Bayanin Mafi Yawancin Kwanakin Jinin Biƙi

0
468

Shin nawa ne mafi yawancin kwanaki na jinin biƙi?

Jinin Biƙi – An karɓo daga Ummu-Salama, Allah ya yarda ita, ta ce:

“Mai jinin biƙin ta kasance tana zama a lokacin Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; tsawon kwanaki arba’in”.

Kuma Imam Tirmizi, Allah ya jiƙan sa, ya ce: Haƙiƙa malamai da sahabbai da tabi’ai da waɗanda suka biyo bayansu, sun haɗu a kan cewa:

“Haƙiƙa mai jinin biƙi tana barin salla tsawon kwana arba’in, sai dai, idan mai jinin biƙin ta ga tsarki kafin haka; to haƙiƙa za ta yi wanka ta yi salla”.

“Idan ta ga jinin bayan kwana arba’in, haƙiƙa mafi yawancin malamai sun ce: “Ba za ta bar sallah ba bayan kwana arba’in”. Kuma shi ne maganar mafiya yawancin Malaman Fiƙihu.

Sai iyakacin kwana arba’in ya kasance shi ne galibin yawancin kwanakin jinin biƙi.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Darasi Na Shida Game da Hukunce-Hukuncen Jinin Haila da na Biƙi danna nan.

Don karanta cikakken bayani a kan Duhun Kan Mace Mai Gaba da Kisihiya. danna nan.

labarin da ya wuceAmbaton Abin Da Ake Sanin Zuwan Jinin Al’ada Da Shi Da Yankewar Sa
Labarin na GabaHukunce-hukuncen Jinin Haila Da Na Biƙi