Ummulkhair Sani Panisau
DOYA DA SOUCE ƊIN KWAI.
ABUBUWAN BUƘATA;
DOYA
ƘWAI
TUMATUR
ALBASA
LAWASHI
ATTARUHU.
YADDA AKE HAƊAWA:-
Hajajju ki zage ki burge mai gida ba kullum cima guda ba ko kullum. Doya da miya ba, a a dinga canja salo.
Da farko ki feraye doyarki , ki wanke tas ki ɗora a tukunya ki zuba ki saka ɗan gishiri ki sa ruwa ki ɗora. Za ki dafa doyarki ta yi laushi amma bai tuɓus ba. Sai ki samu ƙwanki ki fasa a cikin bowl mai zurfi ki sa maggi a ciki ki kaɗa. Ki samu koren wake da peas ki dafa ki zuba a ciki za ki iya saka attaruhu kaɗan ba yaji sossai ba ya danganta dai da yadda kike son yaji.
Ki samu frying pan ki zuba mai in ya yi zafi ki ɗauko ƙwanki ki zuba a kai ki sa cokali ki dinga juyawa ya farfashe kina juyawa sai ki zuba wannan vegies ɗin a kai kina juyawa sai ya soyu sai ki kwashe ki ci da doyarki. Hajiya a ci daɗi lafiya.
Danna nan don karanta Chinese Rice
Edita:@rumasau-kallamu