Halittar Lokaci Da Ƙarewarsa

0
1043

Halittar lokaci da ƙarewar sa, duk yin Allah ne. Ƙudurar Ubangiji kaɗai, ita ce mai wanzuwa. Domin kuwa tun farko babu jiya babu yau, ba nan ba can, babu gaba ba baya. Ba a san nesa ba, bare kuma kusanci, ƙamshi ko wari babu su, dare da rana babu zuri’arsu, lissafi da kwatance ba mai tunanin su. Domin babu sama ba ƙasa ba halitta.

Sai Allah (Subahanahu Wa Ta’ala) ya halicci sarari da lokaci, sannan ya samar da halittu da rayuwa da mutuwa da kuma ma’aunin ayoyi masu ƙarfafa wannan ma’ana:

“Sannan Ya daidaita zuwa ga sama, alhali kuwa ita (a lokacin) hayaƙi ce, sai ya ce mata, ita(sama) da ƙasa ku zo bisa ga yarda ko a kan tilas, suka ce “Mun zo, muna ɗa’a”. Sura, Fussilat-Aya 11.
Wannan aya tana nuna farkon halittar sarari (space) tun a farkon al’amari.

Daga nan kuma halittu suka bijire da matsuguni. Kamar yadda Ubangiji maɗaukaki ke faɗa dangane da farkon halittar Annabi Adamu a lokaci yana cikin Aljanna da matarsa Hauwa’u: “Kuma kuna da matabbaci da ɗan jin daɗi ya zuwa wani lokaci a bayan ƙasa (doron duniya)”. Sura Bakara Aya 36

Rayuwa ɗan-Adam a doron ƙasa ba za ta yiwu ba, ba don Ubangiji ya hore ta gare shi ba. Ubangiji na cewa: “Kuma ya hore muku rana da wata dauwamammu da kuma dare. Kuma ya ba ku dukkan abin da kuka roƙe shi. Da za ku ƙirga ni’imomin Allah (Maɗaukaki), da  ba za ku iya ƙididdige su ba “. Sura-Ibrahim:33-34

Domin Karanta Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe Danna Nan

Ubangiji Maɗaukaki na cewa:
“Shi ne wanda ya sanya rana mai haske, wata kuma mai haskawa. Ya gwargwaje shi a masauki don ku san ƙididdigar shekaru da lissafi. Allah (Maɗaukaki) bai halicci wannan ba sai don gaskiya yana rarrabe ayoyi ga mutane masu sani”. Yunus-Aya 5

Saboda Ƙimar lokaci kuwa, Ubangiji maɗaukaki ya yi rantsuwa da shi a wurare da yawa cikin Alqurani:

(Ina) rantsuwa da lokaci (zamani)…………………..
(Ina) rantsuwa da alfijir…………………………….
(Ina) rantsuwa da lokacin walaha……………….
(Ina) rantsuwa da Dare……………………………

Malaman tafsiri na cewa, idan Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da wani abu, to akwai ishara zuwa ga irin girman wannan al’amari da tasirinsa da amfaninsa. Lokaci na shuɗewa ne ta yadda mutum ba zai ankara ba har sai ya zagayo, wata ya wuce, shekara ta zo ta tafi.
Wani mai hikima na cewa:

Ɗaya ta wuce biyu ta biyo ta,
Uku na nufin cin diddigenta,
Hudu ko kamar na rarako ta,
Zancen ya shekara ba wuya.
Ka san da ranar haihuwarka,
Yau ga shi ka zama ɗan gidanka,
Domin gudu nata duniya.

Ka lura da kyau daga ƙuruciyarka zuwa yau ɗin nan, za ka ga kamar mako ne ya wuce. Babban misali a nan shi ne: ɗaukar ciki da haife shi. Yaye da shayi game da karatun firamare da sakandare tare da kammala ilmin jami’a. Ga shi yau har ka yi aure ka zama magidanci. Ashe dai lokaci gudu yake yi amma ba mai gani sai mai idanuwan zuciya da lura.

Lokacin Rayuwa tamkar zaren kaset ne. Lokacin rayuwa ga kowannenmu, ya danganta da irin yadda Ubangiji Maɗaukaki ya ɗebar masa. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam) na cewa “Rayuwarmu shekaru sittin ko saba’in ce, kaɗan ne ke wuce wannan”.

Mu ɗauka wasu za su kai shekaru casa’in wasu ɗari. Wasu kuwa talatin wasu arba’in ko  hamsin da sauransu. To ka ga kuwa rayuwarmu tamkar kaset ne mai 60 ko 70 ko 90 ko 100 ko 30 ko 40 ko 50 gwargwadon yawan shekarun da aka ƙaddara mana, ba daɗi ba ragi.

Da zarar an haifi jariri sai kaset ɗin rayuwarsa ya fara naɗe bayanan motsinsa da ayyukansa masu kyau da munana. Hatta minshari da kaki da ihu da ashariya da kuma ibada, kaset ɗin zai cigaba da juyawa cikin zaren lokaci ba tsayawa.

Ruwan mutum ne ya kama tasbihi ko karatun Alƙur’ani ko barci ko ya shiga kakaci da batsa, kaset ba zai tsaya ba. Kuma ba zai dena naɗewa ba har sai ya je ƙarshe. Da ya je ƙarshe kuwa, mutum zai bar duniya ko da shiri ko ba shiri. Jama’a mu lura a kowanne lokaci zaren rayuwarmu ƙarewa yake yi, kullum cikin daƙiƙa. Mu ribaci lokutanmu, domin in ya tafi ba zai dawo ba.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Ubangiji Maɗaukaki Na cewa: “Lallai ajalin Ubangiji Maɗaukaki in ya zo ba a jinkirta shi. Da kun sani (hakan)”. Surah Munafiƙun-Aya-11

Game da gaggauta ayyuka nagari kuwa Ubangiji Maɗaukaki na cewa:
“Ku ciyar daga abin da muka azurta ku, tun kafin mutuwa ta zo wa ɗayanku”. Sannan ya ƙara da cewa, “Ubangijina ina ma ka jinkirta mini zuwa wani ɗan lokaci na zamo cikin nagartattu.”

“Allah (maɗaukaki) ba ya taɓa jinkirta wa wata rai idan ajalinta ya zo. Kuma Allah (maɗaukaki) mai ba da labari ne game da abin da kuke aikatawa”-Sura Munafiƙun: Aya 10

Ƙimar Lokaci a Rayuwar Ɗan Adam

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassalam) ya ce: “Ka ribaci abubuwa biyar kafin abubuwa biyar (su zo):

  1. Ƙuruciyarka, kafin tsufanka
  2. Lafiyarka, kafin rashin lafiyarka
  3. Wadatarka, kafin talaucinka
  4. Faragarka, kafin shagaltuwarka
  5. Rayuwarka, kafin mutuwarka

Bugu da Ƙari, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam) ya ce:” Ƙafafun ɗan-Adam ba za su gushe ba a ranar alƙiyama har sai an tambaye shi game da abubuwa huɗu:

  1. Rayuwarsa, ta yaya ya ƙarar da ita?
  2. Ƙuruciyarsa, ta yaya ya tsofar da ita?
  3. Dukiyarsa, ta ina ya same ta, kuma ta yaya ya kashe ta.
  4. Ilminsa, yaya ya yi da shi?

Akwai hadisin da Bukhari ya ruwaito Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam) ya ce: “Ni’imomi biyu ana yi wa mutane da yawa kamunga a cikinsu”. Ma’ana suna tozarta su cikin abinda ba zai bayar da amfani ba. Lafiya da samun dama”.

Yadda Musulmi Zai Ribaci Lokacinsa Na Rayuwa

Kwaikwayon Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam) a dukkan fuskokin rayuwa. Kasancewar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam) shi ne mafi cikar mutane wajen kamala da tsoron Allah Maɗaukaki, kuma ya fi kowa sanin lokaci da yadda za a ribace shi.

Sai rayuwarsa ta zamo cike da abubuwa masu amfani, kuma masu kusanta mutum zuwa Ubangiji Maɗaukaki. Babu wani motsi ko minti a rayuwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) wanda bai yi wa dabaibayi da ayyuka nagari ba.

Tun daga wayewar gari har zuwa kwanciya, akwai nau’ikan zikiri da nafiloli da ayyuka nagari da yake yi. Cin abincinsa, sanya tufafinsa, ƙailulansa da barcinsa duk ibada ne, domin yana yin su bisa yadda Ubangiji Maɗaukaki yake so a yi. Zikirin safiya da maraice duka ɓangare ne na rayuwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

Mai ƙoƙarin bin koyawar Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) da ɗabbaƙa su cikin awoyi 24hr a kowace rana babu shakka zai fi kowa cin ribar lokacinsa.

“Tirmizi ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi bn Umar cewa: Akan ƙidaya (istigfarin Annabi) (Sallallahu Aaihi Wassallam) a zamansa guda (tsakanin sahabbansa) kafin ya tashi sama da sau 100 yana cewa:
“Ya Ubangiji ka gafarta min, ka karɓi tubana, domin kai ne mai yawan karɓar tuba kuma mai yawan gafara”.

Duk motsin da Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) zai yi akwai nau’in zikirin da yake yi idan ya farka daga barci, ko zai sanya tufafi ko zai fita daga gida ko zai shiga. A halin tafiya, yayin hawa ko gangara. In ya sha. Idan Iska ta taso, ko ruwa ya sauka ko an yi tsawa ko sabon wata ya kama. A yayin da wasu al’amura suka wuyata ko kuma yayin haɗuwa da abokan gaba ko  kuma magauci. Da zikirin shiga kasuwa ko hawa ko sauka a wani gari.

Don neman ƙarin haske game da irin addu’oi da zikiran Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) cikin awoyinsa 24hr, sai a nemi littafin Hisnul Muslim ko a duba Zadul Ma’ad na Ibnul Kayyim ko kuma Alkalimuddayyib na Shehul Islam ibn Taimiya.

Game da sauran ayyukan ibada kuwa, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ce “Wanda ya yi sallah raka’a goma sha biyu ta nafila, to za a gina masa gida a Aljannah da su”. Kuma ya yi wa Abu Huraira wasiya da kar ya bar azumtar kwanaki uku na kowanne wata da yin sallar walaha da kuma wuturi.

Wanda duk ya bar kwaikwayon rayuwar Annabi (Sallallahu Alaihi Wassallam) ya saki reshe ya kama ganye. Domin rayuwarsa ba za ta cika da ayyukan ba.

Shagaltuwa Da Yin Da’awa

Kasancewar da’awa sana’a ce ta Annabawa, don haka duk ƙoƙarin umarni da kyawawan aiki da hana munana ko kira ya zuwa Ubangiji Maɗaukaki zai sami matsayin da babu irinsa.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ce: “Wanda ya nusar da wata sunna kyakkyawa to yana da ladan wanda ya aikata ta”. Kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ce: “Ubangiji ya shiryi mutum guda ta hanyarka, shi ya fi maka daga jajayen raƙuma”. Imamun Nawawi ya ce, “Jajayen raƙuma na nufin dukkan wata dukiya mai daraja”.

Sauran ayyukan da ya kamata a ribaci lokaci da su sun haɗa da:

  1. Kawar da abu mai cutarwa a hanya.
  2. Amsa sallama da yawan yin ta.
  3. Sada zumunci.
  4. Karatun Alƙur’ani.
  5. Nuna kyawawan ɗabi’u.
  6. Yin jihadi don Allah Maɗaukaki.
  7. Bin iyaye.
  8. Kaiwa da komawa don biya wa mutane buƙata.
  9. Kirdadar lokuta masu falala don yin ibadu ciki, kamar goman farko na Zul-hijja, ranar Arfa da daren lailatul ƙadri da sauransu
  10. Yin sadaƙatuj jariya kamar gina masallaci da tona rijiya ko koyar da ilmi da yi wa ‘ya’ya tarbiyar Musulunci.
  11. Neman halak da kyautatawa iyali da sauransu.

Imamu shafi’I na cewa, “Da ba a saukar da wata sura a Al-ƙur’ani ba sai suratul Asr, da ta isa mutum ya samu tsira da ita”.
Ma’ana kada mutum ya sake rana ta hudo ta faɗi, ba tare da ya yi ayyukan da wannan sura ta zayyana su ba. Domin kuwa rashin yin su, na nuna ɗan-Adam ya yi asara cikin wannan rana. Wannan ayyuka sun haɗa da:

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

  • Imani da yin ayyuka nagari.
  • Yin wasici da gaskiya.
  • Yin wasici da haƙuri.

Baihaƙi ya ruwaito cewa sahabban Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) sun kasance idan suka haɗu ba sa rabuwa har sai ɗaya ya karantawa ɗaya suratul-Asr.

Dole ne musulmai su kiyaye abubuwa masu ruguza ayyuka don su tsira da ribarsu ta ayyuka nagari cikin lokutan rayuwarsu. Waɗannan ayyuka sun haɗa da:

  1. Shirka da tsafi da duba da roƙon aljanu ko kuma amsa umarnin su, bai wa wani abin halitta haƙƙin mahalicci da sauran dangogin shirka.
  2. Riya.
  3. Laifukan harshe.
  4. Kallon haramun.
  5. Jin haramun.
  6. Cin dukiyar maraya.
  7. Neman abinci ta hanya haramtacciya.
  8. Cin amana.
  9. Kisan kai.
  10. Zina.
  11. Luwaɗi.

Domin karanta cikakken bayani a kan kada harshe ya gushe da ambaton Ubangiji danna wannan koren rubutun

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan 

labarin da ya wuceAbubuwan Da Za su Taimaka wa Mutum Wajen Tsara Lokacinsa
Labarin na GabaNazarin Wasu Dokokin Tsarin Sautin Harshen Hausa