Yanayin Jinin Al’ada

0
3208

Jinin al’ada ya sha bamban tsakanin mata. Ba lallai yanayin jinin al’adar mace da wata macen ya zama iri ɗaya ba.

Kwanakin da kika saba yi da adadin jinin da kike zubarwa, ba lallai sai ya yi daidai da na wata macen ba. Kowace mace tana da nata yanayin.

A lokacin da jinin al’ada zai zuba ko kuma yake zuba, akwai canjin yanayi da yakan iya faruwa a jikin mace. Wannan canjin yanayi shi ake kira da ‘premenstrual syndrome‘. Alamomin Premenstrual syndrome sun haɗa da ciwon mara, ciwon nono, saurin fushi, damuwa, gajiya da sauransu. Ba kowane lokaci ake jin waɗannan alamomin ba, kuma ba a buƙatar a sha magani saboda premenstrual syndrome sai dai idan abin ya yi tsanani sosai.

  • Lalurorin jini al’ada
  1. Zubar jinin al’ada da yawa.
  2. Zubar jinin al’ada ɗan kaɗan.
  3. Daɗewa/ƙara kwanakin zubar jini.
  4. Raguwar kwanakin zubar jinin.
  5. Daina zuba/ɗaukewar jinin.
  6. Saurin zagayowar al’ada
  7. Ciwon mara lokacin al’ada da sauransu.

Idan mace ta samu ɗaya daga cikin waɗannan lalurori, to ta garzaya asibiti domin neman shawarar likita.
  • Kammalawa

Jinin al’ada, alama ce da take nuna cewa mace za ta iya ɗaukar ciki. Yakan iya zuwa da wasu lalurori. Idan mace ta ga ɗaya daga cikin waɗannan lalurori, to ta je asibiti domin neman shawara

Domin kararanta yadda ake da mai gida lokacin al’ada  ko menene Jinin haila ko Dalilin yin jinin haila danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceDalilin Yin Jinin Al’ada (Haila)
Labarin na GabaCiwon Mara Lokacin Al’ada
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa