Gangliyon Sist [Ƙarin Mahaɗar Ƙashi]

0
37

Ganglion cyst a kimiyyance wani Ɗan kumburi ne da wasu kan ambata da ƙari, ɗan ƙarami da galibi aka fi ganinsa a bayan hannu saitin wuyan hannu wato [wrist joint].

Galibi Ɗan qullutu ne, baya zafi, ba kuma ya hana mun mutum sakewa, hasali ma inba kazo shafa mai ko wani abu ba kakan manta dashi. Saide akan sami kaso kaɗan da nasu kan musu zafi, amma de kaso 90% baya zafi, bakuma ya hana komi.

MEKE HADDASA SHI

Yana faruwa ne idan ruwan grease ɗin guiwoyin jikinmu wato “synovial fluid” dake taimakawa guiwoyi ko dukkan inda ƙashi ya haɗu da ƙashi wajen tafiya da lankwashesu batare da jin zafi ko tauri ba… Ya zamto ya sami wata yar ƙofa ya ziraro daga cikin guiwar zuwa ƙasan fatar mu… inda yakan Ɗan taru sai ya bada wannan tundun da wasu kan kira da ƙari. Shiyasa duk inda ka gansa zaka samu kan guiwa ne wato mahaɗar ƙashi. 

Galibi yawan amfani da hannu ta hanyar aiki kamar masu Sana’ar bubbuge-bubbuge ahankali sukan ga girmansa na qaruwa, amma in ba’a komi da hannun ko yawan aikin karfi za’a ga baya wani qara girma.

Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

Shi irin wannan ƘARIN na iya bayyana ako ina walau guiwar hannu, kusa da idon ƙafa, saman ƙafa, ko wuyan hannu ta ciki. Saide galibi anfi ganinsa a bayan wuyan hannu wato dorsum of hand kamar yadda kuke gani a hoton kasa. An kuma fi yawan ganinsa a MATA saboda yawan aikace-aikacen gida, wanki, shara, girki, wanke-wanke ds.

Galibi likita baya bukatar gwajin komi kafin ganesa.

MAGANI

Ana iya barin sa batare da yi masa komi ba matukar baya damun mutum. Wasu da kansa yakan baje musamman in basa wani yawan aikin sarrafa hannu, wasu kuma mammatsashi yau da gobe kansa ya baje tunda dama ruwa ne. 

Hakazalik saboda kwalliya ko a wadanda yai girma sosai ana iya sa babbar allura me girman baki a zuqe saboda a tikke ruwan yake me ƙaurin gaske. Saide galibi bayan anzuqe yakan iya kuma dawowa a wasu ma har yafi nada girma.

Don magance baki daya shine likita yakan danyi allurar kashe zafi ya yanka gun ya zaresa cikin kwansonsa baki daya a maida bandeji a manne, shikenan an rabu.

Kamar yadda nace inbaya damun ka/ki ana iya barin sa kuma bakomi.

Karanta bayani akan Damar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata

labarin da ya wuceDamar Samun Da Na Miji Ko Diya Mace Ga Ma’aurata
Labarin na GabaPeptic Ulcer Diseases