Ciwon mara lokacin al’ada yana ɗaya daga cikin ‘premenstrual syndrome’ da aka yi bayani a baya.
Galibi, ciwon ba mai tsanani ba ne, amma yakan iya zama mai tsanani a wurin wasu matan. Kuma ko an sha magani ko ba a sha magani ba, ciwon zai yi sauƙi.
Don haka, ba lallai sai an sha magani ba, sai dai idan ciwon ya yi tsanani sosai. Mafi yawancin mata suna daina wannan ciwon bayan ‘ƴan wasu shekaru.
-
Kammalawa
Jinin al’ada, alama ce da take nuna cewa, mace za ta iya ɗaukar ciki. Yakan iya zuwa da wasu lalurori. Idan mace ta ga ɗaya daga cikin waɗannan lalurori, to ta je asibiti domin neman shawara
Domin kararanta yadda ake da mai gida lokacin al’ada ko mene ne Jinin haila ko Dalilin yin jinin haila danna koren rubutun nan