Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa

    Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa

    Turawa sun zo sun iske ƙasar Hausa cike da ilmin abin da ya shafi karatu da rubutu a cikin Hausar ajami, kenan ko da Bature ya zo ƙasar Hausa ya iske su da ilmin zamani. Masana da dama kamar su (Magaji, 1982 da Sa`idu, 1985 da Hafsat Tsiga, 1987 da Yahya, 1988 da Ampah, 1989 da da Dogara, 2008 da Sulaiman, 2008 da Gusau, 2008 da Malumfashi, 2009,) sun kawo bayanai gwargwado masu gamsarwa game da samuwar rubutun boko  da yadda ya yi tasiri a ƙasar Hausa.

    Abin da kurum za a ƙara a nan bai wuce cewa an fara samun ɓurɓishin labarin ƙasar Hausa a wurin Turawa ta hannun Al-Hassan Ibn Muhammad Al-Wizas Al-Fasi, wato Leo Africanus wanda aka tsare a kurkuku a ƙasar Italiya inda ya bayyana a cikin littafinsa Na Bakwai ziyarar da ya kai ƙasar Barno da wasu daulolin na Hausa a tsakanin 1513 zuwa 1515.  Samun wannan littafi shi ya ba mutanen ƙasar Turai haske kan yanayin ƙasa da rayuwa a wasu ƙasashe na Afirka ta Yamma.

    Wannan haske da ƙasashen Turai suka samu game da ƙasashen Afirka, shi ya sanya suka fara ƙoƙarin turo mutanensu domin su dubo musu abin da ke faruwa a wannan yanki na Afirka. An samar da ƙungiyoyi masu manufofi daban-daban, musamman waɗanda za su binciko ainihin yanayin ciki da wajen Afirka.

    (Yahaya, 1988:75) ya ruwaito Turawa masu yawon gano Afirka na farko hankalinsu ya fi karkata ne kan labaran ƙasar wuraren da suka ziyarta kamar kogunansu, tuddai, tsirrai, bishiyoyi, albarkatun ƙasa, sunayen garuruwa da fasalin mazaunansu, da tsarin mulkinsu, da cinike-cinikensu da sauransu. Saboda haka, su ba su ƙarfafa bincike kan harsunan waɗannan mutanen ba.

    Daga ƙarni na 18 zuwa na 19 ne aka fara turo masu bincike, musamman bincike kan al`adu da harsuna da addinan ƙasashen Afirka. Akwai ƙungiyar ‘yan mishan wadda ta zo Afirka a daidai wannan lokaci ƙarƙashin jagorancin J.F Schon, da C. H. Robinson, da Hans Vischer, da G.P Bargery da wasunsu da dama.

    Daga hannun waɗannan `yan mishan ɗin da `yan leƙen asiri labaran ƙasar Hausa da jama`arta suka isa ƙasashen Turai. Wasunsu kuwa kamar su Robinson, da Miller, da Richardson, da Ryder, da Burgin dama sun zauna a Tripoli sun koyi harshen Hausa, wannan ya sa ko da suka zo ƙasar Hausar ba su sha wata wahala ba, kuma wasu daga cikin su sun zagaya, kuma sun zauna a sassan ƙasar ta Hausa, daga baya suka koma gida suka bayyana abubuwan da suka gano, wasu kuma suka ci gaba da rayuwa a ƙasar suna ayyukan yaɗa addini. (Malumfashi, 2009).

    Zaman waɗannan mutane a ƙasar Hausa ya ba su damar fara samar da abubuwan karantawa daga abin da suka ji, wanda wannan ya taimaka ƙwarai da gaske wurin gina adabin Hausa da al`adun Hausawa. J.F Schon shi ne zaƙaƙuri, kuma fitacce wurin rubuce-rubuce cikin Hausa a Turai a cikin ƙarni na 19. Bayan shi akwai irin su G.P Bargery, da W.R. S. Miller, da Hans Vischer waɗanda duk ƙungiyar mishan ta C.M.S ta turo su.

    Wannan zuwan bakin Turawa ya zama tubali wajen juya adabin bakan Hausa ya koma a rubuce a karo na biyu. Za a iya cewa kusan tun daga wannan lokacin ne aka fara mai da labarai da tatsuniya da karin maganganu da maganganun azanci da kuma al`adun Hausawa  a rubuce cikin Hausar boko.

    Kusan daga ƙarshen wannan ƙarni na 19 zuwa farkon ƙarni na 20 ne aka samar da litattafai masu yawa da suke ɗauke da wannan fasalin, wasu daga cikinsu sun haɗa da ; Hausaland na C.H. Robinson (1893), da Spécimens of Hausa Literature na C. H. Robinson (1896), da Hausa Notes na W.R. Miller (1901), da Batu Na Abubuan Hausa na W.H. Brooks (1903), da Littafe Na Tatsunniyoyi Na Hausa na Frank Edgar (1911), da Hausa Superstitions and Customs na Tremearne (1913), da sauransu dai da dama. (Yahaya, 1988:81).

    Bayan `yan Mishan da suka mamaye ƙasar Hausa, sai kuma Turawa `yan mulkin mallaka suka diro wa ƙasar. A daidai 1900 ne gwamnatin Ingila ta miƙa wa Gwamna Lugga jan ragamar mulkin Nijeriya ta arewa. Daga kama aikin shi na Gwamna ya fara aiwatar da wasu canje-canje. Ya tumɓuke tutar Royal Niger Company a Lakwaja ya sanya ta mulkin Ingila.

    Ya tashi hedikwatar jihar arewa daga Lakwajar ya mai da ta Zungeru. Ya dinga aika wa sarakunan ƙasar Hausa da su ba da kai, wasu sun bi, wasu kuwa suka ƙi. Ya tura da sojoji garuruwan na ƙasar Hausa kamar Zariya da Yola da Daura da Bauci da Barno da Katsina sai Sakkwato, inda bayan hijirar sarkin musulmi Attahiru suka ƙulla yarjejeniya bayan an fafata (Yahaya, 1988:89).

    Bayan Turawan mulkin mallaka sun ci ƙasar Hausa, dama sun iske harsashin da ƙungiyoyin mishan suka assasa na koyon karatu da rubutun boko, ga kuma na ajami da Larabci da ya daɗe tare da al’ummar, sai suka gina makarantun boko bisa wannan harsashi, duk rubutu da karatu aka ci gaba da yin su cikin Hausar boko.

    Saboda haka, kusan daga wannan lokacin ne aka fi samar da ayyuka wajen adana labaran gargajiya na Hausa a rubuce. Daga wannan lokacin ne, wato a farkon ƙarni na ishirin lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mamaye ƙasar Hausa ƙarƙashin jagorancin gwamna Lugga, sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu domin su tafi da hanyar rubutu ta Ajami da Larabci, don cimma burinsu na mulkin mallaka da ayyukan mishan, amma ba a je ko`ina ba suka kasa.

    Wasu daga cikinsu suka ba hukumomin mulkin mallakar shawarar lallai hukumar ta sake salo, domin kar a bar Hausawa wurin samun ayyukan gwamnati. Shi kan shi gwamna Lugga sai ya hango cewa dole ne ya sami ma’aikata `yan ƙasa waɗanda za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulki a ofisoshin gwamnati a bisa tsari irin na Turai, kafin a samu yin haka kuwa, dole sai an kafa makarantun ilmin boko, haka kuma hukumomi sun lura ya kamata a ba al`ummar Hausa ilmin da mulkin mallaka ya zo da shi, wato karatu da rubutu irin na Ingilishi, maimakon wanda suke da shi na Larabci da Ajami. Wannan shi ne ya haifar da buɗe makarantun boko a arewacin Nijeriya daga Turawan Mulkin Mallaka.

    Bayan samuwa da bunƙasuwar makarantu da malamai a sassa da Lardunan Arewa, sai wata matsala ta kunno kai, wannan matsalar kuwa ita ce ta samar da litattafan koyarwa a waɗannan makarantun. Ganin wannan matsalar na neman kawo tsaiko ga makarantun nan, sai Gwamnatin jihar Arewa ta kafa hukumar fassara (Translations Bureau ) a shekarar 1929, An ɗora wa wannan hukuma ta fassara nauyin samar da litattafai ta hanyar fassara daga wasu harsuna musamman Larabci da Turanci zuwa  Hausa.

    Sannan kuma ta taimaka wurin wallafa litattafai cikin harshen Hausa, ta kuma shirya litattafai domin manya da ƙanana don karantarwa a makarantu, daga ƙarshe kuma ta taimaka wa `yan ƙasa su yi wallafar ƙagaggun labaran cikin Hausa. Wannan hukuma ta yi aiki ƙwarai da gaske wurin samar da litattafan da aka sa ta samar.

    Domin faɗaɗa aikin wannan hukuma ne ya sanya a shekarar 1933, aka canza wa wannan hukuma ta fassara suna zuwa hukumar Talifi (Literature Bureau) domin ta faɗaɗa daga aikin da hukumar fassara ke yi. Wannan hukuma ta Talifi ta yi ta ƙarfafa bayar da ilmin boko, ta kuma samu goyon baya daga `yan ƙasa, daga baya ta ga ya kamata a faɗaɗa wannan shirin ya haɗu da tarihin ƙasa da sauransu. Saboda haka sai aka samar da Jaridar mai suna ‘Jaridar Arewa’ wadda ake bugawa cikin harsunan Hausa da Larabci, da kuma Turanci, har zuwa shekarar 1939 da aka samar da Gaskiya ta fi Kwabo.

    Ayyukan wannan hukuma sun ci gaba har cikin 1945, amma fa duk wannan aikin da wannan hukumar ke yi, ba ta da injunan ɗab`i nata na kanta, sukan tsara aikinsu, su aika da su maɗaba’a ta Jos, ko Kaduna ko kuma Ikko, in kuma ta yi ƙamari sai a tura da shi Ingila. Domin a samu wurin buga litattafai da jarida da sauran talife-talifen da hanzari a hukumar, sai Gwamnan Nijeriya na wannan lokacin Sir Arthur Richards ya nemi Gwamnatin Ingila ta taimaka wa hukumar Talifi  da kuɗin sayen Injunan buga litattafai da kuma na gina kamfanin wallafa.

    Wannan ne ya sa aka kafa kamfanin Gaskiya wanda ake kira Gaskiya Corporation a Tudun Jukun cikin garin Zariya a shekarar 1945. Shi wannan kamfani na Gaskiya Corporation shi ne ya ci gaba da ɗaukar nauyin wallafa duk litattfai da jaridar da Hukumar Talifi ke samarwa. Ire-Iren waɗannan litattafn sun haɗa da ; Ka Koyi Karatu, da Ka Ƙara Karatu, da Ka Yi Ta Karatu, da Bala Da Babiya, da Yawo Duniya Haji Baba, da Mango Park Mabuɗin Kwara da sauransu da dama. (Yahaya, 1988:97).

    A shekarar 1953, Gwamnan jihar arewa na lokacin Sir Bryan Sherwood Smith (Mai Wandon Karfe) ya kafa wani kwamiti na yaƙi da jahilci, wannan kwamitin ya duba hanyoyin da suka kamata a bi domin samar da ilimin zamani. Sannan kuma suka ba da shawarar hanyar da za a bi domin a yi yaƙi da jahilci, ita ce a samar da litattafai cikin Hausa rubutun boko da na  ajami da kuma wallafa litattafai cikin harsunan arewa.

    Wannan ne ya sa aka samar da Hukumar Yaƙi Da Jahilci Ta Arewacin Nijeriya, Northern Region Literacy Agency, (NORLA) a shekarar 1954, aka naɗa mata shugaba wani Bature W.F. Jefferies, daga nan sai aka ɗauke nauyin buga Litattafai daga Gaskiya zuwa NORLA, kuma yawancin ma`aikatan Gaskiya ɗin suka koma NORLA ɗin. Hukumar NORLA ta yi matuƙar ƙoƙari wurin samar da litattafai, domin a iya cewa babu wata hukuma da ta yi aikin da hukumar NORLA ta yi.

    Baya ga litattfan yaƙi da jahilci da wannan hukuma ta samar, ta kuma wallafa litattfai don makarantu da sauran jama`a masu son abin karantawa don ƙaruwa da ilimi ko don nishaɗi.

    Haka kuma NORLA ta sake buga wasu litattafai da hukumomin baya suka samar, daga cikin litattafan da NORLA ta samar akwai na addini; Ibada Da Hukunci, da Jagorar Mai Sallah, da Tarbiyya ga mutum, da sauransu. Akwai na labaran hira ; Bayan Wuya sai Daɗi, da Sauna, da Nagari Na kowa, da Tauraruwar Hamada, da Da’u Fataken Dare da sauransu. Akwai kuma na tarihi kamar su ; Sarauniyar Zazzau, da Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa, da Wali Ɗanmarna da sauransu.

    Bayan litattafai da hukumar NORLA take tsarawa, ta kuma rinƙa buga jaridu na kusan kowane lardi, duk da cewar kuma jaridar Gaskiya wadda dama ita ta kowane lardi ne tana nan tana fitowa. Ita dai Hukumar NORLA duk da wannan jan aiki da ta yi, ta samu matsala, inda a 1959 ta durƙushe saboda hada-hadar siyasa da ta mamaye arewacin Nijeriya.

    `Yan kuɗaɗen da hukumar ke samu daga Gwamnatin Jihar Arewa suka tsaya, daga nan sai hukumar ta mutu. Ita dai wannna hukuma ta NORLA ta yi zamani ne daga 1954 zuwa 1959, amma sauran kayan aikin hukumar sai suka koma kamfanin Gaskiya inda aka ci gaba da kula da su, sannan kuma kamfanin na Gaskiya ya ci gaba da buga litattafan da hukumar NORLA take bugawa.

    Da tafiya ta yi tafiya ne Gwamnatin jihar Arewa ta lura ayyukan sun yi wa kamfanin Gaskiya yawa, wannna ne ya sanya aka ɗauke aikin buga jaridar Gaskiya ta fi kwabo daga kamfanin Gaskiya, domin a rage masa aiki, aka bar su da buga litattafai kurum. Da gwamnati ta ga aikin ya yi yawa, sai ta yi ƙoƙarin samun wani kamfani wanda zai ci gaba da wannan aikin. Wannan ne ya sanya aka nemo kamfanin Macmillan daga Ingila inda aka ƙulla yarjejeniya da shi aka samar da kamfanin wallafa na NNPC (Northern Nigeria Publishing Company) a watan Oktoba na 1966.

    An sakar wa kamfanin NNPC mara na ya zaɓi duk littafin da ya ga dama bugawa, shi kuma kamfanin Gaskiya sai aka bar shi kurum a matsayin kamfanin kasuwanci. Sannan kuma shi wannna kamfani na NNPC yana karɓar litattafai daga marubuta Hausa domin ya buga musu.

    Wannnan kamfani shi ma ya sake buga wasu daga cikin litattafan da hukumomin baya suka samar, wasu daga cikin litattafan da suka samar sun haɗa da ; Tauraruwa Mai Wutsiya na Umaru Dembo, da Uwar Gulma na A.M. Sanda, da Daren Sha Biyu na Ibrahim Yaro, da Iliya Ɗan Mai Ƙarfi na Ahmadu Ingawa, da Matar Mutum Ƙabarinsa na Bashir Roukbah, da dai sauransu da dama, wasu na addini ne, yayin da wasu waƙoƙi ne ko labarai ko kuma wasa kwaikwayo.

    Bayan wannan kamfani na NNPC da gwamnati ta samar, akwai wasu kamfanonin wallafa na raya al`adun Hausawa da samar da ƙagaggun litattafan Hausa. Akwai kamfanin litattafai na Oxford wanda ya koma Úniversity Press Limited’ (U.P.L), akwai kuma kamfanin Longman, shi ma na tallar litattafai ne, akwai kamfanin Thomas Nelson, akwai kamfanin Alhuda-huda Publishers, da Ilesanmi, da Truimph Publishers da dai sauransu da dama .

    A shekarar 1978 ne, kamfanin NNPC ya sanya gasar samar da ƙagaggun labaran Hausa da kuma wasan kwaikwayo. A tarihin ƙagaggun labaran Hausa, a iya cewa wannan gasa ita ce ta biyu, marubuta da yawa sun shiga wannan gasa, amma daga ƙarshe aka fitar da waɗanda suka lashe gasar kamar haka;

    • Mallakin Zuciyata  na Sulaiman Ibrahim Katsina
    • So Aljannar Duniya na Hafsat A. Abdulwaheed
    • Amadi Na Malam Amah   na Magaji Ɗanbatta

    Bayan wannan gasa da kamfanin NNPC ya samar, akwai wata gasa da za a iya kira ta uku a shekarar 1982, wadda ma’aikatar al’adun gargajiya ta tarayya ta shirya don bunƙasa manyan harsunan Nijeriya. Mutane wajen 30 sun shiga wannan gasar, amma dai an zaɓi guda bakwai waɗanda ake jin sun yi fice aka buga su, waɗanda aka zaɓa kuwa su ne;

    • Turmin Danya Na Sulaiman Ibrahim Katsina
    • Zaɓi Naka Na Munir Mohammed Katsina
    • Ƙarshen Alewa Ƙasa Na Bature Gagare
    • Tsumangiyar Kan Hanya Na Musa Muhammad Bello
    • Dausayin Soyayya Na Bello Sa`id
    • Soyayya Ta Fi Kuɗi Na Hadi Alƙanci
    • Wasa Ƙwaƙwalwa Na  Mohammed Yahuza

    Daga wannan lokaci ne abubuwan ɗab’i suka fara sauya fasali a arewacin Nijeriya, harkar samar da ƙagaggun labaran Hausa suka fara ɗaukar wani sabon salo, samar da litattafan sai suka tashi daga kamfanonin na hukuma ko waɗanda hukumar ta amince da su, sai marubuta suka fara samar da litattafansu, suna fiddo su, sannan kuma fasali da jigon litattafan duk suka sauya daga yadda aka san su, suka koma na wasu jigogi daban, wannan sabon fasali shi ne masana suka bayyana da Adabin Kasuwar Kano ko Labaran Soyayya, ko ƙagaggun Labaran Hausa da sauransu, kamar yadda za mu gani a babi na gaba.

    Naɗewa

    A wannan babin an kalli samuwar ƙagaggun labaran Hausa kama daga tatsunniya da tarihihi da labari da kuma ƙissa har zuwa lokacin da suka canza fasali suka tashi daga na ‘KA’ suka koma a rubuce wato bayan haɗuwar Hausawa da baƙi (Larabawa da Turawa).

    Sannan an ga yadda aka fara samar da karatu da rubutu a ƙasar Hausa da kuma yadda aka samar da ƙagaggun littattafan labaran Hausa daga gasa, wanda wannan ya kasance tamkar mabuɗin farko wajen samar da abin da ake kira Adabin Kasuwar Kano.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Buki A Bahaushen Tunani

    Buki A Bahaushen Tunani

    Gabatarwa
    Buki wani abu ne da ke cikin tsofaffin al’adun mutane da, da wuya a tantance ranar da aka fara shi. A duniyar da muke ciki yau, babu al’ummar da ba ta da buki, kuma babu al’ummar da ta yi watsi da bukukuwan da ta gada kaka da kakanni.

    A ra’ayinmu ɗaliban al’ada, buki ya leƙa duk wata gargajiya, wayewa, da ci gaban mutanen da ke aiwatar da shi. Don haka, cikin hada-hadar buki za a iya ƙyallaro wani abu daga tarihin mutanen da ke aiwatar da shi da kuma dangantakarsu da maƙwabtansu, masoyansu, magabtansu, baƙinsu, da magabantansu da mamaya bayansu. A tarihance, buki Mahdi ne mai dogon zamani. A la’adance, wandon roba ne daidai da kwankwason mutum na kowane zamani.

    Kadadar Nazari

    Ba dukkanin bukukuwan Bahaushe wannan ‘yar takarda za ta yi nazari ba. Takenta ya yi faɗi, ya yi tsawo, sosai, amma “tunanin Bahaushe” da aka kawo ya ɗan takura mata iyakokin nazarinta. Takardar ta yi garkuwa da “Sallar Gani” a Daura domin ta ƙyallaro Bahaushen tunani a kan buki.

    Don haka, manufa ita ce a kalli Bahaushen buki tare da ƙyallaro Bahaushen tunani a kan faruwarsa, dalilansa, yaɗuwarsa da muhimmanci da ke tattare a ciki. Bahaushen tunani za a kalla a ciki, za a yi garkuwa da Sallar Gani a Daura da masarautun da ke mara mata baya domin ci gaba da wanzuwarta.

    Ra’in Bincike

    Yayin da aka nemi in ce wani abu kan Sallar Gani a Daura, na ga ba makawa sai na bi diddigin tarihin samuwarta. Na so in ji sunanta na fari gabanin ta kasance: “Salla”. Cikin kai da kawo na ga daidaitaccen tafarkin da ya kamata in daidaita wannan ɗan yunƙurin shi ne: “In babu ƙira me ya ci gawai”? Matuƙar maƙera bai ga gawayin da ya ajiye a maƙera ba, zai nemi yaransa da su zo su gaya masa wa ya yi ƙiri wurin?

    Dalili kuwa shi ne, gawayi ba a cinsa, dabbobi ba sa ci, a can da ba a sayar da shi, in ba maƙera ba babu mai amfani da gawayi. To! In babu ƙira me ya ci shi? Na danganta wannan batu da cewa, a ko ina aka tarar da ana buki dole da dalili. Babu bukin da ake yi ba ya da tarihi, ba ya da mafari, ba ya da wata fa’ida ko da kuwa ɓoyayya ce.

    Da an ga Bahaushe na gudanar da buki a ƙasarsa, babu shakka an yi irin sa gabanin ya yi. Haka kuma, idan an shiga taliyon bincikensa, za a gano a ina ya fito? Matuƙar babu hujja ta al’ada Bahaushe ba zai iya buki ba, dalilina kenan na cewa: “In babu ƙira me ya ci gawayi”? Me ya sa ƙasar Daura da Gumel da Haɗeja kawai ake gudanar da Sallar Gani? In babu ƙira me ya ci gawai?

    Dabarun Bincike

    Tattare da irin muhimmancin Sallar Gani a wuraren da ake gudanar da ita da tarihin garuruwan da ta yi ƙamari, ba a samu wani gawurtaccen aiki a kanta ba a rubuce da sunan bincike. Tilas na dogara ga bayanan baka da aka tsinta daga Sarakunan Daura, Gumel da Haɗeja ta bakin wasu jami’ai daga masarautunsu.

    Haka kuma, na yi amfani da wasu abokan aikina da ɗalibaina na garuruwan da ake gudanar da bukukuwan, da ɗan abin da suka kalato daga bakunan kunne ya girmi kaka. Na sake lalubo taskokin adabin bakan Bahaushe domin kwakkwashe bayanai. Na tattaka da kaina na yi rangadi a Daura domin in ji ta bakin masu abu.

    Da yake zamani riga ne, na ga ba a sa wa “Sallar Gani” rigar zamani ba, domin an neme ta ƙaura Wambai a intanet ba ta. Wannan ba ta hana aka sa hular zamani ta amfani da wayoyin hannu domin sadar da muryoyinmu na bincike a wuraren da dugadugan mai bincike ba su wada kai ba. Ta haka aka tsinci abin tsinta aka watsar da na bari.

    Fashin Baƙin Fitilun Kalmomi

    Taken wannan bincike shi ne: Buki a Bahaushen Tunani: (Duba Cikin Hada-hadar Sallar Gani a Ƙasar Hausa). A Bahushen tunani, buki wani taro ne na gangamin jama’a domin gudanar da wata hidima. Bahaushe shi ne wanda ba ya da wani harshe sai Hausa, ba ya bugun gaba da wata al’ada sai ta gargajiyar Bahaushe. A same shi uba da kaka da kakanni duk Hausawa ne cikon sunna ne makaho da waiwaya.

    Tunani shi ne, abubuwan nazari da ke bayyana cikin adabi da harshe da al’adun mai tunanin, kuma su ne tunaninsa ko ya yarda ko ya ƙi, ƙaddara ta riga fata. Duba shi ne, tsura ido ga abin da aka sa gaba a kansa. Sallar Gani ita ce farfajiyar da ake so a duba. An danganta batun da “ƙasar Hausa” dalili kuwa shi ne, Daura ta shahara da Sallar Gani, kuma a Hausance Daura ita ce tushen Hausa, ita ce Hausa, ita ce ƙasar Hausa mai dalili a tarihi da tarihihin Bahaushe.

    A tunanin wannan bincike “Sallar Gani” buki ce domin Daurawa da Haɗejawa da Gumawa suna ce da ita: Bukin Sallar Gani”. Ashe kalmar “Buki” wata babbar kafaɗa ce da wannan bincike zai dafa ya miƙe tsaye a gan shi, don haka fayyace ta ya zama dole.

    Menene Buki?

    A al’adance, gidan kowa ana buki, garin kowa ana buki, ƙasar kowa ana buki, a addinin kowa akwai buki, a matakan rayuwar kowa akwai buki. Samun taron mutane a buki bai da makawa kamar yadda hidimomi da hada-hada cikin cikin kowane buki ya zama suturar ƙawa ga bukin. Ƙamusun Bargery ya fassara buki da cewa:
    (a) Feast, e.g, in celebration of a marriage or on naming day

    (b) (bikin farar kaza balbela ba gayya ba ce) a relation or intimate friend needs no invitation in a feast

    (c) at a feast given by a white hen the buff-backed heron would naturally attend without needing, waiting for, or expecting an invitation…

    Fashin baƙin Bargery buki shi ne shagulgulan aure ko suna, kuma buki gayyatar abokan hulɗa da arziki ake yi. Ɗan uwan da bukin ya shafa ba sai an gayyace shi ba domin su ne masu gayyata. A tunanin Ingilishi a fassarar The New International Webster’s Comprehensie Dictionary of the English Language Deluxe Encyclopedic Edition ya ce:
    Ceremony n. pl. (nies):

    (1) A formal or symbolical act or observance, or a series of them, as on religious and state occasions.

    (2) The doing of some formal act in the manner prescribed by authority or usage. The ceremonies at an ordinary inauguration, or coronation.

    Da gangan na kawo fassarar “buki” ta Ingilishi domin tabbatar da cewa, buki al’adar duniya ce, ta ‘yan duniya, don a ci duniya, a more duniya. A nan, mun ga cewa buki harkar taro ce, yana kasancewa na al’ada ko addini ko ayyuka na gudanar da hukuma yadda ta shata a yi su. A taƙaice a wurin Bahaushe buki shi ne:

    Taron masha’a da assha ko mu ce, taron dariya da gintse fuska. Yadda duk ya ksance akwai hidimomi da hada-hada a ciki. Ba a koyaushe yake gudana ba, amma a koyaushe buƙata ta taso, ko tarihi ya maimaita kansa, za a yi shi. Mai buki da ‘yan uwansa ke buki, wani ba su ba, taron a ci buki ne. buki ba a yin sa sai da mafari, mafarinsa shi ne tarihinsa.

    Bukin A Taskar Adabi da Al’ada da Harshe

    Al’adun da mutane suka gada kaka da kakanni za a ci karo da su cikin adabinsu da al’adunsu da harshensu. Duk abin da adabin mutane ya kawo, to a je a binciko shi cikin al’adunsu da nahawun harshensu za a ga wurin da salka ke tsatsa. Ga yadda buki ya yi naso a adabinmu:

    • Bukin farar balbela, kaza ba gayyatarta ake ba.
    • In gani a ƙas, an ce wa kare ana buki a gidansu.
    • Ƙudan buki, ba gayyar ku ake ba.
    • Arha matan buki.
    • Ban ci buki ba, buki ya ci ni.
    • Uwar buki, ba ruwanki da ɓarakar zane.
    • Bukin Sa’a ba kyanta ba ne.
    • Bukin Magaji, ba ya hana na Magajiya.
    • Bukin wani kundumi, bukin wani doka.
    • Ba ya bukina, ba na bukinsa.

    Waɗannan karuruwan maganganun da zantukan hikima in an bi su daki-daki ba ƙaramin kundin PhD za a rubuta ba. Buki a jinin mutane yake, adabinsu ke fitar da shi a sararin adabi a harare shi. Bukin Bahaushe da na farin ciki, da na baƙin ciki, duk akwai hidimar kyauta a ciki. Malamin Kiɗi Ibrahim Narambaɗa, ya tabbatar mana da haka a waƙar “Ya ɗau girma ko ba a so”

    Jagora: Ko way yi buki bai ba ka ba
    : In na yi buki ba ka ba shi ba

    Yara: Ya san ba ka da laifi ko ƙiris

    Gindi: Ko way yi buki bai san da kai ba
    : In ka yi buki ba ka ba shi ba

    Yara: Ya san ba ka da laifi ko ƙiris

    Gindi: Ya ɗau girma ko ba a so
    : Maƙi gudu baban ‘yan ruwa

    Babu wai, adabi ya tabbatar muna, a cikin buki, akwai ciye-ciye, da tanɗe-tanɗe, da shaye-shaye, da haɗuwar mata da maza da, gudunmuwa ta ‘yan uwa da abokan buki, ga su nan dai. Buki na Sarauta irin su “Sallar Gani” cincirindon talakawa cikin ado da bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, su ne adon Sarki da masarautarsa. Ƙin fitowar talaka a yi da shi, laifi ne na nuna bijirewa, kamar yadda ƙin ba da tasa gudunmuwa ga bukin ‘yan uwa da abokan arziki laifi ne ga dokar buki da sabgar dangi.

    Lokutan Buki Da Halayyar Ribantar Su

    Hankalin Bahaushe ya zarce tunanin na bayan fage, da dabirtaccen ɗan boko, mai ra’ayin duniyar baƙar fata baya take ga ci gaba. Bahaushe, da ci gabansa, da wayewarsa, aka gan shi, duk ci gaban zamani da ya riske shi, ba a rasa nasonsa da hancin adabinsa ya sunsuno. A kowace hada-hada ta buki Bahaushe na da:

    • Lokacin Buki
    • Wurin Buki
    • Fitar Buki
    • Ribantar Buki

    Lokutan Bahaushe na buki uku ne: sassafe tun gabanin hantsi ya dubi ludayi, musamman in bukin ya shafi dafe-dafe, da toye-toye, da soye-soye. Da rana tsaka, bukin da ya shafi maza zalla ake yi musamman bukukuwan da ke buƙatar a ɗebe wa ido kwantsa. Da dare, ana bukukuwan da ke buƙatar sirri ko kuma ba su da nauyin sai a bayyana su da rana. Sallar Gani da rana tsaka ake aiwatar da ita ba ta kunyar idon kowa, kowa na son ganinta.

    Wuraren bukin Bahaushe sun haɗa da gidan buki idan bukin ƙarami ne, kuma na ƙaramin gida, ko kuma wanda dole sai a gidan za a yi shi. Akwai dandalin unguwa idan ya shafi mutanen unguwa. Akwai na kasuwa ko maciya, idan abin na gari ne gaba ɗaya. Babban buki gagarumi sai Kan Wuri wanda ya shafi mutanen gari da maƙwabtan garuruwansu irin bukin “Sallar Gani”. Ana gabatar da wasan bukukuwa wuraren ban gaskiya da maƙabarta idan sun shafi mutuwa da addini.

    Ga al’adar Bahaushe, fitar Buki ta musamman ce, za a yi wa yara maza da mata kwalliya gwargwadon halin iyayensu. Manyan maza da mata za su sha kwalliya irin ta yara ko fiye da ita. A wasu bukukuwan kuma za a fita da kayan gado na shirin kare martabar magabata. Babu bukin da za a yi fita Bambarakwai a ƙasar Hausa in ba na roƙon ruwa ba ne. Bukukuwan da suka shafi fada da Sarauta manya ne ga Bahaushen tunani, wani ba su ba ƙanana ne. Sallar Gani babba ce ta kowa da kowa sannan na hawa irin na kowace salla.

    Ribantar buki na kowa da kowa ne. A tsarin buki, abinci ba sai an saya ba, kowa zai kawo tasa gudunmuwa har sai an kasa cinye na kowa. Masu wasannin gargajiya, da wasannin gwada martabar gado, da magani da buwaya, da ƙwarewa kan kowane irin abu na iya bayyana a dandalin babban buki a ji su, a gan su. Taka rawar gado da za su yi, zai ba da damar a yi musu karin kuɗi da ƙadara, tare da yaba musu, da gode musu, da saka su cikin adabin ƙasar a taskace sunansu a tarihi.

    Matakan Bukukuwan Bahaushe

    Bukukuwan ƙasar Hausa matakai gare su da al’ada ta kiyaye da su. A farfajiyar nazarin al’adar Buki a ƙasar Hausa, matakan bukukuwa su ne:

    • Bukukuwan Matakan Rayuwa
    • Bukukuwan Tsari da Yaƙi
    • Bukukuwan Buɗi
    • Bukukuwan Dattako
    • Bukukuwan Naɗi
    • Bukin Dubu da Tambarci
    • Bukukuwan Ban Gaskiya
    • Bukukuwan Saukakkun Addinai
    • Bukukuwan Tsafe-tsafe da Siddabaru
    • Bukukuwan Sana’o’i
    • Bukukuwan Kafa Tubalan Harsashe
    • Bukukuwan Askewa (Tuba)
    • Bukukuwan Gayya

    Bukukuwan Matakan Rayuwa: Su ne bukukuwan aure, raɗa suna, kaciya da mutuwa da duk wani abu da ya shafe su na buki. Sallar Gani ba ta ciki domin daga baya ta zo.
    Bukukuwan Tsaro da Yaƙi: Su ne bukukuwan gwazangwari na zagayowar wata rana da aka ci wata nasarar yaƙi da wani gari ko wata ƙasa. Haka bukukuwan tunawa da mazajen da suka faɗi a wata arangama yaƙi da aka yi da wasu, sai a zaburar da maza su ɗauko fansa, Kabawa da Gobirawa suka shahara da waɗannan. Sallar Gani ta saɓa musu domin ba da makaman gaba ake yin ta ba.

    Bukukuwan Buɗi: Buɗar Dawa, Buɗar Hurumin Kogi ko tabki na su. Sallar Gani ta ban girma da ban gaskiya da tuna baya ce.
    Bukukuwan Dattako: Bukin Aza Gemu, Bukin Kai Bante ga amare mata. Ana bukin aza geme daga shekaru 30-40, kai bante kuwa da amarya ta tare gobe da safe mata za su yi.

    Bukin Naɗi: Naɗin Sarautar ƙasa, Sarautar gado ta sana’a ko Sarautun girshi, Sallar Gani babba ce ba a sakaɗa naɗin kowace Sarauta ranar da gudanar da ita.
    Bukin Dubu da Tambarci: Sai manomi ya kai babban goje zai noma dami dubu na hatsi ko masaki dubu da tsabar shinkafa ko wake da sauransu. Ana yi musu buki na musamman da tamburan yaƙi. A gona ake fara bukin in an dawo gida a yi ban gajiya.

    Bukin Ban Gaskiya: Ban gaskiya shi ne bukukuwan Girka da Bori da Kan gida.
    Bukukuwan Addini: Salloli, Musulunci babba da ƙarama, Hajji, Jumu’a, Saukar Karatun Alƙur’ani, Maulidi, buɗa masallaci da gangamin wa’azin ɗariƙu da ƙungiyoyi.
    Bukukuwan Tsafe-Tsafe da Siddabaru: Shan Kubewa ga Kabawa, Shan Gumba ga Rundawa, Cin Tama na Maƙera, Kafin Gari, da cin Sabu ga ‘yan bori.

    Bukukuwan Sana’o’i: Cin Tama na maƙera, Hawan Ƙaho na Rundawa, Ɗaurin Ruwa na Masunta da Ɗaurin Daji na mafarauta.
    Bukin Kafa Tubalin Harsashe: Bukin kafa kasuwa, kafa gari, buɗa wata babbar hanya, kafa wata sabuwar Sarauta.

    Bukin Askewa: Bukin aske zanƙon dambe, cire tukkuwar kokuwa, aske gemun wasa, cire ƙanƙarun maita, tuba da sata ko fashi.
    Bukin Gayya: Gayyar Sarakuci, Gayyar rashin lafiya, Gayyar Masallaci, Gayyar gyara wani muhimmin abu a gari, ƙasa, ko unguwa.

    Ina Sallar Gani ta Faɗo Daga Cikin Waɗannan?

    Waɗannan bukukuwan sun game ilahirin ƙasar Hausa, jiya da yau. Dukkanin ƙasashen da ke karɓa sunan ƙasar Hausa, Gobir, Kano, Kabi, Zazzau, Katsina, Maraɗi, Damagaram, da sauransu duk ana aiwatar da su, amma a Daura da Haɗeja da Gumel kawai Sallar Gani ta yi suna.

    Masu bincike sun ce, ana yin bukukuwan Sallar Gani a Daura tun gabanin bayyanar addinin Musulunci. Da Musulunci ya zo, ya samu karɓuwa da bazuwa, ta sake zani ta kutso ciki da rigar Maulidi. Silalin wannan tarihi ya sa za mu ce, “Sallar Gani” tana daga cikin: Bukukuwan Tsaro da Yaƙi da Bukukuwan Addini

    Kasancewar Daura tsohon garin tarihi, wannan bukin an daɗe ana yin sa. Idan aka dubi sigar da ake gudanar da shi, buki ne da ke da alaƙa da tanadin yaƙe-yaƙe da tsaron ƙasa. Da aka ga amfaninsa bayan da yaƙe-yaƙe suka kau, aka riƙe shi wani matakin tsaro ta fuskar sadar da zumuncin da ke cikinsa.

    Bayan da Musulunci ya zo, ba a sauya masa siga ba, saboda sanin muhimancinsa aka sakaɗo hidimar Mauludi ciki. A halin yanzu, ni ina ganin “Sallar Gani” tana da wani matsayi da za a kira “Bukin Sada Zumunci”. A koyaushe aka hau ta, za a tuna baya domin sake gyara zama a yau, a san yadda za a tunakari gobe.

    Sunan Sallar Gani

    Idan Bahaushe ya ji an ce: “Salla” addinin Musulunci zai fara zo masa a tunaninsa. Ni kaina, shekaru da yawa a baya, da na ji sunan bukin “Sallar Gani” a Daura haka na yi zato. Yayin da na je Maraɗi wani bincike (2000), na tunkari Maraɗawa na samu bayani a kanta.

    A bukukuwan da Jamhuriyyar Nijar ke yi na zagayowar shekararsu ta samun ‘yancin kai, na samu halartar tarukansu na ƙara wa juna sani cikin bukukuwan da suke yi shekara-shekara a jihar Maraɗi da Dosso da Damagaram, kowanne daga cikin ‘yan siyasarsu da ‘yan bokonsu da walilan tsaronsu da dukkanin Hausawan ƙasar da Arawa da Zabarmawa da Dandawa da Buzaye da Fulaninsu da sauransu suna yi wa bukin suna da “Salla”.

    A wajensu, duk wani buki da za a yi, a fito a yi kwalliya, manyan gari da masu gari su fito da jama’arsu, sunansa “Sallah”. Ban yi musu ba domin za a ji Hausawan duniya na cewa:

    • Yau take salla
    • Salla mai yawan ƙawa
    • Kukan zakara buki “Gobe Salla a yanke manya, a bar ƙanana”
    • Buki ba naka ba ka bi; ‘yan kaji da yanka

    Idan muka dubi wurin da ƙasar Daura take, da dangantaka da kusancinsu da Jamhuriyyar Nijar, da kuma dangantakar tsagarsu ta gado “dogaye biyu a haɓa” irin ta Arawan Nijar, da Arawan Nijeriya, da Gubawan Jamhuriyyar Benin, za mu ce, buki na da suna biyu a wajensu: Buki da “Salla”.

    Wataƙila saboda irin tasirin da Musulunci ya yi a Daura suka zaɓi amfani da kalmar “Salla” da ke da makusanciyar dangantaka da Musulunci suka yi watsi da kalmar “buki” da ke da nason gargajiya a ruhin ma’anar ta. A kan wannan tunani ta zama “Sallar Gani” ba “Bukin Gani” ba.

    Fashin Baƙin Kalmar Gani

    Daga cikin Sallar Gani, kalmar “Gani” na son a waiwaye ta. A furuci, Daurawa da Haɗejawa da Gumalawa da maƙwabtansu suna furta kalmar da sautin /gaa/ da dogon wasali da /ni/ da gajeren wasali. A rubutun aruli, kalmar za ta kasance /gaani/. A lura, kalmar gaɓa biyu gare ta takan ɗauki ma’anoni kamar haka:

    Ganii: abin da mutum ke kallo ƙuru-ƙuru
    Ga nii: wanda aka kira ya karɓa kira, kuma ya zo, zai ce: “gaa ni na zo”
    Gaanii: ɗebe kifin da aka kama a haƙo na kalli ko mamari ko undurutu. Haka kuma, haƙo zuma a raminta ko burtumin da aka haƙa ta duk “gaanii” ne.

    Waɗannan kalmomi uku su suka fi kusantar ma’anar kalmar da ke cikin “Sallar Gani”. Daga cikinsu na zaɓi kalmar “gaa nii, mai ma’anar gaa ni naa zoo”. Yayin gudanar da Sallar Sarakuna da Magajiyoyi kan taru, Sarki ya kai gaisuwa ga Magajiya ya ce: “Gaa ni na zo gaisuwa”.

    Idan muka dubi yawancin kirari da maganganun da zabiyoyi ke yi wa Sarki a lokacin Sallar Gani za mu yi kirdadon wata Bahaushiyar kalma wai ita “guunii” mai jam’i “gunaagunii”. Guuni wata maganar zuci ce da baki ke furtawa da wani nishi daga cikin bakin, wanda zai hana mai sauraro gane abubuwan da ake faɗa har sai ya ce: “Wane gunaguni ne ake yi”?

    Duk wanda ya halarci dandalin zabiyoyin da ke yi wa masarautar Daura jinjina zai tabbata maka daga su matan da ke yi, sai Sarki, da mutanen fada ke iya kama ma’anonin abubuwan da suke faɗa. Ganin irin gurbin mata a tarihin masarautar Daura musamman Sarauniya Daurama, da wasu masana tarihi ke ganin tun fil azal Sarautun mata ke akwai ƙasar Hausa daga baya maza suka ƙwace. Wataƙila, can gabanin Musulunci “Buki/Taron Guunii” yake saboda mata ke sarauta, mata ke zabiya, mata ne Magajiya.

    A hasashe na biyu na dubi yanayin mutanen da ke zaune “Daura”. Tun fil azal, akwai Larabawa, akwai Barebari, akwai Arawa, da Arewawa, da sauran nau’o’in Hausawa da Buzaye. Tunani da tarihin Bayajidda ya sa na yi tunanin kalmar Balarabiya ce, musamman idan aka lura da irin adabin Larabci da yadda waƙa da waƙoƙin mata suka yi tasiri a ciki.

    Wanda ya karanci tarihin Daular Banu Umayyad da Abbassid ba zai musanta hasashen ba. A Larabci, waƙa ana ce da ita “alginaa’u” mawaƙi “almuganni”. Wataƙila ‘yan waƙoƙin da matan ke yi ya zama sanadiyyar kiran bukin “Bukin Gaanii” wasali “i” na “n” ya zamo dogo /nii/ ya zamo “bukin zabiyoyi”. Hasashe na uku shi ne, sunan mata na Hausa “Gana”. A garuruwan Hausawa a can da, ana sa wa ɗiya mata suna “Gana” yana da kyau a ɗan nazarce shi.

    Bitar “Sunan Daura”

    Daura ita ce tushen Hausa. Masarautar Daura kaɗai ce daga cikin masarautun ƙasar Hausa da ke da ikon ba da Sarautar Hausa. Sunan Daura babba ne a tarihi domin tarihin Bahaushe a ko’ina yake ba ya kammaluwa in ba a kawo Daura a ciki ba. Idan muka ɗora kalmar Daura cikin kalmomin Hausa za mu ga akwai:

    Daura: Sunan garin da muke zance a kai
    Daura: Kalma ce mai nuna, “kusa ga”: Gidan nasa na daura da gidan Sarki
    Dauri: Ma’ana a da ko a da can da nisa.
    Daura: A lugar Larabci kalmar taro ko matattara ko haɗuwa ta musamman. Ɗaliban ilmi da suka yi karatu a ƙasashen Larabawa sukan haɗa ɗalibai wurare daban-daban don yi musu bita a wuri ɗaya da sunan “daura”.
    Daure: Ƙoƙarin cijewa da ƙin nuna gazawa da ƙin raki.

    Ba mu samu tabbacin wanda ya raɗa wa Daura suna ba, amma idan muka yi duba cikin ma’anonin kalmomin /Dauraa/ da muka gabatas kalmar “daura” da “dauri” sun fi kusa da juna kuma su ne, makusantan sunan garin. Kalmar “daura” ta Larabci zuwan Bayajidda Daura ya kore ta.

    Masu tarihin Daura, sun tabbatar da cewa, Balaraben Iraƙi ne kuma ya taras da Sarauniya Daurama na mulki har ta aure shi. Wannan ya nuna tun Larabawa ba su zo Daura ba sunan garin Daura yake Daura. Haka kuma nan suka tarar da garin Daura ba su suka sare shi ba.

    Kwakkwahe Batu Kan Kalmomin “Salla”, “Gani” da “Daura”

    Kalmar “Salla” sabuwar kalma ce ta sadu da Hausawa bayan da addinin Musulunci ya zauna da gindinsa a ƙasa da zuciyar masu ƙasa. Kalmar ta tabbatar da akwai wata gabaninta, wadda ba wata ba ce face “buki”. Buki ita ce kalmar da wani addini bai yi naso cikinta ba.

    Gani a daidaiciyar ma’ana ta al’adar Daurawa ita ce daga: “ga ni na zo” takan fito bakin wanda aka kira ko aka gayyato ko kuma ya zo karan kansa amma da wata magana ta daban. Kalmar Daura Bahaushen suna ne da Daurawa suka ƙago abinsu. Gabanin yau 2019, Bukin Gani a Daura yake. Da addini ya mamaye masarauta ya koma Sallar Gani a ƙasar Daura. Wannan sunan shi ne ke ci har yau ta koma Sallar Gani a ƙasar Hausa.

    Tsarin Sallar Gani a Daura

    Tarihin Sallar Gani ba zai kammala ba sai an waiwayi tarihi da tarihihin Garin Daura. A tarihance, Daura babbar ƙasa ce da manyan garuruwa da yawa ke ƙarƙashinta. A tarihin zuwan Bayajidda, an tabbatar da zuwansa Daura da matarsa da yaronta. Bugu da ƙari, tarihin ya nuna ko zamanin zuwansa Daura babbar masarauta ce ƙarƙashin Sarauniya Daurama.

    Ya tarar da Daura ta bunƙasa har da babbar rijiyar shan ruwa “Kusugu”. A tarihin, an yi saɓani kan zancen macijin da aka tarar a cikinta a kan matsayinsa. Tsohuwa “Ayana da ya tarar ta ɗan ɓulguta masa matsayin macijin a Daura ta wancan lokaci. Da ya kashe maciji, sai auratayya ta shiga. Cikin auratayya aka samu ‘ya’yan da suka kafa Hausa Bakwai da Banza Bakwai, wanda a yanzu ake yi wa sunan: Yannai Bakwai da ƙannai Bakwai.

    An ce, a kowace shekara Yannai Bakwai da Ƙannai Bakwai sukan baro masarautunsu zuwa Daura su kwana, cikin dare za su kwana ana bitar nasarorin da aka ci, da cikas da aka samu, da yadda za a fuskance su. Taron za a kwana zaune ana karatun abubuwan cikin dare, da safiya ta waye a shirya ‘yan bukukuwan ban kwana da kilisar sadar da zumunci.

    Daga nan Bukin Gani a Daura ya soma har ya sarƙu da addini ya sauya masa suna zuwa “Sallar Gani”. Babu tabbacin ranar da aka fara yin ta, da Basaraken da ya fara mai da ita buki. Abin sani shi ne, ƙasar Daura da Gummel da Haɗejiya sun fi ba abin muhimanci fiye da kowace ƙasa ta ƙasar Hausa.

    A Daura, Sallar Gani, Salla ce ta tunawa da Sarakunan da aka yi mata. Babbar ɗiyar Sarki ita ake naɗawa Magajiya. A ranar Sallar Sarki zai je gaishe ta da shi da hakimansa, amma kowannensu ba zai saka alkyabba ba a ranar, amma ita Magajiya za ta saka. Sarki tare da jama’ar za su kai gaisuwa, Sarki zai gaya mata: “Gani ni na zo”. Hakiman Magajiyar Daura duk ‘yan tsatson Sarauta ne irin su:

    • Yarkuut
    • Gabsai
    • Dangawa
    • Saraki
    • Gizir-Gizir
    • Hamata
    • Jamata
    • Yambamu
    • Saudamat
    • Tawata
    • Mai Babban Ɗaki

    Muhimmancin Sallar Gani da Tasirinta

    Sallar Gani ƙasaitacciyar buki ce da ta cika dukkanin sharuɗan buki na al’ada guda huɗu (4). Duk wurin da sunanta ya kai, daga Daura ya fito, kuma a Daura aka san shi. Daga cikin muhimmancinta akwai:

    • Haɗin kan masarautun ƙasar Hausa gaba ɗaya Yannai bakwai da ƙannai bakwai.
    • Adana tarihi da al’adun ƙasar Hausa na Sarauta da masu mara wa na Sarauta baya.
    • Sake jaddada cewa, Daura ita ce tushen Hausa domin Hausawa su yi bugun gaba da ita.
    • Adana tarihin Sarautun mata na gargajiya na Magajiya da ɗiya mata ke yi.
    • Fito da ɗawainiyar mata a fagen adabi na Zabaya da Maguɗiya da suka soma mutuwa a yanzu.
    • Hawan daba, da riƙe martabarsa, da koyon sukuwa da dawaki na artabo da tsaro.
    • Sarƙuwar Sallar Gani da Mauludi wani sabon salo ne na ƙara adana Sallar Gani da jaddada ta.

    Sakamakon Bincike

    Sallar Gani tsohuwar al’ada ce da kowa ya tashi ya tarar da ita a Daura. Rashin samun Sarkin da ya fara ta a zamaninsa, ya nuna tun gabanin bunƙasar Sarautu a ƙasar Hausa ake gudanar da ita. Ga ɗan abin da bincike ya ƙyallaro akwai:

    • Tabbacin cewa, tun gabanin Musulunci ake yin ta, da addini ya zo aka cigaba har aka sako shi ciki.
    • Asalin bukin Sarautun mata ne gargajiya ya assasa shi ya wanzu har zuwa ga Daurama zuwa yau.
    • Ƙasar Daura Sallar Gani ta tsira, a ko ina aka gan ta balaguro ta je.
    • Asalin Sallar Gani kwana biyu ne yini ɗaya. Da dare Sarakuna ke tattaunawa da rana a yi hawa a watse.
    • Duk da muhimmancin Sallar Gani, da tsawon shekarunta, a ƙasar Daura kawai ake aiwatar da ita.

    Shawarwari

    Tsawon ƙarnukan da aka ɗauka ana yin abu ɗaya a Daura da sunan Sallar Gani, ya kamata a ƙirƙiro wasu abubuwa kamar:

    • Tsereniyar sukuwar dawaki, da fitar da zakara na kowace shekara, tare da kyautar kofi da kuɗi da ƙadara, da sunan ɗaya daga cikin Sarakunan Daura.
    • Samar da sahihin tarihin Daura, tare da ƙara sabunta shi kowace shekara, ana raba wa Daurawa da Sarakunan ƙasar Hausa.
    • A yi tunanin kafa gidauniya ta Sallar Gani, wadda za a tanadi kuɗin da za a gina makaranta da asibiti da filin motsa jiki na mata zalla, domin tunawa da sarautun mata da hidimominsu a gargajiyance.
    • Kowace shekara a riƙa gabatar da shahararriyar ƙasida ta fannonin ilmi daban-daban, da za a gayyato masana ƙwararru su rubuta bisa ga wani abu muhimmi na shekarar a kuma riƙa ba laccar suna “Daurama” a wallafa a raba wa jama’a.
    • A samu gagarumin gidan rediyo ko talabijin a buɗa a yi masa suna “Daurama” dukkan ma’aikatansu su kasance mata, kuma shirye-shiryensu ya shafi mata kawai.

    Naɗewa

    Ilmi ba kayan gidan kowa ba ne, wanda duk ya nemo shi, ya samo shi, ya zama kayan gidansu. Nagartattun al’adunmu da muke yi wa riƙon sakainar kashi su suka dabirta tarihin mu da irin gudunmuwar da ya bayar har aka kai ga harsashen kafa wannan asa tamu mai suna Nijeriya.

    Na yarda cewa, da wasa ake gaya wa wawa gaskiya, cikin bukukuwanmu na gargajiya nan za a tsinci tarihinmu da sana’o’inmuu da hikimomi da basirun da ke ciki domin amfanar da jama’armu. Harsashen kafa Bukin Sallar Gani shi ne samun haɗin kan masarautu da masu sarauta maza da mata, da tuni da juyayin fitar mulki ga hannun mata zuwa ga maza.

    Wannan shi ya sa Sarki da kansa ke zuwa ga babbar ‘yarsa Magajiya da sauran ‘ya’yan Sarauta mata waɗanda ba sa hawa karagar mulki kuma abin da suka haifa ba zai hau ba don ɗan mace ne. Cikin hikima, an girmama su an kyautata musu, kuma ƙasa ta zauna lafiya.

    MANAZARTA

    Adamu, M. (1977) “Towards the Definition of Hausa Culture in African Context” paper presented at Centre for Nigerian Cultural Studies, Zaria: Ahmadu Bello University.
    Ahmed, S. B. (1990) “Tsarin Sarautar Gargajiya a Haɗeja”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
    Balbasatu, I. (2009) “Gudummuwar Mata ga Havaka Rubutaccen Adabi”, kundin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
    Bargery, G. P. (1993) A Hausa-English Dictioanary and Eglish Hausa Vocabulary (2nd ed.) Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
    Barker, C. (2012) Cultural Studies: Theory and Practice (4th ed.) London: Sage Publications.
    Bichi, A. Y. (2011) “Bayajidda Legend in the 21st Century: A Reassessment”, in Yalwa, L. D. et al., (ed.) Studies in Hausa Language, Literature and Culture, Kano: Bayero University.
    Bunza, A. M. (2006) Gadon Fexe Al’ada, Lagos: Ibrash Islamic Publications.
    Bunza, A. M. (2009) Narambaɗa, Lagos: Ibrash Islamic Publications.
    Daura, H. K. (2016). “Kirarin Saraki a Bakin Mata: Nazarin Zabiyanci a Ƙasar Hausa”, kundin PhD, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
    Gama, A. M. (2012) “Tasirin Siyasa a Masarautun Gargajiya Musamman a Makarantun Sakkwato da Katsina da Kano da Daura Daga 1960-2000” kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
    Hauwa, R. D. (2005): Sarautar Mai Babban Ɗaki a Fadar Kano”, kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
    Hitti, P. K. (1961) History of the Arabs, London: Macmillan Company Limited.
    Ibrahim, A. (1991) Alhaji Muhammadu Bashar: A Biography, Katsina: Himma Press Limited.
    Ibrahim, M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Bahaushe ta Gargajiya”, kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
    Koforowola, E. O. (1982) “Hausa Performing Art and the The Emirs Court”, PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
    Mack, B. B. (2004) Muslim Women Sing: Hausa Popular Song, Blomington and Indianapolis: Indiana University Press.
    Magaji, A. (2002) “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Katsina”, kundin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
    Maimuna, L. D. (1987) “Fadar Daura”, kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
    Nuruddeen, M. (1982) “Sallar Gani a Daura”, kundin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
    Ramlatu, J. D. (2012) “Sarautun Ƙasar Daura da Muhimmancinsu ga Al’umma” cikin Champion of Hausa Cikin Hausa, Amfani, A.H. da Wasu (ed) Zaria: Jamhuriyar Ahmadu Bello.
    Saulawa, A. M. (2001) “Origin of the Hausa States Revisited” in Degel Journal, Faculty of Arts and Islamic Studies, Sokoto: Usmanu, Ɗanfodiyo University.
    Shafa’atu, M. T. (2013) “Kirarin Mata a Ƙasar Sakkwato”, kundin MA, Sokoto: Usmanu Danfodiyo.
    Smith, M. G. (1978) The Affairs of Daura, London: University of Califonia Press.
    The New International Webster’s Comprehensive Dictionary of the English Language Deluxe Encyclopedic Edition (1996).
    Tsiga, I. A. (1978) “Sarauniya Daurama”, takarda, taron Ƙungiyar Hausa, Kano: Jami’ar Bayero.
    Turai, U. M. Y. (1983) “Binta Zabiya da Waƙoƙinta”, kundin BA, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
    Wakili, H. (2005) Turawa a Ƙasar Haɗeja, Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Mutanen Da Aka Tattauna Da Su

    Sarkin Tarihin Daura Alhaji Muhammadu Lawan.
    Dr. Halima Kabir Daura, Dept. of African Languages and Culture, ABU Zaria.
    Malam Bala Safana Federal Government College Daura.
    Dr. Bashir Sallau Sarkin Aska Safana, Dept. of Nigerian Language Umaru Musa Yar’aduwa University, Katsina.
    Dr. Yakubu Aliyu Gobir Dept. of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University Sokoto.
    Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad Head Hausa Unit, Dept. of Languages, Sule Lamiɗo University Kafin Hausa.

    Danna nan don karanata Bikin Kamun Kifi 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani

    Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani

    Da yake mun ga yadda ƙagaggun labaran Hausa na baka suka sauya fasali bayan haɗuwar Hausawa da baƙi, musamman Larabawa. A wannan ɓangaren kuma an kalli yadda waɗannan ƙagaggun labaran  na gargajiya suka sauya fasali, suka koma a rubuce, ta yadda maimakon a kai da ake riƙe su, sai yanzu suka koma a rubuce, a zamanin zuwan Larabawa da Turawa.

    Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa a Zamanin Larabawa

    Ƙagaggun labaran Hausa sun sauya fasali ta wata hanyar daban bayan da Hausawa suka haɗu da Larabawa, ta inda a wannan karon aka mai da wasu daga cikin waɗannan ƙagaggun labaran a rubuce a maimakon a ka da suke adane.  Daga binciken da aka yi an fahimci babu adabin gargajiyar Bahaushe da ake da shi a rubuce, sai lokacin da Hausawa suka haɗu da Larabawa, inda suka fara yin rubutun su cikin Ajami.

    Masana da dama (dubi Magaji, 1982, Dokaji, 1978, Yahya, 1988, Gusau, 2008 da kuma Malumfashi, 2009) duk sun yarda da Musulunci ya shigo ƙasar Hausa da daɗewa, tun wajen ƙarni na goma sha ɗaya zuwa na goma sha uku. Su kuwa Magaji, 1982, da Abdullahi, 1997 sun ruwaito cewa, ‘a wajen ƙarni na 12 zuwa na goma sha uku, wato lokacin da sarkin Kano Naguji Ɗan Ɗariƙu (1194-1247) wasu Larabawa ‘yan kasuwa suka fara kawo Musulunci Kano.

    Daga baya kuma zamanin sarkin Kano Aliyu Yaji (1349- 1385) wasu Wangarawa mutanen ƙasar Mali suka fara zuwa ƙasar Hausa don ƙarfafa addinin musulunci. Sun zo Kano tare da litattafan koyar da addinin Musulunci, kuma suka kafa makarantu da masallatai.

    Tarihi ya nuna kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, Hausawa ba su da wata hanya tasu ta karatu ko rubutu. Adabin Hausa a lokacin na baka ne, ana kuma watsa shi ta baka, a kuma adana shi da kai. Saboda haka zuwan waɗannan malamai shi ne matakin farko na koyon karatu da rubutu a ƙasar Hausa.

    To sai dai, duk da bayyanar waɗannan malaman da kuma samun cikakkiyar hanyar karatu da rubutu bayan watsuwar addinin Musulunci da kuma samar da sababbin masu ilmi cikin al`umma, wannan bai haifar da wani abun a-zo-a-gani ba game da samuwar adabin Hausa da ta shafi addinin Musulunci ba.

    A wannan lokacin, duk faɗi-tashin da malamai da almajirai suka yi ta yi, ta tsaya ne a kan yadda mutane za su fahimci addinin Musulunci, da kuma yadda za su yi aiki da shi cikin al`amurransu na yau da kullum. Wannan ya sanya adabin Hausa bai samu wani canji ba, yana na dai a adane cikin ƙwaƙwalwar mutane, duk lokacin da  ake buƙata sai a aiwatar da baki kuma a inda ya dace, kamar dai yadda Sulaiman, 2008 ya ruwaito daga Hisket (1975).

    Sai daga baya ne malaman addini da sarakuna suka yi amfani da rubutun Ajami ƙwarai da gaske wajen aikawa da saƙonni zuwa ga ‘yan uwansu sarakuna da malamai. Malamai sun yi wallafe-wallafe da dama cikin ajami don watsa addinin Musulunci, wasu a tsarin waƙoƙi, wasu kuma maganganun azanci ne suka rubuce, wasu kuma fassara suka yi.

    Wannan ya sanya yawa-yawan ayyukan adabin Hausawa, musamman waɗanda suka shafi ƙagaggun labarai na gargajiya da waɗanda aka tsinto daga Larabci suka shigo da sabuwar riga ta rubutun Ajami da Larabci ta yadda daga baya za ka ɗauka cewa tun can asali da wannan rigar aka haife su.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Domin karanta Gwamutsuwar Labaran Gargajiya Na Hausa Da Baƙin Al’adu danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Gwamutsuwar Labaran Gargajiya Na Hausa Da Baƙin Al’adu

    Gwamutsuwar Labaran Gargajiya Na Hausa Da Baƙin Al’adu

    Abin lura a wannan sashe shi ne waɗannan adabin baka na Hausa masu alaƙa da ƙagaggun labaran gargajiya za a ga duk a kai suke, ana kuma gudanar da su da fatar baki, sai dai wasu sun canza fasali ko kuma siga sakamakon haɗuwar Bahaushe da baƙin al’ummu na kusa da nesa.

    Kafin mu fahimci yanayin canjin ya dace mu san cewa waɗannan ƙirƙirarrun labaran na gargajiyar Bahaushe da ya tashi ya gan shi cikinsu tsamo-tsamo sun taimaka masa sosai wurin fito da ɗabi’u da al’adunsa fili, ta yadda kowane ɗaya daga ciki aka ɗauka za a samu nason irin yadda Bahaushe ya tashi yana gabatar da rayuwarsa ta yau da kullum a cikin wannan zamani da suka wanzu.

    Waɗannan ƙagaggun labaran na Bahaushe sun samu ne kafin zuwan baƙi, bayan haɗuwarsa da Larabawa sai suka fara sauya fasali. Wasu, kamar yadda muka yi bayani da ma Bahaushe yana da su, amma zuwan Larabawan sai yaƙara fiddo da su, ko kuma a ce cuɗanyarsa da Larabawa sai suka fito da wasu sassan adabin nasa na baka cikin waɗansu kamanni daban, waɗanda tun kafin zuwansu, yake tare da su ko kuma ya samar da wasu sababbi da ya gino su daga cuɗanyarsa da Larabawan, a nan ana magana ne kan almara da ƙissa da kuma hikaya da sauransu.

    Ita dai almara kalma ce ta Larabci, kamar yadda muka yi bayani Bahaushe yana da labarai nasa na ban dariya da sanya nishaɗi da raha, amma ba za a kira su labaran jaruntaka ko na matafiya ko kuma na yaƙe-yaƙe ba. Bayan Bahaushe ya aro kalmar almara ne da abin da ke cikinta daga Larabawa, sai ya haɗe su suka zama labarai na ban dariya da wasa ƙwaƙwalwa da makamanta su.

    Wannan ne ya sa aka ba ta ma’ana mabambanta, wasu masanan na ganin ‘almara ita ce hanyar gabatar da wasu matsaloli kara-zube ko kuma ta hanyar labari, sannan a buƙaci mai sauraro ya bayar da amsa ko kuma ya zaɓa tsakanin abubuwan da aka ambata, (Magaji, 1982:5).

    Shi kuwa (Gusau, 1995:59), yana ganin almara wani shiryayyen labari ne na hikaya da jawo hankali da ake bayarwa don kaifafa tunanin masu sauraro ko nishaɗi. Amma (Umar, 1983:14) na ganin almara ba ta fiye tsawo sosai ba; sai dai takan ƙunshi wani abu na ban dariya ko ƙalubalen da za a nemi mai sauraro ya warware. Haka kuma (Ɗangambo, 1984:16) na ganin  almara labari ne ƙirƙirarre wanda ba lalle ne ya auku ba.

    Abu muhimmi dai shi ne, dama can tun kafin Hausawa su haɗu da Larabawan suna da ire-iren waɗannan labararrukan na ban dariya da sa nishaɗi, sai dai kawai a ce dacewarsu da ire-iren na Larabawan ne waɗanda suke kira Al-mizahu. Saboda haka tattaruwa aka yi tsakanin labaran Hausawa na gargajiya da irin na al’amarar Larabawan a waje ɗaya domin dacewa da zamani.

    Muhimmancin almara kamar sauran fannoni ne na sassan adabin bakan Bahaushe bai wuce haɓaka basira da ƙara hankali da kuma zurfafa tunanin mai sauraro ba. Ita ma hikaya kamar almara an aro sigar ne daga Larabci labaran gargajiya ne waɗanda akasari na masu hikima ne, wato ko dai sun faru da gaske saboda abin da suke koyarwa aka kawo shi, ko kuma ana tunanin idan aka sarrafa hikimar ta wannan hanyar za a ci nasara.

    Duk da cewa kalmar ta Larabci ce amma wannan ba wai yana nufin Hausawa ba su da labaran hikaya ba ne tun asali, a a, su ma Hausawa suna da labaran hikaya tun asali, waɗanda suke yi ba wai sai da suka haɗu da Larabawa ba. Sannan kuma akwai wasu labarai da dama da suka danganci hikayoyin da Hausawa suka samo daga na Larabawa. Tasirin gargajiya da hulɗa da al’ummomi da shigowar addinin Musulunci da karatun littattafai shi ne ya haifar da samuwar hikaya a tsakanin Hausawa (Gusau, 1995:65).

    Sai dai su al’ummar ƙasar Larabawa na tun asali, wato na lokacin jahiliyya, suna ganin hikaya na nufin kwaikwayon wani abu da wani ya yi, sai daga baya ne suka faɗaɗa ma’anar ta koma ba da wani labari. Da Hausawa suka aro kalmar, suka sanya ma labarai irin nasu da suke ba junansu, sai suka kira ta da hikaya.

    Hikaya labari ne da ake ba da wa da ya faru dangane da mala`iku, ko aljannu ko mutane ko rauhanai ko dabbobi ko tsuntsaye ko kuma ƙwari. Wani lokaci kuma takan ɗauki yanayin ƙago wasu labaran don ƙarin bayani kan wani abu ko kwaikwayon sa.

    Irin wannan yanayi ne ƙasar Hausa da Hausawa suka samu kansu dangane da labaransu na gargajiya da yadda suka shiga cikin wani fasali bayan haɗuwarsu da baƙi, musamman Larabawa da yadda ya sa suka gina waɗansu sababbin fasaloli da suka aro daga Larabawan. Wannan yaƙara tabbatar mana da cewa wannan tada ta kasance da daɗewa tsakanin Hausawa.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Ƙagaggun Labaran Hausa Cikin Tarihi danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

  • Ƙagaggun Labaran Hausa Cikin Tarihi

    Ƙagaggun Labaran Hausa Cikin Tarihi

    Babi Na Biyu: 

    A cikin wannan babin an bi salsalar ko kuma an kawo taƙaitaccen tarihin samuwar ƙagaggun labaran Hausa ne. An dubi yadda aka fara samar da labaran Hausa na gargajiya kafin su koma a rubuce, da kuma yadda suka samu cuɗanya da baƙin al’adu.

    Ya’allah baƙin nan na kusa ne a cikin ƙasar Hausa ko kuma na nesa kamar Larabawa da kuma Turawa domin ganin yadda ƙagaggun Labaran Hausa suka samu canji da fasalce-fasalce daga garjiya zuwa zamani.

    Ma’anar Ƙagaggun Labaran Hausa

    Masana da dama sun kawo ma`anar ƙagaggen labari da cewa warwarar bayani ne bi-da-bi a kan aukuwar wasu abubuwa da yadda suke gudana, saboda haka ma’anar labari ta haɗa da jerin bayani, da ambaton dukkan muhimman al’amurra da iya siffanta su a lafazi mai kyau (Zarruƙ, 1990).

    Ke nan a iya cewa ƙagaggen labari ya ƙunshi waɗansu labarai masu ɗan tsawo, ana kuma yin su ne a lokacin hira kamar, labarai na jarumai ko `yan fashi ko na almara, irin su labaran hikima ko wasa ƙwaƙwalwa da kuma tatsuniyoyi irin na su gizo da ƙoƙi da hikayoyi na iskokai ko kuma aljannu.

    Haka kuma Magaji (1982:47) ya ce labarin zube (ƙagaggen labari) ya ƙunshi labarai masu ɗan tsawo kamar tatsuniya (Ga ta nan), da almara, da hikayoyi, da ƙissoshi da sauransu. Haka kuma akwai guntattakin maganganu na hikima kamar kirari, da karin magana, da kacici-kacici, da zaurance, da salon magana da dai sauransu.

    A taƙaice za a iya cewa labarai sun kasu gida biyu; na haƙiƙa ko kuma masu ƙamshin gaskiya, wanda aka fi sani da ƙissa ko tarihi ko tarihihi da kuma na ƙirƙira ko kuma ƙagaggen labari, wanda bai da asali ko tushe.

    Saboda haka ana iya bayyana ƙagaggen labari da wata hikima, ko basira ko tunani irin na ɗan Adam da ya ƙaga kan wani abu wanda bai ji ba, kuma bai gani ba, ya furta shi da fatar baki domin watsa wata manufa don koyarwa ko kuma hannunka-mai-sanda da jagora don nishaɗi.

    Akwai ire-iren waɗannan ƙagaggun labaran da yawan gaske a cikin adabin Hausa da suka haɗa da tatsunniya da almara da hikaya da zaurance da salon magana da kirari da take da zambo da sauransu da dama.

    Haka kuma ana iya kallon ƙagaggun labarai na baka da zance na hikima da ake shiryawa cikin azanci da yake zuwa a kara zube, kuma mai ɗan tsawo, mai kuma ban sha’awa da koyar da dabarun zaman duniya ta hanyoyi da matakai daban-daban.

    Samuwar Ƙagaggun Labaran Hausa

    Tun kafin haɗuwar Bahaushe da baƙi, yana da hanyoyi da dama da yake amfani da su domin ilimantar da kuma tarbiyantar da ‘ya’yansa ta yadda za su tashi cike da dabaru da kuma ilmin zamantakewa. Waɗannan hanyoyin kuwa su ne ire-iren ƙagaggun labaran da ya tanadar, sun kuwa haɗa da maganganunsa na azanci da sauransu.

    Tambayar da aka yi ita ce yaya aka yi waɗannan abubuwa suka samu? Daga waɗannan maganganun azanci ne aka samar da ƙagaggun labarai, waɗanda tushensu shi ne adabin bakan al’umma.

    Kuma kamar yadda masana suka nuna wannan ba sabon abu ba ne, domin kuwa ko a zamanin ci gaban Girkawa, ire-iren waɗannan sassan adabin aka fi ba muhimmanci wajen tarbiyantar da jama’a, domin labarai da maganganun azanci da suka yi tashe a wancan lokacin da baki ake aiwatar da su, daga wannan birni zuwa wancan (Malumfashi, 2004:6), sun kuma taimaka wajen ilmantar da al’ummar.

    A nahiyar Asiya kuma irin waɗannan al`adu na fasahohin baka  sun ginu, ta yadda a fadojin masu mulki da masu arziƙi, an samar da manyan masana labarai da maganganun azanci don su zama tamkar makaranta ta koya wa ‘ya’yan masu mulki da sauran masu arziƙi tarbiyya, su kuma nishaɗantar da al`ummar nahiyar. Labaran Sansikirti a Indiya da maƙwabtanta duk irin wannan fasalin suka ɗauka, kuma da yawa daga ire-iren waɗannan labaran sun kasance asalinsu ɗaya ne, wato tatsuniyoyi da almarorin jama’ar wannan yanki ne, (Malumfashi, 2004:6)

    Saboda haka, muna iya cewa a ƙasar Hausa ma irin wannan adabi ya yi tashe a lokacin maguzanci ko jahiliyya. Wato gargajiya ita ce jahiliyyar Bahaushe, lokacin da al’ummar Hausawa ba su waye ba ko kuma lokacin ba su haɗu da wasu baƙi ba, wannan zango ne tsakanin ƙarni na 10 zuwa na 11.

    A wannan lokacin ana neman matakai waɗanda za a fara rayuwa ta kan su, lokaci ne na neman wurin zama da abinci da gina shugabanci da yadda za a tsara shi, da kuma tsarin  sana`o`i daga wurin mutane. Don haka, ilahirin wannan lokaci ya ƙunshi fafutukar gina al`adu na gargajiya. Wannan shi ne zangon da ya samar da adabin baka da sassansa da lokacin da ake ganin ana da adabin ka na tsantsar Hausawa.

    A wannan lokacin ne aka samar da kirare-kirare na bauta da kirarin noma da na farauta da kuma waƙe-waƙen mata da labarun gargajiya da labarun tatsunniya da na jaruntaka da kuma na ban dariya (Muhammad, 2005:6).

    Saboda haka ko da irin wannan adabi na baka ya ginu, ya tashi ne kurum ya gan shi cikin al`ummar Hausawa, ta yadda Hausawan ke koyar da ‘ya’yansu dabarun zaman duniya ta yin amfani da sassan adabin baka na zube (ƙagaggun labarai) da suka haɗa da tatsuniyoyi da labarai da makamantan su. Bari mu dubi wasu daga cikin waɗannan sassan ƙagaggen labarin Hausa, mu ga yadda suke a taƙaice.

    Tatsuniya

    Tatsuniya tana daga cikin manyan rassa na adabin bakan Bahaushe, kuma ƙagaggen labari ne da Bahaushe kan ba ‘ya’yansa domin tarbiyya ta yadda za su tashi cikakku kuma kamilan mutane.

    Masana da dama sun daɗe suna kallon tatsuniya ta fuskoki daban-daban, Umar (1978: 25) yana cewa “tatsuniya wani ƙagaggen labari ne da magabata kan shirya, musamman don tarbiyya bisa ga tsarin gargajiya”. Amma shi kuma (Gusau, 2006:112) cewa yake “tatsunniya wani tsararren labari ne wanda magabata (musamman tsofaffin mata) suke shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da raha ga rayuwa da kuma cinye dare”.

    Duk da irin yadda tunani ya bambanta tsakanin masana game da ma’anar tatsuniya, sai dai masana da dama (Yahya, 1972 da Umar, 1978 da Alhassan da wasu, 1982 da Ɗangambo, 1984) duk sun yarda da cewa tsofaffi ne kan shirya tatsuniya, kuma ƙagaggen labari ne da akan shirya domin ilimantarwa ga yara.

    Daga nazarin da aka yi an fahimci cewa tun can farkon al`amari Hausawa suna da labaransu na tatsuniyoyi waɗanda su ne suka ƙirƙiro su da kansu don nishaɗi da koyarwa. Sun mallaki wannan hanya ta bayyana matsayinsu, musamman ga yara, tun jimawa, ba sai da suka cuɗanya da wata al`umma ta koya musu ba.

    Hasali ma dai ba za a iya bugun gaba a ce ga lokacin da aka fara yin ta ba. Tatsuniya gadon gado ce, ta ginu a sakamakon tasirin al`adar rayuwa ta Hausawa, har ta zama ruwan dare game duniya (Yahya da wasu 1992). Haka kuma, labari ne ƙagagge ake harhaɗawa a tayar da gangar jikin tatsuniya, har a kaɗa ta, ta bayar da wani amo da ake son sadarwa ga masu saurare.

    Saboda haka muhimmancin tatsuniya ya fi gaban a ambata, domin kuwa tatsuniya makaranta ce ta malam Bahaushe, ta nan yakan ilimantar da `ya`yansa dabarun zaman duniya tun kafin Bahaushe ya sadu da baƙi. Al`adun Hausawa ne suka haifar da tatsuniya kuma wajibi ne a yi la`akari da cewa tatsuniya ta samu tun kafin Bahaushe ya iya karatu da rubutu balle ya kafa makaranta.

    Tatsuniya ta wanzu cikin al’ummar Hausawa wadda tunaninta  da hikimominta da fannonin ilminta duk da baki ne akan baza su, daga wannan mutum zuwa wancan da kuma wannan zamani zuwa wancan. Koyo da koyarwa, ɗabi’ar ɗan Adam ce, saboda haka ya zama tilas ga Bahaushe ya ƙirƙiro wata hanya ta aikawa da hikimominsa da al’adunsa daga zamani zuwa zamani.Ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ita ce tatsuniya. Ta amfani da tatsuniya Bahaushe kan kaifafa tunanin ‘ya’yansa.

    Labari

    Labari shi ne wani zance da yake abkuwa tsakanin mutane ko tsakanin mutum da mutum wanda ya wuce tsayawa a gaisa kurum. Kusan duk wani abu da ya danganci samar da wani abu game da wani abu mai tsawo ko gajere ana iya kiranshi labari.

    Shi dai labari zai iya kasance wa tsararre mai ma`ana sannan kuma yana da farko da kuma ƙarshe wanda kuma zai iya cusa tarbiyya ko kuma a koyi wani darasi daga cikin shi. Kazalika, labari na iya kasancewa a rubuce ko a magance.

    Labari na zuwa ta hanyoyi daban-daban, kamar Yanayin abinda labarin yake ɗauke da shi ta fuskar jigo ko siffa, wato dai a taƙaice abinda yake koyarwa. Kamar labarai na jaruntaka, da tarbiyya, da girmamawa, da zaman duniya da sauransu da dama.

    Ƙissa

    ƙissa kalma ce da aka samo daga harshen Larabci wadda ta shige tsundum a cikin adabin Hausa. Ita da wannan kalma tana ɗauke da ma’anoni biyu ne a cikin harshen Larabci. A ma’ana ta  lugga ƙissa na nufin bibiya ko ƙididdigewa, wato mutum ya bi diddigin wani abu har zuwa ƙarshensa.

    A ma’ana ta fannin ilimi kuwa, ƙissa na nufin ba da labarai dangane da mutanen da suka shuɗe, ko kuma ba da labari a kan waɗansu abubuwa da suka auku a da, ko kuma wani labari da ke kara zube da ya ƙunshi shiryarwa zuwa ga addini ko gaskiya ko neman tsira kan wani abu.

    A ra`ayin masana  (Gusau,1995:68) an fi danaganta ma’ana da manufar ƙissa a kan labarun da suka danganci addini kawai. Wato bayanai a kan rayuwar annabawa da sahabbai da waliyyai da sauransu. Duk da haka akwai wasu labarai na ƙayatarwa da jawo hankali da za a iya kiran su da ƙissa, kamar irin ƙissoshin da suka shafi soyayya. Don haka akan ce ƙissa wata hanya ce ta cusa wata manufa cikin zukatan masu saurare.

    Duk da irin wannan hasashe game da ƙissa an fahimci cewa ta shafi abin da ya biyo labaran Annabawa kamar yadda ya zo cikin Alƙur’ani mai girma, inda ake da surori da suke bayyana labaran annabawa da aka zayyana a cikin Alƙur`ani.

    Sai dai ita ƙissar da Bahaushe ke bayani ta shafi wadda aka gina bisa tunanin Bahaushe, wato ga yadda labarin yake a zahiri amma a ƙara masa wani abu ko dai don daɗin labarin ko kuma domin a ƙara ƙayatar da mai sauraro. Misali ƙissar Annabi Yusuf  ko ta Annabi Sulaiman ko kuma ta Annabi Nuhu za a same su da ɗan bambanci da wadda Alƙur’ani ya zo da ita.

    1. Ƙissar Cinye Dare: Wadda ta ƙunshi labarai da zuntuttukan da mutane suke yi don cinye ko ƙarasa dare.
    2. Ƙissar Addini: Wannan ta ƙunshi labarai ne da ake tsarawa a kan wani abu da ya auku na addini a lokacin annabawa da sahabbai da waliyyai da shehunnai da sauransu.

    A Hausance ke nan, ƙissa labari ne na gaskiya da aka bayar a kan rayuwar Annabawa da sahabbai ko waliyyai ko shehunnan malamai, ko wasu bayin Allah da sauransu waɗanda suka shafi addinin Musulunci, musamman waɗanda Alƙur’’ani da hadisai suka kawo bayanansu.

    Masana (Gusau, 1995: 69) sun raba ƙissa zuwa gida huɗu;

    1. ƙissar Annabawa wadda ta bayyana rayuwarsu ta haƙiƙa da irin gwagwarmayar da suka sha wajen isar da saƙon Ubangiji.
    2. ƙissar sahabbai da waliyyai da shehunnai wadda ke ƙunshe da rayuwarsu.
    3. ƙissar sauran bayin Allah wadda ke nuna rayuwar wasu bayin Allah nagartattu waɗanda suka miƙa wuyansu ɗungurungum zuwa ga addini Allah
    4. ƙissar kangararrun mutane waɗanda suka bijire wa addinin Allah.

     Tarihihi

    Asalin wannan kalma ta tarihihi an samo ta ne daga kalmar tarihi ta hanyar liƙa wa kalmar ɗafe-ƙeya na ‘hi’, sai ta koma ‘tarihihi’. Sai dai abin lura a nan shi ne tarihi dai yana nufin wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma.

    To amma shi tarihihi za a iya cewa  wani labari ne na wasu abubuwa da suka taɓa wakana na haƙiƙa a cikin al’umma, sai dai irin wannan labarin yana cakuɗe da wasu abubuwa da ba a tabbatar da faruwarsu ba. Don haka idan aka ce tarihihi, a taƙaice ana nufin gurɓataccen tarihi, wanda aka cakuɗe shi tsakanin gaskiya da ƙarya.

    Tarihihi labari ne na da ake riƙe da shi a kai, kuma kasancewar kai ba mariƙi ba ne, ballantana har ya yi ajiya, sai wajen ruwaito abubuwan da suka faru a rayuwa ake gwama su da waɗanda ba su faru ba. Wato dai yawancin tarihihi ya ƙunshi labarai ne na kunne-ya-girmi-kaka, waɗanda ba a iya tabbatar da abkuwarsu.

    Akwai tarihihi kala-kala a ƙasar Hausa, sai dai waɗanda suka yi tashe sun haɗa da na tarihihin zuwan Bayajidda ƙasar Hausa, da na sarkin Katsina Korau, da WaliƊanmarna, da WaliƊanmasani, ko naƊanwaire da sauran su.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Domin karanta Al’adun Hausawa Na Jiya Da Na Yau danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

     

     

  • Ina Mafita?

    Ina Mafita?

    Kowacce cuta tana da magani, kuma kowace matsala tana da mafita, don haka mafita ga wannan mummunan hali da muka shiga ya zama wajibi a kanmu mu yi tunanin samar da hanyoyin da za a iya bi don rage ko ma kawar da wannan matsala baki daya, tunda illolin shaye-shayen kayan maye yana shafar al’umma ne baki ɗaya.

    Don haka yaƙi da su wani alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, wato sai an yi taron dangi, kowa sai ya ba da tasa gudummawar daga kan gwamnati da hukumomin suke kula da hana fatauci da kuma shan miyagun ƙwayoyi da ƙungiyoyi da kafafen yaɗa labarai da malaman makarantu na addini da na boko da iyaye da mariƙa da yayye da ‘yan uwa da abokan arziƙi da su kansu matasa maza da mata da kuma sauran jama’ar gari.

    Ya zama wajibi a yi duk abin da za a yi wajen tabbatar da ganin an yi nasarar shawo kan wannan mummunar ɗabi’a, don abin ya fi ƙarfin mutum ɗaya ko hukuma ita kaɗai, abin ya zama tamkar kan ɗaki sai an taru. A nan, za a yi bayanin ire-iren matakai da gudummuwoyin da kowa zai iya bayarwa kamar haka:

    Matasa Maza da Mata

    1. Matasa su lura sosai da ire-iren abokan da za su yi abota ko ƙawance da su.

    2. Ya kamata ko ma ya zama wajibi matasa su lura da ire- iren masoyan da za su yi soyayya da su, domin shiga soyayya da mashayi ko mashayiya yana iya haifar da koyon wannan mummanar harka ta shan ƙwayoyi da abubuwan masu sa maye, musamma tun da soyayya tana da matuƙar tasiri a rayuwar matasa musamman mata, waɗanda suke da raunin zuciya, yanzu-yanzun nan sai a juya musu tunani a sanya su a wata hanya marar kyau.

    3. In ba ki fara ko ba ka fara shan kayan maye ba to kada ki soma ko kada ka soma shan su. In kana sha ko kina sha, ka yi ƙoƙari ko ki yi ƙoƙari ki daina shi ne mafi alfanu ga rayuwar kowane matashi ko matashiya; Iyaye su bi hanyoyin lura da irin ƙawaye ko abokai da kuma samarin da ‘ya’yansu suke yin hulɗa da su.

    Don a makaranta ana samun miyagun’ abokai maza da mata, kuma in suna yin irin waɗannan shaye-shayen ƙwayoyi sukan koya wa ƙawaye ko abokai ko kuma masoyansu. Saboda haka iyaye su dinga bibiyar lamuran ƙawayen ‘ya’yansu a makaranta ko a gida ko kuma masoyan (samari) da suke tare da su. Yin hakan  yana da matuƙar  muhimmanci.

    Iyaye da Mariƙa

    4. Iyaye lallai su  ɗauki matakin sanya ido wajen tarbiyyar yara.

    5. Su lura wajen sanin halayen matan aure ko zaurawa da ‘ya’yansu suke shiga gidajen su suna yin hulɗa da su. Domin ana samun wasu gidajen matan ko zawarawan suna zama matattarar waɗannan matasa masu irin halayen na shaye-shayen magunguna don su koyi maye, kuma wasu a nan suke koya wa wasu matan ko ‘yan matan; kai har da yara matasa masu shiga gidajen sukan koyi irin wannan harka ta shaye-shaye.

    6. Duk lokacin da iyaye suka ga ‘ya’yansu da wani magani na ƙwaya ko na ruwa ne lallai su matsa da tambayar su da bibiyar sanin ko na menene.

    7. Iyaye su dinga kai ziyarar ba zata cikin dakunan ‘ya’yansu kuma su dinga bincika jakunkuna da akwatunansu da sauran wuraren da ake tunanin yarinya za ta dinga ɓoye wasu abubuwa da ba ta so a gani.

    8. Iyaye su dinga sanya ido a kan lokutan da ‘ya’yansu suke fita daga gida da kuma lokacin da suke dawowa, kada a bar wa yarinya damar ta dinga kulle gida da kanta, domin wannan wata wawakekiyar ƙofa ce ta yarinya ta yi abin da ta ga dama iyaye ba su sani ba.

    9. Idan iyaye suka ga ‘ya’yansu ko maza suka ga matansu suna yawan barci babu gaira babu dalili, nan ma su matsa su gano menene yake jawo hakan.

    10. Iyaye ko mazaje su dinga yawan kula da kan harshen ‘ya’yansu da kuma matan aurensu. Lokuta da dama masu tsotsar wata ƙwayar kan harshensu yana nuna launin kore ko shuɗi saboda yawan tsotsar ƙwayar da suke yi.

    11. Iyaye su guji sanya ‘ya’yansu yin aikin ƙarfi wanda ya fi ƙarfin ‘ya’yan don hakan yana sa su sha ƙwayoyin da za su ji ƙarfin da zai sa su yi aikin da ya fi ƙarfinsu, wanda daga nan in ba a yi saʼa ba sai shan ire-iren waɗannan ƙwayoyin ya zama jiki ga ‘ya’yan.

    12. Iyaye su guji cusawa ‘ya’yansu dogon burin da zai sa su neman duniya ido rufe.

    13. Su taimaka wa hukuma wajen yaƙi da taʼammali da miyagun ƙwayoyi ta duk hanyar da Allah Ya huwace musu.

    14. Ya zama wajibi iyaye su dinga koya wa ‘ya’yansu yadda ake zaɓin miji na gari da zaman aure da kula da miji da abinci da kula da yara da sauransu.

    Gwamnati da Hukumomi

    15. Gwamnati ta samar wa da matasa aikin yi wanda zai hana su zaman banza da zai shigar da su wasu tunane- tunane da kuma faɗawa cikin wannan harka ta shaye- shaye.

    16. Ta dinga shirya tarukan ƙara wa juna sani da yaƙi da wannan harka ta shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

    17. Ya kamata hukumomin da suke kula da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA da hukamar kula da ingancin magunguna da abin ci da sha wato NAFDAC su ci gaba da sa ido sosai a kan wannan matsala, sannan kuma su matsa kaimi a kan kantunan sayar da magunguna don a sami raguwar sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma magunguna marasa inganci.

    18. Su ci gaba da taimakawa wajen faɗakar da matasan da shan ƙwaya ya zamar musu jiki, ta hanyar kawwame su ɗaɗɗora su a kan tafarki mai kyau.

    19. Waɗannan hukumomi in sun kama masu sayar da miyagun ƙwayoyi masu sa maye a daina sakin su a tabbatar an zartar musu da hukunci mai tsanani don wasu nan gaba kada su yi.

    20. Masu sayar da miyagun ƙwayoyi su ji tsoron Allah su daina, su sani duk abin da suka aikata akwai ranar sakamako. Ba kawai duniya da abin da za su samu za su duba ba, su dubi Allah da ranar lahira.

    21. Gwamnati da hukumomi kowane lokaci a kai a kai su dinga shirya bitoci da kwasa-kwasai ga hukumomin tsaro da kula da shige da fice da hana fatauci da sayar da miyagun kƙwayoyi kuma a samar musu da wadatattun kayan alki kuma na zamani kamar yadda ƙasashen da suka ci gaba suke yi.

    Masu Sarautun Gargajiya

    22. A matsayin masu riƙe da sarautun gargajiya waɗanda ake girmamawa, kuma suke kusa da al’umma, ya zama wajibi a gare su su riƙe abubuwan da suka saba yi tun da na sa ido da tattara bayanai wanda masu unguwanni da dagatai da hakimai da sarakuna suke yi a cikin al’ummarsu, kuma su isar da shi ga gwamnati.

    ‘Yan Majalusun Jiha Da Na Tarayya

    23. ‘Yan majalisun dokoki na jiha da na tarayya ya zama wajibi gare su su dubi wannan al’amari su samar da dokoki masu tsauri ga mutanen da suke yaɗawa da kuma tallata miyagun ƙwayoyi ga jama’ar su.

    Alƙalan Kotunan Jihohi Da Na Yanki Da Kuma Na Tarayya

    24. Ya kamata alƙalan kotunan jihohi da na yanki da na tarayyar Nijeriya su daina jan ƙafa wajen zartar wa da masu safara da fatauci da sayar da miyagun ƙwayoyi kai har ma da dillalai da masu jirage na ruwa da na sama da motocin dakon kaya da masu manyan ma’ajiyun kayayyaki wato sito, kotu ta dinga hukunta su ba sani ba sabo.

    Kantunan Sayar Da Magunguna

    25. Kantunan sayar da magunguna su yi taka tsantsan wajen sayarwa da matasa magunguna barkatai, su dinga bibbiyar dalilan da ya sa matasa suke zuwa sayen magani domin ta yiwu ba an zo saya saboda ba a da lafiya ba ne, sai don a sha a yi maye, a yi mankas. Yin haka zai taimaka mana ƙwarai da gaske wajen rage waɗannan masifu da suke bibiyar mu.

    Masu Sayar Da Magunguna A Cikin Baka (Kan Faranti Ko Kwali)

    26. Ya zama wajibi masu kantafi da rayukan jama’a a kan baka ko farantai ko kwalaye ko masu baje shi kamar ana sayar da gyaɗa a cikin kasuwa waɗanda ake kira (kyamis ba ƙyaure), su lura da wannan sana’a tasu da yadda take jefa rayuwar al’umma a ciki haɗari marar iyaka, wanda dama gwamnatocin Afrika da duniya baki ɗaya ba su yi naʼam da tsarin wannan sayar da magani a kan titi ba, su dubi Allah su sami matsuguni kuma su sami horo da izini daga hukuma don su yi wannan san’a cikin doka da tsari, kuma su tsira daga fushin Ubangiji.

    Masu Magungunan Gargajiya

    27. Masu magungunan gargajiya da suke amfani da amsa kuwa (lasifika) su dinga zuga magungunan da suke sayarwa suna maganganum batsa a cikin tallace tallacensu, suna kira ga matasa, kuma matasan suna saya suna amfani da shi ba bisa ƙa’ida ba, ya kamata su daina su kuma sani yin hakan yana tunzura maza da mata suna affakawa ga wata rayuwa da ba ta dace ba musamman ta shaye-shaye, zai fi kyau su sami waje su zauna suna sayar da magungunansu cikin tsari da doka.

    28. Haka su ma ‘yan masu ganye, mata masu bin gidajen matan aure, musamman ma masu sayar da magungunan mata, su sani suna haifar da illoli ga matan, domin wasu mata in sun yi amfani da ire-iren waɗannan magunguna yana cutar da rayuwarsu, daga cikin jikinsu da wajen jikinsu da kuma ƙwaƙwalwarsu, tunda an sami misalai da dama na irin ɓarnar da waɗannan magunguna suka yi ga mata, na aure da zawarawa da ‘yan mata, kuma sayar da ire-iren waɗannan magunguna yana haifar da zinace-zinace tsakanin matasa.

    Ƙungiyoyi

    29. Ƙungiyoyi waɗanda ba na gwamnati ba, wato masu zaman kansu su dinga shirya tarukan ƙarawa juna sani da wayar da kai da kuma yaƙi da waɗannan abubuwa da suka addabe mu, wato shaye-shayen ƙwayoyi masu sa maye, musamman ga mata.

    30. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam su daina ɗaure wa masu fatauci da sayar da miyagun ƙwayoyi gindi na cewa an tauye musu haƙƙi ko an ci zarafinsu, domin illolin da suke haifarwa ga al’umma suna da yawa ƙwarai.

    31. Ƙungiyoyin sanya ido tsakanin al’umma su dinga nemo matasan da suka faɗa wannan yanayi na shaye-shaye don a kauwame su a saita musu tunani da tafiyar da rayuwarsu, domin gwamnati kawai ba za ta iya yin wannan aiki ita kaɗai ba, sai an yi taron dangi.

    Malaman Makarantun Addini

    32. Malaman makarantu na addini su ne za su yi jagoranci wajen yaƙi da shaye-shaye ta hanyar yin bayanai a wajen koyarwarsu da wa’azi da nuna illar shan duk wani abu da zai jirkita hankali da kuma irin matsalolin da shaye-shaye suke haddasa wa mutum a rayuwarsa da kuma irin abin da zai haɗu da shi a wajen Ubangiji ranar ƙiyama.

    33. A cikin huɗubobin limaman masallatai su dinga sanya wannan batu na shaye-shaye a ciki.

    34. Ya kamata makarantu su dinga fito da wasu darusa waɗanda ba sa tsarin koyarwa na jiha ko na tarayya, gyaran ƙafa da farce da ƙunshi sabulu da bambita da kitso da gyaran gashi wanki da guga da ɗinkin hula da kwaɗo da linzami da dafa abinci da sauran su.

    Malaman Makarantun Boko

    35. A dinga yin addu’a bisa neman kariyar Allah a kan lamuran da suke damun rayuwarmu baki ɗaya, a duk lokacin da aka kammala karatun, makarantar addini.

    36. Makarantun boko su dage wajen yaƙi da shaye-shaye ta hanyar sanya ido ga ɗalibansu wajen abubuwan da suke shiga da shi aji na ci ko na sha ko na shaƙawa.

    37.Hukumomin makaranta su dinga kai ziyarar ba-zata a ɗakunan kwanan ɗalibai don bincikar kayan maye in akwai su.

    38.Ƙungiyar iyayen yara da malamai su dinga aiki tare wajen binciken haɗin gwuiwa a ɗakunan ɗalibai, duka ɓangarorin su dinga sanar da juna ire-iren bayani da suka samu game da yaran a gida ko a makaranta, wannan zai jawo raguwar waɗannan lamura.

    39.Su dinga yi wa dalibansu faɗa a game da abubuwan da za su yi amfani da su na sha, su kuma  nuna musu kada su yi abota da mutanen banza, don yin abota da mutanen banza yana sa wa a koyi munanan ɗabi’u.

    40.Su dinga jawo dalibansu a jikinsu su kuma nuna musu illolin shaye-shaye, ko cewa sai an sha ƙwaya za a yi  karatu ko za a iya shiga aji don ɗaukar karatu, sannan su dinga shirya wasannin kwaikwayo da za a yi wani batu na illar shaye- shayen miyagun ƙwayoyi. Kuma a dinga shirya gasa tsakanin ɗalibai ta yin rubutu a kan shaye shaye da illarsu ga rayuwar al’umma.

    41.Ya kamata makarantu su dinga fito da wasu darusa waɗanda ba sa tsarin koyarwa na jiha ko na tarayya ba, kamar na ƙananan sana’o’i irin su gyaran waya da ɗaukar hoto da kula da shuke-shuke da sayar da ruwa zobo da kunun zaƙi da kowane irin abubuwan sarrafawa da kuma kayan ƙwalam da maƙulashe kamar nakiya da alkaki da dubulan da fanke da acama da awara da gurasa da dai sauran kayan ciye-ciye da sauransu.

    Masu Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi

    42.Ya kamata masu sayar da miyagun ƙwayoyi su kwana da sanin cewa akwai hukunce-hukunce masu tsauri da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tana da ga masu wannan mummunar sana’a, don haka su guji fushin hukuma da kuma fushin Ubangiji, domin an ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, don haka kere na yawo zabo na yawo wata rana za a gamu.

    Kuma su tuna da rayuwar duniya ba ita kaɗai ce ba akwai ta lahira, duk abin da suka yi na ɓata tarbiyyar al’umma don su sami kuɗi, ranar alƙiyama za su samu sakamakon duk abubuwan da suka aikata na lalata tarbiya da rayuwar jama’arsu.

    Kafafen Yaɗa Labarai: Talbijin da Rediyo da kuma Yanar Gizo

    43.Ya kamata kafafen yaɗa labarai su dage wajen wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shaye.

    Talabijin

    Ya kamata gidajen talbijin su dinga tace finafinan da suke nuna wa ta hanyar cire duk wani abu da zai nuna yin amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma tasirinsu, da kuma shirya wasannin kwaikwayo masu nuna illar shan kayan maye.

    Rediyo

    Zai yi kyau su ma gidajen rediyoyi su dinga sanya ido a kan waƙoƙi da kaɗe-kaɗen da suke sanyawa, musamman na waɗanda aka san sun shahara a fagen shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ko kuma masu nuna a sha kayan maye, don sanya ire-iren waɗannan waƙoƙi suna zama wata barazana ga tarbiyyar da rayuwar matasa. Kuma su dinga shirya wasannin kwaikwayo masu nuna illar shan kayan maye.

    Yanar gizo

    Ya kamata gwamnati ta sa ido, kuma ta kafa wata hukuma da za ta dinga kula da kafafen sadarwa na yanar Gizo, duk waɗanda aka samu suna yaɗa harkar shaye-shaye, to a toshe su a daina samun su a Nijeriya.

    Masu Shirya Finafinai

    25 Masu shirya finafinai suna da abubuwan da za su yi a cikin finafinansu masu taimakawa wajen koyar da tarbiyyar matasa ta hanyar sanya wasu abubuwa waɗanda za su yi yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi. Tunda matasan nan, musamma mata suna kallon waɗannan finafinan sosai.

    44.Marubuta za su zama a sahun gaba wajen kawo gyara a cikin al’umma ta fuskar rubuce-rubucensu da sanya illoli dan matsaloli da haɗuran da ke cikin shaye-shayen ƙwayoyi masu sa maye.

    Sauran Jama’ar Gari

    45.Kowane mutum mai hankali da sanin ya kamata zai ƙyamaci wannan mummunar hanya ta shaye-shaye: Don haka sauran jama’ar gari su ma suna da tasu rawa da za su taka ta ƙoƙarin hana wannan sabgar, ta hanyar yin nasiha ko faɗakarwa ga duk wanda suka lura yana son jefa kansa cikin wannan hanya.

    46.Ya zama wajibi ga sauran jama’ar gari su ba da tasu gudummawa wajen yaƙi da wannan annoba da ta shigo cikin jama’armu, wato shaye-shayen kayan maye, ta hanyar kafa ƙungiyoyin da za su dinga nusar da matasa su guji wannan abubuwa, sannan kuma su dinga sanar da hukumomi don a dinga kama masu sayar da waɗannan kaya masu sa maye, tun da dama daga cikin masu sayarwar an san su, ‘yan unguwa ne, dole ne a kawar da sani ko sabo don a magance wannan matsala. In ba haka ba kuwa, in an ƙi sharar masallaci za a yi ta rumfar kasuwa. Sannan su kafa ƙungiyoyin tsaro da sa ido a unguwanninsu.

    Mawaƙa

    47.Mawaƙa ma suna da muhimmiyar rawa da za su taka wajen wannan fafutuka ta yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tun da waƙoƙi suna da matuƙar tasiri ga rayuwar al’umma, musamman ma matasa, tun da suna sauraron waƙoƙin sosai, kuma suna tasiri sosai ga rayuwar su matasan.

    Idan muka ɗauki misalin wata waƙa da Ahmad Tijjani Gandu ya yi mai taken ‘Yar Maye, ta yi matuƙar tasiri ga matasa musamman mata yan shaye-shaye, tun da ta sanadiyyar sauraron wannan waƙa wasu sun bar shaye- shayen har abada. A duba rataye na 1 za a ga kaɗan daga cikin abin da wasu baitukan waƙar suke cewa.

    Har ila yau akwai wani shahararren mawakin Hausa, marigayi Malam Abdullahi Sani Makarantar Lungu ya taɓa yin wata waƙa ta hani da wannan harka ta shaye-shayen ƙwayoyi masu sa maye, tun ma lamarin bai ɓaci haka ba, domin wannan waƙa an fi shekara goma da yin ta amma ta yi daidai da wannan lokaci da muke ciki. A duba rataye na 2 za a ga baitukan waƙar da kuma abubuwan da ta ƙunsa.

    Shi ma shahararren makaɗin kuntigin Alhaji Dr. Danmaraya Jos ya yi waƙa game da hani a kan shan ƙwaya, in an duba a rataye na 3 za a ga abubuwan da ya bayyana.

    Fatanmu dai Allah ya tsare mu daga waɗannan munanan ayyuka, ya shiryi zuriyarmu baki ɗaya, amin.

    Wassalamun ala manittaba’al huda..

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Don karanta Wasu Alamomin Da Ake Iya Gane Mai Shan Kayan Maye danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Wasu Alamomin Da Ake Iya Gane Mai Shan Kayan Maye

    Wasu Alamomin Da Ake Iya Gane Mai Shan Kayan Maye

    Akwai wasu alamomi da ake iya gane masu shan ƙwayoyi. Wasu daga cikinsu sun haɗa da:

    • Yawan tara kwalaben maganin mura da tari ko sirinji
    • Allura ko kuma yankakkun takardu
    • Yawan kunna turaren (ƙamshi) wuta a cikin ɗakin matasa
    • Ƙin shiga cikin mutane, musamman a gida
    • Yawan ƙamshin turare iri daban-daban don kawar da warin da yake tare da su
    • Rashin ƙoƙari a makaranta (amma wata sa’a kuma an ce wai ƙoƙari suke sa wa)
    • Yawan ladabi da gaishe da mutane (wanda ba a saba gani a da ba, ko kuma ana yi amma lokaci ɗaya a ga abin ya ƙaru)
    • Lokaci ɗaya yarinya ta sauya ƙawaye, ba ta kuma damu da ƙawayenta na da ba, sannan yanayin harkokinta su sauya
    • Rashin dawowa gida da wuri da daddare (don shaye- shayen miyagun ƙwayoyin an fi yin su daga yamma zuwa dare)
    • Sauyin halaye da ɗabi’un yarinya waɗanda ba a saba da ganin ta tana yi ba
    • Yawan sa baƙin tabarau
    • Yawan son tafiya wajen biki, a je kuma a daɗe ba a dawo ba
    • Sauyawar yanayin bakin matashiya, a dinga ganin ta tana nuna wani launi daban a leɓe ko kan harshe
    • Sauyawar ƙwayar ido ta koma ja, idon yana iya ɗaukar fiye awa biyar bai koma daidai yadda yake kafin a sha ƙwayar ba, ko kuma idon ya dinga rawa, kamar ƙwalla ko kuma ana rufe shi ana buɗewa
    • Karkatar da kai ko kaɗa kai, musamman ga masu shan hodar Iblis (cocaine)
    • Lokacin da ake magana da matashi ko matashiya a ji suna sambatu marasa kan gado
    • Yawan yin tamɓele a maganganunsu
    • Zazzare idanuwa haka kawai, wanda suke kira ‘cin magani’
    • Yawan fushi ko ɗacin rai
    • Neman faɗa babu dalili
    • Yawan barci.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Matsalolin Da ‘Yan Maye Suke Cin Karo Da Su

    Edita@rumasau-kallamu

  • Matsalolin Da ‘Yan Maye Suke Cin Karo Da Su

    Matsalolin Da ‘Yan Maye Suke Cin Karo Da Su

    Akwai matsaloli masu yawa game da shan miyagun ƙwayoyi, kuma yana yin tasiri sosai a rayuwar mashayan musamman ta fannin lafiya.

    Masu shaye-shaye suna haɗuwa da waɗannan cututtuka masu alaƙa da illolin da waɗannan sinadarai sukan yi wa jiki in an sha ba tare da ƙa’ida ba sakamakon abubuwan da suke sha masu sa maye:

    • Matsanancin ciwon kai
    • Matsanancin ciwon ciki
    • Matsanancin ciwon ƙirji
    • Ciwon hanta
    • Ciwon ƙoda
    • Ciwon saifa
    • Ciwon huhu
    • Ciwon zuciya (kalbu)
    • Ciwon daji (cancer)
    • Ciwon hawan jini
    • Shafar jaririn da ke cikin mace mai ciki
    • Rashin gani
    • Rashin jin ɗanɗano a baki
    • Rashin cin abinci
    • Rashin natsuwa
    • Rashin tsafta
    • Yawan tunani
    • Yawan jin tsoro
    • Yawan kasala
    • Yawan ramewa
    • Tsotsewar jikin mutum
    • Saurin kamuwa da Tarin fuka (tuberculosis wato TB)
    • Taɓuwar ƙwaƙwalwa
    • Saurin kamuwa da “cutar Sida (AIDS), sakamakon munanan ɗabi̇’un da shaye-shaye kan haifar ta hanyar jima’i ko allura.

    Sannan kuma a cikin rayuwar masu shaye-shaye akwai waɗannan abubuwa da suke cin karo da su wato aikata mugayen laifuka waɗanda suka haɗa da:

    • Sata
    • Fashi da makami
    • Karuwanci
    • Kisan kai
    • Rataye kai
    • Damfara
    • Ha’inci
    • Ƙarya
    • Yawan faɗace-faɗace
    • Yawan mutuwar aure
    • Rashin kulawa da tarbiyyar yara
    • Rashin zuwa makaranta
    • Rasa aikin da ake yi
    • Rashin cika alƙawari
    • Rashin tsayar da ibada a kan lokaci
    • Zama alaƙaƙai a cikin al’umma
    • Zaman daba
    • Shiga ƙungiyoyin asiri.

    Duk matashiyar da ta zama ma’abociyar shaye-shayen kayan maye tana tattare da fuskantar matsalolin rayuwa da kuma zamantakewarta cikin jama’a, kuma za ta ci gaba da fuskantar waɗannan abubuwa matuƙar ba ta daina ba:

    Mace in tana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da wuya ta zama tana da abokai na ƙwarai. Matashiya mai shaye-shaye idan ta haifi ‘ya’ya da wuya ta ba su tarbiyya mai kyau. Kuma ire-iren waɗannan matasa in suka zama shugabannin al’umma mai zai faru ga waɗannan al’umma musamma wannan lokaci na mulkin damokaraɗiyya?

    Matashiya, mai shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ba a bari saurayi na kirki ya zo neman auren ta. Kamar yadda ya faru ga wata budurwa ‘yar shekara ashirin da biyu a duniya, wadda ta gama karatu ba tare da kyakkyawan sakamako ba.

    Ƙawayenta wasu duk sun ci gaba da karatu wasu sun yi aure, amma ita tana nan a gida kuma haɗuwa da mugayen abokai suka koya mata shaye-shaye, wani saurayi ya gan ta suka yi maganar aure har an buga katin gayyata aka zagaya aka kai wa saurayin labarin cewa wadda zai aura ‘yar maye ce, daga nan ya ce a ba shi kayansa ya fasa.

    Domin karanta Zaurancen ‘Yan Maye danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Lalurar Mele (Vitiligo) Take

    Yadda Lalurar Mele (Vitiligo) Take

    Yanayi ne da wani kaso cikin mutane kan samu kansu na kasancewar wani sashi na jikinsu ya bambanta da wani ta ɓangaren haske a fata. Kama daga tafin hannu, fuska, wuya, gefen kai, baya, kuiɓin ciki da dai sauransu.

    Wato dai ka ga mutum in baƙar fata ne amma ga wani sashi na hannuwansa ko fuskarsa ya zamo fari-fat, in kuma farar fata ne hakan ya sa fatar ta ƙara haske a inda abun ya fito, kai har gashin gurin yakan zamo fari shi ma.

    Kamar yadda kuka san muna da rukunin mutane ZABIYA wato ALBINO waɗanda fatarsu take fari fat gaba ɗaya, sannan ba sa iya jure zafin rana, gami da rashin gani sosai a tsakiyar rana ko hasken wani abu. A sakamakon ƙarancin sinadarin da ke ba fata launinta wato MELANIN.

    Toh su ma masu VITILIGO wannan MELANIN ɗin suka rasa a tsalmin inda farin ya bayyana. Kun ga kenan su ZABIYA duk fatar jikin ce suke da ƙarancin MELANIN, yayin da su kuma masu VITILIGO wani sashi ne na fatar babu.

    Shi yasa wasu sai ka ga ana ƙyamarsu a riƙa zaton ko wani ciwo ne na fata don kar mutum shi ma ya kwasa, ko kuma in ka gansu sai ka ɗauka irin ƙonewar nan suka yi gurin ya warke shi ne ya zamo haka. Eh ai ko ƙuna abinda yasa in ta warke in dai babba ce ake ganin gurin ya sauya kala shi ne dai rashin melanin ɗin.

    Don haka VITILIGO ba ciwo ne da ake iya ɗauka ba. Ku daina jin ƙyanƙyamin raɓar jikinsu. Yawanci ana alaƙanta shi da ƙwayoyin halittun gado (inheritance) da kuma tangarɗar ƙwayoyin garkuwar jiki (Auto immune) wanda a maimakon su yaƙi ƙwayoyin jiki sukan koma su yaƙi lafiyayyun ƙwayoyin da ke samar da melanin a jika wato MELANOCYTES. 

    Larurar ba ta da magani, kuma hakan bai jefa mutum cikin wani hatsari. Kurum in dai ka karɓi kanka yadda kake to shike nan.

    Domin karanta Ciwon Nono Ga ‘Yanmata Masu Ƙananan Shekaru danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

  • Ciwon Nono Ga ‘Yanmata Masu Ƙananan Shekaru

    Ciwon Nono Ga ‘Yanmata Masu Ƙananan Shekaru

    Ciwon nono ga ‘yanmata masu ƙananan shekaru yawanci ba ya nuna cewa suna da wata babbar matsala a nonon su. Yakan zamo yana da alaƙa ne da canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinsu (hormonal imbalances). Waɗannan sinadaran suna shafar balaga, jinin haila, ko girman nonon mace.

    Yawancin mata matasa suna jin zafin nono ko rashin jin daɗi a matsayin wani ɓangare na tsarin girman halittar jikinsu. Ana kiransa da ciwon nono na lokaci-lokaci (cyclical breast pain), kuma yawanci yana warkar da kansa bayan wani lokaci, ko kuma mace ta ji sauƙinsa bayan ta sami sauyin rayuwa idan ta yi aure.

    Amma, idan ciwon nonon ya zamo mai tsanani kuma bai daina ba na tsawon lokaci, ko ya haɗu da kumburi ko wasu canje-canje marasa kyau a nono, ko nono guda ɗaya  ya shafa na tsawon lokaci, ko ba yana faruwa ba ne a lokacin jinin al’ada, to, ya kamata ki je asibiti domin likita ya duba ki ido-da-ido.

    Sa’annan ya kamata ku san cewa ciwon nono a daidai lokacin mace tana budurwa  zai iya zamowa sakamakon abubuwa ne kamar haka:

    1. Sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinki (hormonal changes), kuma shi ne ake kira “cyclical mastalgia”. Wannan ba matsala ba ne In-sha-Allah.
    2. Buɗewar fatar ƙirjinki, da kuma haɓakar girman tsokar nononki (developmental  stretching of skin and tissues as the breasts grow).
    3. Tasirantuwar fata da tsokar nononki idan aka taɓa su (breast sensitivity), domin wasu matan ko an taɓa nononsu ba su jin komai, amma wasu ko yaya aka taɓa su, to, suna tasirantuwa sosai. Wannan yanayin halitta ne.
    4. Rashin samun halittar ƙasusuwan baya, ƙirji, da kafaɗu masu kyau (poor posture). Wannan yana nufin idan halittar ƙasusuwan ƙirjinku, da kafaɗunku, da bayanku sun sunkuya ba su tsaya a tsaye ƙyam ba, to hakan zai sanya tsokoki da fatar nononku su takure, daga nan sai nononku ya riƙa yi muku ciwo a kai-a kai, har zuwa bayanku. Idan haka halittar ƙasusuwan ƙirjinku suke, to, za ku iya samun sauƙin ciwon ne ta hanyar yawan yin atisayen banƙare ƙirjinki da bayanku (postural exercises), tare da zama ko kwanciya a wuraren da bayanku da kafaɗunku ba za su takura ba.
    1. Canje-canjen nono sakamakon ƙullutun nono (fibrocystic breast changes), wanda yake faruwa saboda kullum fibroadenoma.  Fibroadenoma shi ne ƙullutun nono wanda yake sanya tsayuwar nono ƙyam. Wani lokacin yakan kumbura ko ya dinga ruwa, ya haddasa jin zafin nono idan aka taɓa ko ba a taɓa ba.

    Don karanta Kumburin Mahaifa Mai Sanya Zubar Jini (ENDOMETRITIS) danna nan

    Edita@rumasau-kallamu