ta kula da matsuguninsu da abincinsu da ‘yar buƙatarsu ta yau da kullum, to kuwa za ka ga an magance wani kaso mafi girma daga matsalolinsu.

Don haka, irin matakan da gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta ɗauka a Kano wani abin koyi ne ga dukkan gwamnatocin Arewa.

Domin karanta cikakken bayani akan Matakan Farfaɗo Da Tsangayun Alƙur’ani Da Raya Su danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Zubin Tsangaya Yake danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceFassarar Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai Alfarma 7th February 2025
Labarin na GabaTarihin Sheikh Muhammad Barnoma