Dangantakar Harshe da Waƙa

0
548

Harshe da Waƙa – Harshe wani muhimmin sinadari ne wanda al’umma take bayyana al’adunta da hali na zamantakewarta. Mutane a ɗaiɗaya ko a rukuni ko a ƙungiya na isar da muradansu a rayuwa ta hanyar harshe.

Idan aka dubi kowace irin al’umma ko ƙabila za a ga tana da harshe nata; wanda take amfani da shi a matsayin harshen sadarwa.

Harshen Hausa, harshe ne wanda yake sarrafa ƙwayoyin sauti cikin gaɓoɓi da kalmomi da jumloli; ya shirya magana wadda za ta ƙunshi wata ma’ana ko saƙo; wadda idan an sadar da ita, mai sauraro yake ji, ya fahimta.

Ɗantumbushi (2012: 37); ya nuna harshen Hausa yana girma da ɗaukaka da faɗaɗuwa a cikin shuɗewar lokuta. Wannan harshe na Hausa yana kuma da karuruwa (Ɗantumbushi, 1998 & 2004; Amfani, 2011), musamman yana da karin gabas da karin yamma; waɗanda sukan sami bambanci ta hanyar sauti da kalmomi da siga ko tsari na gina jumloli da sauran wasu sassa na nahawu.

Karuruwan Hausa

Karin Gabaci Karin Yammaci

Kananci – Sakkwatanci
Dauranci – Garewanci
Zazzaganci – Katsinanci
Bausanci – Gobiranci
Gudduranci Kurfayanci
Zamfaranci
Arewanci

Makaɗin Hausa ya ɗauki harshen Hausa abokin hulɗa, ta haka harshen ya zama mai tagomashi a gare shi; wanda yake aiki da shi a kowane lokaci ba tare da wata tankiya ba. Makaɗi yakan iya fyauce hankali da tunanin mutum a yayin da ya sarrafa harshe bisa tsari da yanayi na waƙar baka. Harshe yakan haɗa hulɗa tsakanin makaɗa da jama’a ba dangi na iya ko na baba.

Alan waƙa ya amince da harshen waƙa, harshe ne mai shigar kutse a cikin zukatan jama’a. Ga abin da ya ce:

Jagora : Hikkima ba ruhi ko jiki ba hangena,
: Ba aibn kallo ko ɗauki duba tuna,
: Hikkima ba Rauhanai ka bai ba dangina,
: Hikkima Ilhamiyya nake karatuna,
: Jakadiyata waƙa mai tafi da saƙona,
: Jakadiyata ba ƙwuya a aika saƙona.

Makaɗan baka sukan yi amfani da harshe a bisa wasu mabambantan halaye. Harshe yakan zama zubi na mutum, makaɗi; tun ma ba idan aka yi la’akari da yadda tunani yake ginuwa a ɗayan-ɗayan mutane ba. Haka kuma nauyin ilimi da yin nutso a falsafa da fasaha; da wayewa kan sanya hanyoyin amfani da harshe a wajen makaɗa su bambanta (Alhassan, 2012: 128).

A lokacin da makaɗi ko mawaƙi yake shiryawa da aiwatar da waƙa shi yake da mulki da harshe; baiwa da azanci da zalaƙa suna yi wa mai waƙa, makaɗi, jagora a zubi na waƙa (Yahaya, 2012: 233).

Kila wannan harshe na waƙa mai kaifafa ma’ana ya sanya waƙa take saurin isar da saƙo; da fitar da ma’ana a cikin kalmomi ƙalilan.

Domin karanta cikakken bayani akan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan.

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka; wanda Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAddu’a Idan Mutum Ya Yi Fushi
Labarin na GabaAddu’ar Wanda Ya Yi Atishawa
Prof. Sa’idu Muhammad Gusau
FARFESA SA'IDU MUHAMMAD GUSAU, An haife shi a Gusau jihar Sakkwato, (Maris 24, 1952). Ya yi karatun firamare na Islamiyya daga 1965-1969, ya je kwalejin sarkin Musulmi Abubakar daga Junairu 1970 zuwa Yuni 1973. Ya yi Diploma, Digiri Na farko (B.A), na biyu (M.A) da Digiri na uku (Ph.D) duk a jami'ar Bayero, Kano.